Showing 9001 words to 12000 words out of 26600 words

Chapter 4 - WANKA DA GARI BOOK 1 COMPLETE by Fatima Sunusi Rabi'u .pdf

ya ce, "Hajiyata Sakinaa ba kowa ba ne ubanta, hasalima yarinya ce ƙarama bata wace
16years ba, ba kowa ba ne ubanta sai matalauci, sai dai ina son ki san wani abu guda, idan ban
same ta ba wallahi mutuwa zan yi." Kallon ɗan nata tayi cikin so da kauna, wannan wacce irin jarabawa ce ɗan ta zai kamu da son
'yar matsiyata? Amma ba tayi ƙasa a gwiwa ba ta ce, "tashi muje gidan." haka ta tasa shi a
gaba har ƙofar gidan a tsiya ce ta kalli gidan ita unguwarma sam bata mata ba,
"Yanzu Mubarak ka rasa gidan da zaka ɗauko aure sai a unguwar matsiyata, don Allah kabar
wannan maganar 'yar wannan akurkin gidan za ka ce kana so? Gabaɗaya yankin nan bai mini
ba."
Ya ce"Hajiya kina so ki ra sani ko? To ina son ki sani 'yar wannan akulkin gidan ce farincikin ɗan
ki, tunda dai wanka da gari ba shi maganin yunwa sai an sha." Numfashi taja cike da ƙyanƙamin

layin.
Fita tayi ta nufi cikin gidan, Umma na zaune kan kujera 'yar tsugunnau tana firfita wutar itace a
mirhu. Sakinaa kuwa ta fito kenan cikin shirin islamiyya Abba yana gareji.
Ko sallama Hajiya ba ta yi ba, sosai suka tsorata. Umma har da salati, kallonta Hajiyar tayi cike
da kyama ta ce, "Gurin Sakinaa nazo." Daga Sakinaar har Umma ido suka zuba mata cike da
mamaki, duk a zatonsu ba musulma ba ce jin ba tayi sallama ba, kuma ko hijabi ko gyale babu
a jikinta kuma sai su kaji tayi hausa. Cike da takaici Umma ta ce, "Malama lafiya gidan musulmai fa ki ka shugo." Harara Hajiya ta
ban ka mata ta ce, "Ai ina sane sallamar ce bata da ce da na muku ba, domin baku isa ba shi
ya sa."
Kallonta suka ci gaba da yi ta sake cewa tambayar Sakinaaa tazo nema. Ganin kallon da
Umma take aika wa yarinyar da ke tsaye a gurin yasa Hajiya ta ga ne ita ce Sakinaa, kama
hannuwanta Hajiya tayi suka fita waje, Umma kuwa saboda mamaki kasa cewa uffan tayi sai
raka su da ido. Hajiya ba ta tsaya da Sakinaa ko ina ba sai bakin mota. Mubarak na ganinsu ya fito yana washe
baki, tana ganinsa gabanta ya buga da ƙarfi har lokacin Hajiya bata saki hannun Sakinaa ba.
Mubarak zubawa Sakinaa ido ya yi ita ma ta zuba ma sa ido.

Yayin da Hajiya ke ta wasu 'yan surkullenta da hannun Sakinaa lokaci guda, Sakinaa taji kan ta
ya mata wani nauyi lunshe idanuwanta ta fara zuwa wani lokaci tayi luuuw zata faɗi da sauri
Mubarak ya ruƙota jikinsa. Hajiya ta ce, "Aiki ya yi kyau shi ya sa nace maka ko ɗiyar shugaban
ƙasa ka ke so zaka samu in dai ni ce uwarka." Murmushin farin ciki ya yi ya ce, "Shi ya sa nake
ƙaunarki Hajiyata, tsafinki yana aiki kobme nake so kina mini gaskiya naji daɗon gadon nan da
kika yi na mahaifinki." Murmushi kawai tayi ta dafa saitin zuciyar Sakinaa wajen minti biyu
sannan ta dafa saitin zuciyar Mubarak. Dariya su ka yi gabaɗaya sannan ta bubbuga jikin
Sakinaa nan take ta farko zata kurma ihu Mubarak ya yi saurin ɗaura hannunsa saman leɓenta,
nan take tayi shuru sai ta zuba musu ido.
Hajiya ta ce, "Sakinaa ina son ki shiga cikin zuriata hakan ba zai samu ba sai kin amince da
auren ɗana Mubarak ko me ki ke so za muyi miki abinda ma yafi wanda iyayenki ke miki."
Shuru tayi tana kallonsu gabanta ya tsananta bugawa. Mubarak ya ce"Ina ƙaunarki Sakinaa
kema kina so na?" A hankali ta buɗe baki za tayi magana sai suka jiyo muryar Zaliha na kiran
Sakinaa.
Daidai ƙarasowar Zaliha Sakinaa ta buɗe baki ta ce.
Ta ce, "Ina sonka nima kuma zan aure ka." Hajiya da Mubarak suka kalli juna su kai murmushi.
Zaliha kuwa dafe ƙirji tayi tana kallon Sakinaa kafin ta ce "Sakinaa lafiyarki kuwa?"
Kallonta Hajiya tayi ta ce, "Wace ce ke?" Cikin rawar murya ta ce "Ni ƙawarta ce." Hajiya zatayi
maganantu sai ga Abba shi da Hamma Umar gurin, suka ƙara so har da Umma, wacce jin
Sakinaa shuru ta fito domin ta ga ko lafiya.
Abba ya ce, "Sakinaa Zaliha me ku ke a nan?" Shuru dukansu su ka yi suna kallon-kallo, a nan
Umma ta sanar masa abinda ya faru, cike da mamaki ya kalli Hajiya kafin ya kalli Sakinaa ya
ce, "Zo ki wuce." Kasa ɗaga ƙafarta tayi tana son bin umarnin Abbanta amma ta kasa.
Murmushi Hajiya tayi ta ce, "Kai malam ka ke kowa, to bari kaji ɗana ne gashi nan Sunansa
Mubarak, ta nuna sa taci gaba da cewa "shi ne ke son 'yar ka bayan ma ya nace me za mu yi

da 'yarka yana sonta kuma cikin satin nan nake son a ɗaura musu aure."
Cike da tashin hankali suka bita da kallo Abba zai yi magana Hamma Umar ya ce, "Wannan
wanne irin hauka kike, ke kuwa matar nan kina da cikakken hankali da tunani? A wanne garin
mahaukatan ake haka?" Abba ya ce, "Gaskiya da dai sauƙi Ummaru, to ina son ki sani bazan
ba ɗanki 'yata ba domin daga ke har ɗan naki ban ga kuna da alamun tarbiyya ba, ke barama
kiji me kankat nawa 'yata miji lokaci kawai nake jira a ɗaura mata aure."
Sakinaa ce ta kalli mahaifinta a rikice ta ce, "Ka ba da ni kuma Abba? Ni dai ban so wannan
nake so." Ta nuna Mubarak daga Abba Umma Hamma Umar Zaliha ido suka kyalalo suna
kallonta.
Hajiya da Mubarak kuwa murmushi suka yi, Hajiya ba ta ce komai ba ta kama hannun Mubarak
suka koma mota, bayan sun shiga Mubarak ya ce, "Hajiya ya na ga haka?" ta ce "kai dai ja
mota mu tafi Sakinaa da kan ta zata nemeka."
"Amma ban sanar da ita inda nake ba."
"Kai dai muje gobe zaka dawo....
08104335144


#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakina
_Gawurtattu uku 2024_


WANKA DA GARI...


©UmmuAffan


*Book 1 Page 9-10*


Ina kuke mata? Mata nake magana waɗanda suka amsa sunansu na mata ba muna mata ba!
Kaya ne masu inganci waɗanda zai mai rabo ke samu. Ki buɗe bakin aljihu Hajiyata kiyi gyara
da ingantattun kayanmu na GHT muna da.
Royal jelly-karin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda.
Akwai Garlic oil _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji
sunbatu.
Muna da Ganoderma reishi _xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam
Yana gigita maxa.
Sannan akwai Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara
ya gyra skin yyi fresh.

Ba anan muka tsaya ba muna da irin su Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya
wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Da su Longzit-matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn
labari.
Ga Panicept_duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau.
Kuma akwai Sto care_ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara
da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu.
Da Female _masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace
in Sha Allah.
Duk abin da kake buƙata zaka samu daga GHT sayen nagari mai da kuɗi gida kai tsaye kayi wa
wannan number mgn domin haɗaku da sha yanzu magani yanzu wato Maman Amal GHT
08104335144


Shahararru goma a duniyar kayan mata Maman Zee ƙamshi and Kayan mata, duk wasu nau'i
na kayan mata na gargajiya da na zamani gumba tsumi tabaje zuma masu ƙyau da inganci ku
nemi maman zee ƙamshi an kayan mata a number kamar haka 0806 384 5136 Tana Bauchi
tana aika kayanta gari-gari Ƙasa-ƙasa. Sayen na gari mai da kuɗi gida.

*Masu buƙatar ɗaura musu tallah suyi mgn cikin farashi mai sauƙi.* A saman rubutu ko a ƙasa
ko wanne da farashinsa. Na gode.



A ɓangaren su Abba kuwa Sakinaa na ganin su Mubarak sun tafi ta saka kuka, da yaja motar
kuwa bin bayansu tayi Hamma Umar ne ya kamota, kuka take sosai da haka suka shiga cikin
gida.
Umma saboda takaici rufe Sakinaa tayi da bugu Abba kuwa zurum ya yi yana tunan. Bai taɓa
hasaso ko tunanin Sakinaa za tayi haka ba, ɗan yau kenan da baka shaidar shi, sai ya baka
kunya a idon duniya. Yanzu ga shi ya ɗau alkhawarin bai ma Umar ita ga shi za ta ba shi kunya.
Babu wanda ya kai Umar tashin hankali don suna shugowa ya musu sallama ya tafi gida kawai. Allah ne ya kai sa gida lafiya domin gudun da yake ya wuce ƙa'ida ga shi baya cikin haiyacinsa,
bai san ma ya aka yi yazo gidan ba, domin tunaninsa fita ya yi a ƙwaƙwalwarsa, yana parking
ya fito ko motar bai iya rufewa ba. Yana shiga Parlour kuwa ya zube yana wani irin numfashi da
kakarin amai. Su Dad daga sama suka farajin kakarin aman sa sun ji tsayuwar motarsa amma suka ji shi
shuru bai hawo sama ba. Da sauri suka fito ai hango sho su ka yi zube yana amai, da sauri
suka ƙarasa, tuni Mummy ta ruɗ nan ta fara kuka ganin aman jini yake. Dad ma hankalinsa ya
tashi rungumesa ya yi yana tambayarsa abinda ya faru, ya kasa magana sai saitin zuciyarsa da
yake nuna musu zuwa can ya yi luww! Ya zube jikin Daddy a sume.
Mummy ta saki wani rikitacciyar ƙara mai haɗe da sautin kuka ta kurma ihuw. Daddy ne ya yi
ƙarfin halin ɗauko ruwan sanyi ya zuba masa amma ko ɗan yatsansa bai yi motsi ba, nan fa

suka sake ruɗewa, Da ƙyar Daddy ya iya cicciɓar Umar don shiɗin cikakken namiji ne ga tsayi
ga shi kuma ƙaƙƙarfa, sai da Mummy ta riƙe ƙafafuwansa shi kuma ya riƙe can wajenuwar jikin
da kai sannan suka nufi harabar gidan, cikin mota suka saka shi Mummy ta shiga bayan tare da
ɗaura kansa bisa cinyarta tana ta kuka shi kan sa Daddy ƙarfin hali yake da haka yaja motar
suka nufi asibiti.
Suna isa aka ɗauko irin kujerar nan ta tura marasa lafiya a kai aka ɗaurasa suka nufi ciki, nan fa
Lokitoci suka fara ba shi taimakon gaggawa.
A gidansu Sakinaa kuwa rigima sabuwa domin haƙiƙancewa tayi ita fa Mubarak take so.
Umma dukanta take amma bakin yaƙi mutuwa don Umma ba ta da haƙurin irin haka.
"Don ƙaniyarki mu muka haifeki ba ke ki ka haifemu ba, da zaki ce ba zaki bi umarninmu ba."
Cikin kuka ta ce, "Wallahi Umma ko kashe ni zaki yi bazan daina ce miki Mubarak nake so ba."
Saitin bakin Umma ta buga nan kuwa ya fashe Sakinaa ta saki wani gigitaccen kuka duk da
haka ba ta fasa cewa Mubarak take so ba. Abba ne ya jenye Umma daga bugun da takewa Sakinaa ya ce, "Rabu da ita Hadiza kanta
tamawa mu dai take gayawa irin waɗannan kalaman ko, duk wanda yaƙi ji ai ku to ba zai ƙi gani
ba, duniya ce ta ishi kowa riga da wando."
Bayan wucewarsu Zaliha ta din ga kallon Sakinaa rai ɓace ta ce "Yanzu Sakinaa saboda wani
banza can ki ke wa iyayenki wannan cin mutuncin? Abinda baki taɓa ba, duk gatan da iyayenki
ke miki ki rasa da abinda zaki saka musu sai na butulcewa ina ji miki tsoran wataran ki girbe
abinda kika shuka." Miƙewa Sakinaa tayi cike da bala'i.
"Ina ruwanki, me ya shafeki? Nayi ɗin iyayenki ne ko nawa? Daƙiƙiya wawiya kawai." Zaliha ta
ce, "Kai ni ki ke zagi haka Sakinaa? Ai gaki nan babbar daƙiƙiya marajin maganar iyayenta,
akwai wawiya da ta fiki?" Ai kafin ta rufe baki Sakinaa cikin zafin nama ta kai mata bugu a baki
Zaliha ma ta ce ba ta isa ba nan suka fara danbe na bala'i. Sai da Abba ya shugo ya raba su ya ce, "Zaliha rabu da ita ai abinda mutum ya shuga shi yake
girba, tayi lokacinta ne, wata rana sai labari, waɗanda suka yi abin da yafi nata ma yanzu ina
suke?" Haka ya kama Zaliha suka fita, Sakinaa kuwa ko ajikinta wai an tsikari kakkausa, zama
tayi tana zan tsaki Mtsuw ta ce A bayyane "Wallahi ba wanda ya isa ya raba ni da Mubarak ina
son sa kuma sai na aure shi."
A can asibiti kuwa an samu Umar ya farfaɗo sai dai da sunan Sakinaa a bakinsa, ita kawai yake
kira Likita ya sanar da Daddy tabbas a kawo Sakinaa domin sun masa allurar bacci suna so da
ya farko ya ganta idan ba haka ba kuwa akwai matsala. Hankalin a tashe Daddy ya nufi gidansu
Abba, ya sanar masu duk kan abinda ya faru. Umma kuka kawai ta fara Abba ya fara sallallami
hawaye kwance a idonsa.
Ɗkin Sakinaa Abba ya nufa, kwance ya isketa tana hawaye tana ganinsa ta juya masa baya
cike da mamaki Abba yake kallonta kafin ya ce, "Sakinaa Umar yana asibiti babu lafiya shi ne
na ce ki shirya muje."
Turo baki gaba tayi cikin halin ko in kula ta ce, "Ni Abba babu inda zani." Buɗe ido ya yi yana
kallonta kafin ya iya furta. "Sakinaa ni mahaifinki Mamal Abdullahi Bakanike ki ke faɗawa
wannan maganar mai zafi da ɗacin furzarwa, kina da hankali kuwa?"
Banza ta masa tana ƙunƙunai abin ya ɓata wa Abba rai bai san lokacin da ya kwasa mata mari
ba, riƙe kuncinta tayi tare da sakin wani rikitaccen kuka ta ce, "Ni wallahi babu inda zan je."

Jin kukanta Daddy da Umma suka shugu. Daddy da bai san wainar da ake toyawa ba ya yi
tambaya, nan suke sanar ma sa duk abinda ya faru, kallonta ya yi "Sakinaa me ke damun ki
iyaye ba abin wasa ba ne, sam."
Ko ƙala ba ta ce ma sa ba, sai harare-harare da take. Daddy ne ya ce, "Tunda ba za ta ba shi
ke nan." Lallaɓa ba irin wacce Abba baiwa Sakinaa ba taƙi, mai haƙuri bai iya fushi ba haka ya
rufeta da bugu amma ko gezai ba tayi ba, akan bata zuwa. Daddy ne ya bawa Abba haƙuri
sannan suka tafi duka asibitin. Ko da Umar ya farfaɗo ya ga su Abba kuka ya saka ya ce, "Abba ka mini alk'awarin zaka ba ni
Sakinaa don Allah ka bata haƙuri kar ta guje ni ita ce FARIN CIKINA."
Abba da Umma me za su yi ba kuka ba. Abba ya ce, "Umar tabbas na maka alƙawarin baka
Sakinaa amma ban taɓa tunanin ko kawo za taƙi bin umarni ni ba ɗan yau ne ka haifesa amma
baka haifi halinsa ba tabbas Sakinaa ta ba ni mamaki amma duniya ce ta isheta riga da wando
har da zanin ɗaurawa." Hawaye Umar yake yana danne saitin zuciyarsa tabbas Allah ne ya dasa masa ƙaunar Sakinaa
ba shi ne ya sawa kan sa ba.
Haka Umar ya yi jinyar kwana biyu yaji jiki sosai, amma Sakinaa ba ta zo ba, Zaliha tana zuwa
tare da Umma ta tausayawa Umar sosai har kuka take idan suka je.
Bayan sun koma gida. Daddy ya ɗauki Mummy da Umar suka je gidan Abba, don Umar ya
matsa yana son ganin Sakinaa. Ranar da suka je suka iske durama domin Mubarak ne yazo
Abba yanawa Sakinaa magana taƙi ji wai lallai sai tabi Mubarak, wasu zafafan hawaye ke
zubowa a fuskar Hamma Umar, ganin yadda Abba yake dukan Sakinaa yasa yaje ya riƙeshi ya
ce, "Please Abba rabu da ita indai don ni ne wallahi daga yau na haƙura da Sakinaa ka bata
wanda take so, ba zan so na auri Sakinaa amma zuciyarta tana gurin wani ba, na haƙura
Abba."
Gabaɗaya zuba ma sa ido su kai cike da tausayi kowa na hawaye, ɗaga Sakinaa ya yi ya ce,
"Sorry Princess Abba zai baki wanda ki ke so, kwantar da hankalinki ƙanwata."
Daddy ya ce, "Allah na gode maka da ka ba ni yaro adali wanda yasan ya kamata, tabbas
abinda kayi shine daidai Umar masoyin gaskiya shine ke iya sadaukar da farin cikinsa domin
farin cikin abinda yake so, wannan shine so na haƙiƙa wanda babu gauraye ko algus a cikinsa."
Abba ya dafa Umar ya ce, "Allah ya maka albarka Umar tabbas Sakinaa ta ba ni kunya, amma
kan ta tabawa ina roƙon Allah ya baka juriya da hakurin rashinta ya kuma zaɓa maka mata ta
gari." Hawaye ne suka gangaro a fuskarsa ya ce "Amin Abba."
Juyowa Abba ya yi ya kalli Mubarak Ya ce, "Ina so ka turo iyayenka yau ɗin nan su kawo sadaki
kawai nake buƙata dubu Ashirin gobe Juma'a a masallaci za a ɗaura muku aure. Ba na ƙaunar
wannan butulun yarinyar ta ƙara wuce gobe a gidana."
Ai daga Sakinaa har Mubarak murmushi a ka ga suna yi. Mubarak ya ce, "To na gode bari naje
na sanar musu." Ya kalli Sakinaa suka sake yin murmushi ya fice. Dukansu kasa magana su ka
yi abin ya ba su al'ajabi haka Sakinaa ta wuce ɗakinta cikin murna har da tsalle.
Daddy suka musu sallama jiki a sanyaye suka fita. Abba da Umma ba wanda ya iya magana
dukansu sun yi jigum-jigum.
Zaliha ce ta nufi ɗakin Sakinaa wacce ke ta faman haɗa kayanta waje guda na tafiya ɗakin miji,
don har a zuciyarta ta ƙosa safiyar gobe ta waye.
Kallonta tayi galala ta ce, "Sakinaa wai kan ki guda kuwa?" Ba ta waigo ba ta ce, "To duba da

ƙyau dai, idan kuma na haɗa shi da naki ne to?" Zaliha ta riƙe baki cike da mamaki kafin ta ce,
"Sakinaa zaki yi kuskure babba kuwa kinƙi bin umarnin iyayenki ba abu me sauƙi ba ne, ki dawo
haiyacinki Sakinaa. Tsuwww Sakinaa taja tsaki ba ta kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login