Showing 12001 words to 15000 words out of 26600 words
Chapter 5 - WANKA DA GARI BOOK 1 COMPLETE by Fatima Sunusi Rabi'u .pdf
tanka mata ba. Zaliha ta zuciya
sosai ta ce, "Sakinaa tabbas zaki ga ne kuranki, masoyinki na haƙiƙa Hamma Umar sai Allah ya
saka masa haka iyayenki ma."
Cikin tsananin fushi Sakinaa ta ce, "Wai Zaliha ina ruwanki ne? Iyayenki ne ko nawa? Idan kin ji
haushi ki auri Hamma Umar ɗin mana.
"Ni bazan auresa ba, amma ina son ki sani sai na rama masa abinda ki ka masa ni Zaliha
Shehu nayi alkhawarin sai nasa kin yi da nasanin abinda kika yi, daga ke har wannan shegen
Mubarak ɗin." Kuka Sakinaa ta kama "Allah ya isa tunda ki ka kira sa, shege wallahi da ki zagi
Mubarak gara ki zage ni shi ba shege ba ne da ubansa." Baki da hanci da kuma kunne sai ido Zaliha ta saki tana kallon Sakinaa a mamakance, nan take
wani tunani ya faɗo mata anya kuwa Sakinaa cikin haiyacinta take? Domin biri ya yi kama da
mutum abin ya yi yawa." Fita tayi amma tasa a zuciyarta ko ta halin ƙaƙa sai ta ceto ƙawarta
daga wannan halin, sai ta nuna mata abinda tayi babban kuskure sai ta nuna mata zaki ko a
dawa shi ne sarki.
Mubarak kuwa cike da murna ya shiga cikin gidansu, tun daga harabar gidan yake kwalawa
Hajiya kira.
Da sauri Hajiya ta fito tana cewa "Mubarak lafiya kuwa?" Domin ta zaci ko wani abin ne ya faru
da shi, jikinta ya faɗa yana cewa "Hajiya mun ci su da yaƙin, Abban Sakinaa ya ce a kai sadaki
gobe za a ɗaura mana aure."
Wani irin shu'umin murmushi tayi "Wa ya faɗa musu barno gabas take? Daman me na faɗa
maka?"
"Hajiya kizo muje kawai a kai sadakin." Murmushi ta kuma, wayarta ta ciro ta kira ƙaninta Buhari
ta ce, "Kazo yanzun nan ina son ganinka."
Ba a yi cikakken awa ba sai ga shi bayan sun gaisa take sanar da shi kuɗin auren Mubarak za
su kai kuma gobe ne bikin.
Cike da mamaki yake kallonta ya ce, "Kuɗin aure kuma Hajiya? Goben nan biki amma ba mu ji
ba sai yau?"
"Abin ne yazo na gaggawa yanzu iyayen yarinyar mu ma suke sanar mana, ka ga indai
maganar kuɗi ce mu ba mu da haufi, don haka ka tashi muje mu kai kuɗin." Zaro ido ya yi
"Hajiya mu zamu kai kuɗin? Ina su Alhaji Sani da Alhaji Lawan ƙannan mahaifinsa? Ai su ya
dace su kai komai dangin ubansa." Harara ta banka masa ta ce, "Kasan dai ni da yarana ba shiri muke da su ba, don haka bazan
bari su shaga maganar yarana ba yanzu kuɗi suke magana ko ba dangin uba?" Zai yi magana
ta katse shi "Ka ga Buhari idan kai ma ba za ka je ba, ni kaɗai sai inje tunda ƙafa gare ni.
Saboda yana matuƙar jin tsoranta yasa shi ammasawa da "To idan kin shirya sai mu wuce."
Amma shi dai ai ya san da uba ake ado.
Mayafi da jaka ta ɗauko suka fita Mubarak ya kai su gidansu Sakinaa, bayan sun gaisa da
Malam Abdullahi suka masa maganar sun kawo kuɗin auren ne.
Daga Umma har shi suka kalli juna cike da al'ajabi, to ya suka iya 'yarsu ce ta musu wannan
kwashe-kwashen wai uwar yaro da kawo kuɗin auren ɗanta ba su taɓa gani ba. Ko a garin
mahaukata.
Dubu ɗari biyu ta ba da ta ce, "wannan kuɗin nagani ina so, ta bada wasu ɗari biyar ta ce na
sadaki ta bada ɗari uku ta ce na uwa da na uba. Harararta ita da kuɗinta Abba ya yi ya ce, "Ki
kwashe abin ki ba su muke buƙata ba abinda kawai nake so dubu ashirin sadakinma don ya
wajabta da bazan amsa ba. Ta ce, "Shi ke nan, kayi wa kan ka, amma ba ma so ku kawota da komai ita kaɗai muke so."
Haushi ya cika Abba ya ce"Idan mun kawota da su sai ku zubda, sannan ya tashi ya fita.
Zuciyarsa na suya kamar an ɗaurata a tukumar tsure...
08104335144
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUuku
#LabarinSakina
_Gawurtattu uku 2024_
WANKA DA GARI...
©UmmuAffan
*Book 1 Page 11-12*
Ina kuke mata? Mata nake magana waɗanda suka amsa sunansu na mata ba muna mata ba!
Kaya ne masu inganci waɗanda zai mai rabo ke samu. Ki buɗe bakin aljihu Hajiyata kiyi gyara
da ingantattun kayanmu na GHT muna da.
Royal jelly-karin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda.
Akwai Garlic oil _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji
sunbatu.
Muna da Ganoderma reishi _xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam
Yana gigita maxa.
Sannan akwai Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara
ya gyra skin yyi fresh.
Ba anan muka tsaya ba muna da irin su Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya
wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Da su Longzit-matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn
labari.
Ga Panicept_duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau.
Kuma akwai Sto care_ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara
da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu.
Da Female _masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace
in Sha Allah.
Duk abin da kake buƙata zaka samu daga GHT sayen nagari mai da kuɗi gida kai tsaye kayi wa
wannan number mgn domin haɗaku da sha yanzu magani yanzu wato Maman Amal GHT
08104335144
Shahararru goma a duniyar kayan mata Maman Zee ƙamshi and Kayan mata, duk wasu nau'i
na kayan mata na gargajiya da na zamani gumba tsumi tabaje zuma masu ƙyau da inganci ku
nemi maman zee ƙamshi an kayan mata a number kamar haka 0806 384 5136 Tana Bauchi
tana aika kayanta gari-gari Ƙasa-ƙasa. Sayen na gari mai da kuɗi gida.
*Masu buƙatar ɗaura musu tallah suyi mgn cikin farashi mai sauƙi.* A saman rubutu ko a ƙasa
ko wanne da farashinsa. Na gode.
Hajiya kuwa taɓe baki tayi aikin ɓul, inji tusa a ranta kuwa ta furta 'Wallahi can da su gada. Ku
ne matsiyata kuma a haka zaku ƙare, matsiyatan banza kawai da ba ku san alkhairi ba, ko ina
dai matsiyaci sunansa kenan.'
Washe gari Juma'a aka ɗaura auren Mubarak Tahir da Sakinaa Abdullahi a masallacin Juma'a
bayan idar da salla. Umar da ƙarfi ya runtse idanuwansa lokacin da yaji ɗaurin auren, ji ya yi
kamar an saukar da guduma a kan sa.
Da yake shi da Daddynsa sunzo ɗaurin auren. Abba ya kalle shi cike da tausayi, Allah ya gani
yaso haɗa zuri'a da wannan natsattsen yaron, amma Allah bai nufa ba, ina ma ace yana da
wata 'yar bayan Sakinaa, tabbas da ya wanke ma shi ruwan idaniyarsa da raɗaɗin da Sakinaa
ta furza ma shi, amma ba komi yana ma shi addu'a Allah ya ba shi mata tagari wacce tafi
Sakinaa a ko mi, ko da yake bikin shi da 'yar uwarsa Zubaidaa sauran sati biyu inji Daddynsa.
Amma ya san ba wai yana ƙaunarta ba ne, idan ita ce alkhairinsa Allah ya tabbatar ma shi.
Mubarak ya fi kowa farin ciki haka aka gama ɗaurin aure lafiya, daga baya aka ɗum guma
zuwa gida. Mubarak ya riga kowa isa gidan Abba, kamar yadda Abban ya sanar masa idan an
ɗaura aure yazo ya tafi da matarsa.
Bayan sun iso, tare suka shiga ciki, UMAR Daman daga masallacin wucewa su ka yi gida shi da
Daddy.
Umma na zaune tsakar gida ta buga uban tagumi tun lokacin da aka tafi ɗaurin auren take cikin
damuwa ta rasa me ya sa ta tsinci kanta cikin rashin sukuni ko da yake dole a rina wai an saci
zanen mahaukaciya mai rasa nasaba da wannan ƙaddararren auren da Sakinaar ta zaɓawa
kan ta, tana jin zafi da ɗacin abinda Sakinaa ta musu haƙƙun. Ita ma Sakinaa tun lokacin da taji Abban nayi wa Umma sallamar sai ya dawo take cikin farin
ciki, yau za a aura mata abin sonta, murna ta dun ga yi daga bisani ta fara tattara komai nata, ta
kintsa guri guda sai da tagama haɗawa kuma taji gabanta na faɗuwa sai ta kama kuka tana so
taji tausayin iyayenta da Hamma Umar ɗinta amma zuciyarta na hanata, hakan yasa zazzaɓi
mai zafi ya rufeta, kwantawa tayi bisa katifarta tana rawar sanyi tana kuka sosai, a haka su
Abba da Mubarak suka shugo.
Abba ya zauna kusa da Umma. Mubarak ya yi tsaye a kan su babu alamun tarbiyya ya ce, "Ina
matata Sakinaa take." Kallonsa su kayi Abba ya yi ƙarfin halin cewa tana ɗaki don Umma ji take
kamar ta shaƙesa ya mutu.
Ɗakin ya shiga da sauri ya yaye lilliɓin da tayi da zani ya ce, "Kinaata lafiya kuwa?" Hawaye ne
kwance a idonuwanta "Ba na jin daɗi ne Mubarak zazzaɓi mai zafi ya rufe ni kuma ba na son
rabuwa da su Um...."
Bai bata damar ƙarasawa ba ya rufe bakinta da nasa, ya ɗaki wani lokaci kafin ya sakar mata
baki idanuwan nan nasa tuni suka sauya launi.
"Kar in sake jin kin faɗi hakan, yanzu ne za ki yi rayuwa mai daɗi da ni Kinaata, nayi alƙawarin
jiyar da ke daɗi da saka nishaɗi. Ki man ta da kowa da komai kin ji."
Sake lafewa tayi jikinsa tana hawaye domin Abbanta da Ummanta na ranta, ɗaukarta ya yi
kamar wata jariri ya yi waje da ita, suna fitowa ta fara ƙoƙorin sakkowa tana zullewa amma bai
bata damar hakan ba saboda irin ruƙon da ya mata, "Abbana! Ummata" Abinda ta iya faɗa
kenan ya fi ce da ita. Su kuwa girgiza kai kawai su ka yi.
Kai tsaye wani asibiti mai zaman kansa ya nufa da ita, yana zuwa ya ce a ba ta gado a samata
ƙarin ruwa hakan kuwa a ka yi, yana zaune bakin gadon inda ta sami bacci sakamakon allurar
bacci da aka haɗa a ruwan, wayarsa ya ciro ya kira Hajiya ya sanar mata nan take ta aiko Laura
ita da Direba suka taho musu da abinci domin a can gidan ba ƙaramin biki suke sha ba. Sai bayan magrib ta farka jikinta ya mata sauƙi, taji ƙarfi alwala tayi tayi sallolin da ke kanta har
isha'i da ake kira yanzu, bayan nan Mubarak da kan shi ya zuba mata abinci zaunawa ya yi a
daddumar kusa da ita ya ɗaura kafafuwanta bisa cinyarsa da sauri zata zame ya riƙe
ƙafafuwan, ita kuwa duk kunyar Laura ta isheta a hankali ta juyo ta kalleta gani tayi hankalinta
ma baya kansu chating kawai take a wayarta.
Abaki ya dun ga bata abincin sai da ta ce ya isheta sannan ya rabu da ita yaci nasa, a ranar ya
matsa wa likita ya sallame su, da ya ce ya bari sai gobe ta ƙara samun ƙarfin jikinta yaƙi.
A ranar gidan Hajiya ta kwana a ɗakinta akan gadonta zo ku ga yadda Hajiya ke ji da Sakinaa.
Washe gari tun da safe mai lalle tazo ta zanawa Sakinaa uban ubansu haka mai saloon da me
kwalliya, bayan ya bushe aka mata wankan dilka zo ku ga kwalliya. Ma sha Allahu ƙyawun
Sakinaa ya ƙara fitowa ainun. Ƙayatacciyar liyafa aka gabatar a wani babban holl, ai susucewa Mubarak ya yi da ya ga
Sakinaarsa hannunsu na sakaye da juna, sai wani irin kallo yake ai ka mata kai daga gani na
tsantsar sha'awa da so ne.
Haka aka gabatar da liyafar cikin kwanciyar hankali, kafin a kammala tuni Mubarak ya fara
zuzucewa.
Gidan Hajiya aka mayar da ita, Da Hajiyar ta ce ya bari gobe sai a kai ta amma yaƙi, ya ce a kai
masa matarsa yau, nan aka fara shirin kai ta domin ita duk abinda Mubarak ya ce shi take yi.
Ɗan so kenan.
Ƙawayenta su ne suka kai Sakinaa katafaran gidan Mubarak iya haɗuwa ya haɗu ba ƙarya gida
ne na gani a faɗa bayan kowa ya gama wucewa Ango da abokansa suka shugo inda suka dun
ga shaƙiyancinsu abin mamaki har da mata ita dai tana cikin mayafi ba ta iya ɗagowa ba balle
ta kallesu sai dai da alama suna da yawa don yadda take jin muryoyinsu da yawa.
Bayan sun gama shaƙiyancinsu suka musu salla sannan suka ajiyewa Sakinaa kuɗin sayen
baki ta bawa ƙawayenta.
Mubarak bayan ya musu rakiya ya dawo, zaunawa ya yi bakin gadon ya ce, "Amarya kin sha
ƙamshe." Daga cikin mayafinta tayi murmushi.
"Ba za a buɗe mini kyakkyawar fuskar nan na gani ba ko sai na saya ne?"
A hankali ta yaye duka mayafin suka zubawa juna ido.
"Mubarak kafi ƙarfi komai a gare ni, fuskata fuskarka ce bazan taɓa cewa sai ka biya ni kafin ka
kalle ni ba, da ni da kai duka abu guda ne." Murmushin jin daɗi ya saki.
"Na gode my Sakinaa ina sonki da yawa."
Numfasawa tayi,
"Nima ina sonka Mubarak burina dai ka riƙe ni amana karka juya mini baya saboda kai nabar
ahlina don Allah Mubarak ka riƙe ni amana."
Ta faɗa a raunane tare da haɗe hannayenta waje guda a lamar roƙo, riƙe hannayen nata ya yi
yana murzawa a hankali "Sakinaa ni da ke daga yanzun mun zamo abu guda ne ba najin zan
iya juya miki baya har abada kisa a ran ki Mubarak yana tare da ke har ƙarshen rayuwarki."
Murmushi tayi cike da jin daɗin furucinsa ta ce, "Na gode Habibi." Shima murmushi ya yi,
"Ki tashi mu gabatar da sallah domin nuna godiyarmu gurin Allah." Babu musu ta tashi toilet ta
shiga ta ɗauro alwala, bayan ta fito shima ya shiga.
Sai dai babban tashin hankalin da Sakinaa ta fara riska tattare da Mubarak shi ne rashin iya
sallah, sam babu abinda ya sani gami da ibadarsa don ko fatiha da kyar ya kawota. Shuru tayi
gabanta na faɗuwa a ran ta kuwa ta sa zata koyar da shi abinda ta sani domin ya gyara
ibadarsa, bayan sun idar jikinta a sanyaye tana kallonsa cike da tausayi shi kuwa ko ajikinsa
wai an tsikari kakkausa, ledar da suka shugo da ita ya jawo ban ƙararriyar kaza ce da su fresh
milk, nan suka ɗanci duk da Sakinaa ta ƙi ci shine ya tilastata sannan ya bata a baki.
Bayan sun gama tana niyyar shiga bathroom ta wanke baki sannan ta watsa ruwa amma ya
riƙeta, cikin jin kunya ta ce, "Bari na dan watsa ruwa." Ƙiri-ƙiri ya hanata nan fa labarin ya canza
salo.
Sakinaa taci baƙar wuya hannun Mubarak sam bai tausaya mata na ganinta ƙaramar yarinya
ba, ya mance ba irin 'yan matansa ba ce da yake harka da su, a gareta wannan ne na farko,
saboda azaba sumewa tayi, sai da ya gama hankalin sa ya dawo jikinsa sannan ya ga
katoɓarar da ya yi. Kinkimarta ya yi zuwa bathroom nan ya sakata cikin ruwan zafi, jin ta cikin ruwan zafi ya farfaɗo
da ita ta saki kuka, haka dai ya yi ta gasata harta ɗan sami sauki.
Sai sambatu yake mata "Ni daman irin matar da nake so kenan Sakinaa ki ce daidai da
ratuwata komai naki yayi mini haka nake so." Ita ko magana ta kasa a ranta kuwa mamakinsa
take, tunowa da tayi babu addu'ar da ya yi kuma ya sameta cikakkiyar budurwa maimakon ya
godewa Allah sai faman sambatun banza yake da ba su da wani tasiri a gareta. Haka fa Sakinaa kullum suke cikin amarcinsu, maimakon aga amarya na kyau da ƙiba kamar ko
wacce amarya sai aka samu akasin haka wannan karon, domin Sakinaa duhu tayi sosai ga
rama saboda tunani, sai dai tayi fresh abin ta domin sam Mubarak ya fara fitar mata a rai
saboda zuwa yanzu da suke wata biyu da aure ta gama fahimtar duka halayensa kama daga
rashin ilminsa shaye shayensa neman matansa da duk wani abu, duk da zuciyarta nanan
kumshe da son sa bata ganin laifinsa ga yawan takura mata da yake da nema wannan shi ne
yafi ɗaga mata hankali don bai mata da sauki.
Wani zuwa da Hajiya tayi taga yadda ta rame ta tambayeta sai ta ce ba komai suna zamansu
lafiya.
Watansu huɗu da aure Sakinaa ta fara ciwo yawan amai da rashin cin abinci ko da sukaje asibiti
likita yatabbatar musu ta sami ciki na wata biyu.
A furgice Mubarak ya miƙe yana kallon likitan "Doctor ciki fa ka ce wanne irin ciki wata huɗu
kachal da aure?" Daga likitan har Sakinaa bin sa su ka yi da kallo cike da mamaki.
Likita ya ce"Wannan ai abin farin ciki ne Allah ya baka sai ka miƙa godiyarka gare shi baka
butulce masa ba." Cikin fusata ya ce, "To ban shiryawa zama uba a wannan matakin ba, idan
zaka zubar to ka zubar na biyaka idan kuma bazaka iya ba sai muje gurin masu zubar wa."
Likita ya ce, "A'a mu ba mu zubda ciki ka iya tafiya." Fin cikar hannun Sakinaa ya yi su ka yi
waje ita kuwa dubansa take cike da tashin hankali, sai da ta zauna cikin mota ta iya kakalo
kalamanta domin tuni yawun bakinta suka kame, "Mubarak me nake ji haka? Kana nufin baka
son cikin da ke jikina ko ya?" "Tabbas ban shirya zama uba a yanzu ba, to ke Sakinaa in ban da abin ki mene ne abin ɗaukar
ciki a wannan lokacin haka nan kawai ki kashe mana jin daɗinmu ki zo ki tsufar da kan ki, ba ma
wannan ba kina ganin dai makaranta ki ke zuwa ko secondary ba ki gama ba, ke wannan ba
abin kunya ba ne ƙawayenki su ganki da ciki?" Kallonsa kawai take don ta kasa maganantuwa juya kalamansa kawai take a ran ta, lallai
mutumin nan babban jahili ne, shi yanzu har zai iya cewa sai lokacin