Showing 3001 words to 6000 words out of 26600 words
Chapter 2 - WANKA DA GARI BOOK 1 COMPLETE by Fatima Sunusi Rabi'u .pdf
makarantarta a ƙaramar jakarta da kuɗaɗenta waɗanda
Abban Yusra ke bata kafin su fara samun wannan matsalar, ta sagala jakarta ta jawo a kwatinta
ta fito.
Har zuwa lokacin suna Parlour, suka kalleta ta kallesu gyara tsayuwa tayi ta kalli Hajiya da
Zaliha ta ce,
"Na gode da abinda ku kai mini ba zan ce komai ba domin nasan ni najawa kaina.'' Kallon
Abban Yusra tayi.
"Kai kuma tsakanin ni da kai wanda ya cutar da wani Allah ya saka ma shi."
Sannan taja akwatinta tana kuka tabar gidan, bata tsaya tambayar yaranta ba domin tasan
yadda Hajiya ke ƙaunarsu ba zata ba ta su ba.
Tana fita ta samu a daidaita sahu ta tsayar tahau bayan ta sanar da shi inda zai kaita, suna
zuwa ta biya shi kuɗinsa sannan taja akwatinta zuwa cikin gidansu wanda ginin ƙasa ne ɗan
madaidaici, irin na malam Shehu.
Da sallama ta shiga cikin gidan jiki a sanyaye, daga can cikin ƙuryar ɗaki taji ana amsa mata
sallama, wata mata ta fito wacce ba Ummanta ba ce, ta gaishe da matar tare da tambayarta,
"Umma ba ta nan ne?" Matar ta ce,
"Wacece Umma kuma?"
Sakinaa ji tayi kamar an buga mata guduma a ka, ta ƙarewa gidan kallo tabbas nan ne gidan
iyayenta gidan da tayi ƙuruciyarta a ciki ta dawo da kallonta ga matar.
"Ba nan ba ne gidan Malam Abdullahi Bakanike ba?"
"Gaskiya ba nan ba ne sai dai ban sani ba ko waɗanda suka tashi ne ki ke nufi, kuma
shekararmu uku a gidan nan mijina saya."
HAwaye ne ke bin fuskar Sakinaa ta ce, "Don Allah ko kin san inda suka koma?" Matar ta ce
"Wallahi ban sani ba." Cikin shassheƙa Sakinaa tayi wa matar godiya tare da fita jikinta na
ƙyarma, mummanan tsoro ya shigeta ga tsananin tashin hankaki.
Jan akwatinta tayi gaba tana tafe tana kuka, kai tsaye garejin da Abbanta ke aiki ta nufa bayan
sun gaggaisa da mutanan da ke wajen waɗanda ba ta san su ba take tambayar ɗaya daga ciki.
"Don Allah Malam Abdullahi nake nema." Wani mutumi ya ce, "Wane ne kuma haka?" Tayi
masu kwatancen kamaninsa yadda zasu gane, wani dattaju ya ce, "Ai ya daɗe da barin garejin
nan kusan shekaru uku kenan."
Nan take tashin hankalinta ya nunku har ya gaza ɓoyuwa a fuskarta. Ta fito garejin tana kuka
sosai bayan sun tabbatar mata ba su san inda ya koma ba.
Can nesa da garejin ta samu guri ta zauna bis a wani ɗan dandamali tana kuka, ina iyayenta
suka je? Meke faruwa da su a halin yanzu? ta sake sakin wani rikitaccen kuka nan take
rayuwarta ta baya ta fara dawo mata, tagumi tayi tana hawaye ta fara tariyo rayuwarta ta baya.
TUSHEN LABARIN
Malam Abdullahi talaka ne sosai sana'arsa Kanukanci wato gyaran moto babura har da kekuna.
Malam Abdullahi mutum ne me wadatar zuci duk da shi talaka ne bai hana ya wadata gidansa
da abinci da sutura ba domin gidansa ba anemi komai an rasa ba daidai gwargwado yana da
ƙoƙarin neman na kansa. Matarsa ɗaya Hadiza, asalinsu 'yan Bakori ne ƙaramar hukumar jahar Katsina, domin daga shi
har Hadizan 'yan can ne, ya je garin Kaduna ne domin neman kuɗi shida abokinsa Saminu, abu
kamar wasa har ya dawo da Hadiza nan, tun suna gidan haya har Allah ya buɗa masa ya fara
gini don mutum ne me ƙoƙarin neman na kai. Bayan ya kammala suka dawo garin gidansa, ɗakuna biyu ne a madaidaicin gidan ɗaya ciki da
falo sai ɗaya guda sai kuma kitchen da bayi na wanka dana bahaya a waje, ginin ƙasa ne
amma ya yi masa fulistar na suminti haka tsakar gidan shafe yake da suminti tas.
Sun daɗe ba su sami haihuwa ba, sai da suka shekara takwas da aure, aikuwa da Hadiza ta
samu ciki sun yi murna da farin ciki mara musaltuwa, nan aka dun ga renon ciki da tattalinsa har
ya isa haihuwa, ta haifi kyakkyawar ɗiyarta mace.
Sosai suka yi murna da farin ciki da samun ƙaruwar nan, inda ranar suna yarinya ta amsa
NANA Sakinaa. Yarinya kyakkyawa wanka tarwaɗa, anyi bidiri don 'yan Bakori sun zo a ka sha
bikin suna daga baya suka koma gida.
Sakinaa ta taso cikin so da ƙaunar iyayenta suna ji da ita sosai musamman Abbanta. Abba
akwai sanyi ko laifi tayi baya bugunta sai dai nasiha, garama Umma tasha bugunta idan tayi ba
daidai ba
Ummanta mace ce mai natsuwa da kamala ga son addini da son mutane, haka Abbanta kowa a
unguwarsu yana yabonsa ya samu shaida ta mutane kam.
Shekarar Sakinaa uku Abbanta ya sata boko da islamiyya don yarinya ce mai kazar-kazar ga
surutu, ai kuwa ana sata baki ya ƙara buɗewa gata da ƙoƙari sosai.
Abbanta ke kaita boko da safe biyu na rana ya ɗaukota, idan yaci abinci ya koma wajen aiki
daman da ya kai ta da safe yake wucewa aikin, idan yaci abinci ya koma huɗu na yamma yazo
ya kai ta islamiyya, ƙarfe shidda ya ɗaukota su dawo gida shi ma daga lokacin ya dawo aiki
kenan sai ya yi wanka ya fita masallaci sai anyi isha'i ya ke dawo wa daga nan kuma su zauna
baranda su ci abincin dare sai ya yi wa Sakinaa tatsuniya da haka har tayi bacci sannan su je
su kwanta. Haka rayuwarsu ta ke har zuwa lokacin da ta iya zuwa makaranta da kan ta.
Lokacin shekarunta goma, har abinci ita ke kai wa Abbanta gareji.
Ƙawarta wacce suka shaƙu sosai da ita itace Zaliha ɗiyar baƙotansu ce, kaf unguwarsu da ita
aka san ta, kullum tare suke zuwa makaranta boko da islamiyya ajinsu guda ne.
Shekarun Fatima sha biyu ne lokacin tana Jss one, ɗin ƙaramar Secondary ta dawo kai wa
Abbanta Abinci ne a gareji, tafiya take a hankali cikin natsuwa kamar wata babbar mace.
Shi kuwa yana cikin moto yana kallonta yanayinta ya burge shi, yasha haɗuwa da manyan mata
'yan ƙasar nan da wajenta amma bai ga yarinyar da ta burgesa ba irin wannan ƙaramar
yarinyar.
Bin ta yake a hankali cikin mota, ganin ta shiga wani lungu da mota bazata iya shiga ba, sai ya
fito ya din ga bin ta a baya, ganin za ta ɓace masa ya sa ya yi saurin ƙara takun sawunsa yana
kiran "Ƙanwata! Ƙanwata!!"
Ji tayi kamar daga sama ana kiran ƙanwata sai ba ta wai ga ba, domin a tunaninta ba ita ake
kira ba ganin bata da yaya ita ɗaya iyayenta suka haifa.
Jin ana ƙara kusanto ta ana kiran, "Ƙanwata ji mana ko baki son sabon Yaya?" Hakan ne yasa
ta tsaya chak tare da juyowa.
Wani kyakkyawan saurayi dogo taga ni yana zu ba mata murmushi, sanye yake cikin ƙananun
kaya Jeanse da t-shirt ya yi kyau sosai sumar kan nan nasa baƙ wuluk sai shinning take,
hannusa ɗauke da wani agwogwo daga gani zaka gane na gold ne saboda ƙyallin da yake,
kana ganin takalmin ƙafarsa zaka ga ne na manya ne domin daga yanayinsa ka san komi na shi
na musamman ne.
Ƙaraso wa Ya yi hannayensa zube cikin aljihu ya ce, "Ni suna na UMAR FARUUƘ."
A zuciyarta ta furta.
'Kuji mutum kamar na tambaye shi sunansa, amma fa sunan ga daɗi kuma suna manya ne,
hakan ma na musamman ne.'
"Ke mene ne sunanki?" Ya katse mata tunani da tambaya.
"Ni?" Ta tambaya tana nuna kanta, cike da ƙuruciya. Abin ya ba shi dariya ya ce, "Yes ke ni ba
kiji na faɗ miki nawa sunan ba?"
"Sakinaa!" Ta faɗa kai tsaye domin ita ba ta iya ƙarya ba.
"Wow nice name, suna me daɗi kuma babban suna." Murmushi kawai tayi.
"Ni zan wuce kar Ummana ta ji ni shuru." Bin bakinta ya yi da kallo yadda take magana cikin
natsuwa. Murmushi ya yi. "Ummanki ko dai Ummanmu? don haka wuce muje gidan tare."
Cike da mamaki take dubansa za tayi magana ya rigata, "Ko baki son inje incewa Umma tayi
sabon ɗa kuma yayan Princess?" Kallonsa tayi "Wace ce kuma Princess?" Cike da yarinta tayi
tambayar.
"Ke ce mana, sunanki yana da girma a wajena."
Rufe fuska tayi cike da kunya, murmushi ya yi "Mu je ko?"
A can gida kuwa Umma taji Sakinaa shuru, saɓa hijab tayi zata fito kenan sukaci karo da Abba
ya ce, "Lafiya ina zuwa kuma Hadiza?"
"Garejin daman za ni naji Sakinaa shuru."
"Shuru kumakina nufin bata dawo ba? Ai tuntuni ta tafo gida." Dukansu sai hankalinsu ya tashi
za su fita nemanta kenan sai ga su.
Kallon-kallo suka fara Umar ya ce, "Sannunku da gida." Ya duƙa har ƙasa ya gaishesu, suka
amsa cike da mamaki. Abba ya ce, "Lafiya dai ko yaro? Sam ban waye ka ba?"
Murmushi ya yi "Lafiya ƙalau kawai mun haɗu a hanya ne." Nan Sakinaa take sanar musu abin
da ya faru.
Abba ya ce, "A'a shugo daga ciki a shumfiɗa maka tafarma." Ya miƙe yabi bayansu, Umma ta
shimfiɗa musu tafarma a barandar gidan.
Umar ya ƙara gaishe da su Abba, suka amsa masa cikin sakin fuska. Ya ɗaura da cewa. "Suna
na Umar Alƙasim Inuwa mun haɗu da Sakinaa a hanya shi ne na tsayar da ita muka gaisa har
na biyota gida in gaisheku."
Abba ya ce, "Babu komai Ummaru da fatan dai lafiya, ba wani abin tayi maka ba? domin ba a
shaidar ɗan yau haihuwarsu ake ba a haifi halinsu ba."
"Babu komai Abba kawai dai haka nake jinta kamar Ƙanwata." Gaba ɗaya sukayi dariya. Abba
ya sake cewa, "Ai haka Allah ke ikonSa baka san mutum ba sai kaji ya kwanta maka, kamar
yarda nima kallo ɗaya na maka naji kashi ga raina daga ganinka gidan mutunci ka fito."
Umar ya yi murmushi "Na gode Abba ƙwarai nima jinku nake kamar iyayena."
Umar ya daɗe gidan sai da yaci tuwan daren Umma sannan ya bar gidan, yadda suke sai ka
ɗauka daman sun daɗe da sanin juna. Wanda wannan ne kuma silar faruwar ko wacce zanen
ƙaddara daga rayuwar Sakinaa..
**** **** ****
Da sallama ya shiga katafaran Parlourn gidan. Daddy ne ya miƙ da sauri ya ruƙo shi.
"Faruuƙ daga ina ka ke? Har ka iya kai wa irin wannan lokacin?"
Mummy ta ce, "Ka ta da mana hankali ko abinci mun kasaci Faruuƙ ina ka je?"
Murmushi ya yi.
"Dad an Mum me kuka mayar da ni ne?"
Da sauri Daddy furta "Ƙaramin yaro."
Mummy ta ce, "Jaririma zaka ce Daddyn Faruuƙ."
Ɓata fuska ya yi cike da shagwaɓa ya ce "Duk girman nan nawa amma kuke cewa haka ko
aure fa aka mini lafiya ƙalau zamu zauna da matata "
Mummy ta fara tafa hannu ya yin da Daddy ya riƙe baki.
"Faruuƙ aure! Karatun kuma fa?" Murmushi ya yi "To ai naji kuna ce mini ƙaramin yaro ne.
Dundu Mummy ta kai masa ta ce, "Kaci gidanku daga ina ka ke, sai fa ka faɗa mini ko dai taɗin
kaje don mu ga ne ka isa auren?"
Zama ya yi kusa da ita ya ce, "Daga gidansu Sakinaa nake." Nan ya sanar musu komai ya
ɗaura da cewa "Wallahi suna da ƙyirki sosai."
Mummy ta ce, "Faruuk ba dai saurin yarda ba, kar fa ka ɗauko mana abin da wataran zai saka
mu kuka."
"Haba Mummy don Allah ki yi mana fata na gari." Shafa kan sa tayi "Is ok my son tunda kana
son su muma dole mu so su.'' Daddy ya ce, "Wannan haka yake."
Washe gari ya dauki iyayensa sai gidansu Sakinaa, ƙwarai sun yi mamakin ganin gidan, ba su
taɓa tunanin talakawa ba ne, haka suka shiga sun ga karramawa gurin Abba da Umma, haka
ma Sakinaa
Kallo ɗaya Mummy tayi wa Sakinaa taji yarinyar ta shiga ranta shima Daddy haka.
Tun daga wannan rana zuminci mai ƙarfi ya kullu tsakanin iyalan gidan su Sakinaa da Umar kai
ka ɗauka daman 'yan uwa ne su tun usul....
08104335144
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattUku
#LabarinSakinaa
_Gawurtattu uku 2024_
WANKA DA GARI...
_Ummu Affan_
*Book 1 Page 5-6*
Zuwa yanzu su Sakinaa sun kammala ƙaramar Secondary ɗin su, wato JSCE har sun shiga
SS1. Ba laifi sun yi girma sun zama 'yan mata amma ba can ba, ba laifi Sakinaa kyakkyawa ce
wankan tarwaɗa. Tana da ɗan jiki kaɗan, doguwa amma ba tsowo sosai ba sai dai Allah ya
hore mata mazaunai sosai. Sannan tana da cikar ƙirji ga ƙoƙari a makaranta Allah ya ba ta
ƙyanwa mai saurin ɗaukar karatu, domin ita ke amsar na farko a ajinsu, iyayenta suna alfahari
da ita domin saboda natsuwarta da kamun kai da biyayyarta zuwa lokacin shaƙuwa mai
gauraye da wani babban al'amarin da ƙarancin shekarunta ya hanata ganowa shi ke wakana
tsakaninta da Hammanta Faruuƙ, shi tabbas yasan yana ƙaunar Sakinaa sai dai ita kawai ta
ɗauka shaƙuwa ce a tsakaninsu.
Suna hanyarsu ta dawo daga makaranta, tafiya suke irin ta 'yan makarantar da aka ta so su
ƙarfe biyun rana, ga yunwa sannan ga galabaita yadda rana ke dukansu.
Zaliha ta dubi Sakinaa ta ce, "Wai Sakinaa in tambaye ki mana, ya ku ke da Hamma Umar ne?"
Sakinaa ta taɓe baki.
"Yadda na sanar miki ko baki yarda ba ne?"
"A'a kawai na gan shi kyakkyawa kuma ɗan gayu a mota fa yake zuwa duk idan zai zo
gidanku."
"Ke dai baki gani ki kyale komai sai kinyi magana, kina ɗaya daga cikin sa'idinawa ana ruwa
kuna irgawa."
Dariya Zaliha tayi, "Na fiki ne? Na zata duk ɗaya muke tunda sai hali yazo guda ake ƙawance."
Sakinaa tayi murmushi.
"Uhmm ke dai Zaliha ba dai iya zance ba, ni nan wallahi na ƙosa mu kai gida duk na gaji yasin."
Zaliha ta ce, "Ke dai bari kawai ga shi ana rana yau sosai."
Haka suke tafe har suka kai gidajensu suka wa juna sallama.
Sakinaa na shiga ta iske Hamma Umar yazo, daman tun a waje ta ga motarsa, da murna ta
ƙarasa da sallama. "Oyoyo Hamma Umar." "Oyoyo Princess kin dawo?"
"Na dawo Hammana."
Gabaɗaya su ka yi murmushi.
Ɗakinta ta wuce ta cire Uniform taja ruwa ta watsa sannan tayi alwala, bayan ta idar da sallah ta
fito cikin wata doguwar riga ta shadda. Umma da Hamma Umar suna zaune suna hira ta
ƙaraso.
"Umma sannu da gida." Ta amsa da, "Yawwa." kitchen ta wuce don ɗauko abincinta, me zata ga
ni Fate ne, ɓata rai tayi don duk a cikin abinci fate ne ba ta so
Dawowa tayi tana ƙunƙunai da cin magani. Umma ta kalle ta. "Lafiya me ya faru?" Turo baki
tayi gaba. "Umma fate ne fa kika yi."
"I na sani ai, ni nayi ko?" Nan ta fara hawaye. "Amma Umma kina sa ne ban shan fate ko?"
Umma ta ce, "Hmmm shagaɓa wai tarwaɗa da kukan ƙishin ruwa, ni dai yau shi nake marmarin
sha haka ma Abbanki ga Hammaki ma nan yanzu ya gama sha yana santi." Da sauri ta ce,
"Faten?"
"Ƙwarai kuwa, shi Faten ba abinci ba ne?"
"Ni dai Umma ki ba ni abinda zan ci yunwa nake ji."
"Sai kuma kiyi ai, don ni ba ni da komai sai ki jira na dare."
Zubewa Sakinaa tayi tana riƙe ciki tana cewa, "Wayyo cikina yunwa nake ji Umma za ta kashe
ni, ta hana ni abinci . Abbana wayyo Abbana kazo.''
Mai Hamma Faruuƙ zai yi ba dariya ba, har da tafa hannu Umma miƙewa tayi,
"Sai kiyi ta yi, fate ne idan ba za kisha ba sai kiyi ta zama da yunwarki." Nan fa taci gaba da
kururuwa tana burgima.
Hamma Faruuƙ ya ce cikin dariya.
"Wai Princess mene ne hakan? Da girmanki ki ke haka?" Kallon shi tayi cikin hawaye ta ce,
"Hamma Faruuƙ Umma fa na sa ne ba na sha shi ne tayi."
"To yanzun ya ki ke so ayi?"
"Kawai ni dai yunwa nake ji, kuma bazan iya kai wa har sai na dare ba."
Miƙewa tayi bari inje gurin Abbana na san zai saya mini abu naci.
Shi ma miƙewa ya yi
"A'a kar ki wahalar da Abba muje na saya miki." Da sauri ta ruga ɗaki cikin murna ta ɗauko hijab
taje ta yi wa Umma sallama.
"Allah ya so ki yau Alhamis babu islamiyya da ba inda zaki je." Fita tayi kawai tana murna.
Buɗ mata motar ya yi ta shiga wani ƙamshin daɗi ya bugi hancinta sai da ta lumshe ido, shiga
ya yi ya mata key suka tafi, ƙira'ar malam Ahmad Sulaiman na tashi lumshe ido tayi cikin wani
sabon yanayi turaren Hamma Faruuƙ na mata daɗi sosai wanda B for B gidan ƙamshi ke haɗa
masa. (Turarenta ƙarshe ne domin wallahi ni Ummu Affan na gyada yana kama jiki sosai shi ne
turaren da Hamma Faruuƙ ke sakawa, mai buƙatarsa ya tambaye ni zan haɗa shi da B&B gidan
ƙamshi.)
Kai tsaye gidansu ya wuce da ita, daman tun a hanya ya kira Mum ya sanar mata suna hanya,
'yar ƙauye Sakinaa ta zama lokacin da suka shiga katafaran gidan su Hamma Faruuƙ,
kalle-kalle kawai take, ai hankalinta bai tashi ba sai da suka shiga Parloun gidan, gabanta ya
din ga bugawa a ranta ta aiyana ko dai Hamma Faruuƙ sayar da ita yake son yi? Nan fa
idanuwanta su kai rau-rau ta kalle shi.
"Hamma Faruuƙ don Allah kayi haƙuri kar ka sayar da ni ka ga ni ɗaya su Umma suka haifa
kayi mini rai don Allah."
Dariya ma taba shi kallonta ya yi.
"Ko da ina sayar da mutane Sakinaa bazan taɓa iya sayar da ke ba, ki sa a ranki komi wuya
Umar ba zai