Showing 1 words to 3000 words out of 26357 words

Chapter 1 - AZURFA Book Free BY AMINA MA’AJI.docx

AZURFA

STORY AND WRITING BY AMINA MA'AJI MAMAN KHAIRAT

Alhamdulillah nayi farin ciki sosai da kammala littafina mai suna Hangen nesa wanda ya ƙunshi abubuwa masu tarin yawa haka kuma ya kunshi da rusa da yawa acikin ta yanzu ma na kuma da wowa da sabon littafi Mai suna AZURFA wanda zakuji daɗin shi fiye da tunanin ku kuzauna ku nutsu zaku sha karatu tare da kuma nishadi duk a cikin littafin AZURFA

Kai tsaye zaku iya tuntuɓana ta wannan number kamar haka 08068748984 ko 08061686324 sai na jiku .

Ɗanɗano Ɗanɗano

Ruwa a ke tsulawa kamar da bakin ƙwarya kowa ce kusurwar ɗaki ɗauke da ƙaramar kwano da bokiti wajen taron ruwa dake zubowa daga indararo wasu yaran a tsugune suke wasu a tsaye,ko wacce mata tana bakin ƙofar ta duba ga yadda ginin ɗakunan suke ta rawa kamar zasu zubo ƙasa tsabagen lalacewar ɗakin babu ɗaki mai kyau da za,ace matan zasu haɗu a ɗaki ɗaya su zauna kowa a tsaye take a kan ƙafarta .

Shikuwa Malam Sabo yana cikin ɗakin da babu ,abun da babu acikin ta kujeru gado kayan kallo duk wani jin daɗi na rayuwa babu abun da babu a cikin ta in ana ruwa haka zai zauna yana shan kayan marmari acikin nutsuwar da kwanciyar hankali .

Duk hayaniyar da a keyi babu wanda ya isa ya tako koda bakin ƙofar shine da sunan ya zo neman mafaka da zai zauna ,tsabagen mungun halin shi da daure fuska sai yana neman aure zaka gane yana da fara,a daga zaran ya aura in Kinga dariyarshi to wani auren yake so ya ƙara in ya tashi auren turmi biyu biyu zai muku da hijabi da talmi shike nan ya gama da ku kenan .

Gidan Malam Sabo daga waje kamar gidan ƙaramin attajiri daga ciki kuwa tamkar gidan malam Shehu mai saƙar taburma manomi ne na rani dana damana,a cikin kayan lambu babu abun da baya nomawa komai da shi kowa yasan irin tarin dukiyar shi amma matan sa da yaran sa basu,isa suyi gadara da wannan kuɗin ba ko nuna isa a kan dukiyar shi ko,akasin haka .

Mata hudu ne gareshi ko wacce tana da yara kusan bakwai Asabe ita ce mai yara shida sai kaltume yara bakwai zuwaira yara biyar Fati yara uku duk cikin matan Fati ne tayi makaranta a cikin su auren saurayi da budurwa a keyi musu ga auri saki da ya ɗaura a kanshi ga neman mata masu yi mishi aiki a gonar shi danne su yake yi yayi lalata da su ƙarfi da yaji ko suna so ko basa so ma,aikacin gwamnati ne babba ma a ma,aikatar noma da kulawa da shukoki

Duk yawan matan da ke gidan da wanda suka rabu yaransu suna gidan in ya sake mace zaki ,ajiye mishi yaron shine ki kama hanya a haka har yaran suka kai talatin da biyu duk yawan yaran gidan taliya leda biyar a ke dafawa kuma kowa ya samu babu yarinyar da bata makaranta a cikin su kana kaiwa munzali zai sanya ka a makaranta mata iyaka cin su secondary maza ne suke yin gaba a cewar shi su samu wanda ko da an sake su zasu iya karanta sakin batare da ko,wa ya fahimci me suke ciki ba .

Wannan kenan

Babu ƙofar da babu karuwa a cikin su kowace ƙofa in anyi abinci bai ishe suba yaran ne masu fita su nemo abun da zasu ci su zauna gidan kamar gidan karuwai yaran Fatine kawai suke nutse ga shegen ilimin addini da na boko a na yawan sasu ,a cikin harkan karatun Alkur'ani da na boko tsabagen ƙoƙarin su Halisa yarinya ce mai ilimi shi yasa kowani malami yake alfahari da ita cikin makarantar su,sabo da ƙwazon ta sai Nabeel autar su Humaira yaran ƙofar Fati kenan shi yasa duk cikin matan sa yafi son Fati yana ji da,ita saboda ita yar aminin shine kuma ubangidan shi .

Yaran Kaltume Khalisat tafi kowa rashin ji a cikin su Zuwaira kuma Abida yaran Asabe itace uwargidan malam Sabo tafi kowa hakuri da kauda ido a duk abun da tagani dan tun malam Sabo bashi da komai Allah ya haɗa su aure da shi babu kalan abun da basu juya ba har Allah ya azurta su da yaro mai suna Usman shine yaro na farko acikin gidan yana aiki har da matar shi da yaran sa guda hudu duk yawan gidan malam Sabo yara sha biyu ya aurar uku sun rasu sai sauran yaran gidan .

Wanna kenan

Asabe ne keda girki tun asuba da ta tashi daga bacci gashi in kece da girki haka zaki kwana a ɗakin sa ki tashi ki dafa mishi abinci da shayi yana , da fa abincin sa tunda kitchen ne da shi da store aciki a ƙasa zaki kwanta shikuma yana kan gado in yana da buƙatar kine zai ce ki hau kan gado ki kwanta bayan buƙatar sa ta biya zai ce kitashi kiyi wanka ki dawo ƙasa ki kwanta bake fita daga ɗakin sa sai ƙarfe takwas in ya gama tashi kika bashi abinci da shayi ya sha kafin ki dauki abun da zaki, dafa na karyawa in kuwa tuwo ya rage dumame zakiyi da koko suga ta dubu ɗaya kunun cikin lamba goma zaki samata sugar kowa ya sha,a haka ga kuɗi kamar ya cinye shi amma ƙamo da ruwa duk ya mishi katutu a zuciyar shi .

Sai da lokacin yayi Asabe ta fito yara duk sun gala baita da jin yunwa babu wanda baya hamma a take ta haɗa wuta ta daura musu abun kari a ka raba kowa ya ɗauki na shi .

Yara suna cin abinci Abida tashigo tare da Khalisat ko wacce cikin dauke da ƙatuwar leda a hannun ta kowa ta shige ɗaki zuwaira ce tace nifa shegiyar tuwan nan ta,ishe ni ga yar albarka ta shigo kaltume ma haka duk suka tashi suka bi yaran su da basu kwana a gida ba shi yasa basa rasawa ko wacce yarta ke ciyar da ita da kuɗin iskanci

Abida

Umma wallahi kibar shiga harkan Baba nidai duk abinda kike so babu abunda bazan kawo Miki ba yanzu ki haɗa shayi ki sha tunda Kinga na siya Miki abun girki irin na Baba kuma yau da dare za,a zo a jifge Miki kayan abinci babu ruwan ki ki daina macin ƙazamin tuwan nan da ko manjan kirki babu a cikin ta haba kinfi karfin haka nifa Alhajin nan ka she mun kuɗi ya keyi sosai ga wannan dubu ashirin ɗin yace in baki .

"Kaji yar albarka kin kyauta kuwa shi yasa nake mutuƙar ji dake sosai a rayuwa ta Allah yayi Miki albarka uwata.

"Allah Yar albarka shiyasa nake kaunar ki sosai Allah kare mun ke daga dukkan bangarori kinfi mun mutane dayawa haihuwa tayi rana duk abinda ta kawo haka sukaci da yaran kowa ya ƙoshi suka bar,saura dare nayi Alhaji Murtala Muhammad haka ya kawo duk abin da ya dace a ka dinga shigowa da shi kasancewar anyi ruwa kowa yana ɗaki babu wanda ya fito waje kowacce tana tare da yaranta .

"To Umma zan tafi sai jibi zan dawo tunda Kinga Baba ba tambayar mu yake ba balle ya gane in ya tambaya kice kin aikeni kawai haka sukayi sallama tana fita tayi karo da Khalisat ita tana waje suna hira ce mata tayi yar uwa sai da safe kinsan bazan iya kwana a gidan nan ba sauro sai suyi maka illa sai da safe beby muje kawai .

Haka suka kama hanya suka wuce Khalisat itama ta kama gaban ta babu wanda ya kwana a gida rayuwar su suke kowace mace in har ta shiga da muwa to ita taso yaran su sun zame musu gata ƙarfi da yaji .

Kwanan Abida hudu ummanta bata sata ,a ido ba kiranta tayi "Abida kwana biyu shiru keda kikace zaki dawo washe gari ya kuma kika kwana hudu ?

"Umma wallahi bana gari zan dawo gobe ina Abuja ne amma karfa kice zaki ɗaga hankalin ki beby yana kula dani mekike sone sai a tura Miki ki gayamun duk abun da kike so baki da matsala kidai na yawan aiki kinji babu abunda bazan yi miki ba "

Kuɗin waje nane ya ƙare shiyasa nake son ki turomun dan Allah koda babu yawa ne baki da damuwa zan tura Miki yauma dubu hamsin zan tura Miki yaran nan a cenza musu takalmin gobe zan turo da tela ya gwada su zaiyi musu dinki ina son nima ƙannena su fita daban acikin yaran gidan tsoho na mai dattin hula shewa sukayi ta kashe wayar .

Washe gari kuwa tela ne yazo yayi duk abun da ya dace sai da tayi kwana bakwai ta dawo tare da kudade kasancewar bada mutum ɗaya take mu,amala ba .

Abubuwa da yawa ta kawo musu in kaga yan ƙofar su tufar kalla Masha Allah

Khalisat ita ma haka duk wani buƙatar su dana iyayen duk sun ɗauke babu wanda yake cikin wahala yaran zuwaira da kaltume kam sun cire iyayen su daga talaucin gidan malam Sabo Asabe ne da Fati suke cikin talauci sai dai Asabe yaron ta yana taimaka mata Fati ne da kuɗin da take koyarwa take rufawa kanta asiri su zauna cikin rufin asiri tunda duk ranan girkin ta kowa sai yaci ya ƙoshi abun shi abinci a wadace dan har nama za,asa a girkin kowa yaci ya ƙoshi tsabagen haƙurin ta da son da yake mata ba laifi yaranta suna samun kyauta alhamdulillah za,ace .

Umma ta !

Na,am Abida

Ki tashi muyi magana dan Allah ki nutsu kwai muyi maganar nan

Ina jinki Abida yar ummanta

"Akwai wani abokin saurayi na yace in nema mishi babbar mace wanda zata kai shekara arba,in da dauriya wanda zasu dinga hutawa wanda ta,iya soyayya mai diri mai jiki yace ko yaranta nawa ne babu da muwa kine namun wa kike ganin ya dace kenan da wannan abun ni kinsan ba harkar ƙawaye nakeyi ba wanda shekarun Abida bai wuce ashirin a duniya ba kuma itace yar fari agun mahaifiyar ta Zuwaira.

"Haba Abida waye ya dace kuwa gani bakida matsala in dai nine ai da ki nemo wata ta touna Miki asiri gara ni mutaru mu rufawa kanmu asiri har gida mu siya mubar shege ma tsiyaci daman hanyar rabuwa da mahaifin ku nakeyi yanzu in wannan har kan tazo ai Kinga na more .

Umma ke kuma a'a wallahi kinemo wata dai zaifi abokin wanda nake tare da shine fa haba kuma .

Kinci gidan ku babu wani abokin shine ne dai kawai kefa barikin nan muntaɓayin shi kawai dai nawa mukayi ne amma yanzu zamu dawo karki da mu,a haka suka gama Abida ta bata number Alhaji Jafar suka fara waya har yaga umman Abida ya kuma yadda zatayi mishi yadda ake so komai jin dadi ya tattara ga mata manya masu daraja sirrin da ke gun matar aure yayi yawa ga Sun iya sarrafa mutum cikin hikima a kan budurwa da komai sai an koya mata shi.

Tunda ganan harka ya bude duk ranan da ba girkin taba suna manne da Alhaji Jafar har kwana takeyi da safe ta dawo ko tsakiyar dare in sun gama holewar su .likafa taci gaba nan ta fara murmurewa da kwalliya irin ta matan bariki.

Gida ne da har ƙarfe hudu ko asuba abude take turawa ,akeyi ko wa ya shiga babu da muwa tsabagen mutanan da ke cikin ta kowa yana rayuwa ,a cikin gadara da nuna ,isa iyakar iyawan shi .

Duk cikin hikima take takun ta daman gida ne da kowa gashin kansa yake ci kowa ce mace ita ke tallafawa rayuwarta malam Sabo mutum ne wanda bai da mu da yaransa da matan sa ba sai wanda suke waje ne zasuci kuɗin shi na ciki kuwa sai gani sai hange mu,amala yake yi da yaran da basu wuce shekaru goma sha biyar zuwa shida ba da dabara da kayan lashe lashe yake afka musu da yaran suka gane koda ya ɗauki aiki wasu basa zuwa sai dai in zasu haƙura in kuwa ya tareki haka zai taɓa miki nono kamar tsohun maye.

AZURFA

STORY AND WRITING BY AMINA MA'AJI MAMAN KHAIRAT

Book 1

Kai tsaye dan magana da marubuciyar ku tuntuɓeni ta wani mahangar yanar gizo ko kiran waya ta wannan nombobin 08061686324 08068748984

LAMBA NA BIYU

FATI

Ummi wallahi mutanan gidan nan basa tsoron Allah ki duba yadda kowa yake abun da yaga da ma shiyasa in mun fita a tacewa yayuna yan iska ne har da Babana shima wai tare yara yake ya cire musu wando haba Ummi ya zamuyi da wannan abun kunyar ne kuma duk ba mutanen arziki suke kawowa ba nikam zan gudu gidan kaka kawai in barku a nan na gaji gida kamar gidan yan bori ki duba muma irin wahalar da muke sha kowa har yana Allah Allah girkin ki ya zagayo amma agunsu kece wanda suke ƙonawa rai .

"Halisa kenan kar in ƙara jin zancen nan a bakin ki kedai kawai kici gaba da yi musu addu,a wataran sai labari Baban ku kuma shima kiyi mishi addu,a jarabawa ta yana ɗaya daga cikin auran mahaifin ku ban ,isa in cenzawa ƙaddara ta ba kiyi hakuri kin san mahaifin ku baya so ku dinga yawan zuwa gidan mutane cewa yake yi kun raina abun da yake kawo wa amma kiyi mishi uziri.

Haba Ummi ranan fa ina ganin wani ya kawo Adda Abida a mota yana tafiya wani yazo ya ɗauketa washe gari da nayi mata magana cewa tayi sai tayi mun duka inda rabu da ita wai duk ba ubanmu bane ya ɗaurata a kan tafarkin nan

Ya,isa kitashi ki tafi in da na aike ki karkuma kijima yanzu ki dawo da wuri kinjiAllah ya kiyaye hanya ya dawo mun dake lafiya .

Amin Ummi

Babu jimawa ta dawo aguje bata wuce gun kowa ba sai gun Asabe tunda ga ƙofar gida take ta kwaɗa mata kira

Maman Usman yanzu naga mutane akan Yusuf sun taru anata dukan shi wai sata yayi kuma gashi duk sun jimishi ciwo ko tsayuwar kirki bayayi gyalen ta ta ɗauko ta yafa suka fita cikin gudu da sauri har suka ƙarisa koran yaran tayi wani mutum ne yace

Malama kibarni in yiwa wannan yaron lahani wanda koda nan gaba ne yaga kayan mutane bazai ɗauka ba ko shi waye ne yaro kamar ɓera shagona ya shiga ya ɗauke mun kuɗi har dubu ashirin yau hukuma ce zata rabani da shi daman ya dade yanayi mun sata yaune dubun ya cika shege dangin kwarata.

"Haba malam baka da yaro ne ko baka san zafin haihuwa ba baka tunan wataran zai iya zama wani abu ne ko kai baka haihu ba, ko kai angama maka naka jarabawar ne wallahi ƙaddara yana kan kowa zai iya faɗa maka kaima nasiha zakayi mishi ba duka ba yanzu ka duba yadda kaji mishi ciwo ko tashi bayayi in kuma ka,kashe shifa ?

Mezaka ce ko kana da hujjar da zaka iya biyar diyyar shi

Ko sauraron ta baiyi ba ya wuce da Yusuf policetetion nan a ka dauki bayanin komai cen ma sukace wannan yaron kwanaki sun haura gidan mutane sunyi musu sata kulle shi akayi haka asabe ta dawo da takaici da kuka .

Malam Sabo ta kira ta gaya mishi cewa yayi babu ,in da zai je akan kowa agidan nan duk wanda ya ɗebo abu ya ƙaremishi shikam babu ruwanshi da kowa duk yadda a kayi yaje yace ba zai je ba haka ta shiga neman kuɗi Usman ya bayar aka sake shi ya dawo da zazzaɓi da raunuka a jikin shi wannan Yusuf ɗin shine ƙaddaran Asabe duk yadda a kayi shine matsalan ta

Malam Sabo

Yayi tafiya ƙano haka yayi kwana uku bai dawo ba ga kayan abincin su da ya bari ya ƙare babu wanda zai basu yara ne sukaje lambun shi suka debo dan kalin Hausa da ya dawo a ka gaya mishi ya hau masifa

Tirƙashi ana wata ga wata agidan nan

Zanyi maganin ku

"Duk sai kun biyani a ƙasa nake nemo kuɗin ne da zan bar abu kudebo meyasa bazaku bari in dawo ba yunwar kwana biyu ne zata kashe ku ke Asabe kene kika zuga yaran nan dan zuwaira bata da mu da komai nawa ba kaltume ita ma haka kece wallahi in ana son a zauna lafiya sai an biyani kudina dan kalina na dubu goma ce tun daga waje ake jin murya duk matan sunyi shiru babu wanda ta Kula shi zuwaira shiga ɗaki tayi ta kawo mishi kuɗin shi .

Ga shi malam ka gayawa mutanan da basuda zuciyar nema irin Asabe da bata tsinana komai nikaga kayan miya ma nafara siyarwa ƙarshen tsiya babu kunya ya karɓa ya wuce ɗakin shi

Zuwaira ta tara duka matan gidan

Ke yaya kece babba tunda yau malam yayi mana rashin kirki a cikin gidan shi a Kaci amma yace a biya shi to dan Allah kar kowa ta kulashi nine da girki kuma babu in da zanje ina da kwalin taliya da shinkafa zan dafa mana muci da yaran mu ko zuwa in da yake bazan ta kura ba Allah yasa karan nan nice zanyi gaba yace zuwaira na sake ki wallahi wata ɗaya bazanyi ba sai da aure

Kwana biyu ita taciyar da gidan da kuɗin ta ko ta kanshi bata biba yazo har ɗakin ta suna cin taliya ya ɗaga labule "wato wuyar ki ta,isa yanka shine kika ƙaurace mun kin barni da yunwa in mutu ko wallahi baki ,isa ba kice zakiyi mun walaƙanci .

Malam kenan borin kunya kakeyi taya zakace a biya ka wallahi auren ka baya gaba na kuma ko shekara zaka yi baka bamu abinci ba sai dai kaga nayi jiki nifa tsoron ka ne yanzu banaji dade

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login