Showing 24001 words to 26357 words out of 26357 words
bacci gagara hakuri ta taɓo wani saurayin ta suka hau video call tsirata take amma rashin imani da cin amana bai hana ta ,su biya wa kansu buƙata ba Adnan ya sake baki ina ta bacci ƙarfe biyar da rabi kamar hadin baki duk sun fito kowa yana ƙokarin rufe ɗaki Abida ce ta fara kallon Zuwaira Khalisat taga malam Sabo zuwaira ma ta ga malam Sabo da gudu ta koma ɗakin Alhaji Jafar ya biyo ta "me yafaru ne wai naga kin rugo da gudu ?
Mai gida nane na ganshi tare da wata "shine daman mijin naki na sanshi nima ai mutumi nane wallahi muna gaisawa bari in fita kuma naga Abida ita ma tazo nan yau naji kunya gaskiya "Abida ba tace ke matar gidan su bace wai yayarta ceke to Meye aciki kuma yanzu wannan shine mijin ki Zuwaira ya fini zulama gaskiya amma bari in dauke mishi hankali sai ki fito ki tafi kinji .
Fita yayi suna gaisawa da malam Sabo har taje bakin get kenan wayar ta ,tamanta ta dawo dan ta dauka kenan juyowar da zatayi suka haɗa ido da Khalisat agun kawai ta tsaya malam Sabo yana gun suna ta magana Hajiya Balaraba ta fito don tayiwa malam Sabo magana taga abokin mijin ta Jafar Khalisat da gudu ta buya ,a bayan Bashir data ga malam Sabo yana nufo ta haka ta kauce yace Khalisat
Meyafaru meya kawo ki nan Khalisat lafiyan ki kuwa jikin ta sai rawa yake yi a lokacin zuwaira ta shige ɗaki taki fitowa ya zubawa Khalisat ido ya kira sunan ta .
Mekikazo yi nan Khalisat ?
Abun da kazo yi ne Baba duk abun da ya kawo ka shine ya kawo ni suna cikin magana Abida ta fito ita da adnan hannun su riƙe da juna suna tafiya ganin mutane Abida ta leka suka haɗa ido hudu da malam Sabo take ta sake hannun Adnan jikin ta sai nawa yake yi tare da tsarewa ta kauda kanta taci gaba da tafiya kamar bata ga mahaifin ta ba sai cewa takeyi beby mu tafi mana ka tsaya ne kayi shiru ko dai kasan shine naga sai kallon ka yake yi abun shi .
Abokin Babana ne wannan malam Sabo
Shine mahaifin ki ?
Nasanshi dai amma babu wani hadi da muka yi da shi wallahi kawai dai yaban mamaki ne Khalisat zo mu tafi Baba da Hajiyar shi ce karta ganmu .
Iyayen Ramatu da yan rugar su sunzo lambun malam Sabo basu sameshi ba suka ta jiranshi duk da sanda a hannun su ,saboda cin zarafin da yayiwa yarinya Fulani da zuciya sun tambayi mai kula da wajen yace baizo ba sai gobe haka haka suka wuni agun shiru sai sun ɗauki fansar abun da yayiwa yar uwarsu sukata jira shiru wani ne labbo yace a kwatanta mana gidan shi muje kawai ya basu haƙuri tare da rarrashi sannan yace shi bai taɓa ganin yarinyar ba sai in dai sharri zatayiwa ogan shi to amma shiru har kusan magariba ya kira malam Sabo har sau uku shiru ba,a ɗauka ba ya ƙara kira shiru take ya rubuta mishi saƙo ya tura mishi
Jidda
Tunda a ka bata brush ta rasa me yafaru gashi maganganun Affi yana nuni ne da wasu magana har ƙarfe kusan tara bata ji dirin kowa a gidan ba ta rasa me ke mata daɗi duk abun da tayi ba,a cikin hayyacin ta tayi ba abun ƙaryawa ta gama shiru wanka tayi ga abincin amma ta kasa cin koda abu ɗaya ne tana ta zullumi jin ana kiranta Affi sai da zuciyar ta ya tsinke da sauri ta zo a ladafce ta gaishe shi cikin sakin fuska ya amsa da fara,ar shi "jidda jikin Zeenat yayi zafi bata jin daɗi kawo mata brush ɗin ta sabon nan da na siyo ɗazu sai ki watsa mata ruwa jikin yayi zafi da yawa .
To yallabai da sauri taje ta kawo mata duk yadda yayi a kan Jidda tayi mata wanka amma taƙi "Affi ba zanyi wanka ba ka barni don Allah yayi rarrashin duniyar nan taƙi yace jidda ta kawo musu abin karyawa a nan da sauri taje ta kawo ta tsaya .
"Jidda kije kawai sai sha biyu zan fita in na gama zangaya miki yau dai mutumiyar taki bata son zama dake ko me ya faru ɗan mutum kenan haka yake ba shida garanti wai ina Salma ne ko ta fita ne tun jiya na jita shiru lafiya kuwa ?
Affi tun jiya da ta dawo shiru amma naje bakin ƙofar ɗakin ta naji tana kuka ban san Meye ya faru ba kuma har da nishi takeyi .
"Shikenan duk abun da ya sameta in har bazatayi magana ba ya rage mata kuma babu ruwa na tunda taƙi ta gayamun jin sallamar Aleena ne ya juya "Affi ina kwana ya gida tun jiya da dare muke kiran Salma shiru shine Ummi tace in dubo ta ko lafiya kowa ya kira shiru " ki duba ta mana nima tun da na dawo ban gan taba amma ki duba tafiya ta fara yi har ta,isa ƙofar ɗakin tajishi a rufe ta buga shiru sai da tayi da gaske ƙofar ta bude dubawa ɗakin tayi bata ga Salma ba ta ƙara duba ko,ina shiru ta juya zata duba ban ɗaki ta ganta a ƙasa ga jini da ke zuba wani har ya daskare a gigice ta nufi ɗakin Affi "ya Ammar Anty Salma ta mutu ga tanan a cikin jini "wace Salmar ba dai Salma ba muje yana zuwa ya jijjiga ta yaga tana da rai ɗaukar ta yayi sai cikin mota da sauri ya figi motar sai asibiti na FMW sa sauri ma,aikatar wajen suka karɓe ta tai makon gaggawa a ka bata a wansu biyu kafin kace Meye asibiti ya cika da mutane da yawa kowa yana son doctor ya fito a ji meyafaru amma shiru sai da doctor Nasir ya fito tare da wasu mata guda biyu a bayan shi kowa ya,iyo kanshi "doctor me yasa mu Matana don Allah me ya faru ka gayamun ?
"Kaine mijin ta ka biyo ni tare da wani daga ɓangaren su ummi da Ammar suka bi shi bayan sun zauna ne yace "da farko muna buƙatan asamata jini leda biyu sannan kuma kaine mijin ta
e nine mijin ta doctor
Matar ka tasha maganin zubar da ciki ne sannan wannan maganin da ta sha yafi ƙarfin mahaifarta bashi da kwarin da zai ɗauki wannan maganin bayan ta yi yunƙurin zubar da cikin ya ƙi fita ya lalace amma bai fito ba sai da muka yi da gaske za,ayi mata wankin ciki sannan in har ta ƙara shan wani magani in ta samu ciki to mutuwa zatayi in har tace zata yi yun ƙurin zubar da ciki dan lafiyar mahaifarta ya kamata a kiyaye .
Tun da doctor ya fara magana shiru yayi yana nazarin wasu abubuwa masu tarin yawa ummi ne tahau salati da mamaki "ummi kin gani ko ta zubar mun da gudan jinina me nayi Miki ne mena rageki da shi wanda tun da na aure ki nake ganin ta shin hankali me nayi Miki don Allah me na tsare Miki na fuskanci wannan hukunci daga gareki me nayi Miki wallahi sai nayi Sharia da ke a kan zubar mun da ciki da kika yi sannan duk wanda yasa kika zubar mun da ciki da wanda ya siyar Miki maganin duk yana ciki.
Tashi yayi yabar office ɗin doctor yanzu Meye abun yi kenan wannan yarinyar da ilimin ki da hankalin ki keba yarinya ba malamar jami,a ce fa Salma akwai wauta Allah.
A hanzarta a nemo wanda zamu samu jinin a gunshi kuma a bashi hakuri a mijin ta don ita ce tayi mishi laifi ba wai shine yayi mata laifi ba a wa mutane,biyu a ka samu wanda zasu bada jini a ka saka mata duk abin da ya kama duk anyi mata shi tun da Ammar y fita da ga asibitin ko zuwa bai ƙarayi ba kuma babu wanda ya sanar a yan gidan su da man babu wanda ya keson Salma sabo da halin ta kowa baya son ta jin ta take tafi kowa hakiƙa gidan su Salma sunfi gidan Su Ammar kuɗi a tarbiya kuwa gidan su Ammar sune a kan gaba .
Jidda
Zonan zeenat shine kika gayawa Affin ki ko to Meye yasa ya cenza miki brush ina tambayan ki kinyi mun shiru "ban gaya mishi ba wallahi ban faɗa ba sake kuka tayi
Na dakeki ne da kikeyimun kuka waye ya taɓaki wallahi duk ranan da kika faɗawa mutane abun da nake yi Miki sai na ka sheki yanzu Meye yasame ki kike cewa zazzaɓi kikeji .
Gun da nake zama ne in da kike sakamun hannu yake yimun ciwo ɗazu da nasa wando zafi yayi mun ga ya kumbura shine ya sani zazzaɓi .
Bari na sakaki a cikin ruwan zafi da detol kinji ko zai daina kiyi shiru anjima zamuje mu duba mamanki kinji ko da ruwan zafin nan zaki dinga yin tsarki in kinje fitsari.
Da sauri ta dafa komai har gabaruwa ta zaunar da zeenat a ciki har zeenat taji daɗin jikin ta tasha magani ta kwanta ko,iya zama batayi tun da Affin ta ya fita asibiti a kwance take a ranan jidda ne tayi jinyar Zeenat.
Tunda ya fito daga asibiti makaranta ya wuce yana da darasi a wasu haka ya gama zuciyar shi babu wani da muwa a cikin ta ya duba su Affanan bai gansu ba haka ya haƙura zuciyar shi babu daɗi duk wanda ya ganshi dole zai fahimci a kwai wani abu kiran yan uwan Salma kuwa yawa gareshi babu wanda ya ɗauka duk kiran da sukayi mishi ƙarfe goma na dare ya koma gida ya watsa ruwa ya tambayi jikin Zeenat tace da sauƙi .
Jidda gobe ki tashi kiyi wani abu ki kai asibiti Salma babu lafiya kuje da zeenat ko dai in jiraki ki dawoni sai in je in kin dawo ko a nan ma Zeenat tace a gunshi zata kwana bai hana ta ba ta kwanta in jikin baiyi sauƙi ba sai muje asibiti.
Washegari
Da safe jidda ta shirya taje asibiti kowa ya tambaye ta Ammar yana gida tace shine yace ta kawo abinci babu abun da suka ce kowa yayi shiru abun da Salma tayi bata kyauta ba ko kaɗan wannan ai zalinci ne bana kaɗan ba har ya dawo ya shirya ya wace gun aiki .
Har ƙarfe biyu bai ga Affanan ba shiru ya kirata wajen sau uku shiru a na huɗu ne ta ɗauka tare da sallama ya amsa ta gaisheshi "me yasa baki shigo makaranta ba Meye dalili ina ta jiran ki kawomun topic ɗin shiru
"ko dai kin fasa ne ?
Malam daman kaine ai ban gane ba kayi haƙuri gobe zan kawo maka yau su mommy zasu dawo shine nake yi musu girki kuma su Kausar ma tayani suke yi duk muna gidan mu kayi hakuri don Allah yauwa malam ɗan Aljanna nikam A zan samu tun da ni malamar kace ni .
"Ki rubuta zanzo yanzu in karɓa yanzu zaki ganni kinji ko
Shikenan malam sai kazo in kazo ka kirani zan kawo maka in sha Allah wani irin farin ciki da yake ji a ranshi yau Affanan ce zata shirya abinci saboda taran iyayen ta ai kuwa abun da bai taɓa jin Salma tayi ba kenan ko ruwan zafi key ya ɗauka sai unguwar su Affanan kira biyu a na uku ta dauka tace ga tanan zuwa tana fitowa ya fara mata video har ta,iso da Sallama .
Sannu malam na sakaka, wahala ga shi aiki ne mukeyayi kayi hakuri gobe zamuje yau kam ai ma bamu da kai ai kuwa shi yasa mukwa kwantar da hankalin mu ai in muna da kai mun isa ne ko ba wanka haka zamu tafi tsabagen far gaba .
Har haka na zama a she ban sani ba shikenan kuje kuyi aikin ku kar,in dameki da surutu kinji babu komai nagode har ta juya ya kira sunan ta
Affanan
In kun gama abincin ki zubomun zanci amma wanda kece kika yi da kanki ba wanda a ka tayaki ba kinji "malam wallahi babu ruwa na in har Salma ta ganka shikenan jirani zan kawo maka yanzu minti kaɗan sai ga tanan dauke da abubuwa masu yawan gaske.
Ga shi
"nida wa zanci wannan kuma ai yayi mun yawa ?
Kai kaɗai ne don Salma tace cine da kai duk kaine kake cinye kayan abincin gidan ka kuma gaskiya ta faɗa don mu malamar mu bata ƙarya .
Murmushi yayi yayi godiya sosai sai ce mata yayi Salma bata da lafiya sosai tana asibiti
Meya sameta Allah bata lafiya yace Amin
Gida ya wuce shida zeenat sukaci abincin suna santin daɗi sai yaga duk duniya babu wanda ya,iya girki sama da Affanan sai hajiyar shi har suka ragewa jidda ita ma taji daɗin abincin sosai .
Gareku makaranta littafin azurfa shin asirin jidda yana tounuwa shin ya matsayin auren Salma da Ammar a kwai iyuwar Salma ta ƙara haihuwa ko dai sanadiyar zubar da ciki yasa mahaifar ta lalace .
Kuna ganin Affanan zata yadda da soyayyar Ammar kuwa ya tarbiyar gidan su yake shin Salma zata ƙara daraja a idon Ammar shin Salma tana nadama ta,ajiye aikin ta ta kula da iyalan ta ne duk a cikin littafin azurfa kashi na biyu ki biya kuɗi ki sha karatu
Ya rayuwar gidan malam Sabo shin akwai nadama a tattare da su ko dai sai duniya ta koya musu hankali shin meke faruwa da Ramatu abubuwa masu tarin yawa da kuma faɗakar wa duk a cikin littafin a zurfa ..
A cikin matan Malam Sabo waye yake rabuwa da ita wayake aure shin iyayen Ramatu zasu kai malam Sabo kotu ne ko dai barin shi zasu yi da Allah wani cuta ne ya kama Ramatu yar shekara goma sha biyu.