Showing 9001 words to 12000 words out of 26460 words

Chapter 4 - ZURFIN CIKI book 1 Complete by halima Abdullahi K Mashi .pdf

lbrn abinda ya faru.dariya ahmad yayi
tayi.yace kai amma wannan ummin taku yar dirama ce. abba yace cikin takaici yanxu kai har
kaga abin dariya?yaja tsaki yace allah na tsana ummi, namata muguwan tsana. dubi wannan
yarfin da tai mani. ahmad yace xata bari, wata ranama ko ance tayi watace sam batayi ba.abba
yace taf wannan yarinyan dawuya in xata taba yin hankali, duk wanda ya aureta ya auran ma
kanshi fitina.ahmad sai dry yakeyi. da magariba ya shiga gidan,cikin saa ya samu ummi tana cin
abinci.nan take ya kama hannun ta har saida tayi yar qara, yace muje ki dauko min kwalin kaset
din da kika dauka, Umma tace, Abba na soma tunanin yarinyar nan tan da aljanu da gaske.
abba yace hakama alhaji qarami yace, amma fa anje babu kowa akanta. ya saki ummi bayan ya
ranqwasheta. sannan ya ce, in kika sake yarda ki kaga wani abu a dakina kika dauka sai na
balla ki. washegari abba ya tasa ummi ya nufi gurin masu ruqiyya, amma da aka mata babu
kowa a kanta kamar yadda ya xata. ya dawo ya sanar da umma,umma tace na gode
allah.halinta ne ita kuma irinta kenan? yace irinta kenan umma,baxata canxaba saidai muyi ta
mata addua, soyayyan abba da bishira ta bunqara,har dangin abba sun san da batun,sahura
duk tabaxa ma dangi.sanadiyyan maganan da tayi ma bushiran na cewa an rabata da daxta.

wata rana bishiran tace masa xata xo gaida ummanshi,yace to cikin xumudi sai tace, umman su
bashir fa nake nufi, ba ance ita ce mamanka ba? abba ya ce inji wa? inji ummanka. abba yace
sam, ummana ba xata fada miki ba sai dai ko ita umman bashir din. tabbas itace ta haifeni,
amma ba itace ummana ba.tace dan me? nan take ya hada rai. Abba yace mata ba matsalanki
bane, so ban so ki saka kanki ciki. nan take ta yarda da batun umman bashir.ta a mince qwarai
umman da abba ke kira umman shine muguwa ce.kuma itace ta raba abba da umman shi.dan
haka saita tsiri xuwa gun umman bashir, tare da yi mata kyauta.shiyasa suka saba sosai.duk
xuwan da bishira xatayi sahura saita kukkushe umman abba, tare da yi mata sheri. dan kawai
bishira ta tsaneta,kuma bata xuwa gunta koda taxo anguwan. abba bai taba sanin haka ba,ita
kuma umma bata taba fadan mai ba, dan ummi ta taba fada mata cewan budurwan abba tana
xuwa gun umman bashir kuma bata xuwa gunki. umma tace nida umman bashir duk daya ne
intaxo gunta tamkan taxo guna ne. sai kuma habaicin da take jiyowa ta katanga sahura nayi.har
ya kai umman abba na ganewa in bishira taxo, domin inxata tafi xakaji umman bashir tana
cewa,to na gode yar albarka bakya gajiya da abin arxiki,ai ko baki kawo min komai ba yancina
da kika fara qwato min kin biya ni. kuma ina tabba tan maki inkinga abba bai aureki ba baya ry/
ZURFIN CIKI book 1 part 4
ZURFIN CIKI book 1 part 4
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:45
Wannan furucin ke sa bishira na qara shige ma
sahura, duk wannan sha'anin da sukeyi abba bai
sani ba. wanci tashi abba ya samu digree,
sannan yaje kamp din shi a damaturu jihar
yobe.sati biyu yayi sannan ya dawo. cikin sati
biyun nan da baya nan ummi ta baxa iya
shegenta son ran ta, umma ta qosa abba ya
dawo saboda yanxune ta gane tsoran abba yake
sa ummi tayi mata aiki da aike.dan tasan in ya
sani baruwan shi da pushin tsohuwa,xai
nakadetane, amma ahj da umma duk abinda
ummi tayi daxaran xasu hukunta ta xata sa masu
kuka tace dan de aci mata xarafine.shi yasa suka
sakama ummi sunanta,sannan kuma suke
dukanta a gabanta,imba hakaba maisa basuyima
mai sunnan malan ba?dan dole suke qyaleta ,duk
da ummi ta soma tasawa amma sam bata yi
hankali ba. shekarun ummi sha uku tana js2
amma ko yaushe qara tirewa ummi keyi. addua
kurun sukasa agaba,kuma sunsan allah xai amsa
masu. Ranan da abba xai dawo ummi ta kama
yima umma aiki da aike, dan kar a fadama abba.
a ranan ne ummi taga wata alama da ta
tsoratata cikin fitsarinta. a rudenta da hauka ta
nufi gun umma tana cewa, umma na shiga uku

na, fitsarin jini nake yi. umma tace, wane irin
kuma fitsarin jini? ummi sai tsalle take tana fadin
ta bani ta lalace. umma tace ke xonan. ta jawo
ta xuwa cikin daki, tace ke yimin bayanin yadda
kika ga abin. ummi ta cire xani xata cire siket.
umma tace, ke dakata min bance ki nuna min ba,
yaya kalanshi yace? ko da tayima umma bayani
sai ta fahince girmane ya kama ta. dan haka sai
ta kamo ta ta xaunar kusa da ita, tayi mata
bayani game da abin data gani, sannan ta nuna
mata hadarukan da take ciki a halin yanxu. tace
ummi ki natsu kiyi hankali, kisani yanxu kinkai
wani matsayi wanda xakiyi taka tsantsa da
rayuwanki. hadari na farko shine wasan banxa da
maxa, kece mara hankali indai kin sama abokin
wasa ba ruwanki da maxane ko mata ke dai kiyi
wasa, Umma tace kisani yanxu xaki iya daukan
ciki, indai har kika bari wani namiji ya shiga
harkanki. ummi tayi xullo tace umma ciki irin na
bara'atun baito? umma tace, eh ummi tace
wanda har suka yar da yaran aka xo aka kama
su yan sanda? umma tace tabbas. ummi cikin
fargaba tace to ni umma baxan yi ba. ta soma
kuka, to a kaini asibiti a bani magani mana.
umma tace duk bayanin dana maki baki fahinta
ba? ai wannan kin dunga yinsa kenan har
qarshan rayuwanki, ko kuma in kinkai wani
mataki na tsufa. ummi tace, to shi kenan, yanxu
kuma inna yi wasa da maxa sai in xama irin na
bara'atu? umma tace qwarai kuwa. ummi tayi
tagumi tana tuna yadda suke tsokanan bara'atu
inta fito. suna cewa tayi cikin shege tayi cikin
shege! ta dubi umma tace xan daina ma yan
maxa magana. umma tace ki dinga maganarki da
kowa, kidai kula da kanki, sannan duk sokanan da
kikayi da xunubin da ki ka kwasa to fa ki sani an
bude maki fayel. Umma tace xunubinki xaki
samu,gashi bakya san sallar kan lkc, sannan ga
karya axumi.ummi ta sake tsurewa ,tare da fadin,
to ba tsohuwa tace min inna mutu baxa ayi min
hisabi ba,wai ni yarinya ce wai makarantan
annabi ibrahim xa a kaini.umma tace da kenan
kafin ki soma kalar wannan fitsarin, yanxun kam

in kin mutn xa a tambaye ki a cikin kabari,
tambayoyi uku masu sauqi, masu wuya agun
mara rabo.sannan xa a maki hisabi inkinyi mai
kyau kiga mai kyau. tayi tagumi, umma ta manna
mata tsumma a jikin pant. tace tashi kisa in
kuma kinje gun haukan guje guje ya fado mutane
sun gani shi kenan asirin ki ya tonu, kowa yasan
kin girma. ummi dai ranan lafewa tayi kan kujera
tanata tunani. tana kwance lkcn da ake hayaniyan
dawowan abba kannanshi ne suka shigo mai da
kayansa. qasa ya xauna a dakin umma, ya miqe
qafa domin duk a gajiye yake. umma tayi ta dire
mai abubuwan ci wanda tasan yanaso a gaban
shi. sannan ta ba fati kudi ta sayo mai lemun
kwalba, dariya yayi ya ce,ni dan gatane, shiyasa
ina can ina tunaninki ummana, har nace inama
ana tafiya da uwa da na tafi da ke.umma cikin jin
dadi tace allah sarki abba, niko ina nan ina maka
addua allaih ya baka abin da kaje nema,yace
ummana kenan. ummi dai tana jinsu sam baima
gantaba, sai can ya lura yace a,a kekuma lfy?
umma tace bata dan jin dadine. yace tabdi,lallai
kuwa ciwan nan yayi tsanani, ummi da ko a
gadan asibiti take bata daina halinta? umma tace
ai yanxuma nasan lafawa yayi ko ummi na?
ummi dai kallansu take yi. abba yace allah ya
yaye. suka ci gaba da firan su yana bata lbrn
camp tare da nuna mata hotunan da suka dauka.
yace dan ba kusa bane da kunje min kunyi kallo.
ummi da xata bayi sai tafiya take wani iri tare da
ware qafa. saboda rashin sabo. tsohuwa tace a,a
takwara lfy? ummi tace, fitsarin jinin nake yi.
umma ta fito da sauri tace ke ummi xo. tsohuwa
ta saka salati, tare da cewa yarinnan nan badai
faduwa kikayi ba. ummi tace nifa ban fadi ba
hakanan ya xo min. umma tayi mata daquwa
tace bayin kenan? tsohuwa tace ke suwaiba
yarinyan nan faduwa tayi? da yake umma ta
fahinci hausanta sai tace um,lkcn tane yaxo.
tsohuwa ta saka salati tace, ni habiba yau naga
abinda ya isheni? yarinyan yar shekaru nawane
kwata kwata. lalle xamani, to sai ayi axaman
aurad da ita. umma tace waxai kula ummi da

sunan aure ni suwaiba? ki kalla haukan data keyi
a gari. abba cikin daki yace umma wa tsohuwa
take cema ayima aure? umma tace ummi itama
cikin dariya. yace tabdi jam to wannan takwaran
taki waxai kwasa, ga muni ga rashin hankali.daga
bayi ummi tanata murguda mai baki tana cewa
eh din. Tsohuwa kuwa masifa ta hau yi,"gaka nan
mara mutunci a gabana kake zagin takwara?kai
mai sunan malam ka kiyaye ni" shi dai ya fita ya
nufi dakinsa don kintsawa,yana mamakin ummi
ta zama babba. Koda umma bata fada mishi ba
ya gane haka ne ta yadda tsohuwa tayi maganar.
tsohuwa ta dubi umma ta ce,"ki na daure ma mai
sunan malam gindi yana ci ma takwara kashi a
hannu,alhalin yana zaune a inuwarta.nan fa gidan
ubanta ne." umma ta bata rai matuka,ta ce
"tsohuwa ni da Abba da ummi duk daya suke a
gurina,don Allah kada ki kuma furta haka har
Abba yaji. kai ni da za a ce in zaba tsakanin
ummi da Abba,na rantse Abba zan dauka."bata
jira abinda tsohuwa zata ce ba,tayi ciki abinta.
tsohuwa ta gama yan mitocinta ta shiga daki.
Kwana biu kamar gaske,ummi an nutsu, amma
abinda ya takura mata na daukewa sai umminku
ta ci gaba da gashi, sai ma abinda ya karu. Abba
ya daga ido sama yana kallon wasu tsuntsaye
suna ta shawagi a sama, zuciyar shi tana cikin
matukar damuwa sakamakon sheshshekan kukan
da bishira keyi, bata san cewa ya fita damuwa da
tafiyarshi kaduna ba? in ma da don ta ita ne da
sauki tunda gidansu da waya zai iya zuwa
(telephone) na bakin titi ya kirata. damuwar shi
umman shi. ta katse shi "yanxu Abba haka zan
daina ganinka?" ya sake tausasa murya."haba
bishira, ina kano ina garin kaduna?" ta ce, "tabdi,
nifa dalilin kukana taron matan kaduna nake ji, an
ce kwarjini garesu. kawai kaje ka sa samu wata
ka manta da batuna." Yayi murmushi "bishira
kenan, kada ki dauka son da nake miki mai rauni
ne da har zan canza wata dake, ni dai ki min
addu'a." ta ce,"sam ban yarda da wannan zancen
ba, ni dai bari in kira antina mijinta zai iya
taimaka maka a barka kano." kafin ya ce komai

tayi ciki da gudu. yayi yar dariya. bishira tunda
ya ce kaduna aka tura shi duk ta damu. Anti ta
fito daga kicin, bishira ta ce, anti kizo inji Abba.
anti ta dubeta, "in zo?" bishira ta kama hannunta
"don Allah aunty taimako zaki mana, zo ki ji." 49-
suka xauna sannan abba ya gaidaa anti cikin
girmamawa.bishira ta dube shi ka fada
mata.abba yace me?tace anti kinga fa kaduna
aka tura shi,ni kuma wlh ba xan so yaje garin nan
ba.anty ta sa dariya.to yanxu so kike yaqi xuwa
ko so kike ya tafi dake? tace,ni so nake ki yima
abban nasir bayani,nasan ba xai rasa sanin wani
da ya sani ba.abba da anty suka sa dariya,yace
kamar yaya?tace yayi magana a barshi anan
suka sake tuntsira dariya.tayi fushi ta miqe fuuu
ta nufi cikin falon gidan.anty tace bishira tana
matuqan sanka,dan allah ka kula da ita.ya kalleta
ya sunkuyad dakai,yace nima anti ina santa,kuma
tuni nasa manya susan xancan,saboda in samu
natsuwa,amma tace tana jin tsoron
mamanta.anty tace eh to,dole taji tsoro dan ba
dole bane hjynmu ta yarda,amma shi babanmu
bashi da matsala.abba yace to ni dai xan tura a
kowane lkc,dan ahjna yayi min magana tun kafin
tafi ta camp. Din nan yake ta min zancan." Aunty
ta ce,"to in kun tashi fa ba gurinshi za'a tura
ba,gurin kaninshi ne dake jakara.amma kafin
hakan sai an nemi izinin Alhajinmu din." Abba ya
ce,"to ni ko wa zai shige min gaba gurin neman
izinin?"aunty ta ce,"Abban nasir zan sanar
dashi,insha Allahu har wannan din ma batun
(service)din naka zan mishi bayani." cikin murna
abba ya ce,"to na gode,Allah ya saka da
alkairi"anty ta ce,"ba komai" ta mike "bari in turo
ta don nasan tana can tana cika sai ka bata
baki." yayi yar dariya tare da cewa"to". ta zauna
tana kumbure-kumbureya ce"haba tawan har
yanxu baki huce ba?" ta sake kauda kai gefe,ya
ce"to shi kenan,yanzun dai na fasa barin
kaduna." ta dube shi da sauri,"ka fasa barin
kaduna fa ka ce?" yayi yar dariya"au na
manta.kece duk kin ruda ni,cewa zanyi na fasa
barin kano." ta share yar kwallarta,"to shikenan"

ya ce,"naji dadin kiran anty da ki ka yi.ina ganin
nan da yan kwanaki su Alhajinku zasu sanni,Allah
yasa ace an bani ke." Wayyo dadi,ta tuntsure da
dariya.abbana nawa,bana zaton cewa zaka kai ni
murna a ranar."ya mike zan tafi "ta ce tun
yanzun? to ka ce ina gaishe dasu umma." Ya
ce,"umma bata cin mike,kullum sai ta ci in gaishe
ki da kyau.amma ke kin ki zuwa gaida ta." ta
ce,"kasan fa ni bana iya sakewa da ita,nafi
sakewa gurin umman bashir." ya ce,"kunyarta ki
ke ji?" ta dan tabe baki tare da daga kafada kila.
ya ce,"ina mamakin yanda kika saba da umman
bashir,alhalin ummana tafi saukin kai." ta ce,"ga
wannan kanwar taka mara kunya." ya yi yar
dariya sabida tuno abind ummi ta musu. ya ce a
hankali,"zaki saba da halin ummi."ta dube
shi,"tun ranar dana soma ganin ummi din nan fa
ban taba jin cewa ina sonta ba." ranshi yadan
sosu,har ma ya gimtse fuska,amma baice kala
ba.lura tayi da canzawarsa.don haka sai ta ce"ka
min afuwa in na bata maka." nan ma bai amsata
ba.illa sai da safe. Tamkar Alhaji yasan yadda
abba suka yi da antin bishira,da safe Abba yaje
gaida shi ya ce,"babana zuwa yanzun ya kamata
a ce mun shiga maganarku da yarinyar nan."
Abba ya sunkuyar da kai tare da ce wa,"um,dama
gidan antinta da naje dazu munyi zancen,yanzun
dai su ce sai an nemi izinin shi baban nasu. ta
ce,mijinta zai masa magana,in yaso sai kuji ranar
da zaku je din." Alhaji ya ce,"to shikenan.Allah ya
kai mu.yanzu yaushe zaka tafi kaduna?" kafin
abba ya bashi amsa,ya ci gaba da cewa,ban so
ba sam da wannan yin nisan da zaka yi damu
Abba." Abba ya ce,"ina hasashen cewa za a barni
nan kano da yardar Allah,bisa ga taimakon mijin
yayar yarinyar da nake zuwa gurinta." Alhaji ya
ce,"to Allah ya yarda,sannan in an fada maka
lokacin da zamu gana da waliyyan nata sai ka
sanar dani." Abba ya ce,"to." Alhaji ya ce,"ina son
mu danyi bincike kan yarinyar amma mahaifinta
sannanne ne,anata yabonshi." Abba ya ce,"to."
Ranar juma'a da misalin karfe biyu da rabi Alhaji
ibrahim (wato abban nasir,mijin anty farida),ya

samu sirikinsa a gida. bayan sun gaisa ya
tambayi yan jikokinshi sai Alhaji ibrahim ya
ce,"suna lafiya.dama makasudin zuwan shi
ne,akwai wani yaro da ke zuwa gurin
bishira,yawancinan gidanmu suke zance. to
gaskiya na yaba da hankalin yaron,sannan ya
damu yana son ya turo iyayensa.to shi ne nace
bari in nemar musu izini tukun." mahaifin bishira
ya kalli surukinsa ya ce,"aisha ko bishira?" Abban
nasir ya ce,bishira ce." ya gyara zama. "bishira
ta gama sakandare ne?" Abban nasir ya ce,"ai
Alhaji ba yana nufin ayi auren yanzun bane,a san
dashi ne." Alhaji ya ce,"bana haka,ka sani sai dai
tayi abu daya,in karatun karatun,in auren to
auran. Ibrahim kasan wani abu daya? duk lokacin
da kasa yarinya ta soma tsayawa da saurayi
bayan tana karatu,musammanirin bishira irin
wadda tasan tsarina amma ta danne ta turo min
saurayi to gara ayi mata auren. Domin doguwan
soyaryannan bata da ma'ana,qarshe sai wata
shedana ta biyo baya,balantana bishira tana da
rawan kai.ya matsa kusa da wayan tangaraho
wadda aka jona ta ke amfani a daukacin gidan,ya
dannan nanbobin sannan ya kira hjy.ta amsa
daga sashanta,yace bishira na ciki? tace tananan,
yace ki turo mani ita,tace to.gaban bishira ya
badi,ganin mijin yarta a gidan dan tasan abinda
ya kawo shi.ta xauna can gefe tace,gani dady,ta
gaisa da abban nasir.mahaifinta yace nasan
kinsan dalilin xuwan ibrahim ko? kanta a qasa
tace,a'a. yace.yace to saurayin da ce xuwa gunki
ne yake san ya turo magabatansa,kuma nasan
kinsan da batun?sai dai inasan kisan abu daya
bana san doguwan soyayya,da xara nagama
buncike akan yaran wanda shari'a tace.inna
gamsu,to fa aurad dake xanyi kije can ki qarasa
karatun in kina so.ahj ibrahin yace yaran yace shi
ba dole sai anyi yanxu ba.nufin shi a amince
mashi.shi kuma xai jira har ta gama
makarantanta. ahj ya katseshi ta hanyan daga
mai hannu,ibrahin kaidai sheda ne bewan bana
haka, kuma ba a haka dani ko?yace auran yata fa
kakeyi,ka san tsarina.ibrahinyace na sani ahj.

yace yauwa,ina nan ban canxa ba.yace yanxu
abinda nake san ka dashi kafin na amince da
xuwan iyayan shi.ya dubu bishira yace kinasan
shi kin amince dashi? tace eh yace tashi ki tafi
angama.kai kuma inasan kashiga unguwa uku ka
binci komin labarin yaran da usilin shi.ahj ibrahin
yace angama.yace naso ace sai ta gana
karatu,dan sai anyi sa'a xata qarasa,anma hakan
xaifimin akan doguwan soyayya kafin inxo inajin
haushi.ibrahin ya miqe to ni xan tafi.ahj shima ya
yunqura xai tashi sai waya ta kama ruri dan haka
sukayi sallama anan. ummi ta shiga gida daga
makaranta take,akuyan umman bashir tagani ta
gani a gidansu tana masu barna a kicin da sauri
ta koma ta saka sakatan gidan,sannan ta
dawo.ta kama akuyan ta kaita bakin fanfo ta tara
kanta sai kuka akuyan take tayi. Umman bashir
ta jiyo daga gidanta,da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login