Showing 24001 words to 26600 words out of 26600 words
Chapter 9 - WANKA DA GARI BOOK 1 COMPLETE by Fatima Sunusi Rabi'u .pdf
fa take 22y yanzu ne take tashen
kyawun komai nata daidai yadda ake so, ta samu ƙawarta ta makaranta Salma, ita ma
natsattsaya ce babu ruwanta kamar Sakinaan karatunsu kawai suka sa a gaba, ranar da
tasanarwa Salma ta taɓa aure har da yaranta biyu nan take Salma ta ƙaryata ta ta ce bata
yarda ba, sosai suka yi musu ta ce,
"Amma Salma me yasa baki yarda nayi aure ba har da yara biyu?" Salma ta ce, "Duk fa wanda
zaki faɗawa wannan maganar Sakinaa ba yarda zai yi ba, wa zai kalleki ya ce ke ɗin ce kika
taɓa aure har da wasu yara dubeki fa? Ta ƙarashe tana nuna jikin Sakinaa.
Murmushi Sakinaa tayi sannan ta ba wa Salma duka tarihin rayuwarta, shuru Salma tayi har da
hawaye ta ce, "Tabbas Sakinaa kin ga rayuwa wannan shi ne kuwa Kinyi Gdun gara kin faɗawa
gidan zago, kuma kin fahimci Wanka da gari ba shi maganin yunwa sai anjiƙa an sha. Amma
duk da haka kar ki yanke ƙauna zuciyata na ba ni tabbas Hamma Umar zai dawo gareki, tunda
har yanzu yana rayuwarki ita kuma Zaliha kanta tayiwa, duk da zuciyata na wasi-wasi akanta ta
wani fannin fa ba ta da laifi."
Numfashi taja ta ce,
"Ni yanzu ba na ta Zaliha wallahi taje da Mubarak ni babu wanda na tsana sama da shi, a yanzu
burina Hamma Umar ya dawo gare ni." Ta ƙarashe da hawaye, share mata hawaye Salma tayi.
"Sakinaa ki kwantar da hankalinki ki sa a zuciyar tamkar ya dawo gareki, kar ki man ce yana
cikin rayuwarki tsamo-tsamo balle idan ya kalli kyakkyawar surar nan taki uhmmm wallahi ke
'yar baiwa ce yaranki biyu amma jibarki har kin fini ni budurwa komai." Tare suka sa dariya.
"Ke ko baki da dama Salma.''
Tana komawa gida tun a farfajiyar gidan taga motoci guda biyu, kallonsu tayi tare da ƙarasawa
ciki a zuciyarta tana cewa 'baƙi mu kayi kenan gidan?'
Haka ta shiga ciki cikin sallama, su wa za ta gani? Daddyn Umar da wasu jama'a masu yawa,
tana shugowa suka saka mata ido, da sauri ta ƙarasa tare da zubewa har ƙasa tana gaishe su
suka amsa cike da fara'a da sakin fuska.
Ta yi wa su Umma sannu da gida sannan ta shige ciki tana mamakin me ya kawo dangin Umar
gidansu, wanka ta shiga tare da ɗauro alwala ta zo ta gabatar da sallah.
Da dare suna zaune a parlour da su Ummanta, Abba ya ce,
"Sakinaa kin san me ya kawo Su Daddyn Umar?" Ji tayi gabanta ya buga da ƙarfi cikin dauriya
ta ce, "A'a Abba." Gyara zama yayi sannan ya kalle ta.
"Sun zo neman auranki ne, tunda tuni ki ka gama iddarki kuma harkin fara karatu." Sosai take
kallon Abba cike da mamaki da al'ajabi ta kasa ga ne yanayin da take ciki farin ciki ko akasin
hakan? Abba ya ci gaba da ce wa,
"Sai dai wannan karon ban yi saurin yanke hukunci akan ki ba saboda ba na so ki sake ba ni
kunya a karo na biyu na ce suje zan tuntuɓe ki idan kin amince zan kira su."
Hawaye suka fara zubo mata a fuska inda tayi ƙasa da kanta ba kukan komai take ba sai na
abinda Abba ya ce ita nasan ko wancen karon ba don abinda aka mata ba babu abinda zai sa
ta tsallake maganar Abbanta.
Umma ta ce, "Me na faɗa maka? Shiyasa na ce karka ce ka amince gara ka fara tuntuɓarta
kafin ta sake zuba mana ƙasa a ido ka ga alama dai ko?" Da sauri ta zube ƙasa bi sa
gwiwowinta ta ce, "Abba da Umma ku gafarce ni, ko waccen karon akasi aka samu amma don
Allah kuyi haƙuri ku yafe mini ku dai na tuno baya, ni na amince da auren Hamma Umar wallahi
ko a gobe za ku ɗaura mini aure da shi to a shirye nake kuma zan masa ladabi da biyayya
daidai iyawata, bazan taɓa ba ku kunya ba iyayena."
Umma ce ta ɗagota ta rungume tana buga bayanta alamar rarrashi "To ya isa haka mu tuni
muka ɗ yafe miki Sakinaa babu komai aran mu."
Abba ya ce, "Allah ya miki albarka Sakinaa tabbas tuntuni mun yafe miki don haka ki dai na
tuno komai aran ki." Share hawaye ta fara.
"Na gode Iyayena."
Washe gari suna zaune a kan kujerun roba cikin makarantarsu Sakinaa ke sanar da Salma
abinda ya faru, ta ɗaura da cewa, "Salma abinda idan na tuno yake faɗar mini da gaba shi ne
ina ji a jikina kamar ba da sanin Hamma Umar ba aka zo gidanmu neman aure na."
Salma ta ce, "Wannan ba lokacin wannan tunanin ba ne, domin ko da bai sani ba idan kin je
gidan zai sani. Ke fa mace ce kin san duk hanyar da zaki dawo da hankalinsa gareki, sannan
kuma yana son ki a baya har yanzuma ina kyautata zaton yana sonki don haka ki cire komai
aran ki, mu fara shirin biki.'' Bugun wasa ta kai mata ta goce, "Ba wani shirin da zan yi yasin."
Salma ta ce, "Shiri fa ya zama dole, kin ga ƙanwar Mamana tana shiri na gyaran amare komai
ya yi zom-zom zan haɗaki da ita kin san Shuwa ce ita tasan sirrin komai, ai Maman Amal
ƙarshe ce da tasan sirri na gara masu inganci mai so na haɗa su ya yi magana ta wannan
number 08104335144 ita ake kira mai da tsohuwa yarinya." Sakinaa ta ce, "Wallahi Salma ba ki
da dama Allah ya shirya ki amma dole na ziyarci Maman Amal GHT domin dawo da martabata
daga Hamma Umar."
"Amin amma fa dole ki gyara ko da baki da kishiya balle akwai." Sai lokacin gabanta ya buga da
ta nuno ashe wai tana da kishiya. Zubaida ta tuno lokacin da ta ganta a gidan su Hamma Umar
da ya taɓa kai ta, gabanta ya sake bugawa tuno abinda ya faru da irin kallon da take mata.
Sosai aka fara shirye-shiryen bikin Sakinaa da Umar. Inda shi ta ɓangaransa bai san komai ba
kamar yadda Sakinaa ta hasaso, Daddynsa ne ya yi komai shi kuma dalilinsa nayin hakan, tun
bayan da Sakinaa tayi aure har yanzu Umar ya kasa dawowa kamar da sannan ga babban
rashin dacen aure da ya yi, duka familynsu sun san abinda ke faruwa a gidan Umar. Zubaida dai muguwar ƙazama ce idan ka shiga bedroom ɗinta idan kai mai ƙanƙami ne sai kayi
a mai saboda zan iya cewa tunda taje gidan bata taɓa shara ba da garan gado, da ta cire kaya
duk inda ta samu nan take ajewa, abu dai babu kyawun gani Umar ya mata magana ta ce sai
dai ya kawo mata 'yan aiki shi kuma ya ce bazai kawo ba, domin ko da cen shi ƙanƙami gare shi
ko abincin 'yan aiki bai iyaci Mummynsa ke masa, amma ita kuwa bata girki ga shegen yawo
yau tana gidan wancen ƙawa gobe ana bikin ƙawa, ko ƙanwar ƙawata ko ƙawata ta haihu, gashi
ƙawayenta suzo su cika gidan su saka kiɗa su dun ga rawa ana ɗaurawa a Tiktok har da masu
shaye-shaye ita kantan tana yi sai dai ba ta bari Umar ya gani.
Babu abinda ta sani sai wanka ta dinga tiƙa rawa tana ɗauka a waya ta ɗaura a Tiktok sai ka ce
ba matar aure ba, sai kum fita unguwa idan a cikin gidan zaka isketa kuwa wata buguzun, tana
zaune gida irin wannan tsaruwa ta ƙarshe ya yi amma idan ka shugo sai ka ɗauka 'yar aikin
gidan ce, wanka sai za ayi rawa ko fita ta kecewa sa'a. Ba ta san hakkin miji ba, yo shi Umar tun satin farkonsu da yasan ya neme ta bai sake bi
takanta ba don shi mutum ne mai tsafta bazai iya da ƙazantarta ba, itan ma bata taɓa zuwa
gurinsa da sunan wani abu ba kuma da bai nemanta ba ta ce masa mene ne dalili ba, haka
suke rayuwa abin ba tsari tun Umar na dannewa har yazo ya fara mata magana akan ƙazanta
da yawo amma taƙi shi kuma saboda zumincinsu ya rabu da ita sai dai ko kallo bata ishe sa ba,
kusan kullum da azumi bakin sa domin kare kanka kuma a gidansu yake buɗa baki, wannan
dalilin yasa iyayensa suka gane yana cikin damuwa da jarabawa, duba da irin son da yakewa
Sakinaa yasa suka nemar masa aurenta sun san yana sonta wani dalilin nasa ne yasa yake
ɓoyewa. (Cewar iyayen Hamma Umar ba ruwan Ummu Affan.)
Wata biyu kawai aka saka bikin, hakan yasa Umma ta fara ƙoƙarin gyaran 'yarta ciki da bai,
Gurin 'yar mutan Bauchi wato shararru goma a duniyar kayan mata, maman zeey ƙamshi da
kayan mata, domin ita ma fa gyana ce fannin na gargajiya hakan yasa duk wasu kayan gyaran
aure gurin Maman Zee Umma tayo oder domin gyara Sakinaa. Ɓangare guda kuma Ƙanwar
Maman Salma wato Maman Amal GHT na nata aikin, hakan yasa kafin wata biyun ya cika idan
ba sanin Sakinaa kayi ba ba zaka shaidata ba tayi kyau na musamman kamar ka saceta ka
gudu. Duk mai son saya wani abu gurinsu ya tuntuɓe ni domin gyaransu iyaka ne.
Umar har zuwa lokacin bai san wainar da ake toyawa ba, bai san komai ba sai ana sauran
kwana biyu ɗaurin auren, inda Daddy duk wani abu da ya dace ya masa shida abokin Umar ɗin
Faisal suka tsara komai, a ranar da Daddy ya sanar masa a razane ya ɗago kai ya ce, "Daddy
aure na kuma sauran kwana biyu, wace zan aura ni na faɗa muku zan ƙara aure ne?'' Daddy ya
ce, "Baka faɗa mana ba amma mu mun san kana cikin wani halin da ƙara auren naka ne mafita,
kuma muna da tabbacin wannan karon zaka dace insha Allahu."
Ƙasa ya yi da kai,
"To Daddy wai wace ce zan aura ne?"
"Sakinaa."
Da sauri ya kalli Daddy tare da zuba masa ido, bazaka taɓa gane yanayin da yake ciki ba.
Daddy ya ce, "Umar tun farko Sakinaa ka ke so kuma ita ce ta dace da rayuwarka ina da
yaƙinin zaka sami farin ciki daga gareta, ka san rabo tun farko rabon yaran cen ne ya kai ta
gidan wancen mijin, kasan wani baya haihuwar yaran wani, dole kuma sai da taje ta ba sa
rabon dake tsakaninsu sannan ta dawo gareka."
Shuru ya yi yana jujjuya kalaman Daddynsa a kwanyarsa kafin ya ce, "Daddy ba komai Allah
yasa hakan shi ne mafi alkhairi, amma da za a ɗaga bikin zuwa wani lokaci na ɗan yi tunani."
"Tunanin me Faruuƙ sai ka ce wani ƙaramin yaro, kai dai kawai ka sawa abin albarka."
Kasa cewa komi ya yi ganin haka Daddy ya ɗauko wani zancen suka ci gaba.
Ana gobe biki Zubaida ta sami labari, cikin masifa da bala'i ta nufi bedroom ɗin Umar tana zuwa
ta banka ƙofar ta shiga, zaune yake yana aiki a computer. Tana zuwa ta wani ci burki gabansa
tana cika da batsewa ta ce, "Algungumi yau asirinka ya tonu daman aure za ka yi baka sanar
mini ba, wannan wanne irin rashin mutumci ne?" Duk da maganarta ta ƙona masa rai amma ko ɗagowa bai yi ba bare ya kalleta asalima duƙufa
ya yi aikan da yake, ita kuwa hakan da ya yi ya ƙara ƙona ranta nan ta fara girgiza ta ce, "Umar
da kai fa nake magana amma kayi mini banza kamar ba ka jin me nake cewa, ko yau ka kurum
ce ne?" Nan ma shuru ya mata, ture computer gabansa tayi da ƙarfi, ai kuwa sai gata a ƙasa. Cikin wata irin zuciyar da bai san yana da ita ba ya miƙe tare da kwasa mata wani lafiyayyen
mari har sau uku, ai nan take ta ruɗe ta fita a haiyacinta ta riƙe kuncin tana wani matsananincin
kuka, tuni bakinta ya fashe ganin jini ta saki wata ƙara tana kururuwa, tare da nufarsa da niyyar
cukukuyarshi, ai duka hannayenta ya haɗa waje guda ya wani girgiza su tare da sakinta nan
take ta zube tana harfe hanyen don ko miƙuwa sun ƙi tana kuka sosai. Kallonta ya yi cike da
takaici ya ce, "Zubaida ina so ki sani kina cin darajar iyayenmu ne kawai amma da yanzu na
man ce da tarihinki a rayuwata, don na zuba miki ido sai raini kuma ya shiga tsakaninmu? To
aure zanyi goben idan kin isa sai ki hana sakarya ƙazamar banza kawai."
Ya fice ya bar ta ɗakin kuka sosai take da haka takai kanta nata bedroom ɗin, ta ɗau mayafi sai
gida. Tunda ta shiga mahaifinta ke mata wani banzan kallo ya ce,
"Ke Zubaida lafiya kuwa?" Zubewa tayi gabansa tana kuka ta ce, "Abba saboda rashin mutumci
irin na Umar da nuna mini ba ni da daraja a gurinsa ace zai yi aure ko ya sanar mini sai a bakin
duniya nake ji, sannan na masa magana ya lakaɗa mini dukan tsiya har da zagina wai
albarkacinku nake ci." Ta saki wani kuka wanda ke alamta irin zafin da turirin da take ji a
zuciyarta.
Mahaifinta ya kalleta cike da takaici ya ce, "Wallahi Zubaida ke dai kin yi asara, shashasha
wawuyar banza kina zaton duk abinda kuke ciki ba mu sani ba ne? To mun san komi mun san
zaman haƙurin da yaron nan Umar keyi da ke, ban san ina kika kwaso wannan mugun halin ba.
To don zai ƙara aure sai ki da mu? Auren da shi kansa bai san da shi ba sai jiyan nan, to abinda
baki sani ba da ni aka je nemar masa auran."
Da sauri ta kallesa tana kuka. Ya ce, "Eh kwarai da gaske don haka ki tattara ki koma gidan
mijinki kamar yadda kika fito da ƙafarki kafin in saɓa miki, idan kin je kin gyara halinki kanki kika
wa idan ma baki gyara ba duk kanki kika wa, kima gode Allah da Umar ya iya zama da ke."
Hannu Zubaidaa ta ɗaura aka ta tare da rushewa da wani gigitaccen kuka, daidai fitowar
mahaifiyarta daga bedroom....
Ƙara-ƙaƙa-ƙaƙa, anan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya wato book 1 domin karanta littafi na biyu
sai ku biya kuɗin karatu 500 kachal mu antaya a book 2 Akwai tarin chakwakwiya a gaba.
Shin za a ɗaura auren Umar da Sakinaa? Zubaidaa zata koma gidan Umar? Idan ta koma
wanne irin zama ne za suyi da Sakinaa? Ya zaman Sakinaa zai kasance da Hamma Umar shin
har yanzu yana ƙaunarta ko kuwa? Ɓangaren Mubarak zai dawo gurin Sakinaa? Ya zamansu
zai ci gaba da Zaliha? Shin Hajiya zata warke har ta ɗauki fansarta ko kuwa ƙaiƙayi ne zai koma
kan masheƙiya? Ku biyoni a Book 2 domin amsa muku duka tambayoyinku. Wanda zai biya ga
yadda tsarin yake a ƙasa..
*Albishir ga masu karanta Littafin WANKA DA GARI mutum 20 ɗin farko da suka fara biya to na
musu rangwame akan su turo 400 kamar yadda na ce mutum 20 na farko don haka dama ce ga
duk waɗanda zasu fara biya kafin book 1 ya kammala, da zarar na kammala book 1 duk mai
buƙatar WANKA DA GARI zai biya kuɗi 700*
_Zaku iya turawa kai tsaye ta wannan account 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC_
Shaidar biya ta wannan number 08104335144
Mutanenmu na ƙasar Niger zasu turo da 500f na katin Moov ko Orange ta wannan layin
08104335144 idan kuma na kammala book 1 zaku turo 700f ne, Na gode.
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakina2024