Showing 15001 words to 18000 words out of 26357 words
kufara bibiyan littafin Azurfa wanda ya kunshi abubuwa masu tarin yawa .
In kin San ba comments zakiyi ba dan Allah karma ki siyi littafin nan ki zauna ko na Allah ya,isa a kawo Miki labarin Azurfa ya faru da gaske in labarin yayi dai dai da rayuwar wasu ina neman afuwan ku .
Kai tsaye zaki tura kudin karanta littafin Azurfa a wannan asusun 8068748984 Amina ma'aji opay sai shedar biya ta wannan nunber 08068748984 kafin in gama Free page 300 in nagama 500 mutane uku zasu iya biyan kuɗi su biya 700 sai na jiku .
Marubuciyar
Aminatu
Halacci ne
Zaɓi biyu
Yancin mata
Halin maza
Gidan marayu
Wata mahangar
Damai rai ake rikichin duniya
Hangen nesa
Ɗan Adam butulu.
Azurfa.
LAMBA NA TAKWAS
Uban waye ya fita a cikin gidan nan wallahi in baku gayamun wanda ta fita ba duk sai ranku ya ɓaci taya zaku zamar dani mutumin banza yanzu kenan duk abun da a ke gayamun a she kuna cin amana ta tare da yaran nan ina ita zuwairan da kaltume har Fati kowa ya fito wallahi sai kun gayamun wacece ta fita a cikin gidan nan ku gayamun ko duk ranku ya ɓaci na gaya muku .
"Haba malam ka bi komai a hankali mana baƙuwa fa yarinyan nan tayi shine yarinyar tana sauri mijin ta yazo ɗaukar ta Meye ne abun faɗa yaran da kake magana ita Abida tun dazu,na aike ta gidan Hajiya Rabi sun tafi ita da Khalisat kawar tasu ma bata same suba kafa daina yadda da maganar mutane wallahi sai sun kaika sun baro ka kuma kune zakuji kunya yaran mu dai an yi musu addu,a tun da suka fito duniya kaji da kyau .
Nifa kamar Khalisat nagani taya zakice tun dazu kika aike su bayan ƙarfe hudu muka gama taron nan haba dan Allah meyasa zakuyi mun haka kuɗin ga kulawa da yaran nan dan Allah.
Haka ya gama bambamin shi ya hakura ya wuce cikin gida bangaren shi ya wuce zuwaira ne keda girki duk abun da yake buƙata duk sai da tayi mishi .
Malam gobe nefa tafiyar tamu zuwa Kano shine nace mekake son ,in tanadar maka in kuma mai wahala ne in fara aikin shi tunda ga yanzu .
Masa nake so kuma kowa ne zaici bani kadai ba kinsan kowani jumma,a abun da akeyi kenan a gidan nan ba,a gama wa kuma da wuri
Kwana ,nawa zakiyi in kin tafi ne zuwaira ?
sai naji ban yadda da Wannan tafiyar ba sam hankalina ya gagara samun nutsuwa da wannan tafiyan da zakuyi sunan waye a dangin ku da ban taɓa sanin ta ba ki sanar da ni dan Allah keda wama zakuje ne ?
"Malam kenan wallahi duk kwanakin da kace inyi zanyi koda kwana ɗaya ne koda a ce ba,a gama sunan ba zan dawo bana son ranka ya ɓaci wallahi kasan yadda dai nake matukar da muwa da buƙatun ka ba zanyi abun da zaka yi fushi ba ko .
Kashe shi tayi da kalamai masu daɗi
Kwana uku zakiyi babu komai amma gaskiya yau a barni na more kinsan yau da ishirruwan ki na tashi tun safe kece a raina tabada kai buri ya hau da safe komai ta shirya babu abun da bata gama ba har abincin rana duk ta kammala ƙarfe sha biyu tayi sallama da matan gidan ta kama hanya ta fice babu in da ta tsaya sai in da Alhaji Jafar yace ta jirashi.
Faran mace alkebban mata takawar ki lafiya Hajjaju yanzu sai mu wuce kenan na ɗauka bazaki zoba kwana nayi da tunanin ki a raina
" mekikace mishi a mijin naki .?
Haba mace nefa niba namiji ba suna nace zanje kaga kuwa dole ya barni tunda nima da na haihu an zomun ɗaukar hanyar Kano sukayi cike da farin ciki duk wanda ya kalle su yasan suna cikin kwanciyar hankali zuwaira irin matan nan ne masu jiki iya misali ga diri duk da ta haihu da yawa bai hana jikin ta zama,a yadda yake ba hatta nonon ta basu kwanta irin na sauran ba mace iya mace in banda rabon haihuwa me maza tayi da malam Sabo sai dai yana da wani sirri da sai macen da suke tarayya ne zata fahimci hakan kuma ta gane in da daɗin yake .
Ƙarfe uku suka sauƙa a Kano hotel mafi tsada ya kama musu bayan sun watsa ruwa an kawo musu abinci sunci gajeren wando ne a jikin shi ko riga babu ita kuma tawul ne a jikin ta babu wani kunya da take ji ko yaji nata gudanar da soyayyar su ,suke yi cikin kwanciyar hankali tamkar wacce a ka ɗaura musu aure da shi duk yadda zata sarrafa shi duk tabi ta gigita shi ya susuce .
"Hajiya wallahi ki kashe auren ki zan aure ki wannan ɗanɗanon ba zai sa in rabu da keba ki riƙe mun amana sosai karki rabu da ni ki bijire mishi kawai ya sake ki gaskiya kishi nakeyi sosai .
.karfa ka damu babu abun da zaisa in zauna da mutumin nan biyayyar iyaye ne ai shidin ma ɗan hannu ne yana more wa a ce mu bazai barmu ba karka da mu ka kwantar da hankalin ka zanyi maganin abun yanzu gida nake son siya ka cika mun kuɗin miliyan ɗaya ne ya rage .
Bari in Miki transfer kafin ma kikoma kawai kigama komai hakan kuwa a kayi ya tura mata ita ma ta turawa wanda sukayi cinikin gidan .
Kwanan su uku babu kalan abun da basu yi ba hotel uku duk sai da suka zagaye cikin kwanciyar hankali kiran Abida ne ya shigo .
Hello umma baki dawo bane har yanzu jiya nazo ,a kace kinyi tafiya yaushe zaki dawo ne
Kano naje amma yau zan dawo kema yau ki kwana a gida karkije ko,ina ki jirani tsaraban me zan kawo Miki ne ki gayamun ko ki rubuto duk abin da kuke so duk zan Miki .
Kasuwa suka shiga tayi soyayya da yawa har da sarin ta kalma na maza da na mata tsaraban malam Sabo da ban nasu kaltume daban .sun iso gari mai a dai dai ta tatara ya Kaita har ƙofar gida yarane suka shiga yi mata sannu da zuwa ta amsa cikin sakin fuska duk jama,ar gidan sannu suke yi mata ganin ƙofar malam Sabo a rufe shine ya tabbatar mata baya gida .
Khalisat suna cikin hotel sun kammala duk abun da zasu yi kenan ta fito zata fara tafiya daga idon da zatayi taga malam Sabo rungume da wata mata yana ta fara,a suna hira daga wani ɗakin ya fito tare da wata babbar mace wanda ta amsa sunan ta mace daga ganin matar nan kuɗi ya zauna mata haka ta ƙare mata kallo ta kuma ƙarewa malam Sabo kallo ganin damin kuɗin da ya miƙawa matar sai da zuciyar Khalisat ya tsinke sai da taga fitar su kafin suma suka fito ita da Bashir .
Ammar
Kenan zakasa in gagara hakuri wallahi taya zaka dinga barin ɗalibai suna shigo maka office zan ɗauki mataki a kan yarinyar nan zan nemi sunan ta in ja mata kunne "Salma in har kin fasa ayya kinyi kama kuwa da aikin ki kuwa taya dan Kinga dalibai sun shigo bari to in gaya Miki karki bari yaran nan su ganeki zaki sha mamaki har suna sai su sanya miki .
Sai me kenan susamun kuma wallahi zaka sha mamaki abun da zan aikata ka zuba mun ido kawai ka sha kallo.
Meyafaru kika zo mun office ?
Zan wuce gida ne sai ƙarfe tara zan dawo gida shine nace bari na gaya maka "tunda kinyi niya kin kuma yanke hukunci Meye nawa in kinje gidan wani amfani zakiyi mun tunda babu abun da kike yi mun kije nima gida zan tafi daga nan banajin daɗi ne gashi kinzo kin sani ciwon kai da surutu .
Ai kuwa Salma in har tasa su kausar a gaba wallahi nida kaina zance suyi mata rashin kunya kuma in goye musu baya tunda bata jin magana in da mutane zasuji shawara na sudinga duba matar da ta dace bawai soyayya ya ruɗesu ba suyi irin nawa duk Salma ta ficemun daga rai yadda na tsara ba haka ,na samu ba ko kadan key ya ɗauka ya rufe office ɗin ya hau mota unguwar su Affanan ya wuce haka kawai zaije ya zauna ya ga ko zata fito ko wani ɗan uwanta zai fito amma ya lura gidan kullum a rufe yake haka daman gidan manya yake sai mutum yazo ake bude mishi get .
Har zai tada motar sai ya hango Affanan tana fitowa ita da wata ƙawarta sai dariya suke yi ita ma dariyar takeyi daga ganin wannan a cikin farin ciki suke in tayi fushi ma kyau takeyi sai da suka tsaya wata motar tazo ta tsaya a kusa da su ,kawar Tata a ka ɗauka daga wa juna hannu suke yi tare da kewar juna kamar kar ta shiga gida tana waya ta shiga gida sai da ta shiga yaja motar shi yayi gaba tare da tunaninta a ranshi. Ya ƙara dubawa ko ta bude sallamar da yayi mata amma shiru kake ji babu halamar ta bude ko kaɗan.
Jidda
Yar aikin gidan Salma a duk lokacin da aiki yayi mata yawa babu kalan abun da bata sa zeenat har wanke wanke gyaren ɗaki komai yi mata takeyi Salma tana fita shayi take haɗawa mai zafi tare da kayan haɗin da ya dace kayan Salma take sawa Tata dauƙar photo ta kwanta a kan gado ta sha baccin ta har sai taji dirin motar ɗaya daga cikin su kafin ta tashi .
Wani rana karfe goma sha biyu an tashi kenan direba ya kawo ta kenan jidda tana aiki a kitchen tana ganin zeenat ta samu gu ta zauna tace zeenat ne zatayi haka yarinyar tanayi tana kuka har ta gama taki bata abinci har karfe biyu kafin taci abinci ta gaji a ƙasa take barin ta tayi bacci har sai taji dirin mota ne take kwantar da ita a kan gadon ta .
Zo nan zeenat wallahi in har kika gayawa mommy ki,abun da nake Miki wallahi ranki in yayi dubu sai ya ɓaci kuma yan kaki zanyi in bawa kare su cinyeki ki rasa kowa ko Affin ki bazaki ƙara ganin Shiba har abadan.
Da gaske bazan ga Affi na ba
"Anty Jidda bazan faɗa ba ma shiru zanyi ko hannu da kike samun a duwawuna ma bazan faɗa ba ranan brush da kika turamun ban faɗawa kowa ba amma yayi jini har kika sani a ruwan zafi kuma kikace in yi tafiya mai kyau wallahi Anty Jidda ban faɗa ba .
"Yauwa zeenat zan baki abun daɗi ki daina fadawa kowa kinji karki fada yau kwana biyu babu aikin da zakiyi har sai kin warke karatu kawai zamuyi koda mommy ki ta kiraki karfa kije kinji Affin ki ma ki daina zuwa wajen shi sosai kinji .
Haka take shan azaba tare da ciwo da hannun da jidda take samata a gaban ta batare da kowa ya sani ba jidda tun tana shekara uku Salma bata ƙarayi mata wanka ba a hannun jidda take irin su jidda fuska biyu ne gare su bazaki taɓa gane wa ita munguwa bace duk yadda take da kai gidan su Ammar suna kulawa da ita har gidan su Salma babu abun da ba,ayi mata komai take so in ba,an gaya maka yar aiki bace ba lalle ka gane hakan ba duk yadda kake da ita gata da fara,a da son yara amma muguntar ta yafi na wanda ya bayyana halin shi a bayya ne
Sai ƙarfe takwas Ammar ya shigo cikin gida Mai gadi ne yayi mishi salama suka gaisa shiga yayi cikin gidan bai samu kowa a waje ko falo ba haka ya dinga kiran zeenat a murtuƙe ta taho
",Me yafaru kuma yau shagwaba ne ya tashi shine har da kukan ki gayamun abun da ya faru kinji mamana .
a'a kwaro ne ya faɗa mata kuma ancire mata shine take kuka "shikenan ga kayan daɗin ki mamana zauna anan kici kinji kawo mun abinci jidda .
Da sauri ta kawo komai ta ajiye amma zuciyar ta ya gagara samun nutsuwa ko kadan in har asirin ta ya tounu shikenan ka sheta za,ayi sai da ta kawo abinci zar zata juya sai da bara ya faɗa mata .
Zeenat zoki cenza kayan ki ki,saka na kwanciya kinji.
Tashi mamana sai ki dawo muyi hira yau game zan baki kiyi wasa kinji
Hararanta Jidda tayi sai cewa tayi Affi bacci nake ji sai da safe
Da wuri haka shikenan Allah ya kai mu ki kwanta yau kadai yaji tausayin zeenat uwa bata da lokacin yarta wannan wace kalar rayuwa ne
Nace me ka sani in kula ne da sauƙi
AZURFA
STORY AND WRITING BY AMINA MA'AJI MAMAN KHAIRAT
Ina jama,a albishir dan Allah kuce mun goro ku zauna kufara bibiyan littafin Azurfa wanda ya kunshi abubuwa masu tarin yawa .
In kin San ba comments zakiyi ba dan Allah karma ki siyi littafin nan ki zauna ko na Allah ya,isa a kawo Miki labarin Azurfa ya faru da gaske in labarin yayi dai dai da rayuwar wasu ina neman afuwan ku .
Kai tsaye zaki tura kudin karanta littafin Azurfa a wannan asusun 8068748984 Amina ma'aji opay sai shedar biya ta wannan nunber 08068748984 kafin in gama Free page 300 in nagama 500 mutane uku zasu iya biyan kuɗi su biya 700 sai na jiku .
Marubuciyar
Aminatu
Halacci ne
Zaɓi biyu
Yancin mata
Halin maza
Gidan marayu
Wata mahangar
Damai rai ake rikichin duniya
Hangen nesa
Ɗan Adam butulu.
Azurfa.
LAMBA NA TARA
Bashir
Ya naga kin zubawa wannan mutumin ido babu dai ruwan ki da kowa bebyna kawai in Kinga mutum kibar shi a matsayin da kika ajiye shi ina ruwan ki da shi wanda kike kallon nan yawanci muna haɗuwa da shi a nan kawai kowa da irin nashi ɗabi,an ne amma har gaisawa mukeyi da shi .
Ko dai kin san shine har kishi nakeyi Wallahi share kawai .
Babu wani sanin shi da nayi kama kawai yake yi mun da wani wanda na sani sun dade suna ta surutu har ya ƙarisa da Khalisat gida sukayi sallama a kan ƙarshen watan nan ta shirya su tafi tare tace ta yadda .
Abida ne take ta murna da tsaraban da umman ta,takawo mata kowa farin ciki kawai yake yi a take ɗakin zuwaira ya cika da yan barka da dawowa har malam Sabo ya dawo irin makirci irin na tsofin yan duniya tayi mishi .
Sannu da dawowa malam ga ma tsarabar ka na kawo maka kasan Kano ance makkan yan Nigeria ganin fuskar Zuwaira ya ƙara kyau sosai "Zuwaira kamar ba wani aiki kikajeyi yi ba ki duba har wani haske kika ƙara to nagode duk hayaniyar da akeyi ko,idon fati babu wanda ya gani daga ita har yaran ta injin niƙa Fati ta siya take ɗan samun abun da zata rufawa kanta asiri tare da yaran ya kuma"ummi wallahi ita ma maman Abida ta ɗauki halin su Abidan kullum sai naganta ta fita yau ma ina ganin wani mutum ya ajiye ta shine tace daga tafiya take amma wallahi wanine ya sauƙe ta ina ganin su .
"Babu ruwan ki Halisa ki kiyayeni wallahi in har kina shiga abun da babu ruwan ki wallahi , mutanen sharri zasu biki da shi babu ruwarki dai kiyaye
Koda wuta kika ga zasu shiga naki kawai ido ne ya in ba haka ba wallahi babu ruwa na kina dai ganin irin duk wata wahala da muke sha mutane yan bala,i ne "ummi naga ranki ya ɓaci wallahi mutuncin mu suke zubar wa ba komai ba amma babu komai hakan ma yayi dai dai sai da Fati tayi da gaske kafin Halisa ta hakura ta bada mahimmanci a rubuta exam din da zasu yi tafi maida hankalin ta ga a shekarar ƙarshe suke tana kuma rubuta wani exam na scholarship committee Allah ya bata nasara a ran da zasu rubuta exam ɗin ne malam Mustapha ya kirata.
Halisa ki nutsu ki rubuta exam wanda zakiji daɗin shi fiye da kowani exam kasar waje zaki wuce kiyi karatun ki wanda zakiji daɗin shi za,a dauki ɗawainiyar karatun ki na likita har ki gama karatun .
Malam in sha Allahu kace zaka gayamun wani magana kuma kayi shiru ka gayamun tamkar ɗan uwa na ɗauke ka babu banbanci da sauran yan uwana har ka fisu a waje na .
Halisa kiyi ma shiru kar jama,a su jiki na,isa in fi dan uwanki kidai bari zan sanar da ke in sha Allah Allah ya rufa asiri kawai har a ka tashi na rasa malam Mustapha ga shi exam ɗin mu shine ƙarshe sallama muka yi da sauran ƙawaye na kowa ta kama gaban ta .
.ina shiga gida ganin mutane a tsakar gida ga Yusuf a tsakiya wai yayiwa maman Khalisat sata sai ya biya ta ko dai taje ta rufe shi da duka babu ɓarawa a gidan nan sama da Yusuf .
"Kaltume kin tabbata shine yayi Miki sata to yau ka tattara naka kabar mun gida na abun da kake yi mun ya,ishe ni sai dai kabar mun gida shege tsinan ne ga yayan ka kasimu da yaga babu sarki dai Allah soja yake nema yanzu training ya tafi kaine zaka bijire mun Asabe dauko mishi kayan shi kawai zaifi.
Haba malam ina kake so yaje kar kuma abun yaci gaba wannan ba ɗaukar mataki bane kayi haƙuri ka barshi tunda har ya dawo da ragowar kuɗin
Gidan kune ko nawa haka nace kuma babu makawa dole sai ya barmun gida na ko ya biyata sauran kudin ta shege dangin ɓarayi kawai