Showing 18001 words to 21000 words out of 26600 words

Chapter 7 - WANKA DA GARI BOOK 1 COMPLETE by Fatima Sunusi Rabi'u .pdf

waɗanda zai mai rabo ke samu. Ki buɗe bakin aljihu Hajiyata kiyi gyara
da ingantattun kayanmu na GHT muna da.
Royal jelly-karin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda.
Akwai Garlic oil _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji
sunbatu.
Muna da Ganoderma reishi _xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam
Yana gigita maxa.
Sannan akwai Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara
ya gyra skin yyi fresh.
Ba anan muka tsaya ba muna da irin su Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya
wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Da su Longzit-matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn
labari.
Ga Panicept_duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau.
Kuma akwai Sto care_ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara
da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu.
Da Female _masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace
in Sha Allah.
Duk abin da kake buƙata zaka samu daga GHT sayen nagari mai da kuɗi gida kai tsaye kayi wa
wannan number mgn domin haɗaku da sha yanzu magani yanzu wato Maman Amal GHT

08104335144


Shahararru goma a duniyar kayan mata Maman Zee ƙamshi and Kayan mata, duk wasu nau'i
na kayan mata na gargajiya da na zamani gumba tsumi tabaje zuma masu ƙyau da inganci ku
nemi maman zee ƙamshi an kayan mata a number kamar haka 0806 384 5136 Tana Bauchi
tana aika kayanta gari-gari Ƙasa-ƙasa. Sayen na gari mai da kuɗi gida.

*Masu buƙatar ɗaura musu tallah suyi mgn cikin farashi mai sauƙi.* A saman rubutu ko a ƙasa
ko wanne da farashinsa. Na gode.



Cike da fushi ta tashi ta nufi bedroom, miƙewa ya yi ya biyota yana kiran sunanta, "Sakinaa!
Keenahta! Haba Keenar Mubarak.
Tana shiga ta faɗa saman gadonta tana kuka, shugowa ya yi ya zauna bakin gadon tare da riƙo
hannayenta da sauri ta fizge cikin kuka ta ce, "Me zaka ce mini? Mubarak me zaka ce mini?
Bayan ka gama cutar da rayuwata ka cutar da ni!" Rufe mata baki ya yi alamar tayi shuru, ya
fara girgixa mata kai. "Ba zaki ga ne ba Sakinaa."
"Taya kuwa zan ga ne tunda ka cutar da..."
Jawo ta ya yi jikinsa cikin sigar rarrashi ya furta, "Kiyi shuru Sakinaata kar aji mu, don Allah kiyi
haƙuri ki yafe mini na gane kuskurena nasan ban ƙyauta miki ba daga ke har 'yar mu, na dawo
ne domin gane kurena domin na gano wanka da gari ba shi maganin yunwa sai an jiƙa kafin
asha." Da sauri ta kalle shi.
"Iye! Yau kaine ke kiran Yusra 'ya bayan ka ce baka sonta?"
"Haba dai baby taya zan ce ba na son 'yata, bayan nasan jinina ce. Wallahi kin ji na rantse ina
kaunar 'yata kuma ta nan matsayinta na 'yata."
Ajiyar zuciya ta saki, taji ranta ya mata sanyi, domin ta shiga furgicin jin ya sadaukar mata da
'yarsu, amma yanzu ranta wasai. Nan ya dinga zuba mata roman baka da daɗaɗan kalamai tuni
Sakinaa ta yarda da maganarsa har taji ranta ya mata sanyi.
Kunsan mace da rauni daman tsakanin mata da miji kuma sai Allah.
Sai kawai gani a ka yi sun fito suna dariya, ko daman Hajiya tasan za a rina, wai an saci zanin
mahaukaciya domin tasan da hakan zai iya faruwa don tuni ta ƙara dantse kamo na tsakanin
Mubarak da Sakinaa duk abinda Mubarak ke so to ita ma shi take so sannan zata iyayin komai
akan farin cikin ɗanta mafi soyuwa a zuciyarta. A ranar suka tattara sai gidansu, sai dai sun bar wa Hajiya Yusra da sunan Muhsin ƙanin
Mubarak zai kawota da dare, nan kuwa tuni sun gama magana kan zata zauna ne an yayeta
amma Sakinaa bata san komai ba akan hakan.
Gidan tsaf suka iske shi tunda daman Mubarak a nan yake kwana, kuma 'yan matasansa duka
suna zuwa, amma daga ranar ya taka musu burkin kar wacce ta sake zuwa matar gidan zata

dawo.
Tunda suka dawo sai aka lula duniyar soyayya ta ma'aurata, daman ya musu take-away ba
wani girki za ta yi ba, ganin har taran dare ba kawo Yusra ba ta ce,
"Wai ni Abban Yusra ya naji Yusra shuru ne?"
Ya mutsa fuska ya yi "Ku kenan matan hausawa da an haifi yaro ko yarinya shi kenan miji ya
koma baban wance ko Daddyn wance ko Abban wance haba ba za ku faɗi suna mai daɗi ba?"
Murmushi ta yi "Sorry Abban Yusr... Ayya sorry my honey." Taɓe baki ya yi "Kin kai su dai idan
kaya ne." "Wa wannan ba naji Yusra shuru?"
"Kiyi haƙuri My Sakinaa nasa Hajiya ta yayeta ne." Zaro idanuwa tayi.
"Yaye kuma Abban Yusra shekararta guda fa kenan?"
"I ai Hajiya ta ce ana yaye har 'yan shekara daya."
Tagumi ta saka tare da zuba masa ido zuciyarta na faɗa mata anya Mubarak ba sha'awarta
kawai yake ba, ta lura kawai shi ita ya sani alamunsa suna nuna hakan, amma wani ɓangare na
zuciyarta ya kasa gasgata hakan, haka tayi haƙuri aka yaye Yusra wacce ke da shekara guda
kachal. Ana wata ga wata, ai dawowarsu da wata guda sai ga wani cikin a jikin Sakinaa, zo kuka
durama tatur Mubarak ya nuna sai dai a zubda cikin wannan karon ma taƙi yarda, zuciyarta ba
ta taɓa dakewa irin ta wannan karon ba, abu ya sake kai su gaban Hajiya wannan karon ma
bayan Sakinaa tabi domin ita mace ce mai son yara, musamman ma da suka fito daga ɗan
lelanta, nan fa Mubarak ya dunga masifa da zage-zage "Mace sai ka ce tunkiya ko kaza da
antaɓa sai ciki shi wallahi ba haihuwa ya aurota ta dunga masa ba.
Zai fita Sakinaa ta bi shi ya ce, "Ina zaki bi ni kamar raƙumi da akala?"
"Gidan mijina mana!" Mtsuuw! Ya ja tsaki mai ƙara. "Ai yanzun ma sai dai ki zauna anan idan
kin haihu kin yaye sai ki koma." Harara ta banka ma shi.
"Bari kaji Mubarak wallahi baka isa ba, ƙafarka ƙafata ba inda zan zauna sai gidanka." Harara
ya banka mata itama ta mayar masa ficewa ya yi ta bi sa, ko a mota ba wanda ya yi wa wani
magana har suka isa gida.
Tunda suka dawo sai Mubarak ya haɗa kayansa cikin ƙaramar akwati ya bar mata gidan
"Wallahi bazan zauna ina ganin bakin ciki ba, gara ni nabar miki gidan." "Au yaji zaka yi, yau na
shiga uku ni Sakinaa namiji da yin da daka barkono ya bar gidansa." Ko kulata bai yi ba, bayan
fitarsa ta zauna ta saki kuka wannan wacce irin rayuwa ce haka. Tun tana jin tsoron kwana ita ɗaya a gidan har ta saba, haka ta reni cikinta har zuwa lokacin
haihuwa, da kanta taje asibitin da take awo, da taji alamar haihuwa cikin ikon Allah ta haifi ɗanta
lafiya, sai bayan ta koma gida sannan ta kira Hajiya ta sanar mata, aikuwa sai gata da ƙannan
Mubarak sun zo. Wannan karon ma anyi abin arziƙi sosai yaro ya amsa sunan mahaifin Sakinaa, domin Hajiya
tambayarta tayi sunan da take so sai ta ce ABDULLAHI sai ake kiransa Fahat wannan karon
ma Zaliha tazo kuma tayo gaiyatar ƙawayensu kamar wancen, anyi komai cikin girma.
Haka take rainon yaranta biyu, don Yusra ma ta dawo gabanta, sai da ta yaye Fahat sannan
Mubarak ya dawo gidan, wannab karon ma zuba mata daɗaɗan kalamai ya yi harta aminta da
shi, inda ita roman bake ke mata sauƙin karɓa, ai kuwa suka ci gaba da zamansu na so, da
ƙauna Yusra shekararta uku Fahat shekara biyu haka yasa su makarantar renon yara boko da

islamiyya idan suka tafi tun safe sai shidda na yamma suke dawowa gida. Wannan shi ne
tushen labarin Sakinaa har zuwa bayan auren Zaliha da Abban Yusra ya yi zuwa sakinta da
Hajiya tasa ya yi da kuma Zuwa gidan iyayenta da tayi basa nan, zuwa zamanta saman
dandamali tana tuna tushenta.
CIGABAN LABARIN
Sosai Sakinaa ke kuka tare da danasanin abinda ta aikata a rayuwarta, tambayar kanta take to
me yasa ma tayi hakan? Iyayenta abin sonta me yasa zata gujesu? Masoyin gaskiya Hamma
Umar shi ne ya faɗo mata a rai, wani irin son sa ne ke kwarara a cikin zuciyarta. Allah sarki
Hamma Umar wallahi ita ma tana ƙaunarsa ba ta san ya a ka yi ba har ta aikata hakan a gare
shi, ta fashe da wani rikitaccen kuka.
Lokaci ɗaya kuma kukan ya tsaya chekk da ta tuno wani abu, Hamma Umar yana aiki gidan
redion taraiya, kuma tasan gidan redion da sauri ta miƙe jin ana kwala kiran magrib, titi ta nufa
ta sami keke napep ta sanar masa inda zata ta shiga, sai da ta shiga kuma tafara wasiwasin ko
shiɗin ya san inda su Abbanta suke, tasan ba zai wuce ya sani ba da haka suka isa gidan redio
ta sallami mai adaidata sannan ta nufi gate ɗin.
Kallon sama da kasa mai gadin ya mata, kafin ya ce "Lafiya?"
"Ummm! Ummm daman nazo gurin Hamma Umar ne."
"Wane ne hakan?" Ya tambayeta, shuru tayi zuwa can ta ce, "A ciki yake aiki."
"Cikakken sunansa fa?" Shuru tayi tana tunani kafin ta ce, "UMAR ALKASIM INUWA." Kallonta
ya yi cike da rashin yarda ya ce, "Shi ɗin ne Yayanki yaro dan gata dan ƙwalisa wanda ko
wacce mace ke rubibi, ko dai kin zo ne domin ki gansa? Ko kina ɗaya daga cikin 'yan matan da
ke zuwa takanas su ce suna sonsa?" Gabanta ya buga da ƙarfi 'yan mata kuma har 'yan mata
ke zuwa cewa suna son sa, hawaye ya zubo mata. "Idan baza ka bar ni na shiga ba don Allah
ka mini magana da shi." Cewa ya yi a'a 'yan mata shugo sai ki zauna zaman jiransa domin bai
daɗ da shiga ba zai yi news na 7:00pm da sauri na shiga, na zauna kan bencin Mau gadin ina
kara hangen cikin harabar gidan redion.
Hajiya ta kalli Mubarak ta ce, "Wai kai lafiyarka ƙaau kuwa, tun bayan fitar Sakinaa sai safa
da marwa ka ke yi wa mutane?" Kallonta ya yi ransa ɓace.
"Wai Hajiya kin kwance Tsafi da sihirin da kika wa Sakinaa ne?"
Numfashi taja "I, amma tun kafin ma na kwance naga da kansa ya rage aiki kasan daman sihiri
ba lallai ba ne ya ɗaure a jikin wanda aka yi wa."
Tsaki yaja, "Amma Hajiya kin san dai ina son ta ko mai zai sa ma mu haɗa bakin na saketa? Ni
wallahi abin ya fara damuna kin san wace ce Sakinaa kuwa? Ita ɗin ta daban ce ko a cikin mata
'yar baiwa kenan."
Harararsa tayi, "Amma ai kai ka ce kana son sakinta ko shi ya sa ni kuma na ce ka saketa."
Zaliha da ke jin su miƙewa tayi, tare da kallonsu kafin ta ce, "Mubarak zo mu shiga ciki ke kuma
Hajiya ki gaida gida."
Zaro ido Hajiyar tayi "Ina magana da ɗana zaki ce haka?" Murmushi Zaliha tayi ta kalli Hajiya
sama da ƙasa.
"Hajiya kenan kar ki man ce wani abu guda ni Zaliha ƙawar Sakinaa ce, duk abinda kika ga
inayi wallahi saboda ita ne, kin man ce a gabana kika yiwa Sakinaa sihiri bayan kin ci mutumcin
iyayenta ita kaɗai suka haifa amma ki ka raba su da 'yarsu akan wani banzan ƙudiri naki, wai

duk abinda ɗanki yake so sai kin masa ke farin cikinsa kike so to ki sa a ranki da zuciyarki daga
yanzu zaki fara ɗanɗanar baƙin ciki, wallahi sai na ramawa Sakinaa da iyayenta da masoyinta
abinda kuka mata."
Zaro idanuwa Hajiya tayi cike da mamaki, domin daman tuni Mubarak ya shige ciki. Zaliha taci
gaba dace wa, "Tabbas ina son ɗanki Mubarak kuma babu wani sihiri da na masa ko nake
niyyar masa a'a indai kissa da kisisina na aiki to daga yau zaki fara ɗaukar hukunci, tsohuwar
banza mai matacciyar zuciya kawai." Ai saboda al'ajabi Hajiya kasa maganantuwa tayi har sadda Zaliha ta bar parlourn tabi bayan
Mubarak, kafin ta miƙe ta fita da sauri domin a yau take son tayi wa Zaliha hukunci tayi alƙawari
a ran ta yau sai ta kashe Zaliha in dai Tsafi na aiki a yau zata rabata da ɗanta, sai dai a ka ce
kana naka shi kuma Allah yana nasa, saboda sauri da Hajiya keyi taje ta ida nufinta akan Zaliha
idanuwanta duka sun rufe burinta ta isa gida ta hada mummunar nufinta, sakamakon gudun
ganganci da take ko gabanta bata kallo sosai ta haɗu da mummunan haɗari a hanyarta ta zuwa
gida.
Wa'iyazu billah, mummunan haɗari kuwa domin da ƙyar aka kwakulo Hajiya daga cikin motarta
duk ta dagargaje aka nufi asibiti da ita, tunani ake ta mutu ko kuwa da sauran numfashinta,
Allah ma sani.
Wajen takwas na dare Umar ya fito daga cikin studio na redion, zuwa lokacin Sakinaa ta sami
buta gurin Maigadi duk tayi sallolin dake kanta zaune take tana jiran fitowarsa, yana fitowa
Maigadi ya nuna mata shi, da sauri ta miƙe ta nufi gurinsa, yana ƙoƙarin shiga motarsa.
"Hamma Umar!" Ta faɗa a matukar rauna ne, shi kuwa jin muryar da ba zai iya mantawa ba a
rayuwarsa yasa shi waigowa da sauri, nan take suka haɗa idanuwansu cikin na juna, zubawa
juna ido sukayi, kafin ya yi saurin kauda idanuwansa gareta, yana wani ciccisgewa da basarwa.
Sosai take kuka ganin yadda Hamma Umar ya sake haɗuwa kamar bashi ba, kwarjini kamala
dattakonsa duk sunan tare da shi, kuka ta fashe masa ta ƙaraso garesa ta duƙa har ƙasa cikin
kuka da raunin murya ta ce, "Hamma Umar ka tausaya mini ka haɗani da iyayena idan kasan
inda suke naje gida ban same su ba. Numfashi yaja tare da tamke fuska "Ummm bari na miki kwatan ce." Da sauri ta ɗago
idanuwanta da ke cike da hawaye, "Ka kaini mana don Allah.''
"Bazan iya ba." Ya faɗa a takaice, kafin ya yi mata kwatance yadda zata gane sannan ya shiga
motarsa ya tadata da gudu ya bar gurin a sittin.
Kuka sosai Sakinaa tasa ka tabi bayan motar da kallo kafin ta tashi ta kakkaɓe jikinta ta koma
gurin Maigadi ta amshi kayanta tare da masa alkhairi da godiya ta fita ta sami adaidata sahu ta
shiga har zuwa lokacin kuka take kamar ranta zai fita, shi kenan yanzu Hamma Umar ya
tsaneta ya za tayi da rayuwarta.....
_WASA FARIN GIRKI, BA A FARA BUGA ƘWALLON BA FA HAR YANZU, SOMIN TAƁI KUKE
JI A LABARIN RAYUWAR SAKINAA._


*Albishir ga masu karanta Littafin WANKA DA GARI mutum 20 ɗin farko da suka fara biya to na
musu rangwame akan su turo 400 kamar yadda na ce mutum 20 na farko don haka dama ce ga
duk waɗanda zasu fara biya kafin book 1 ya kammala, da zarar na kammala book 1 duk mai

buƙatar WANKA DA GARI zai biya kuɗi 700*

_Zaku iya turawa kai tsaye ta wannan account 0037219728 Fatima Rabiu Sunusi StanbicIBTC_
Shaidar biya ta wannan number 08104335144

Mutanenmu na ƙasar Niger zasu turo da 500f na katin Moov ko Orange ta wannan layin
08104335144 idan kuma na kammala book 1 zaku turo 700f ne, Na gode.



#WankaDaGari
#UmmuAffan
#GawurtattuUku
#LabarinSakina2024
_Gawurtattu uku 2024_


WANKA DA GARI...


©UmmuAffan


*Book 1 Page 17-18*



Ina kuke mata? Mata nake magana waɗanda suka amsa sunansu na mata ba muna mata ba!
Kaya ne masu inganci waɗanda zai mai rabo ke samu. Ki buɗe bakin aljihu Hajiyata kiyi gyara
da ingantattun kayanmu na GHT muna da.
Royal jelly-karin Niima jiki yayi kyau yyi sulbi kamar tawarda.
Akwai Garlic oil _maganin infection sadidan ga tightening da yke ka sa skin kyau sa namiji
sunbatu.
Muna da Ganoderma reishi _xai ciccciko Miki da gaba ya motso d shaawa ya matse mace gam
Yana gigita maxa.
Sannan akwai Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya wanko duk wani dattin mara
ya gyra skin yyi fresh.
Ba anan muka tsaya ba muna da irin su Constifree tea _masu kashi d tauri Yana sake ciki ya
wanko duk wani dattin mara ya gyra skin yyi fresh.
Da su Longzit-matan da suka Kai shekaru 40 Niima y fara karanci a jikin su ku Sha longzit ku bn
labari.
Ga Panicept_duk wani ciwon Kashi da gabobi in Sha Allah matsala t kau.
Kuma akwai Sto care_ina masu ulcer duk karfin ulcer in Sha Allah xai magance masu shekara

da shekaru Basu Yi axumi b sun gwada sun fara axumi ynxu.
Da Female _masu matsalar alada , infection,rikecewar jini matsi duk wata harka t gaban mace
in Sha Allah.
Duk abin da kake buƙata zaka samu daga GHT sayen nagari mai da kuɗi gida kai tsaye kayi wa
wannan number mgn domin haɗaku da sha yanzu magani yanzu wato Maman Amal GHT
08104335144


Shahararru goma a duniyar kayan mata Maman Zee ƙamshi and Kayan mata, duk wasu nau'i
na kayan mata na gargajiya da na zamani gumba tsumi tabaje zuma masu ƙyau da inganci ku
nemi maman zee ƙamshi an kayan mata a number kamar haka 0806 384 5136 Tana Bauchi
tana aika kayanta gari-gari Ƙasa-ƙasa. Sayen na gari mai da kuɗi gida.

*Masu buƙatar ɗaura musu tallah suyi mgn cikin farashi mai sauƙi.* A saman rubutu ko a ƙasa
ko wanne da farashinsa. Na gode.



A haka har suka isa unguwar ta Ɗan mani, saitin gurin da ya ce ta sauka ta ce mai Adaidaita
sahun ya tsaya, sannan ta fara kallon layin.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login