Showing 6001 words to 9000 words out of 26600 words
Chapter 3 - WANKA DA GARI BOOK 1 COMPLETE by Fatima Sunusi Rabi'u .pdf
taɓa cutar da Sakinaa ba." Ajiyar zuciya tayi tana kallonsa, murmushi ya mata ita
ma ta mayar masa.
Sama ya wuce, sai gashi suna sakkowa da Mum, nan hankalin Sakinaa ya sake kwanciya ta
duƙa har ƙasa tana gaishe ta da sauri Mum ta ɗagota ta rungumeta.
"Kul Sakinaa ta so kin ji 'yata."
Cike da kunya Sakinaa ta gaisheta.
Mum ta ce, "Ya su Ummanki da Abbanki?"
"Suna lafiya ƙalau." Nan ta kira mai aikinta aka cikawa Sakinaa gabanta da abinci da nasha
kala-kala, ƙasa tayi da kai cike da kunya, Mum ta ce, "Ki saki jikinki Sakinaa nan gidanku ne ki
ɗauke ni tamkar Ummanki."
Ita dai Sakinaa ta kasa cewa komai don sosai take kunyar Mum, ganin haka Mum da kanta ta
zubawa Sakinaa komai ta ce taci, miƙewa tayi zata wuce don Sakinaa ta samu taci wani abu
Hamma Faruuƙ ya ce, "Kai Mum ni shi ke nan an man ce da ni, ko tayi ba ki yi mini ba?" Da
sauri ta zauna kusa da shi. "Sorry my Son me ka ke so?" Ya ce "Abinda ki ka ba ta." Yana nuna
Sakinaa da baki, nan ta haɗa masa tana ba shi a baki, ai sakin baki Sakinaa tayi tana kallonsu,
a ranta take ai yana daman haka Hamma Faruuƙ ya ke. Ganin kallon da take musu yasa ya
ɗaga mata gira tare da kanne mata ido ɗaya, sannan ya nuna mata gabanta, alamar tayi abinda
ke gabanta, murmushi tayi ta fara cin abincin a hankali.
Ba wani sosai taci ba domin daman ba iya cin abinci da yawa tayi ba, turo ƙofar da a ka yi yasa
hankalinsu ya koma can, wata budurwa ce ta shugo kyakkyawa zatayi 25 sanye take cikin riga
da wando matsatstsu sun kamata sosai sai wani ƙaramin mayafi da ta ɗaura a kanta babu
kallabi a kanta hakan yasa kyakkyawan gashin kanta ya bayyana, siririya ce irin sosai ɗin nan,
baka iya ganin idanuwanta sakamakon ƙaton baƙin gilashin da ya kusan rufe rabin fuskarta, ta
kalmin ƙafarta dogo ne sosai, hannunta mai ɗaure da ɗan siririn agwogwo da shi ta ke jan
akwatinta.
Mum ta miƙe da sauri tare da kiran sunanta, "Zubaidaa!" Murmushi tayi tare da nufar Hamma
Faruuƙ ta rungume shi, tureta ya yi daga jikinsa yana cewa "Haba ZubaidaA meme ne hakan?"
Murmushi tayi ta ce, "Hamma Umar har yanzun ka na nan da halinka?" Taɓe baki ya yi, "To mai
za a fasa mutuwar ko hisabin." Juyawa tayi ta rungumi Mum ta ce, "Nayi missing ɗinki my
Mum." Murmushi tayi, "Nima nayi naki 'yata, ya ki ka baro su Hajiya Sakinar?"
"Suna lafiya ƙalau suna gaishe ku sosai."
Umar kallon Sakinaa ya yi wacce ta saki baki tana kallon ikon Allah "Princess tashi in mayar da
ke gida kar Umma ta ji mu shuru." Da sauri ta miƙe.
Zubaida ko cikin ruɗu ta juyo cike da kishi jin My Hamma Umar ɗinta ya kira wata da Princess.
Kallon Sakinaa tayi nan take taji ta tsaneta kai duk wata mace dake raɓar mata Umar ta tsane
ta, tsana mafi muni da munana.
Sakinaa ta katse mata tunani da furta, "Mum zamu wuce na gode sosai." Murmushi Mum tayi,
"Mene ne na godiya? Nan fa kema gidanku ne ina zuwa." Sama ta wuce sai gata da wata
babbar leda tabawa Sakinaa, girgixa kai tayi "A'a Mum na gode." Ɓata fuska tayi "mene ne
hakan Sakinaa? Kema fa 'yata ce kuma babu kyau mayar da hannun kyauta." Hamma Umar ne
ya amshi ledar ya ce, "Rabu da ita Mum dole ne ta amsa." Ƙasa tayi da kai ta duka har ƙasa
tana wa Mum godiya.
Ɗagota tayi ta ce, "Lalala babu godiya tsakaninmu, don uwa ta bawa 'yarta abu sai ta ce sai ta
gode ki gaishe mini da Ummanki da kyau idan na sami lokaci ina nan zuwa."
"To Mum za taji na gode." Har ƙofa Mum ta raka su sannan ta juyo.
Zubaida da ta kusan sumewa a tsaye nan take ta fara hawaye.
"Mum mece ce wannan? meke shirin faruwa haka? Me ki ke so ki ce mini? Don Allah kar dai ki
ce wannan Ƙwailar yarinyar budurwar My Faruuq ce? Zaunar da Zubaidaa Mum tayi Kafin ta ce
"Ki kwantar da hankalinki ba budurwarsa ba ce asali ma ƙanwa ya ɗauketa. Nan ta sanar mata
yadda suka haɗu. Tuni idanuwanta suka kaɗa jawul. Ta ce, "Matsiyata ne fa, kuma talakawa fa Mum me yasa
Faruuƙ ya cika kwashe-kwashe? Duk yadda aka yarinyar nan sonta yake kuma wallahi ba zai
sameta ba, nice zai aura ba wata ba." Fuu! ta tashi tayi ciki.
Mum tsaki taja Zubaidaa har yanzun ba ta da hankali, wallahi bayan wasiya aka bari akan
auransu, da babu dalilin da za ta yadda ɗanta ya auri wannan ballagazar yarinyar, sam ba ta da
natsuwa da kamun kai, me ake da me irin halin Zubaidaa gashi shi kansa Faruuƙ baya son
Zubaidaa, ita dai bata san yadda za a yi wannan cakwakiyar ba. Bayan ya sauketa bai samu shiga ba saboda sallah da ake kira masallaci ya wuce ita kuma
Sakinaa ta shiga gida, Umma alwala take don haka ita ma alwalar tayi bayan sun idar da sallar,
ta nuna mata kayan da Mum ta bata, da saƙonta na gaisuwa. "Shi ne daga baki abu ki ka
karɓo?" "Wallahi sai da na ce ta bar shi taƙi shi ne Hamma Umar ya amso." Umma ba ta kuma cewa
komi ba.
Bayan isha'i tare suka shugo da Abba, nan Umma ta nuna masa kayan sukayi wa Umar godiya
ya ce, "Haba dai sai ka ce wani abu don Allah ku daina mini godiya mun riga fa mun zama
ɗaya, jini ɗaya kuma dangin juna."
Sosai ake daru a gidansu Umar akan auransa da Zubaidaa ya ce Shi ba ya son ta, nan fa
iyaye aka haɗ daman Familynsu yawa ne dasu,(Akwai tarihi a gaba kaɗan.) Yayun Dad ɗin shi
suka ce wallahi bai isa ba mahaifinsu ne yabar wasiya kuma daman can su auran zuminci su
ke, kowa da abinda yake cewa Dad ya dun ga rarrashinsa akan ya amince.
Ya ce, "Zan amince Dad amma sai dai idan za a ba ni Sakinaa domin ban taɓa son wata mace
a duniyata ba irin Sakinaa wallahi ina ƙaunarta please Dad ka naimar mini auranta, ni dai burina
a ba ni ita ko da ba yanzu za a yi auren ba."
Haka Dad yasa mi Malam Abdullahi da maganar, murmushi ya yi ya ce, "Ummaru yaron ƙyirki
ne ni kaina zan so haɗa zuria da shi domin a kwai yaro mai kamala ta ko ina, ni na ba shi
Sakinaa kuma na san ita ma za ta so shi duba da shaƙuwar da take tsakaninsu, amma ina so
ya yi haƙuri har ta kammala Secondary sai ayi auren don haka kar ya da mu yanzu ya auri 'yar
uwarsa." Nan fa Dad da Yayunsa suka yi ta godiya.
Murna da farin ciki gurin Umar kamar me, nan aka fara shirin aurensa da Zubaidaa
Yanzun su Sakinaa sun shiga ss2, kamar kullum suna haryar dawowa gida ita da Zaliha za su
tsallaka titi kenan, wata mota ta rugo a guje sauran kaɗan tabi takansu saboda tsabar tsoro
rungume junansu su kayi gabansu na bugawa, jin anja wani wawan burki suka dago a gigice,
shi kuwa da ke cikin motar da sauri ya wani fito cikin masifa ya ce, "Ku waɗanne irin wawanyen
yara ne? Wallahi da na bige ku na buge banza babu abinda za a yi, kuna tafe ba ku kallon
gaban daƙiƙan yara kawai....
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakinaa
_Gawurtattu uku 2014_
WANKA DA GARI...
©UmmuAffan
*Book 1 Page 7-8*
Ina kuke mata? Mata nake magana waɗanda suka amsa sunansu na mata ba muna mata ba!
Kaya ne masu inganci waɗanda zai mai rabo ke samu. Ki buɗe bakin aljihu Hajiyata kiyi gyara
da ingantattun kayanmu na GHT muna da.
Royal jelly-karin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda.
Akwai Garlic oil _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji
sunbatu.
Muna da Ganoderma reishi _xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam
Yana gigita maxa.
Sannan akwai Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara
ya gyra skin yyi fresh.
Ba anan muka tsaya ba muna da irin su Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya
wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Da su Longzit-matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn
labari.
Ga Panicept_duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau.
Kuma akwai Sto care_ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara
da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu.
Da Female _masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace
in Sha Allah.
Duk abin da kake buƙata zaka samu daga GHT sayen nagari mai da kuɗi gida kai tsaye kayi wa
wannan number mgn domin haɗaku da sha yanzu magani yanzu wato Maman Amal GHT
08104335144
Shahararru goma a duniyar kayan mata Maman Zee ƙamshi and Kayan mata, duk wasu nau'i
na kayan mata na gargajiya da na zamani gumba tsumi tabaje zuma masu ƙyau da inganci ku
nemi maman zee ƙamshi an kayan mata a number kamar haka 0806 384 5136 Tana Bauchi
tana aika kayanta gari-gari Ƙasa-ƙasa. Sayen na gari mai da kuɗi gida.
*Masu buƙatar ɗaura musu tallah suyi mgn cikin farashi mai sauƙi.* A saman rubutu ko a ƙasa
ko wanne da farashinsa. Na gode.
...Cikin tsananin fusata Sakinaa ta ɗago ta kalle shi suka haɗa ido kuwa, da tsiwa ta ce, "Aikin
banza taka wuƙar zakara kawai, kai da ka ke tuƙin kai baka kallon masu tsallakawa ne, ko kai
makaho ne? Ko kuwa titin naka ne? Wallahi da ka bige mu ba ka bige banza sai an ɗaukar
mana mataki, da har zaka fito kana wata fafarka ta banza." Ido kawai ya zuba mata zuciyarsa na harbawa, lokaci ɗaya yaji yarinyar ta tafi da imaninsa,
ganin taja hannun Zaliha za su wuce ya sa shi yin saurin shan gabansu.
Idanuwansa akan Sakinaa ya ce, "Kuyi haƙuri ban san ku ɗin na musamman ba ne. Tabbas na
gane laifina ne amma hakan ba zai kuma faruwa ba."
Wata muguwar harara ta ban ka masa, Kafin a matsagaitan mintoci ta ƙare ma sa kallo, fari ne
yana da tsayi kaɗan ba za a kira shi dogo ba amma shi ba gajere ba ne tsaka tsakiya, yana da
baƙar suma a kan sa ya yi askin nan irin na samari 'yan kwallo an aske gefe sannan an bar
wata cinkum a tsakiya, ba laifi shima yana da kyau daidai misali, sai dai leɓensa sun yi duhu
alamar yana shan sigari. Shadda ce a jikinsa ɗinkin da samari ke yayi, cikin mintuna biyu
Sakinaa ta ƙare ma sa wannan kallon
Taɓe baki tayi domin ko kwatar Hamma Umar ɗinta bai kai ba, sannan ita fa a rayuwarta bata
wani ƙaunar farin namiji sosai, duk da take da duhu tafi son baƙin namiji ko wankan tarwaɗa,
sake magana ya yi a karo na biyu.
"Please ku zo na rage muku hanya na ga ranar nan kamar tana damunku." Sakinaa tayi saurin
cewa.
"Muka sanar maka? Ka ga malam don Allah ja ƙafarka ka ba mu guri, ba ma gayyar soɗi." Ta
ƙarasasa maganar tare da murguɗa ma sa ƙaramin bakinta, bin bakin ya yi da kallo cike da
sha'awa don shi yana son mace me tsiwa haka nan daga kallo ɗaya da ya yi wa Sakinaa yaji
duk duniyar nan baya da abin so sama da ita, wata irin kaunarta ke fuzgarsa. Yadda yake kallon Sakinaa haka Zaliha ke kallonsa, domin kallo ɗaya ta ma sa taji ya tafi da
duka zuciyarta, ba ta taɓa soyayya ba, hasalima dukansu biyun ba su da samari, tana kallon
gayen nan taji ya mata kuma zata iya aurensa.
Sakinaa taja hannunta, "Kin ga Zaliha zo mu wuce wannan ba shi da aikin yi." Riƙe hannunta
Zaliha tayi gam alamar ta tsaya, kallonta tayi cike da mamaki ta ce, "Haba Sakinaa ya gane
kuskuransa ya ba mu haƙuri don Allah mu hakura mana kin ga rana ta ishe mu tunda ya ce zai
rage mana hanya don Allah kizo mu shiga, tunda babu ƙyau mayar da hannun ƙyauta.'' Da sauri
ya ce, "Yawwa ƙanwata na gode gaskiya kina da saukin kai kin burge ni." Murmushi tayi tare da
far da ido, cikon iyayi ta ce "Nima na gode."
Ba domin Sakinaa taso ba haka suka shiga motar. Zaliha ce gidan gaba Sakinaa daman baya
ta shige, ba haka ya so ba amma ba shi da yadda zai yi. Sun fara tafiya ya kalli Zaliha tare da
kallon Sakinaa ta madubi da ke kallon hanya, murmushi ya yi yarinyar na burgesa.
"Sunana Mubarak Sani Gata. Kuma yana da kyau naji sunanku."
Zaliha tayi fari da ido ta ce, "Wow nice name."
"Na gode ƙanwata.''
"Ni suna na Zaliha Shehu ƙawata sunanta Sakinaa Abdullahi."
"Da kyau, manyan sunaye masu daraja." "Mun gode." Zaliha ta furta. Tambayar da ya yi
unguwarsu ta sanar ma sa suka kama hanya.
Daidai ƙofar gidansu Sakinaa ya yi parking yana tsayawa ta fice da sauri ta shige gida Zaliha da
Mubarak suka fito ta ce, "Am kayi haƙuri wallahi ƙawar tawa ni kaɗai nasan kanta." Murmushi ya
yi.
"Kar ki da mu ai ƙawar taki mai tsada ce." Baban Zaliha ya buga addu'a take kar Allah yasa
Mubarak ya ce Sakinaa yake so sai ita amma sai ji tayi yana cewa "Wallahi Zulaihat kallo ɗaya
nayi wa ƙawarki naji duk duniya ba wacce nake so sama da ita, don Allah ki taya ni neman
soyayyar ƙawarki." Ƙirjin Zaliha babu abinda yake sai bugawa, yana ba da wani irin sauti mai ƙara, murmushin
yaƙe tayi, "Kar ka da mu Mubarak, sai dai Sakinaar ce a kwai tsiwa, amma zan taya ka in sha
Allahu."
"Yawwa ƙawarmu na gode sosai. Nan ne gidanku duka?"
"A'a nan gidansu Sakinaa ne." Da hannu ta nuna ma sa nasu gidany.
"Ok na gode sosai Zulaihat."
"Babu komai." Kuɗi ya bata taƙi amsa, ganin ya dage ta amsa sannan suka yi sallama ya wuce,
bin motarsa tayi da kallo, daga bisa ni ta wuce gidansu jikinta a matuƙar sanyaye.
Suna zaune take sanar da Sakinaa duk abinda ya faru, tsaki taja ta ce, "Yana son wa? Wai ni?"
Gyaɗa kai Zaliha tayi alamar
"I."
"Hmmm idan ma ni ce gara ya yi haƙuri domin ni ba aure ba ne a gabana, hasalima karatu zan
yi yanzun nake ss2 ban kammala Secondary ba balle naje jami'a. Don haka ya je ya nemi wata,
kin ga Abbana ma ya mini faɗan kar na kula kowa haka Hamma Umar ya ce kar na kula kowa
nasa karatuna a gaba don haka sai ki ba shiaɗ haƙuri, ke nifa ma mutumin nan bai mini ba
wallahi tunda na kallesa na san baya cikin tsarina, fuska kamar jan ƙosai, kin san fararen maza
ba sa cikin jadawalina." Ota dai Zaliha ba ta ce komai ba sai bin ta da ido take.
Yana parking a babban harabar gidan ya fito da sauri A Parlour ya iske Hajiyarsa da
ƙannansa, jikin Hajiyar ya faɗa yana sauke a jiyar zuciya. Sannu kawai take ma sa tana shafa
kansa, Ƙannansa suka ma sa sannu.
Hajiya ta ce, "Mubarak lafiya yau na gan ka wani iri haka?" Sumar kan sa ya shafa tare da fesar
da huci mai ɗumi ya ce, "Hajiya yau na samar miki surika." Shewa ta zuba haka sauran
ƙannansa Safah da Marwah sai Laurah.
Tuni suka dawo jikinsa Hajiya ta ce,
"Wannan wacce mai sa'ar ce ta sami santalelan yarona ɗan zamani son kowa ƙin wanda ya
rasa, sannan ɗan Hajiya?" Yaƙe ya yi ya ce, "Uhmm Hajiya yarinyar fa na lura ba ta sona ni ne
kawai ke haukana, kuma wallahi idan na rasata daidai yake da rasa numfashina." A harzuƙe ta
ce, "Wace ce wannan? Wane ne ubanta a garin nan? Da har za ta ce ba ta sonka? Uban waye ubanta a ƙasar nan da har zata ce ɗana son kowa ga kuma kwalisa dukiya mulki ga
uwa uba kyawu." Larah ta ce, "Kai Hajiyarmu duk irin wannan washi haka, shi so fa ba ruwansa
da kyawu ko kuɗi da sauransu." Harara Hajiya ta zuba mata ta ce, "Matan zamanin nan me
suke so idan ba kyakkyawan saurayi mai 'ya'yan banki bugun Abuja ba?" Mubarak ya ce, "Duk ba wannan maganar ba, ni dai Hajiya a nemo mini soyayyar Sakinaa
kawai nake buƙata, kuma ko ta halin ƙaƙa ne."
"Ta ya?" Larah ta tambaya.
Hajiya ta ce, "Larah ko ta halin ƙaƙa ne ina ruwanki wai? Tashi ki bar gurin nan domin duk a
yarana ke ce ki ka banbanta da sauran, sai ka ce ba ni ce uwarki ba. Ni Hajiya Amina naci dubu
sai ceto."
Miƙewa ta yi, "Shi ke nan bari in ba ku guri, amma ina son ku sani shi so na gaskiya ba ruwansa
da kuɗi ko ilmin, mutum da kyawunsa Allah yana da sa so ne a duk zuciyar wanda ya yi niyya."
Tana gama wa tayi wucewarta suka bita da tsaki Hajiya kallon ɗan nata tayi mafi soyuwa a
zuciyarta wato Mubarak ta ce, "Yarona faɗa mini sunan ubanta a faɗin ƙasar nan ko 'yar wace
ce dole ta so ka, kai ko da shugaban gasa ne ubanta kuwa."
Kallon Hajiyar tasa ya yi wacce a saninsa ta tsani talaka kowa ye, bata hurɗa da ƙananun
mutane