Showing 21001 words to 24000 words out of 26600 words
Chapter 8 - WANKA DA GARI BOOK 1 COMPLETE by Fatima Sunusi Rabi'u .pdf
Ɓangaren da taje unguwa ce ta masu hali da rufin
asiri babu hayaniya sosai, kollon layin kawai take, da kin sauka saitin layin gida na uku mai
koren gate. Maganarsa ta ƙarshe a masarrafar sautinta, jan akwatinta tayi ta nufi gidan da take
ƙyautata zaton shi ne.
Tsaye tayi bakin gate tana ƙarewa gidan kallo, zuciyarta na aiyana mata anya gidan ne? Gida
ne mai ƙyau sosai duk da bai cika girma ba amma ya tsaru, ita da tasan mahaifinta ba mai hali
ba ne taya zai gina irin wannan gidan?
Numfashi taja tare da buga gate ɗin gidan, mai gadi ya leƙo, gaishe shi tayi,
"Don Allah gidan Malam Abdullahi bakanike nake nema." Shuru ya yi yana tunani sai ya ce,
"Nan gidan Alhaji Abdullahi ne, ban sani ba koshi ki ke nema."
"Nan dai ne aka ce mini in zo."
"To shugo ki tsaya nayi miki iso ko."
Babu musu ta shugo ta tsaya daga bakin gate ta ciki, shi kuma ya shiga cikin gidan.
Mintoci kaɗan ya dawo ya ce,
"Baiwar Allah ki shiga ya ce shi ne."
Hamdala tayi a fili ta fara taka ƙafarta zuwa ciki har zuwa lokacin ba ta daina mamakin yaushe
mahaifinta ya yi kuɗin gina gida haka har da mai gadi ba.
A hankali tayi sallama cikin madaidaicin parlourn wanda ya tsaru sosai da kujeru na alfarma da
ƙayataccen tv ta bango, harda ƙaramin dinning table, kai duk dai kayan more rayuwa na zamani
an tsara su daidai girman parlourn waɗanda suka dace da shi da kuma tsari.
Daga Abba har Umma zuba mata ido suka yi suna kallonta fuskokinsu ɗauke da mamaki, ita ma
su take kallo nan take kuma ta saki wani rikitaccen kuka tayo kansu da gudu bayan ta saki
akwatinta, jikin Abba ta faɗa tana wani rikitaccen kuka faɗi take, "Abba da Umma na tuba ku
yafe mini ko na sami sassauci ku taimaka ku yafe mini laifina ko zuciyata zata daidaita ina cikin
wani hali, nayi nadama wallahi Abbana na gane kuskurena."
Kuka take tamkar zata ƙarar da hawayen idaniyarta, Dukansu kallonta suke, a ka ce tsakanin
'ya da mahaifi ko mahaifiya sai Allah musamman uwa, nan take zuciyoyinsu su kayi sanyi
musamman da suka tuno ba laifinta ba ne, domin tun lokacin da Abba yayi istihara ya gane
wani babban ƙulli aka kullawa Sakinaa tun daga lokacin suke cikin addu'a Allah ya kwanceshi,
to Alhamdulillah komai yazo ƙarshe tsakaninsu ta dawo hayyacinta harta nemesu, ai kuwa dole
su godewa Allah gagara misali mabuwayi, hannu dukansu suka ɗaga sama suna godewa Allah.
A nan take ba su labarin zamanta da Mubarak da abinda ya faru a tsakaninsu da zamanta da
Hajiya duka bata ɓoye musu ba. Umma har da hawaye saboda kuka ta ce, "Sakinaa ƙaddararki
kenan daman Allah ya rubuta hakan ga kuma rabon yara a tsakaninku mun godewa Allah ma
da ta hanyar aure aka same su bata hanyar banza ba." Abba ya ce, "Wannan gaskiya ne, ita
kuma Hajiya Allah ya shiryeta idan mai shiryuwar ce idan kuma ba mai shiryuwa ba ce Allah ya
mana maganinta." Duka suka amsa da amin.
Abba ya ce, "Sakinaa mun yafe miki Allah ya yafe mu baki ɗaya." Rungumesa ta sake yi Umma
ta ce, "Allah mun gode maka da ka ceto mana 'ya daga cikin wancen mayuwacin hali." Nan
sukayi ta addu'a daga bi sani aka ɓige da hirar yaushe gamo.
Abba ya ce taje tayi wanka taci abinci tayi sallah ta kwanta tayi bacci tunda dare ya yi gobe sai
su ɗaura, ba don ta so ba ta miƙe don ta lafe jikin Ummanta. Ɗaki guda suka bata daman 3
bedrooms ne sai parlour da kitchen, sannan a ko wanne ɗaki akwai toilet.
Faɗawa tayi saman katifar dake dakin tana jin sabon wani farin ciki na baibayeta, iyaye babu
abinda ya kai su daɗi tabbas wanda ya ra sa su dole ya yi kuka. (Allah ya ƙarawa iyayenmu
lafiya da nisan kwana, waɗanda kuma suka rasa iyaye Allah yaji ƙansu amin).
Miƙewa tayi ta faɗa toilet wanka tayi tare da ɗauro alwala, bayan ta fito ta ga Umma ta shugo
mata da abinci da sauri ta amsheta tana mata sannu.
"Umma da ma kin bari da nayi sallah zan je kitchen ɗin na ɗauka."
"Kar ki damu kici ki samu ki kwanta ki huta." Murmushin jin daɗi tayi tare da furta.
"Na gode sosai Ummata."
Bayan fitar Umma ta buɗe akwatinta ta ciri rigar bacci da zani da hijab, bayan ta idar da sallar
isha'i da shafa'i da wuturi, ta cire zanin da hijab taci abincin Ummanta mai ɗan karen daɗi
wanda tayi missing shekaru kusan hudu kenan.
Washe gari tun asuba Sakinaa ta tashi ta gyara gidan fes, sannan tayi abin karyawa ta jera bisa
dinning. Abba da ya dawo masallaci ya ga tana jera kuloli ga gidan sai ƙamshin turaren wuta
yake ya ce, "Sakinaa daga zuwa sai fara aiki ba zaki bari ki huta ba?" Duƙawa tayi har kasa ta
gaishe shi ya amsa cikin fara'a, ita ma dariya tayi ta ce, "Haba Abba ai babu batun baƙunta."
Dariya ya yi tare da shafa kanta ya ce "Allah ya miki albarka." Ta amsa da amin tana jin farin ciki
wanda rabon da taji shi tun zamanin tana gida tare da su.
Bedroom ta koma tayi wanka daman tun kafin ta fara aikin tayi sallah, ta shirya cikin riga da
siket na atamfa, sannan ta fito parlour don har tara tayi. Ta gaishe da Umma ta amsa cikin fara'a
da tambayarta ya ta tashi ta amsa da lafiya ƙalau.
"Daga tashi kuma sai aiki?"
"Haba dai Umma to ai ba wani abu ba ne nayi, tuni na saba."
Tare su kayi breakfast, sannan suka dawo kan kujerun parlourn, ta kalli Abba ta ce, "Wai Abba
da yaushe kayi wannann gidan ni har yanzu mamaki nake na sha wuya a can tsohuwar
unguwarmu kowa ya ce bai san inda ka koma ba." Umma ta amsa da
"To wa ya kawo ki nan?" Ta sanar musu gidan redion su Hamma Umar Ta je da yadda su kayi
da shi.
Junansu suka kalla, kafin Abba ya ce.
"Bayan aurenki mun tsinci kan mu cikin baƙin ciki da takaici na irin abinda ki ka mana, ba mu
ɗauka asiri da tsafi ba ne jikinki sai daga baya inda muka gano wani ƙulli ne aka miki, nan take
muka duƙufa addu'a da neman miki tsari.
Hakan bai ɓata zumincin da ke tsakaninmu da ahlin Umar ba sai ma sabon zuminci da mu ka
kulla, ashe suma asalinsu 'yan jahar katsina ne. Mahaifinsa su biyar ne gurin iyayensu maza
huɗu mace daya, Alkasim Inuwa magaifin Umar shi ne babba a gidansu sauran ƙannansa ne,
gidansu sunyi karatu mai zurfi hakan yasa yawancinsu duk ma'aikata ne, shi kuma babban ɗan
kasuwa ne, Umar shine ɗa na uku gurin iyayensa sai dai biyun duk sun mutu shine kawai ya
rayu hakan yasa iyayensa ke ƙaunarsa sosai duk da bayan shi sun sake biyu suma duk ba rai,
sai dai sauran 'yan uwansa sun haifafa sosai suna da yawa. Zubaida ɗiyar ƙaramar ƙanwarsu
Alhaji Alkasim ce ita ce 'ya ta huɗu gurin mahaifiyarta, tunda ta taso take ƙaunar Umar har takai
da faɗawa kakaninsu tun suna da rai kakansu ya ce ko bayan ransa Umar ya auri Zubaida, duk
da dai shi Umar ɗin ba wani sonta yake ba, haka suka taso har zuwa yanzu da take matarsa,
wannan gida da ki ke gani Umar ne ya mallaka mini shi halak-malak har da komai da ke ciki
sannan ya buɗe mini babban shago ya zuba mini kayan hatsi da su manja da man gyada tare
da yara masu sayar mini duk kyauta sannan ya bawa Ummanki jari tana sayarda sarƙoƙi da
'yan kunnaye kuma sosai sana'ar ta amsheta.
Shuru Sakinaa tayi har sanda Abba ya kai aya, hawayen farin ciki ne ke zubo mata tabbas tayi
babban rashi wato rasa jarumi nagartaccen miji irin Hamma Umar. "Gaskiya naji daɗi sosai
Allah ya saka masa da alkhairi shima Allah ya ba shi mai yi masa." Suka amsa da amin.
Rayuwar gidansu tana mata daɗi sosai sai dai cikas guda da aka samu yadda Hamma Umar ko
yazo gidansu bai kula ta nunawa ma yake bai san da ita ba, abin yana mata ciwo sosai, duk
idan yazo zata yi masa magana na gaisuwa amma bai amsawa ko kuma ya amsa a ciki-ciki.
Kamar yauma yazo gidansu sanye yake cikin ƙananun kaya ya yi masifar kyau kamar a sace sa
a gudu, zuba masa ido tayi lokacin da suke magana da Umma wani irin maganaɗisun ƙaunarsa
ke fuzgarta, tabbas Hamma Umar ya kai duk yadda ake buƙata a wajen ɗa namiji, ta shagala
sosai da kallonsa har bata san lokacin da Umma ta bar parlour ba, sai jin saukar ruwa tayi a
fuskarta, a furgice ta dubesa, ruwan da yake sha ne ya watso mata, daure fuska ya yi sosai
kamar wanda bai taɓa dariya ba ya ce, "Kallon na mene ne har haka? Ya isa haka abeg."
Sosai taji kunya ta sadda kanta ƙasa, a hankali ta ɗago ta sake dubansa, gani tayi har ya miƙe
ya fita, da sauri tabi bayansa, yana ƙoƙarin shiga mota ta kira sunansa, "Hamma Umar!"
Tsayawa ya yi ba tare da ya juyo ba.
Ƙarasowa tayi hawaye ne ya wanke fuskarta.
"Don Allah Hamma Umar kayi haƙuri ka yafe mini wallahi na ga ne kuskurena Nayi nadama duk
da ban san na aikata ba amma na yarda KUSKURENA NE sannan tabbas nayi gudun gara ne
na faɗawa gidan zago. Nayi danasani Hamma Umar kai ne ka dace da rayuwar Sakinaa
sannan kai ne a bangon littafin labarin Sakinaa ka yafe mini ka karɓe ni a karo na biyu. Wani mugun kallo da ya aika mata ya saka ta daidaita natsuwarta, a hankali kuma tayi ƙasa da
kanta hawaye na zuba.
"Sakinaa ina so ki man ce da komai da ya taɓa faruwa a tsakanimu, ni tuni na man ce da komai
kuma ba na tunanin yanzu zan iya tuna cewa wani abu ya taɓa faruwa a tsakanimu don haka
kema kawai ki manta!" Yana ga ma faɗa ya shige motarsa tare da fuzgarta a gurin Sakinaa ta
zube tana kukan takaici. Ɓangaran su Hajiya kuwa. Mubarak ne da su Larah sai Zaliha zaune a cikin ɗakin da aka
kwantar da ita dukansu cike suke da damuwa, ganin yadda lokaci guda Allah ya mayar musu da
mahaifiya.
Larah ta goge hawayen da ke gangaro mata cike da tashin hankali ta ce, "Hajiya ako da yaushe
ni mai faɗa miki gaskiya ce a kan abinda ki ke amma baki jin maganata, baki jin shawara yanzu
ai ga irinta nan wa gari ya waya?"
Hawaye ne ke gangarowa fuskar Hajiya ba halin magana don bakinta ya karka ce, likitoci ma
sun tabbatar da ta kamu da cutar nan ta rabin jiki, ko motsi ba ta iyayi sai dai akwantar a
zaunar, kamar wani jariri. Amma zuciyarta duk da haka ba ta karye ba, cike take da turirin
ɗaukar fansa, ba hawaye take da kuka ko da nasanin abin da ya faru da ita ba, hawaye take na
yadda idan ta sami lafiya zata wulaƙanta rayuwar Zaliha, kai har Sakinaa bata jin zata bari
domin ta san har da haɗin bakinta akan abin Zaliha ta ce.
Mubarak yaja tsaki tare da miƙewa ya ce, "No gaskiya Hajiya abin nan ya ishe ni bazan iya ba!
Haba! Mu kenan kullum a cikin asibiti, nifa kin san ban jurar irin haka."
Hawaye ne ke ambali a fuskar Hajiya yaci gaba da cewa. "Wallahi kima dai na kuka don kukan
ba damuna zai yi ba, abinda ke gabana ma ishe ni zan nemar muku tikiti ke da Larah a wuce
dake India ko a dace." Kama hannun Zaliha ya yi su kayi waje wacce duk jikinta ya yi sanyi da
wannan lamari. Hajiya zuciyarta taci gaba da turirin ɗaukar fansa, tasan wannan abin ma da ya aikata Zaliha ce
ta saka shi, tunda da ace bata asirce mata yaro ba ba zai faɗa haka akan ta ba yarda Mubarak
ke matuƙar ƙaunarta, Larah ce ke ta rarrashinta duk tunaninta kukan nadama Hajiyar take....
_WATA MIYAR SAI A MAƘOTA, MUJE ZUWA..._
*Albishir ga masu karanta Littafin WANKA DA GARI mutum 20 ɗin farko da suka fara biya to na
musu rangwame akan su turo 400 kamar yadda na ce mutum 20 na farko don haka dama ce ga
duk waɗanda zasu fara biya kafin book 1 ya kammala, da zarar na kammala book 1 duk mai
buƙatar WANKA DA GARI zai biya kuɗi 700*
_Zaku iya turawa kai tsaye ta wannan account 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC_
Shaidar biya ta wannan number 08104335144
Mutanenmu na ƙasar Niger zasu turo da 500f na katin Moov ko Orange ta wannan layin
08104335144 idan kuma na kammala book 1 zaku turo 700f ne, Na gode.
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakina2024
_Gawurtattu uku 2024_
WANKA DA GARI...
©UmmuAffan.
*Book 1 Page 19-20*
Ina kuke mata? Mata nake magana waɗanda suka amsa sunansu na mata ba muna mata ba!
Kaya ne masu inganci waɗanda zai mai rabo ke samu. Ki buɗe bakin aljihu Hajiyata kiyi gyara
da ingantattun kayanmu na GHT muna da.
Royal jelly-karin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda.
Akwai Garlic oil _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji
sunbatu.
Muna da Ganoderma reishi _xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam
Yana gigita maxa.
Sannan akwai Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara
ya gyra skin yyi fresh.
Ba anan muka tsaya ba muna da irin su Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya
wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Da su Longzit-matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn
labari.
Ga Panicept_duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau.
Kuma akwai Sto care_ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara
da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu.
Da Female _masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace
in Sha Allah.
Duk abin da kake buƙata zaka samu daga GHT sayen nagari mai da kuɗi gida kai tsaye kayi wa
wannan number mgn domin haɗaku da sha yanzu magani yanzu wato Maman Amal GHT
08104335144
Shahararru goma a duniyar kayan mata Maman Zee ƙamshi and Kayan mata, duk wasu nau'i
na kayan mata na gargajiya da na zamani gumba tsumi tabaje zuma masu ƙyau da inganci ku
nemi maman zee ƙamshi an kayan mata a number kamar haka 0806 384 5136 Tana Bauchi
tana aika kayanta gari-gari Ƙasa-ƙasa. Sayen na gari mai da kuɗi gida.
*Masu buƙatar ɗaura musu tallah suyi mgn cikin farashi mai sauƙi.* A saman rubutu ko a ƙasa
ko wanne da farashinsa. Na gode.
Wace ce Hajiya?
Hajiya Ruma mahaifinta ƙasurgumin boka ne wanda yake sana'ar bokanci da tsafi, ita ce 'ya ta
biyar a gurinsa, yana mugun sonta saboda komai nasa ta biyo, wato ita ce tayo gadonsa.
Tuntana ƙarama take zuwa ɗakin tsafinsa tana ganin yadda yake komai harta gajesa, bayan
mutuwarsa taci gaba da komai, haka take ba arabi ba boko, Mahaifin su Mubarak kuwa ta haɗu da shine sakamakon wasu abokan hamaiyarsa da suka
kawo matashi akan tayi wani aiki da zai durƙufar da shi kasancewarsa ɗan siyasa, haka nan da
tsafinta ya nuna mata photonsa taji duk duniya babu wanda take so sama da shi, inda ta masa
wani surkulle da asirinta tasa mata sonta, haka suka yi aure, bayan zuwanta ta korar masa
uwargida, matarsa ta fari kenan, daman ba su haihu da uwargidansa ba, shekara guda ta haifi
Mubarak kuma tana sana'arta ta bokanci har zuwa lokacin. Sai dai shi Alhaji Sani mahaifinsu
Mubarak bai san da maganar bokancin ba to min ta rufe komi ta riga ta asirce shi.
Bayan Mubarak tayi Muhsin da gashi sai Larah, ganin irin dukiyar da Alhaji Sani ya tara domin
bayan siyasa yana kasuwanci hakan yasa ta masa abinda ya kashe shi har lahira, daga nan ta
rufewa 'yan uwansa baki ko gidan ba su taɓa zuwa ba, haka tare ni yaranta ba arabi sai dai
karatun boko sun yisa sosai kuwa har zuwa matakin Mesters. Duk a yaranta tafi son Mubarak
su kan su ƙannansa sun san da haka tun suna jin haushi har suka bari. Larah itace kawai ta
biyo mahaifinsu a halaye sauran kuwa duk Hajiya su ka biyo.
Sannan tunda tayi aure bata ƙara waiwayar gida ba sai ƙaninta Saminu kawai da suke tare
shima don yazo gidanta ne shine fa ta ba shi sana'a har ya yi aure shima ya tara iyali.
Hajiya tayi wata ajiyar zuciya bayan tuno wannan da tayi, rayuwa kenan yanzu ita ce ta koma
haka, ita kawai tasan irin zafi da raɗaɗin da take ji, domin ba ƙaramin ciwo take ji ba, amma ta
san na lokaci ne, tunda likitoci na kula da ita zata sami lafiya har tazo ta tagayyara rayuwarsu
Sakinaa. Tabbas tayi sake ɗan zaki ya girma, amma ita kan ta tsoran tsafin ta take, sai sun san
sun taɓo 'yar boka jikar boka kuma bokanya.
Wajensu Sakinaa kuwa, ta roƙi Abbanta yasa Umar ya samar mata Addimision ta fara
karatunta, ita ma burinta ta zama 'yar jarida kamar Hamma Umar.
Cikin ikon Allah kuma Abba na mishi magana ya nemar mata abin ku ga manyan ƙasa. Tun da
ta fara karatu take sosai ta man ce kowa da komai, tana girmama iyayenta tare da kyautata
musu.
Bazaka taɓa kallon Sakinaa ka ce wai ita ce ke da yara biyu ba, jikinta ya murje ta ƙara kyawu
da haske kyakkyawar yarinya matashiya, sai yanzu ne