Showing 6001 words to 9000 words out of 26357 words
"kin taɓa koyarwa ne ko tsohuwar Malama ce ko ɗaliba
"aa ni yar koyo ce
Bani nakin dubawa yayi yaga yadda ta nuna kwazon ta har wani salution tayi na wasu fumula making yayi tsakani da Allah ya bata makin ɗin da ta bashi har ma ya ƙara mata da makin biyar dan duka tacinye .
"Amma fa kinbani mamaki gaskiya kuma na jinjina Miki amma hakan ba zai baki damar ƙara mun karan bani a cikin aiki na ba kingane ko kibari sai ranan Friday sai ki rabawa kowa har da nawan yauwa Malama ta .
Sai anjima
"Kin tsani halina shiyasa kikayi maganina yau ko .
e kamar kasani ka takura mana karatu bana shiga aljanna ba amma takuran yayi yawa gashi shi kanshi abun da kake koyarwa wahala gareshi amma duk ka takura mana .
Bata tsaya jin mai zaice ba tayi ficewar ta.
Haka taci gaba da duk abun da take yi ko far gaba babu a tattare da ita ko tsoro babu shi rayuwar ta take yi tana ji da ilimin ta da kuma gidan da ta fito wajen kare mata martaba kuɗi a salí nasaba duk tana tare da shi ne zai gaya mata dan shi kaɗai bai isa ya kayar da niba
Wannan shine hanyar da malam zai gane ba,a raina mutum duk ilimin ka wataran sai ka samu wanda ya fika ilimi da kuma fahimta wasu malaman suna da tsanani sosai a kan karatun da aduniya ne kawai take da mahimmanci.
Gidan Malam Sabo
Da safe Abida ta ɗauko police har gidan Usman a kazo a ka tafi da shi babu irin magiyar da Asabe batayi wa Abida ba amma taki saka baki a saki Usman DPO saurayin tane da suke holewar su da shi mayan mata ne ,a lokacin da malam Sabo yaji labari ran shi ya ɓaci sosai
"Yanzu Zuwaira haka kika bari gida na ya zamo gidan bariki kenan yanzu sai kiƙi bawa Abida haƙuri tasa a fito da yaran nan kenan ina take abani ita in yi mata shegen duka .
"Bata nan na,aike ta wayace ya taɓa ta har zaice mun yarinya ,takaruwa shine ya haifa mun ita kenan lalle ma kuwa "umarni nake baki kodan ma bani number ta in kirata .
Amsa yayi "Abida kiwuce asake mun yaro in ba haka ba wallahi za,ajimu da ke mutumiyar banza kawai kuma awa biyu na baki in ganshi a gida .
Sai da aka shafe a wa uku Usman ya dawo gida yama a mahaifin shi godiya tun daga nan ko me za'tayi babu ruwan shi da ita taje tayi duk abun da take so .
Yau da wuri ta dawo gida a wani yanayi a buge take sosai ƙafarta ɗaga wanta sai tayi da gaske kafin take iya gane Umman ta"
Abida mekika shane kikayi shiru haba ki daina yadda suna yi Miki wayo ba gara iskancin ba da gidan shaye shaye haba Abida banfa hanaki duk abun da kike soba amma yana da kyau kibar wasu abun Kinga yau fita zanyi amma ganin ki a wannan halin kar,in barki kifita .
Cikin maye take yin maganar babu komai Umma ki fita kawai sai kin dawo zaki sameni,ina bacci na babu abun da zai sameni in Sha Allah .
Ƙarfe sha biyu a ka zo a ka fita da zuwaira hotel mafi tsada ya Kaita bayan sun tube tsirara haihuar uwarta kafin ta fara magana "babu bata lokaci Alhaji na kayi duk abun da ya dace yau ina bukatar kudi kamar ɗari biyu "haba Hajjaju baki da matsala zan tura Miki biyar ma yau nasha wani maganine so nake in ji ko ya fara aiki ne amma kiyi hakuri "ba komai haka sukayi duk abun da suke so karshe kwana tayi sai kusan asuba ya dawo da ita gida har lokacin Abida tana bacci.
Kiran sunan ta da,akayi shine tarazana .
AZURFA
STORY AND WRITING BY AMINA MA'AJI MAMAN KHAIRAT
Ina jama,a albishir dan Allah kuce mun goro ku zauna kufara bibiyan littafin Azurfa wanda ya kunshi abubuwa masu tarin yawa .
In kin San ba comments zakiyi ba dan Allah karma ki siyi littafin nan ki zauna ko na Allah ya,isa a kawo Miki labarin Azurfa ya faru da gaske in labarin yayi dai dai da rayuwar wasu ina neman afuwan ku .
Kai tsaye zaki tura kudin karanta littafin Azurfa a wannan asusun 8068748984 Amina ma'aji opay sai shedar biya ta wannan nunber 08068748984 kafin in gama Free page 300 in nagama 500 mutane uku zasu iya biyan kuɗi su biya 700 sai na jiku .
Marubuciyar
Aminatu
Halacci ne
Zaɓi biyu
Yancin mata
Halin maza
Gidan marayu
Wata mahangar
Damai rai ake rikichin duniya
Hangen nesa
Ɗan Adam butulu.
Azurfa.
LAMBA NA BIYAR
"Anty Zuwaira ina kuma kikaje jiya naga fitan ki ko bacci banyi ba sai yanzu kika dawo kenan ?
To uwata sai ki bari sai na gama abun da nakeyi kafin kisani agaba da wani shegen kinabibi nifa ba kaltume bace koAsabe da zakiyi mun wani iyaye tafiya tafara da ledoji da yawa a hannun ta ta wuce ɗaki Abida har ta tashi tayi sallah tana zaune daga ita sai ɗan gajeren wando ga ƙannen ta duk suna falon suna kwance "umma kin dawo kenan sannu ina fatan kin dace dan naga fara,a acikin wannan fuskokin naki mai wuyar fassaruwa naji daɗi wallahi "kedai bari kawai Abida a she ana holewa mun zauna a cikin duhu muna ta hidima da kanmu yanzu na sa samu dubu ɗari biyar a hannun wannan mutumin ina cin rabona banda abubuwan nan da ya saimin Alhaji Jafar duniya ne .
Tashi ki ɗaura mana abinda zamuci muda yara Kinga kafin su tashi kingama ko yaya"umma ki ɗaura kayan ki gaskiya na gaji kuma yau nake son in fita a kwai birthday ƙawata da za,ayi so nake in yi fitar kece raini in fita a yar Alhaji sabo ba yar malam ba .
Kihuta kawai bari su sha shayi sai Nima na tashi zan yi musu wani abu yau kinsan girkin kaltume ne sai a hankali gata da simi simi abun ta komai na kaltume haushi take ban in nine nake da kyau ɗin kaltume yadda kika ɗaurani a kan harkan nan ai sai in da mai ya tsaya "kwana biyu bana ganin Khalisat lafiya kuwa don shirun yayi yawa gaskiya ban sata,a ido ba Allah yasa dai lafiya kawai .
Haka kuwa akayi shayi yaran suka sha suma suka kwanta hayaniyar malam Sabo ne ya tashe su cikin bambammi da faɗa .
"Zonan kaltume kamar wani ubanta,taya zaki dauki taliya har guda shida kina nufin bazai,isheku bane da zaki dauki har shida yayi yawa gaskiya so kike kuci har kubar saura yata lalacewa"malam yaushe abinci ma ya taɓa wani saura a nan gidan ganin damina ne cikin mutane buduwa yake yi shiyasa kuma bama ƙoshi haka muke danne cikin ku daga mu sai yara amma gaskiya a cenza lale.
Sauran matan ma duk suka haɗa baki wajen yanayi musu kadan shine ya ƙara musu ya zama bakwai
Dukkan ku ina son yau ƙarfe takwas na dare kowa ya zama ya halacci wannan taron zansa dukkan yayunku da ƴaƴan ku kowa yazo ayi a gabanshi .
Da kunya yabar tsakar gidan ya juya ɗakin sa,dan ƙaryawa a nan ne hankalin kaltume ya tashi ga bata dawo ba ko kadan zuwaira ne tayi Magana "Abida yanzu ya za,ayi kince zaki fita kuma takwas na dare mahaifin ku yana buƙatan kallon ku sannan karfa kice bazaki halacci wannan taron ba dan mu toshe kunnen wanda suke samana,ido kamar Fati .
Umma sai karfe tara ma zan fita Kinga an gama komai ma ba dai shikenan ba amma zan kira Khalisat tazo karfa kwaɓan mu yayi ruwa Allah yasa tana nan bata wuce Kano ba
Kiran ta tayi ,a waya cikin girmamawa ta dauka "ya,akayi ne Abida lafiya kuwa.
Ke ina kika shiga kwana biyu to yau akwai taro dan haka duk abun da kikeyi kibari kawai ki dawo kawai "karfa ki da mu yanzu ma zaki ganni zan shigo Gombe muka wuce da Ahmad amma zaki ganni
Ƙarfe sha ɗaya kuwa ta shigo cikin gidan duk mutanen kallon ta sukeyi ita kuma ko,ajikin ta tayi shiru kawai ta wuce bayanta huta ne ta dawo ɗakin su Abida sukata hira a kan yau zata rakata wani waje .
Ƙarfe takwas tayi ,wakowa ya zauna wanda suke da aure kowa ya kawo matar shi wasu kuma a ,a daidaita suka zo gyaran murya yayi yace abude taron da addu,a "abun da yasa na taraku ,a nan shine na ƙara abincin da nake bayarwa da kuma sabulu da omo da abun masarufi sannan in har za,a aika lambuna a dinga gayamun in ba haka ba ku aika da kuɗin ku yanzu yarana sun girma kuma sun gama makarantar da ta dace ba zai iyu in zuba musu ido suna abun da suke so ba dan haka ko wacce a cikin ku nan da wata ɗaya ta kawo duk wanda take so labarin da ake bani a waje babu daɗi kafin in bawa yarinya miji gara ta kawo da kanta sannan duk macen da zata fita ta sanar dani ta waya don dukkan ku a kwai waya a wajen ku.
Zuwaira ne ta fara yin magana "nikam Abida bata da wani tsayayye don haka ayi mata afuwa in Allah ya kawo sai ta kawo "rufe mun baki ba dan gidan Alhaji Mamman mai kifi yana neman taba mahaifin shi har yayi mun magana .
a'a malam to ita dai bata son shi gaskiya
"Zuwaira zan fa saɓa Miki yarki ko dai yata so kike ki zugata ta zubar mun da mutunci to baki isa ba wallahi haka ,akeyi ne .
Kutashi ku bani waje na gama a in da yayi maganar a nan kowa ya bar mishi har Usman zai tashi "ka dinga kulawa da motsin yaran nan kasa,ido a kansu kaji .
Wallahi Usman koda a gidan karuwai yaga Abida da Khalisat ban yafe mishi ba in har yayi musu magana taya yara suna abun da suke so kana matsayin mahaifin su baka taɓa nuna da muwar ka ba ,da tasa aka ci mishi mutunci duk abun bai isheka ba sai ya tusa kanshi kai dai ka kula da tarbiyar da ka basu .
Malam Ammar
Rana bata ƙarya ranan jumma,a yana da darasi da su Affanan zasu yi practical kowa ya fito da wuri har shima ya fito cikin girmamawa suka shiga cikin aji .
A karon farko yayi shiru yana yi musu magana a kan suyi hakuri ya yabawa ƙoƙarin Affanan ta bada Assignment kuma kowa yayi har shima yayi yanzu ita ce tayi makin da kanta zata rabawa kowa da ke cikin ajin haka ta fara kiran suna kowa ya karɓi nashi har malam Ammar shima ta bashi na shi ya ajiye ya kira sunan ta ya bata nata ita ma gun ya dau surutu kowa da abun da yake faɗa .
"Zan gaya muku nima abun da ta bani ina da makin 27/30 dan haka kunga irin adalci irin nata ita ma zata gaya muku makin ɗin da ta samu ita ma ta faɗa 30/30 take da shi daukar tafi gun yayi yace a yi shiru .
Daga yau duk mai son tambaya zai iya yi mata na tabbata zai samu amsar da yake so ta zama Malama ta nima wannan bai wace da Allah ya bata ku dage tunda kuna da ita bai kamata a ce har zaku zamu c/o a wannan course ɗin ba na gode cikin hikima sukayi practical din su har suka watse .
Yau daman shi ɗaya suke da shi tsayawa sukayi ita da kausar da Maryam suka yi karatu sun gama wajen ƙarfe sha biyu suna tafiya a bakin get kenan ya gansu zuge gilas din motar yayi "Affanan gida zakuyi ne ?
Maryam ce tace e gida muka nufa
Kuzo in rage muku hanya
Kabarshi kawai zamu tafi haka yata yi musu magiya har suka hau motar suna cikin tafiya duk sukayi shiru"yanzu malam in Doctor Salma ta ganka fa kasan kishi ne da.
Murmushi yayi ko magana baiyi ba har suka isa ƙofar gidan su kausar suka bi suka ajiye Maryam Affanan ne ita ce ƙarshe.
Hajiya ta ina zanbi yau dai dole inga gidan su Malama ta shiru tayi ya samu guya ya tsaya "to tunda kinyi shiru Nima bari na samu gu na tsaya kawai zaifi sai kinyi magana kafin ita da motar .
Ɗagowa tayi nan zamubi doneteibe zaka kaini layin governor
Kice kina unguwar masu kuɗi kenan shikenan tafiya yake tayi a hankali kuma cikin natsuwa daga ganin fuskarshi yana cikin farin ciki sosai har suka isa ƙofar gidan kallon ta yayi ita ma zuba mishi ido tayi
"Nagode sosai amma in har aka cewa matar ka ka ɗauke mu tayi mun rashin mutunci nima Zan mayar mata da duk abun da tagaya mun wallahi bazan yadda da cin mutumci ba .
Babu ma abun da zai faru
In ba damuwa Affanan ina buƙatar number wayar ki wataran in har ta cerkemun sai in kiraki ki ƙaramun wasu ,ilimin dan Allah irin baiwar da Allah yayi Miki ne nake Miki fatan samun nasara nida kaina zan shige Miki gaba wajen kin samu gurbin koyarwa daga wasu ɓangaren .
"Kayi hakuri bana bada number na a malamai gudun faɗawa tarkon su,ina tsayawa a matsayi nane gudun faɗawa wani ɓangaren kaifa ba samu zakayi ba gara kawai ka haƙura ko kaje wani wajen ka nema kawai amma nida hannuna bazaka taɓa samun komai daga gareniba ba ka tsaya a matsayin ka don Allah haɗa hannun ta tayi irin na bada haƙurin nan tunda ta fara magana kallon ta kawai yake yi komai nata jinshi yake daban a rashin.
Shikenan Nagode sai Monday in Allah ya kaimu .
Haka yaja motar shi tunda ya fara tafiya kalaman ta ne ke yawo acikin jijiyoyin dake aiki a cikin wani salon ƙaunar tane yake yawo a ranshi yana mamakin ta yadda a kayi har ya faɗa ƙaunar yarinya wannan ko bai faɗa ba so yake mata mai wuyar sha, ani. A kwai wanda zai so bayan salma
Mai gadi ne ya buɗe mishi get ya shiga da motar shi watsa ruwa ya fara yi kafin ya tambaya Salma ta dawo a kace a'a zeenat har kusan ƙarfe biyu basu dawo ba lafiya kuwa kiran direban yayi yace ga sunan Maine ya ƙare a motar sunyi kusa yanzu zasu ganshi.
Lokacin da suka iso kenan a gajiye zeenat take gaishe da Affin ta tayi kawai ta wuce ɗaki ta kwanta sai bacci ne ya ɗauke ta
Ƙarfe hudu kafin Doctor Salma ta dawo ko tabi takan Ammar batayi ba da zeenat wani zama a keyi na rashin kula da yunwa ya dame shi ya nufi ɓangaren ta ya sameta tanata rubutu .
"Wani irin walaƙanci ne wannan kin bar mutane da yunwa kin dawo kinyi shiru mekike nufi kenan
Mekike taƙama da shine ?
Allah Salma ranan da zan ɗauki mataki a kanki bazai yi Miki daɗi ba ke babu abun da kika iya kenan ke ba nunawa mutum so ko wani ƙauna ba ba kula da miji ba kawai dai za,a kiraki ne da sunar mace .
Nidin sweet
Haba sweet akwai fa abinci kaine kace baza ka ci abinci yar aiki ba to ya zanyi kuma gajiye nake wallahi ina bukatan hutu a raina ka taimaka in zuba maka dan Allah
Ki kawo mun ɗaki ina jiran ki wallahi zan nemi wanda zata kula dani bazaki taɓa sani in saɓawa Ubangiji na ba wallahi kinyi ƙadan .
Monday
Affanan
AZURFA
STORY AND WRITING BY AMINA MA'AJI MAMAN KHAIRAT
Ina jama,a albishir dan Allah kuce mun goro ku zauna kufara bibiyan littafin Azurfa wanda ya kunshi abubuwa masu tarin yawa .
In kin San ba comments zakiyi ba dan Allah karma ki siyi littafin nan ki zauna ko na Allah ya,isa a kawo Miki labarin Azurfa ya faru da gaske in labarin yayi dai dai da rayuwar wasu ina neman afuwan ku .
Kai tsaye zaki tura kudin karanta littafin Azurfa a wannan asusun 8068748984 Amina ma'aji opay sai shedar biya ta wannan nunber 08068748984 kafin in gama Free page 300 in nagama 500 mutane uku zasu iya biyan kuɗi su biya 700 sai na jiku .
Marubuciyar
Aminatu
Halacci ne
Zaɓi biyu
Yancin mata
Halin maza
Gidan marayu
Wata mahangar
Damai rai ake rikichin duniya
Hangen nesa
Ɗan Adam butulu.
Azurfa.
LAMBA NA SHIDA
**********Ƙarfe tara yanayi Abida da Khalisat suka kama hanya amotar wani matashi mai suna Adnan suka wuce ɓangaren da a ke ajiya motoci gayu da yan mata kuma banji kiɗa yana tashi ba ko dai an gama komai ne jin wani gun ƙida yana ɗaukar hankali duk wata budurwar da ta amsa sunan ta da shisha,a gefen ta kayan maye kuwa babu kalan wanda babu,a wajen kowani wajen zama an tanadi duk abun da zai gusar maka da tunani ,wasu kayan da suka saka tamkar tsirari suke hayaniya ga babu ruwan kowa da kowa ko wacce har kan gaban ta take yi.
Koda wucewa kikayi babu wanda zai gane a kan ko kewaye ce "Khalisat Kinga abun burgewa ko bari na kaiki in da zaki zauna yanzu zakiga wani yazo ya zauna a kusa da ke dan nan mata basa rashi nuna mata gun zama tayi ta zauna ta dawo gefen Adnan ta zauna suna fuskantar juna daga gani kasan akwai soyayya a tsakanin su ba wai irin na biya buƙata kadai ba .
Ƙarfe tara da rabi wanda a ke Birthday ta ta,iso irin shiga_ da tayi duk sai da kowa ya juya Jameela kenan babu dadewa a kafara ƙoƙarin yanka cake Bashir ya sanya mata a baki ita ma ta bashi kowa saurayin ta