Showing 1 words to 3000 words out of 29422 words
Chapter 1 - JARUMA YAZILA Book by Abdulaziz Sani Madakin Gini .pdf
***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE A
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya fara da cewa:
====================================
A WANI ZAMANI can baya mai tsawo da ya shude a kasar kisra an yi wani karamin kauye mai
suna himsarul aswad ya wanzu a yammacin birnin kisra kuma shi ne gari na karshe wanda yayi
iyaka da birnin rum. mutanen birnin himsarul aswad manoma ne wadanda suka sami albarkacin
kasa domin agaba daya garuruwan dake kar kashin birnin kisra babu inda ake da arzikin noma
kamar himsarul aswad acikin wadannan kauye akwai wani mutum da ake kira hukairu wanda
asalinsa dan uwan hakimin garinne amma saboda bambancin ra'ayi da halayyarsu sai hukairu
yahakura dazama tare dan uwansa hakimi yakoma daji inda yayi gidansa kusa da gonarsa yaci
gabada rayuwa a wajen tare da matarsa guda daya jal wacce akekira humaira shidai hakimin
kauyen himsarul aswad wanda ake kira da suna barzuk yakasance azzalumi kuma make taci
mai danne hakkin talakawa kamar yadda sarkin kisra ya zamo na wannan lokaci dalilin dayasa
kenan ma yadade akan mulkin yana tayin abinda yakeso zanci gaba. Hukairu da barzuk sun
kasance hassan da usaini kuma suna matukar kama da junansu tamkar antsaga kara wani abin
mamaki shine matansuma yan'uwan junane kuma suma hassana da usainane. Sunan matar
barzuk nuzaira. Humaira da nuzaira sun shaku da juna ainun kuma har aka yimusu aure basu
rabuba tunda agidadaya suke zaune lokacan da hukairu da humaira zasuyi hijira subar cikin
kauyen himsarul aswad da kyar hukaira da nuzaira suka rabu domin kankame junayi suka fashe
da.matsanancin kuka A wannan lokaci shima Hukairu kuka yake koda yakama. Humaira yana
kokarin banbareta daga jikin yar uwarta nuzaira saita dubeshi alokacinda Fuskarta ta jike
sharkaf da hawaye tace "yakai mijina saboda me zaka rabani da yar uwata alhalin tunda aka
haifemu Bamu taba rabuwaba Nikam da dai ka rabamu gwara ka barnina zauna anan gidan
koda kuwa zan zama baiwar sune. ". Sa 'adda hukairu yaji wannan batu saiya dada kamuwa da
tausayin Humaira "yace yake matata ki sani cewa ba a sonraina zan raba ki da 'yar uwarkiba,
sai domin mugayen halayen mijinta Nassey ke magana Tabbas bazan iyaci gaba da kallon irin
rashin imani da yake yiwa talakawaba tunda banida IKon Hanashi. Ni a rayuwata bantaba marin
wani mutumba bare ma muyi kace nace amma shi dan uwannan nawa ba a kwana ba kwai sai
yasa ankewa wani hannu kokafa. Sannan yana kwacewa mutane dukiyarsu ko matansu ya
maishesu bayinsu. Kituna cewa ahalin yanzu kina da ciki tsawon wata hudu yaza ayina tafi
nabarki acikin wannan hali alhalin ina son nakula da lafiyarki da kaina kuma naga abin dazaki
haifa. " Sa adda Hukairu yazo nan azancensa sai hukaira ta kara fashe da matsanancin kuka da
kyar tayi shiru sannan tace yakai mijina kasani cewa itama 'yar uwata nuzaira a halin yanzu
tana. Dauke da juna biyu tsawon watanni hudu dai dai da nawa. Ita haihuwa abuce mai hadarin
gasKe. Zan iya rasa rayuwa yayin haihuwar itama zata iya zata iya rasa rayuwarta saboda haka
bana son rabuwa da 'yar uwata awannan lokaci, zan so naga ranar da zata haihu. Don haka ina
rokonka daka barni na zauna tare da ita har izuwa ranar haihuwarta" hmm soyayya kenan
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani
***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE B
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
====================================
NA ZAUNA TARE DA ITA HAR IZUWA RANAR HAIHUARTA. Har Hukairu ya budi zaice wani
abu sai nuzaira ta tari numfashinsa ta dubi humaira tace yake 'yar uwata kada ki guji mijinki
saboda ni domin shima ba shi da kowa face ke, idan babu ke akusa dashi zai iya shiga mugun
hali. Ina son ki bishi kutafi tare, kada kidamu dani nayi miki alkawarin komai rintsi bazan haihu
ba sai agabanki." Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube humaira takara kamkame nuzaira
tafashe da kuka. Haka dai ta hakura sukayi bankwana suka rabu. Tun da hukairu da humaira
suka koma daji basu kara ganin mutum ba daga cikin Himsarul Aswad saboda sunyi nesa da
garin kimanin tafiyar sa'a bakwai,saidai suna ganin tafiyar fatake. Wani iko na allah yanzu
Hukairu da Humaira sunsami tsawon Nassey ke magana wata hudu A wannan daji inda shi
dakansa yagina musu wani narkeken gida. Harda garken dabbobinsu dasuke kiwo da rumbu na
ajiye kayan amfanin gona amma ko sau daya 'yamfashi. Ko 'yan sumame basu taba kawo musu
hari ba. Dalili kuwa shine akwai layar sihiri da wani boka yabashi. Wadda ya binneta a tsakiyar
gidansa. Duk wani mugu idan yazo gidan bazai ganshiba koda da ranane tsaka. A ranar da
cikin Humaira yacika wata takwas ne laulayi yayi mata yawa har ya zamana takasa yin komai.
Ka wai saita zauna. A tsakar gidan tana kallon hukairu alokacin da yake baiwa dabbobi acikin
garkensu. Koda ta dan jima tana kallonsu sai idanunta suka ciko da kwalla, Hawaye ya fara
zuba. Yayin da Hukairu juyo yaga halin da take ciki sai hankalinsa ya dugunzuma yabar garken
da sauri yazo gareta ya tsuguna ya rike hannunta yace matata ina dalilin kukannan naki shin
jikin kine yake ciwo. Kokuwa ninayi miki badaidaiba ?"Lokacinda humaira taji wannan tambayar
sai ta gyada kai tace Ba wani abu bane yasa kaga ina zubar da hawaye ba face tunanin cewa
abune mawuyaci na sake ganin ranar dani kaina zanyi I rin wannan aiki dakakeyi yanzu domin
ina ji ajikina abune mawuyaci na rayu daga hadarin wannan ciki danake dauke dashi." Kodajin
haka sai Hukairu yayi murmushi yace. Ki daina wannan tunanin naki kisani dawo wata nan bisa
umarnin boka nane domin ya tabbatar min dacewa idan kika haihu acikin gari zamu rasa abinda
zaki haifa kuma zamurasa duk abinda muka mallaka. Saboda a shekarar daki haihune za ayi
mugun fari da cututtuka acikin garin amma mu damuke anan wannan annoba bazata
shafemuba. Koda jin haka sai Humaira tayi murmushi cikin karfin hali tace "idan zancenka ya
tabbata Nassey ke magana haka ina fatan "yar uwata nuzaira tazo ta haihu tare dani domin
kada annobar ta shafi abinda zata haifa." Hukairu yayi ajiyar zuciya yace "nima ina fatan haKan
tafaru duk da cewa nasan halin "yar uwarki macece maicika alkawari. Lailai zata zonan ta haihu
tare dake cikin kowane hali. Daga wannan rana hukairu yaci gaba da kulada humaira har cikinta
ya tsufa sosai harma ranar da nakudarta tazo. A wannan ranane hankalin hukairu ya
dugunzuma ainun domin basu da makota bare yasamo mace wadda zata karbi aikin ungozoma.
Amma dayake dama can Yasami cikakken bayani a wajen wata tsohuwar mace tunkafin subaro
cikin gari sai yayi sauri ya shigar da Humaira cikin daki ya kwantar da ita akan shimfida ya shiga
taimakamata. A wannan lokacine hadari yagangamo aka fara walkiya da tsawa kafin ajima
ruwan sama ya kece kamar da bakin kwarya kuma asannane humaira tafara kwalla ihu
sakamakon nakudar data zomata. Duk da cewa Humaira nacikin tsananin shan wahala duk
sanda ta kwala ihu tayi shiru saita kuma kirawo sunan "yar uwarta nuzaira. Al'amarin dayayi
matukar dugunzuma hankalin Hukairu kenan domin yana tsoron cewa idan nuzaira bata zoba
har bayan haihuwar Humaira zata iya shiga cikin wani mugun halin dazata zamo sanadin
salwantar Hankalinta ko rayuwarta.Kwatsam ba zato ba tsammanisai hukairu yajiyo sukuwar
doki a wajen gidansa kuma adai dai lokacinne kan jaririn yafito daga jikin humaira. Namfa
Hukairu yarude yarasa abinda zaiyi shin zai rabu da humairane. Ya ruga waje yagano ko nu
zairace tazo. Kokuwa zai tsayane har sai yaga humaira ta haihu lafiya. Yana cikin wasu wasinne
yaji humaira ta damki hannunsa da kyar, tace ya kai mijina maza ka ruga izuwa.kofar gida
domin ina ji ajikina 'yar uwata ce ta iso kuma na tabbata kodai ta haihu kukuma tana cikin i rin
halin da nake ciki. Karka damu dani zan iya kara sa haihu wa da kaina. Cikin matukar damuwa
hukairu yace menene tabbacin hakan? Humaira tace shinna taba maka karyane? Hukairu ya
girgi za kai yace baki tababa kuma ina gasgata maganarki kamar yadda nake gasgaga
maganar ma haifiyata marigayiya. " Koda gama maganar sai ya mike da sauri yaruga da gudu
yana fita ya arba da keken doki. Kwance acikin keken dokin nuzairace kaca-kaca da jinin
haihuwa gefe kuma ga jaririn data haifa ko motsi bayayi. Itama a kwai a lamun dogon suma tayi
cikin razani hukairu ya ruga gareka ya dauki jaririn ya girgiza shi kuma ya kara shi
akunnuwansa yaji ko numfashi bayayi. Sai tausayi yakamashi. Adai dai wannan lokacinne kuma
yajiyo kukan jarirai acan dakin da ya baro humaira nantake nuzaira tabude idanunta tayi arba
da gawar jaririnta data haifa kuma taga hukairu tsaye akanta. Saita fashe da kukan bakin ciki
amma da ta jiyo kukan jariri adakin humaira. Sai ta fashe da dariya cikin hanzari subiyun suka
ruga izuwa cikin gidan. Da shigarsu cikin dakin da humaira take kwance saisukayi arba 'yan
tagwayen jariranta mata. Guda biyu suna ta tsala kuka.kuma ita humaira ta kasance cikin
Koshin lafiya. Fuskarta cike da murmushi. Koda humaira taga nuzaira babu juna biyu kuma
babu komai ahannunta Nassey ke magana sai ta yunkura donta mike tsaye. Nuzaira ta ruga
gareta da cikin hanzari ta kwanta tace "kwanta ki huta tukunna yake yar uwata kiyi sani cewa
kin zubarda jini mai yawa ajikinki. Kafin nuzaira ta rufe bakinta humaira ta tari numfashinta tace
ina abinda kika haifa nuzaira ta kalli hukairu takasa cewa komai sai humaira tayi murmushi tace
"yake 'yar uwata ai baki da damuwa tunda 'ya'ya biyu na haifa saiki dauki daya ki barmin daya. "
Koda jin wannan batu sai nuzaira ta cika da tsananin mamaki ta dubi hukairu shima sai yayi
murmushi yace "yar uwarki tayi gaskiya domin abinda ta haifa nakine koda kuwa guda dayane
zan iya amincewa ta mallaka mikishi domin zakiyimishi komai kamar yadda zata yi mishi da
kanta. Nuzaira tayi murmushi ta dauki daya Jaririyar ta zauna ta shayar da ita. Bayan
dukkaninsu sun nutsu sai hukairu ya dubi nuzaira cikin tsananin damuwa yace yaya akai kika
baro mijinki kika tahonan ba tare da yasaniba shinkin tabbatar baisa abiyo bayan kiba? Nuzaira
ta gyada kai tace aidama tun kafi ranar tazo nayi kyakykyawan shiri domin na hada baki da
kuyangina tuni sun tanadi wancen keken dokin danazo dashi. Acan bayan gari kuma acikin dare
muka saci jiki muka sulale muka bargarin banyarda wani daga cikin masu tsaro yagammuba
kuma suna dorani akan keken dokin na umarcesu dasu share sahun keken dokin don kada aga
alamar komai kafinna baro gida kuwa nabarwa mijina wasikar cewa nibazan haihuba acikin
garinsa acikin irin wannan lokaci nafari da annoba tun satin jiya gari ya hargitse da wadannan
matsaloli. Saboda haka ninasan cewa mijina bazai biyo sawunaba idan yaga wannan wasika.
Nikam na zabi na karasa. Sauran rayuwata tare da ku anan har izuwa karshen rayuwata
Nassey ke magana. Sa'adda nuzaira tazo nan azancenta sai hukairu ya jawo gwauran numfashi
ya ajiye sannan yace yake Nuzara kiyi sani nasan halin mijinki fiye da kowa a duniya. Tabbas
sai yabiyo bayanki dan haka zamanki anan abune mai hadarin gaske. Aduniya babu abinda
mijinki yakeso sama da samun magaji. Hankalinsa bazai taba kwanciya ba idan baiga abinda
kika haifaba idan yazo nan ya iske cewa abin dakika haifa ya mutu. Zai iya hallakamu nida
matata da dukkan abida muka haifa. Yazama dole ki dauki wannan jaririya guda daya ki tafi da
ita kikoma wajen mijinki. Nayi imani cewa a halin yanzu ya baro gari yataho nemanki. Idan baki
tashi kin tafi yanzu ba kin tareshi a hanya. Tabbas zai zo har nan ya riskemu abinda nake gudu
ya faru sai ya faru.
====================================
Anan zamu dakata
Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani
***★JARUMA YAZILA★***
Littafi Na Daya {1}
TYPE C
***Nasiru**Muhammad**Tijjani***
Marubucin ya cigaba da cewa:
===================================
TABBAS ZAI ZO HAR NAN YA RISKEMU ABINDA NAKE GUDU YA FARU SAI YA FARU.
Kodajin wannan batu sai nuzaira ta fashe da kukan bakin ciki saboda jin cewa zata sake
rabuwa da yar uwarta. Cikin tsananin damuwa Humaira ta dubi hukairu tace yakai mijina shin
gidan nan na dauke da sihirin mugu bai isa yagan shiba? To ai koda dan uwanka Barzuk yazo
nan bazai ga gidan ba kenan. Hukairu ya gyada kai yace ai shima yanada da irin wannan sihirin
nawa kuma yana da makarinsa domin tunmuna yara boka saibur yabamu shi sa'adda mai
haifimmu yakaimu gurinsa. Nuzaira bamu da ishashshan lokaci dan haka dole ne ki tashi kiyi
shirin gaggawa ki koma cikin gari. " Koda jin sai Nuzaira da Humaira suka fashe da kukan bakin
ciki kamar bazasu dainaba nan dai hukairu da humaira suka raka nuzaira wajen keken dokinta
suka bata abinci da kayan marmari. Nuzaira ta goya jaririyar da akabata ta rungume humaira
suka sake fashewa da kukan bakinciki suka kamkame juna. Da kyar suka rabu har nuzaira ta sa
kafarta guda cikin keken dokin saita waigo ta dubi hukairu tace. "Yakai mijin 'yar uwata shin
baka tsammanin wannan farin da annoba bazai shafi wannan jaririyar da kuka baniba". Hukairu
yayi murmushi yace karki damu ba abinda zaisameta kuma ina tabbatar miki nan da kwanaki
kadan wannan fari da annuba zasu kau. " Nuzaira tace wana suna zan sawa ya rinyar?" Caraf
humaira tace "kisamata suna YAZILA mukuma zamu sawa tamu suna DABIRA. " Nantake
nuzaira ta shiga cikin keken dokinta ta kada linzamin da wakanta tayi gaba. A can birnin
Himsarul Aswad kuwa lokacin.Hadari ya gangamo a ka fara walkiya da tsa warnan sai Barzuk
yatafi dakin nuzaira domin ya ga halin da take ciki saboda sanin lokacin haihuwarta yayi a ko
yaushe zata iya haihuwa. Da shigar Barzuk cikin haraba bangaren nuzaira saiyaga abin
mamaki. Bakomai yaganiba face dukkanin kuyan ginta akwakw kwance suna ta sharar barci al
halin lokacin baccinsu bayyiba. Sannan ya ji warin banju yacika gurin gaba daya. Cikin firgici
Barzuk ya toshe hancinsa ya ruga izuwa cikin dakin Nuzaira dazuwa yaga dakin wayam babu
Nuzaira babu alamarta. Cikin tsananin fushi ya fita daga dakin da sauri ya kwalawa Dakarunsa
kira nan da nan kwa dakarun suka rugo gare shi sai ya dubesu yace "maza kuje ku shirya hawa
za afita neman matata lallai anzo an saceta batare da bata lokaciba kuwa barzuk yayi
gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini. Daban tsoro ya hauwani farin ingarman doki ya
jagoranci dakaru dakaru dari biyu suka fice daga cikin birnin. Babban abinda yatayarwa dasu
barzuk hankali shine kokadan ba suga sawon da wakaiba bare su san hanyar daya kamata
subi. Koda ganin haka sai barzuk yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak, suma dakarun nasa sai
suka tsaya a bayansa. Nantake barzuk ya dauko madubin tSafinsa ya shafashi da hannunsa
take barzuk yagano hanyar da yakamata yabi amma bisa mamaki saiya kasa ganin hoton
komai acikin madubin tsafi face hanya kawai al'amarin daya matukar bashi mamaki kenan
domin asaninsa gaba daya kasar kisra in banda sarki Daksur babu wanda ya fishi karfin sihirin
tsafi wanda zai iya hada kafada da shi sai dai dan uwansa Hukairu. Hukairu kuwa ya dade
dayin hijira gabarin gari gaba daya to wane ha tsabibinne haka yazo har cikin garin sa ya sace
masa mata. Nan dai barzuk yakada linzamin dokinsa. Yayi gaba, dakaru suka bishi abaya duu
aguje sai da su barzuk suka shafe tafiyar wajen sa'a hudu sannan suka hango wani keken doki
yanufo garesu aguJe cikin mamaki su barzuk suka yi tur jiya kuma suka zare maka mansu suna
jiran isowar keken dokin. Tun daga nesa kadan barzuk ya shaida keken dokin yagane na
matarsa ne Nuzaira dan haka sai jikinsa yayi sanyi ya maida ta kofinsa cikin kube ya sauko da
gakan dokinsa ya ruga izuwa keken dokin. A gabansa keken dokin yayi turjiya yayi arba da
matarshi Nuzaira rike da linzamin dawakan fuskarta cike da annuri kuma tana dauke da goyan
jariri abayanta al'amarinda ya matukar bashi mamaki kenan. Cikin tsananin farin ciki ya kama
nuzaira ya sauketa dagakan keken dokin ya rungumeta sannan ya karbi jaririn dake baynta ya
kura mata ido yana dariyar farin ciki daga can kuma ya turbune fuskarsa ya dubi nuzaira yace
"bani labarinki yake matata wanene yazo ya saceki har cikin gidana, kuma ai na kika haifi
wannan tsaleliyar jaririya mai kama dani ainun haka?" Sa'adda Nuzaira taji wannan batu saitayi
murmushi tace "yakai mijina kayi sani bansan meya faruba ina cikin turakata sai naji anrufe mini
fuska an shaka mini banju ahanci. " Kawai sai farkawa nayi naganni a tsakiyar dokar daji kuma
babu kowa a kusa dani sai wasu mutane masu shigar bakaken kaya kuma duk sun rufe
fuskokinsu idanunsu kadai ake gani suna rike da muggan makamai. Adadin mutanen yakai
dubu. Babban cikinsu ne kawai da Jajayen tufafi bisa jan doki koda naga wadannan mutane sai
na firgita abin da jawo tasowar nakudata kenan cikin kankanin lokaci na haifi wannan jaririyar
dake hannunka acikin keken doki shugaban wa dannan mutanen ya matso kusa dani yakura
min ido sannan ya bushe dadariya. Yace yake matar babban abokin gabata kisani cewa kinyi
babbar sa'a da yazamana cewa kina dauke da juna biyu da tuni na hallakaki amma saboda
ganin kina dauke da juna biyu shiyasa muka fasa dalili kuwa aduniya bana tausayin kowa sai
mace mai juna biyu. Narasa matata ne alokacin da take nakudar haihuwar dana kuma tamutu
tabarmin dan, har yau har gobe ina tausayin dan saboda ba shi da uwa. Bisa wannan hujjane
zan kyaleki kikoma wajen mijinki wannan karan kan kun tsallake harina amma baza ku tsallake
na gababa. Koda gama fadin haka sai ya doki daya daaga cikin da wakan keken dokina take
suka zabura sukayi tatafiya dani har na hangoku akan hanya wannan shine iyakar abin da zan
iya tunawa ya faru gareni ya kai mijina.
Lokacin da nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk yacika da tsananin mamaki kuma yakamu da
matukar farin ciki yace tabbas babban makiyin mune sarki Raihan yaturo aka