Showing 15001 words to 18000 words out of 26600 words
Chapter 6 - WANKA DA GARI BOOK 1 COMPLETE by Fatima Sunusi Rabi'u .pdf
da ya yi niyya sannan zai
haihu to shi ke da rayuwarsa ma ko kuwa shi ke ba da haihuwar da zai zaɓi lokacin da yake so
sannan ya haihu? Hankalinta ya sake tashi lokacin da ta tuno hirar da suka taɓayi da Hamma
Umar, inda wata rana suna zaune ya kalle ta ya ce, "Wallahi Sakinaa yara suna burge ni, ina
sha'awarar na ga yara suna ta shawaginsu da wasansu cikin gidana." A lokacin ta ce,
"Chaf ka ce zaka tara yara da yawa?"
"In sha Allahu idan Allah ya ba ni zanyi farin ciki ko su nawa ne." Ta saka dariya.
"Lallai Hamma Umar ka ce mata huɗu zaka aje a gidanka?"
Murmushi ya yi tare da furta,
"Sakinaa kenan duk mace guda nake so ta haifa mini yaran nan ni ba ni da sha'awar tara mata
fiye da ɗaya."
"Lallai matar nan taka ta shigenge idan ita kaɗai zata haifa maka yara da yawa."
"To mene ne a ciki? Fatana dai Allah ya ba ni masu albarka waɗanda zan yi alfahari da su
watan wata rana."
Ta amsa da amin tana ma sa wani irin kallo, lokacin da ya ɗago suka haɗa ido ta sadda kai
ƙasa da sauri, matsananciyar kunya ta rufe ta....
08104335144
*Albishir ga masu karanta Littafin WANKA DA GARI mutum 10 ɗin farko da suka fara biya to na
musu rangwame akan su turo 400 kamar yadda na ce mutum 10 na farko don haka dama ce ga
duk waɗanda zasu fara biya kafin book 1 ya kammala, da zarar na kammala book 1 duk mai
buƙatar WANKA DA GARI zai biya kuɗi 700*
_Zaku iya turawa kai tsaye ta wannan account 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC
sai a tura shaidar biya ta wannan number 08104335144_
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakina2024
_Gawurtattu uku 2024_
WANKA DA GARI...
©UmmuAffan
*Book 1 Page 13-14*
Ina kuke mata? Mata nake magana waɗanda suka amsa sunansu na mata ba muna mata ba!
Kaya ne masu inganci waɗanda zai mai rabo ke samu. Ki buɗe bakin aljihu Hajiyata kiyi gyara
da ingantattun kayanmu na GHT muna da.
Royal jelly-karin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda.
Akwai Garlic oil _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji
sunbatu.
Muna da Ganoderma reishi _xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam
Yana gigita maxa.
Sannan akwai Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara
ya gyra skin yyi fresh.
Ba anan muka tsaya ba muna da irin su Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya
wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Da su Longzit-matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn
labari.
Ga Panicept_duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau.
Kuma akwai Sto care_ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara
da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu.
Da Female _masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace
in Sha Allah.
Duk abin da kake buƙata zaka samu daga GHT sayen nagari mai da kuɗi gida kai tsaye kayi wa
wannan number mgn domin haɗaku da sha yanzu magani yanzu wato Maman Amal GHT
08104335144
Shahararru goma a duniyar kayan mata Maman Zee ƙamshi and Kayan mata, duk wasu nau'i
na kayan mata na gargajiya da na zamani gumba tsumi tabaje zuma masu ƙyau da inganci ku
nemi maman zee ƙamshi an kayan mata a number kamar haka 0806 384 5136 Tana Bauchi
tana aika kayanta gari-gari Ƙasa-ƙasa. Sayen na gari mai da kuɗi gida.
*Masu buƙatar ɗaura musu tallah suyi mgn cikin farashi mai sauƙi.* A saman rubutu ko a ƙasa
ko wanne da farashinsa. Na gode.
Hawaye ne suka ɓalle mata lokacin da ta kammala tuno wannan zantuka, da haka suka isa
wani ƙaramin asibiti, bayan ya yi parking suka fito har zuwa lokacin a fusace yake. Kama
hannuwanta ya yi suka shiga ciki.
Wani likita suka gani da wasu 'yan mata biyu, bayan ya sallame su su Sakinaa ma suka shiga,
bin bayansu tayi da kallo ganin yadda ɗayar ke ɗin gishi, bayan sun zauna Mubarak ya sanar
da shi yana san ya zubda cikin jikin Sakinaa. Kallonta ya yi sosai sannan ya kalli Mubarak.
"Ita ma wannan cikin kayi mata? Amma a fuska kamar yarinyar ƙwarai duk da dai da kama ake
ƙota amma ba a gane abin da ke kan fuska, ko dai tilasta mata kayi?"
Gaban Sakinaa ne ya tsananta faɗuwa, ta zubawa Mubarak ido yayin da shima ita ya kalla. A
ɗan rikice, sannan ya kalli likitan muryarsa da alamun rashin gaskiya.
"Haba Doctor Mansir mene ne hakan? Amma sa nake na sanar da kai ɗaurin aurena kuma kai
ma kaje, ai kuwa labarin zuciya a tambayi fuska ko, sannan zaka kawo mini wata maganar
banza?"
Kallon Sakinaa ya sake yi "Ohkey na man ce wannan ita ce matar taka?"
"I," ya amsa masa a takaice. Jinjina kai ya yi sannan amsa.
"M.B ga shawara da zan baka." Da yake haka suke kiransa har abokansa, yaci gaba da cewa
"Wannan matarka ce ta sunna bai kamata ka zubda mata ciki ba." A harzuƙe Mubarak ya taso
"Ka ga malam, ba yau muka saba harkar nan ba zaka zubda ko kuwa muje wani wajen?" Cike
da tausayin Sakinaa ya amsa, wacce zuwa lokacin kuka take sosai gashi ta kasa musawa
Mubarak duk abinda ya yi ko taji haushi a zuciyarta to bazata iya nuna masa a fili ba.
Haka a ka shigar da ita wani ƙaramin ɗaki ya ciro kayan aikinsa sai lokacin ta sami bakin
magana, cikin hawaye ta ce, "Doctor ka tausaya mini don Allah kar ka zubar mini da ciki kamar
yadda ya bukata." Kallonta ya yi cike da tausayi tabbas tun farkon shugowarsu yaji tausayinta.
"Kar ki damu ni ma ba ni da niyyar cire miki amma dole na miki wani abun da zai ga kamar na
cire miki kema sai ki iya taknki." Numfashi taja tare da masa godiya sosai.
Mubarak ne ya shugo hannunsa rungume a ƙirjinsa yana ƙare musu kallon kafin ya furta,
"Wai Doctor Mansir me ka ke jira ne har yanzu?" Ajiyar zuciya Sakinaa ta saki yayin da kuma
Doctor ya ce "Aikin nake yi ka jiramu waje."
Fita ya yi kawai.
Nan ya mata allurar bacci ya ce, "Nan da awa guda zaki farka lokacin sai ki san ƙaryar da zaki
masa ni dai kawai na taimaka miki ne saboda hakanan naji kin ba ni tausayi." Godiya ta masa
nan kuwa ba a ɗauki lokaci ba bacci ya kwasheta.
Mubarak ya kallesa "ina ganin dai aiki yayi kyau?" Numfashi Doctor yaja bayan ya sami guri ya
zauna, "To muna saran haka amma gaskiya aikiin ya ba ni wahala."
"Kana nufin bai fita ba kenan?"
"No kawai dai ina sa ran ace ya fitan."
Shuru dukansu sukayi na wani lokaci kafin Doctor ya sake cewa, "Na mata allurar bacci ta sami
bacci yanzu." Miƙewa Mubarak ya yi tare da jefa masa kuɗi ya nufi ciki kinkimarta ya yi ya fita
Doctor ya bi su da kallo.
Bayan mota ya sakata shima ya zagayo ya shiga sannan ya ta da, kai tsaye gida suka wuce.
Sai dai Sakinaa farkowa tayi ta ganta a gida, da sauri ta shafa cikinta hawaye masu zafi suka
gangaro mata.
Haka rayuwar tacigaba da tafiya inda Sakinaa ke matukar daurewa da nuna masa bata da ciki
take komai kamar da sai dai ita kaɗai ta san wahalar da take sha.
Aka ce shi ciki ɗan duma ne ko an ɓoyesa idan lokacin fitowarsa ya yi to zai fito, hakan ta
kasance a gidan Sakinaa da Mubarak.
Lokacin da cikin Sakinaa ya shiga wata shidda tuni ya fito saboda ita ɗin mai girman ciki ce, duk
da ɓoyen da take da saka manyan kayan da suka mata yawa sai da Mubarak ya gane inda ya
ke ce mata "Me nake gani Sakinaa kamar ciki a jikinki?" Dabarcewa tayi ta fara kakkaucewa
inda ta ce, "Haba dai ni kaina kwana biyun nan na ga ina ta tumbi." Cike da rashin yarda ya ce ta sako
mayafinta tazo.
Babu musu tasa ta fito don bata daɗe da fitowa wanka ba, mota yaja su ita dai ƙirjinta tara-tara
kawai yake bugu, da haka har suka kai asibiti, gwajen farko ya nuna ciki ne da ita har wata
shidda, nan fa Mubarak ya dunga masifa wai a zubda, hawaye ne ya gangaro a fuskar Sakinaa
ta ce, "Bazai yuwu ba!" Ta furta da ƙarfi. Kallonta ya yi cike da mamaki, "Me ki ke nufi?" "abinda kunnuwanka ya jiye maka, Mubarak ina
so ka sani bazan yarda ka zubda mini ciki a wannan karon ba, duk da daman shine babu inda
yaje."
Sosai yake dubanta ganin yadda take masa masifa, matsowa ya yi kusa da ita sosai. "Sakinaa
ni ki ke faɗawa ba za a fitar da cikin ba?" Gyaɗa masa kai tayi cike da rashin tsoro,
"Ƙwarai kuwa Mubarak ina so ka sani sai dai ka kashe ni akan cikin nan domin bazan yarda ba."
Ɗaga hannu ya yi ya zuba mata wani lafiyayyen mari, da sauri ta riƙe kuncin tana kuka, likitan
ne ya ce, "Haba bawan Allah mene ne haka ne? Tunda ta ce bata so ka bar mata a bin ta
mana, ba sai kabarta ba." Duk a tunanin likitan ko budurwarsa ce ya yi wa ciki.
Juyawa Sakinaa tayi ta fice daga office ɗin shima yabi bayanta, kai tsaye ficewa tayi daga
asibitin tana kuka sosai. Mota ya shiga yabi bayanta gabanta ya yi parking.
"Shugo ciki." Banza ta masa zata juya, ya daka mata tsawa ba don taso ba ta shiga motar ya
fuzgeta sai gidan Hajiyarsa.
Suna isa ya yi parking, fitarsa ya yi ransa a matukar harziƙe. Tana hawaye tabi bayansa, ko
sallama babu ya shiga kai tsaye.
A ruɗe Hajiyar take kallonsa kafin ta iya furta, "My son lafiya kuwa?" Zaunawa ya yi daidai
shugowar Sakinaa ya ce, "Daga asibiti muke wai ciki ne da ita suka ce." Nan take Fuskar Hajiya
ta cika da annuri ta washe baki.
"Kai Alhamdulillah amma nayi farinciki aure ya yi albarka nima na kusan zama kaka zan sami
jika."
A ƙufule ya kalleta. "Haba Hajiya nifa cikin nan ba wai ina maraba da shi ba ne nazo ne don
kisan hanyar da za a bi a cire mata shi."
Numfashi taja, "Haba Mubarak kyauta ce fa Allah ya baka don Allah kabar wannan maganar, ko
ɗaya ne ai ka bari ta aifa kafin ku fara tsarin iyali."
Ta janyo Sakinaa kusa da ita tana mata sannu tare da bata haƙuri.
Iya ƙuluwa ya ƙulu, miƙewa ya yi ransa a ɓace ya ce, "Tunda haka ki ka ce to na bar miki ita
idan ta haihu ta yaye abin ta bar miki sai ta dawo." Ya fita a fusace, kuka Sakinaa ta fashe da
shi yayin da Hajiya da Laurah suke ba ta baki akan tayi haƙuri.
Gaskiya ba laifi sosai Hajiya da ƙannan Mubarak ke kula da Sakinaa tabbas suna ba ta kulawa
don suna son cikin sosai, kome ta keso shi suke mata kuma cikin so da jin daɗi. Tun daga ranar
da Mubarak ya tafi ba ta sake ganinsa a gidan ba har zuwa lokacin da ta haifi kyakkyawar
yarinyarta a asibiti mai kama da Sakinaa sak. Tabbas Hajiya da sauran dangin Mubarak sunyi
murna.
Bayan mun koma gida aka kira Mubarak aka sanar masa na haihu babu abinda ya ce saidai ya
turo makudan kuɗaɗe akan ayi duk abinda ya dace, sosai Sakinaa tayi kuka a ranar, iyayenta
suka faɗo mata, bata taɓa kewarsu irin ta ranar ba.
Bata san dalili ba amma tunda tayi aure ba ta taɓa tunosu ba sai ranar, sannan kuma sam na
mance da su. Yanzun ma da ta tunosu gabanta ne ke wani mugun zafi da turiri nan take kuwa
ciwon kai mai tsananin zafi ya rufe ta.
Zaliha ce ta faɗo mata a zuciya, tun bayan lokacin da suka zana waec da neco rabonta da ita,
wayarta ta ciro ta danna lambarta ringing biyu ta ɗauka, dukansu shuru ya biyo baya, zuwa cen
Sakinaa ta daure ta maganantu "Assalamu alaiki!" Amsawa tayi Suka sake shuru. Can dai ta ce,
"Sakinaa manya yau an tuno mu ne?" Hawayen da suka gangaro mata ta goge sannan cikin
sassauta murya ta ce, "Zaliha daman na haihu ne jiya."
Cike da murna ta ce, "Kai barka Sakinaa na tayaki murna Allah ya raya me aka samu?"
"Mace.!"
"To Allah ya raya sai nazo." Sallama muka yi nayi zugun da waya a hannuna tabbas yadda
Zaliha ta amshe ni a waya ban taɓa zato ba. Na ɗauka ma ko wayata ba zata ɗauka ba sai ta
shayar da ni mamaki.
Ɓangaran Zaliha kuwa, wayar tabi da kallo jikinta a sanyaye ta furta, "Tabbas rabo shi ne ya kai
Sakinaa gidan Mubarak balle rabon 'ya mace shi mai zafi ne, wani kuma baya taɓa aihuwar ɗan
wani."
Daman shiri take domin a ranar ne bikin Hamma Umar da Zubaidaa. Bayan tayi wa mahaifiyarta
sallama ta wuce gidansu Sakinaa domin tare za su tafi da Umma.
Bayan sun gaisa take sanar mata Sakinaa ta haihu, ƙura mata ido tayi "A ina ki ka ji Zaliha?"
"Ita ta ce da kan ta ta kira ni." Numfashi Umma taja tare da cewa Allah ya raya, Sannan suka
wuce gidan bikin.
Tabbas anyi biki na yaran gata an kashe kuɗi sannan anci ansha zo kuga Hamma Umar Faruuƙ
saboda tsabar kyau kamar ka sace sa ka gudu, ya yi kyau abin ku ga masu kyan, ita kanta
Zubaidaa babu laifi tayi kyau sosai.
Ba zaka taɓa gane yanayin halin da Hamma Umar yake ciki ba, kawai dai shi daman haka yake
cikin farin ciki ko a kasin hakan ba cika ganewa ake a fuskarsa ba sai dai fuskar nan tasa na
cike da kwarjini da annuri.
Bayan kammala biki su Zaliha suka koma gida sai fatan Allah ya ba wa amarya da ango zaman
lafiya.
A ranar da safe Sakinaa ce zaune ita da Larah suna hira su kaji an saka guda ana sanarwar
auren Umar Alkasim Inuwa da Zubaidaat Bello Inuwa, A tv ƙirjin Sakinaa ne ya buga da karfi,
sake ƙwalalo ido tayi tana kallon photonsa da amaryarsa yadda suka yi wani fitinannan kyau.
Larah ta ce "Allah sarki Umar gayen nan ya yi wallahi tare muke karatu da shi amma shi yanzu
har ya yi mester kin san dan jarida ne ance yana aiki gidan redion taraiya na Kaduna wallahi ina
mugun son gayen nan, shiyasa na sayi redio saboda shi kawai nike jin shirye-shiryensa
musamman news da yake na turanci karfe 2 na rana uhmmm wallahi idan kina saurara har wani
lumshe ido zaki dunga yi saboda daɗin muryarsa ga iya turanci kamar baƙin bature.
Jiki a sanyaye Sakinaa ta kalleta, "Daman ya gama karatu ne?"
"To har ya fara aiki wannan gayen da ki ke gani ƙwararre ne a fagen aikisa ɗan jarida ne
jajirtacce kuma na gari wallahi naso gayen nan ga shi ya yi aure abin shi."
Shuru tayi inda Larah taci gaba da yabon Umar in ban da ligude babu abinda zuciyar Sakinaa
ke yi.
Zaliha tazo sosai Sakinaa ta cika da mamaki, inda take tambayarta daman tasan gidan? I
kawai ta amsa mat a takaice ganin kamar bata son mata maganar ta rabu da ita, don neman
shiri take ita kawaice zata iya kalla tamkar kalla 'yar'uwarta.
Haka ta jera kullum sai tazo har akayi suna abin ya yi wa Sakinaa daɗi domin ranar sunan har
da ƙawayensu na makaranta duk ta gayyato wanda su kai aure da 'yan mata.
Yarinya ta amsa sunan Hajiya wato Rumasa'u sai ake kiranta da Yusra.
Washe garin suna da wuri Zaliha tazo da ita a kayi komai na suya, domin ƙaton Sa da raguna
biyu da Hajiyar ta yanka a sunan Yusra.
Ba laifi Hajiyar ta yi wa Sakinaa kaya haka danginsu da ƙawayenta sosai suka yi mana ƙyautar
kaya suma ƙawayensu Sakinaa da suka zo ba laifi sun yi nasu haka Zaliha ta mata abin arziƙi,
da zata tafi ita ma ta haɗata mata sha tara ta arziƙi, kin amsa tayi sai da na haɗata da Hajiya
sannan ta amsa muka yi sallama. Haka Sakinaa taci gaba da renon 'yar ta cike da kulawar Hajiya har suka shekara guda, babu
Mubarak ba ɗuriyarsa zuwa lokacin tuni Yusra tayi wayau har tafiya ta iya don yarunya ce mai
kazar-kazar ga wayau.
Kwatsam wata rana suna zaune a parlour suna kallo sai ga sallamar Mubarak abin ya ba su
mamaki duka suka bi shi da kallo zuba wa Sakinaa ido ya yi yana kallonta kai tsaye kuwa
gurinta ya nufo ko kunyar su Hajiya bai ji ba ya wani zauna kusa da ita sosai yana aika mata
wani kallo ƙasa-ƙasa....
*Albishir ga masu karanta Littafin WANKA DA GARI mutum 10 ɗin farko da suka fara biya to na
musu rangwame akan su turo 400 kamar yadda na ce mutum 10 na farko don haka dama ce ga
duk waɗanda zasu fara biya kafin book 1 ya kammala, da zarar na kammala book 1 duk mai
buƙatar WANKA DA GARI zai biya kuɗi 700*
_Zaku iya turawa kai tsaye ta wannan account 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC_
Shaidar biya ta wannan lamba 08104335144
#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakina2024
_Gawurtattu uku 2024_
WANKA DA GARI...
©UmmuAffan
*Book 1 Page 15-16*
Ina kuke mata? Mata nake magana waɗanda suka amsa sunansu na mata ba muna mata ba!
Kaya ne masu inganci