Showing 3001 words to 6000 words out of 26357 words

Chapter 2 - AZURFA Book Free BY AMINA MA’AJI.docx

ina tsoron saki amma yanzu nafi kowa buƙata .

Juyawa yayi ya kama hanya duk sai da girkin kowa ya zagayo Zuwaira ne mai basu abinda zasu dafa da yaga babu wanda yake kulashi ya nemi sulhu .

"Yanzu dan nace ku biyani shine kukayi fushi to kuyi haƙuri gacen buhun masara na fitar muku da shi da taliya da shin kafa ko wacce tazo ta auna duk ranan girkin ta tadafa shikenan ko munafukai har da haɗemun baki Allah ya kawo wanda zamu zauna da ita tayi mun biyayya .

Ko kulashi basu yi ba agun suka bar mishi kayan abincin suka dawo ɗakunan nan su

Alhaji Jafar ne yazo ya ɗauki Zuwaira suka tafi hotel ta rufe fuskarta da liƙaf babu wanda zai gane ita ne acikin motar haka suka shiga wani duniyar daban more rayuwar su suke yi cikin kwanciyar hankali sai da suka gama abun da suke yi kafin Jafar ya kira Abokin sa

"Nifa ina hotel ɗin tunjiya muna tare da Abida kazo ne

Eh kazo ina ɗaki mai lamba uku in kagama kayi mun magana ina ɗaki na goma sai mu fita ko babu da Musa Zuwaira taji dai ana waya amma bata gane da wa suke magana ba har ƙarfe goma na dare kafin suka fito abun su kowa ya kama hanya texi Zuwaira ta hau ta dawo gida abun ta cike da tsaraba da abun motsa baki sosai acikin ledar ɗayar kuwa kayan kwalliya ce ƙarfe ɗaya taji ana turo ƙofa a firgice ta ce waye ne .

Umma nine ki bude mun dan Allah da sauri ta buɗe mata ta shiga "umma bakiyi bacci ba a she

"Abida banyi bacci ba meyasa kika dawo acikin daren nan bake tsoron mahaifin ki ya ganki ne kinsan fa an fara kawo mishi tsaigumi a kanku ki dai iya cenza takunki kinji

To Umma ki tashi kici wani abu ga komai "nima ga shicen na taho da shi duk bana jin daɗi ne bakina babu wani ɗan dano ko kaɗan

A dai haka suka kwanta sukayi bacci washe gari da safe kowa nata hada hadan aiki Fati ne da girki ƙarfe bakwai ta fito daga ɓangaren malam Sabo ko kari bata daura mishi ba ta fito har ƙarfe tara babu wanda yasa komai a cikin sa duk ita ,ake jira amma shiru kira ya fara kwaɗa mata

Fati !

Kina ina yaushe kema kika dauki halin irin na zuwaira da Asabe da kaltume yaushe kika fara rashin hankali taya har ƙarfe goma babu girki na babu na yara ,a cikin shi kin wani zubawa mutane ido

"Malam wallahi bana jin daɗi ne tun jiya ina ta maka magana amma ko ɗagowa bakayi ka kulani ba kanata min Shari shiyasa .

Yanzu kenan wuni za,ayi babu girki kenan shikenan ki kwanta "Asabe ki taya ta dan Allah tunda kece babba ita zuwaira rashin kunyar tama bazai barta ba

"Ai kuwa malam gara da kace Asabe don nikam babu wani girki da zan yi in kuwa ka matsa sai dai in dafawa yara banda wannan ƙartin matan .

Yarana tun takwas suka karya a gidan nan kaine dai da yaran ka da matan ka sune a wahale dolen shi yata rarrashin matan har Zuwaira ta,amince a kan zatayi girkin har tayi kusan gamawa kenan ta jiyo muryan Usman

Ina Abida take yanzu lalacewar ta takai har wuceni a mota ita da saurayin ta su watsa mun ruwan datti kenan wani irin rayuwa ne wannan samarin naki sune suka ce ki raina kowa to ki ,kiyayeni zanyi mungun baki mamaki in iskanci kikeji dashi Ni malamin kine a harkan nan "rufe mun baki bakinka ya sari guntun kashi wallahi ina so ka sani yarinya ta ba yar iskabace kuma tafi ƙarfin tunanin ka kaji da kyau in banda lalacewa wai har kai ne zakayiwa Abida nasiha zan tuna maka kaji da kyau .

Dauƙe Abida yayi da mari ita ma ta ɗauke shi da mari jikake tas faɗa ne ya ɓarke sosai girkin da ba,a ƙarisa ba kenan

AZURFA

STORY AND WRITING BY AMINA MA'AJI MAMAN KHAIRAT

Ina jama,a albishir dan Allah kuce mun goro ku zauna kufara bibiyan littafin Azurfa wanda ya kunshi abubuwa masu tarin yawa .

In kin San ba comments zakiyi ba dan Allah karma ki siyi littafin nan ki zauna ko na Allah ya,isa a kawo Miki labarin Azurfa ya faru da gaske in labarin yayi dai dai da rayuwar wasu ina neman afuwan ku .

Kai tsaye zaki tura kudin karanta littafin Azurfa a wannan asusun 8068748984 Amina ma'aji opay sai shedar biya ta wannan nunber 08068748984 kafin in gama Free page 300 in nagama 500 mutane uku zasu iya biyan kuɗi su biya 700 sai na jiku .

Marubuciyar

Aminatu

Halacci ne

Zaɓi biyu

Yancin mata

Halin maza

Gidan marayu

Wata mahangar

Damai rai ake rikichin duniya

Hangen nesa

Ɗan Adam butulu.

Azurfa.

LAMBA NA UKU

______hura mishi kunnen shitayi salon nata tashin kenan ko dai ta kwantar da fuskarta a saitin nashi fuskar Sweet ka tashi dan Allah wannan wani irin bacci ne sai kace baka taɓa bacci ba haba Sweet ƙarfe goma kake da darasi kuma mutane zasu ta tsayawa jiranka wannan bai dace ba gaka da kafiya baka taɓa karban uzurin mutum ko girgizawa baiyi ba yana baccinshi cikin kwanciyar hankali ga sanyi AC dake fura ɗakin ga wani qamshi da ke tashi cikin natsuwa duk yadda tayi ta tasheshi yaƙi tashi sai da yayi ra,ayin kanshi kafin ya tashi.

Babu abun da bata gama ba dan ita ma fita zatayi tana da darasin da zata koyar kasancewar su dukkan su malamai ne acikin jami,a ,a science department suke ɗaya Physics daya Chemistry

"Bebyn Ammar shine ko ki tasheni bayan kin san duk wannan baccin kece sanadiyar yin baccin nawa shine ko ki tasheni tsabagen ƙulewa da tayi ko tabi ta kanshi ,batayi bashan shayin ta take yi cikin natsuwa har ta gama shima ya shirya ko ƙaryawa baiyi ba ya ɗauki key ya fice kowa motar shi ya hau suka kama hanya sunbar zeenat da yar aiki jidda

Sauri ɗalibai suke yi kar malam Ammar ya shiga aji in ya shiga ko kai waye koranka zai yi baya wani tsayawa yace zaiji uzurin ka,in kuwa shine yayi latti ko fara dosowa ma bazaiyi ba haka zai koma ya haƙura da darasin ko kuma ya basu Assignment yace washe gari a kawo mishi .

Ƙarfe goma da minti goma sha bakwai dai dai mutane sun taru ko agogo bai ganiba ya doshi bakin holl din kenan Affanan ta tashi ta tare bakin ƙofar .

"Malam yau kaima kayi latti dole ka karɓi hukunci kuma kabari a koyar da kai irin na daliban da kake koyarwa ido ya bita da shi cikin zuba mata ido irin malaman nan ne masu ra,ayi a duk abun da suka saka agaba ,kowa ya tsaya ana kallon Affanan duk tsoro ya bayyana a fuskokin su sun rasa tacewa wasu na cewa tayi dai dai wasu na cewa batayi ba kowa da abun da yake faɗa .

"Malam yau mune zamu koyar bani komai nine zan koyar ya kalleta duk da ɗalibai suna tsoron shi amma ya rasa yadda akayi,yarinya kamar wannan mai tsaurin idon ta tsaya mishi a rai miƙa mata komai yayi kowa ya shiga aji shima ya zauna ta gaishe da ɗalibai kamar yadda malamai suke yi

Cikin ƙorewa tafara koyar da darasin da malam ya nuna mata,tanayin bayani cikin ƙwarewar aiki kamar daman ita ce malamar kowa yayi shiru sai bayani takeyi akan abun da ya shafi wani ɓangare Chemistry duk sukayi shiru cikin nutsuwa sai da ta gama ta ,tayi tambaya yawanci aka bata amsa suma suka tambaye ta ya warware musu komai malam Ammar yayi shiru da,alama har ɗaliban sunfi gane nata sosai cen waje yayi shiru ko yarwa yayi masifan yi mata kyau sosai.

Ya shiga tunani da mamaki taya akayi yarinyan nan ta gane wasu abubuwan da shi bai gane ba taya yarinyar nan ta ɗauke hankalin shi a kan wannan abun ya akayi har takeda kwarin gwaiwar yi mishi haka me take taƙama da shi yana cikin yin wannan tunanin ne sai yaji tayi mishi tambaya.

Malam!

Malam Ammar akwai tambaya ne in babu zan bada Assignment da kuma group Assignment kowa yayi shi kaɗai sannan a haɗu group mutane shida shida ayi a kawo gobe misalin ƙarfe tara na safe 9am .

Cikin tsarewa take wannan maganar cikin hikima da fahimtar duk wanda yake wajen da kuma darasin da take koyar wa duk wahalal da ke tattare da koyarwa

Ya kasa koda motsi yarinyar nan ba,a taɓa yi mishi abun da tayi mi shi ba sai yau kowa ya watse ana fitowa Maryam da kausar suka rungume ta .

Gaskiya yau kin biya mu kin ga idon malam kuwa karfa kija mana ya kayar da mu dan laifin ki zai shafi duk wanda kuke ,a laƙa da ita ke kanki kinsan haka Meye abun yi wallahi yaban tsoro Kinga yadda ya keta wani shan qamshi kuwa amma fa sai dake Affanan kinyi wuta sosai haka mazan suma suka ta ihu kowa yana fadan albarkacin bakinshi .

Haka ya shiga office ɗinshi sai Safa da marwa yake yi yanzu wannan ya rinyan itace tayi mun haka waye ma sunan ta sannan waye ya daure mata gindi a cikin makarantar nan da har zata yi mun abun da babu wanda a kayi wa a cikin makarantar kiranta zansa ayi in ga dame take taƙama har kusan ƙarfe ɗaya yasa a ka nemo Affanan .

Da sallama ta,isa cikin isa da gadara tayi sallama ko ya amsa in har ma ya amsa ko abun dake cikin office ɗin ba lalle wasu suji ba ko ce mata ta zauna baiyi ba shiru yayi da taga ba shida niyar yin magana tayi magana "malam gani kace in zo Allah yasa lafiya ba kuma laifin na ƙara ba .

Ko jiyowa baiyi ba da taga haka tatashi zata tafi yayi magana

"Meye sunan ki ?

Sunana Affanan Jibrin Usman

"Mekike taƙama da shi har kika yi mun wannan walaƙancin mekike gadara da shi da nací irin wannan gudumawar daga gareki bake ganin cin mutunci ne ko tozarci agun sauran ɗaliban da kika yi mun haka agaresu yanzu in wani ya dauki photon mufa ko wani video kice Meye kenan .

"Menayi kenan?

"Malam kaine ka ɗauka akan wani manufa amma nikan babu komai kai yanzu bai zame maka abun burgewa ba ace dalibar ka tayi koyi da, abubuwan da ka koya mata shine laifin da nayi kenan kayi hakuri ko gobe kayi latti irin hukuncin da zamuyi maka kenan zan iya tafiya in ka gama shiru yayi yana kallon yadda bakin ta yake motsi in tana,magana .

Tashi tayi zata fita ya dakatar da,ita

Waye ya sallame ki bayan bangama miki tambayoyin da zan yi Miki ba "naga baka da niya shi yasa zantafi ina da abunyi ga lokacin sallah yayi in bakayi nizanyi sallah

Shikenan jeki amma gobe ki tabbatar kin karbi Assignment din da kika bayar kuma kinyi making kinji ko komai kiyi sai ki kawo mun ingani .

Har zata fita kuma ta dawo ya kamata kaima kayi ka kawo tunda a matsayin ɗalibi kaima kake a lokacin kuma karfa ya wuce ƙarfe goma .

Lalle yarinyar nan nine take kafawa dokoki kamar wani ɗan ta zanyi maganin ta tunda har tanan ta bullo amma akwai nutsuwa a tattare da ita malam kamilu ne ya shigo ",kai meke da mun kane duk kawani rikice .

Dogon numfashi ya ja kafin yayi magana "ka bari yau dalibai ne suma suka rama abun da nake yi musu rufe ƙofa sukayi har wata ta koyar da su kaji fa yaran nan komai sai da ya gayamishi .

"Amma wace yarinya ce mai irin wannan ƙwazon haka na jinjina mata bata da tsoro ko kaɗan gaskiya haka,ake so amma ai ba komai tunda ya wuce .

Ba wani wuce wa dole tazo ta bani haƙuri kawai ,da na Kirata ko kallo na batayi ba

Ko dai son ka takeyi ne

So kuma haba waye sa,an ta da zatace tana so kawai abun ya na damu nane

Mun shiga wani fanni kuma akwai darusa masu yawan gaske a labarin Ammar

AZURFA

STORY AND WRITING BY AMINA MA'AJI MAMAN KHAIRAT

Ina jama,a albishir dan Allah kuce mun goro ku zauna kufara bibiyan littafin Azurfa wanda ya kunshi abubuwa masu tarin yawa .

In kin San ba comments zakiyi ba dan Allah karma ki siyi littafin nan ki zauna ko na Allah ya,isa a kawo Miki labarin Azurfa ya faru da gaske in labarin yayi dai dai da rayuwar wasu ina neman afuwan ku .

Kai tsaye zaki tura kudin karanta littafin Azurfa a wannan asusun 8068748984 Amina ma'aji opay sai shedar biya ta wannan nunber 08068748984 kafin in gama Free page 300 in nagama 500 mutane uku zasu iya biyan kuɗi su biya 700 sai na jiku .

Marubuciyar

Aminatu

Halacci ne

Zaɓi biyu

Yancin mata

Halin maza

Gidan marayu

Wata mahangar

Damai rai ake rikichin duniya

Hangen nesa

Ɗan Adam butulu.

Azurfa.

LAMBA NA HUƊU

Maryam da kausar sai dariya suke yi yadda taci magani "mema yace Miki shidin kar dai faɗa yayi miki naga kin dawo jikin ki yayi sanyi sosai me yafaru bamu musha "ku bari muje muyi sallah sai in baku labari suka wuce masallaci suka gabatar da sallar azahar sai da suka fito kafin tabasu labarin duk abun da ya faru "kun san Allah wallahi sai nasa yaron nan ko in ce malamin nan yayi laushi ba dai shi ɗan mai taurin kai ba da,isa da nuna gadara zanyi maganin shi muwuce muyi Assignment din kowa yayi daban daban zan kwatanta muku dan kun san sai mun dage tunda da malami muke saƙarsaka,ko ya kuka gani .

Wani class suka wuce a wa biyu suka gama kowa tasa number ta,a jiki basuyi iri ɗaya ba balle yace kwafa sukayi ƙarfe hudu kowa ya wuce gida tare da kewar juna ƙawaye ne amma tamkar yan uwan juna .

Malam Ammar

Tunda ya koma gida ba shida aiki sai mai maita sunan Affanan Jibrin Usman haka yata mai mai tawa har mai aiki ta kawo abinci ta jera yana zaune yayi shiru ko magana babu .

"Sweet lafiya kuwa kafita baka ci komai ba ka dawo ma haka wani abun ne ke damun ko kodai yaya meke faruwa wallahi na rasa gane kanka nikam yau nifa tun ƙarfe ɗaya na dawo ina ta bacci yanzu ma Zeenat ne ta ,tasheni daga bacci shiyasa "dan Allah kubar ni bana son tambaya kusa mutum agaba da tambaya ga abinda ya kamata kiyi amma kin kasa shine kike wani tambaya na saunawa nake cemiki bana son yar aikin nan ta ƙara shigomun falo da zumar ta kawo mun abinci sau nawa na faɗa amma ko yau she kice aiki ya yimiki yawa ke ko kunya bake ji ace abu mafi sauƙi da zaki dafawa mutum acikin gidan nan shine taliya ko shayi wannan wace kalar masifa ne kibar yarinya taci gaba da kulawa da zeenat sannan ke kuma ki dafa mun abinci nací kawai shine ba zai iyu ba, mutum da iyali na a ce kullum sai naje cin abinci ke ko kunya ba kaji Salma.

Haba sweet shine sai kayi faɗa amma fa karfa ka manta wannan aikin irin shi kake yi kaima Taya zan dawo in shiga kitchen kuma ka tausaya mun mana kaifa kana dawowa zaka watsa ruwa sannan ka kwanta nifa kullum cikin aiki na keyi .

Aiki kuma ban gani ba

A kan Salma ya fuce ya yi mata tas har sai da zeenat tayi magana"Affi na nine zan shiga inyi maka girki mommy wallahi bata,iya komai ba kawai dai batason ta koya shine manufarta so nawa Jidda take cewa ta ko ya mata kowai dai bata son koya ne shiyasa .

"Yauwa zeenat ke kin gano mamanki Allah yayi Miki albarka bebyna jeki kwanta kawai kiyi bacci karfa ki tashi sai da safe .

"Yanzu a gaban yarinyar nan kake gayamun magana son ranka haba Sweet meyasa haka ne zeenat da shegen wayo yanzu sai ta gayawa ƙawayen ta duk abun da ya faru kasan ta kuma kasan halin ta shayi ya sha shida kanshi ya dafa indomic yaci ya kwanta duk yadda a kayi bacci ya dauke shi kasawa yayi tashi yayi shima yayi Assignment zagewa yayi har da tambayan sauran Abokan nan shi don suƙara mishi haske har gari ya waye bai ko rintsa ba kawai yana kwance ne .

Ƙarfe bakwai da rabi zeenat ta shigo ta bashi kiss kumatu ita ma Affi zan tafi direba yana jirana sai mun dawo "to mamana Allah ya kiyaye hanya ya kuma dawo da ke lafiya bye .

A gurguje ya shiga wanka ya fito har ya zauna zai karya loma ɗaya yayi yaji babu wani ɗandano fitowa yayi ya fice takwas da rabi ya,isa haka ya kira wani yaro yace ya bawa Affanan .

Kowa ya tara ita da kanta tayi makin amma batayi nata ba tayi na malam Ammar Usman Ali shiru tayi ganin yayi duk abun da ya dace har makin ɗinsu yazo ɗaya da kausar sai da taga gama ta taka har office takai Mishi yana rubutu jin sallamar ya tsaya samun gu tayi ta zauna ta gaisheshi .

Gashi nayi duk abun da kace in yi kuma nayi ka duba nawa kuwa kaine zaka yi making da kanka gashi "ki tsaya in duba "

Yadda yake dubawa kamar damar ita tsohuwar Malama ce mutane da yawa sunci sosai har yazo kan nashi ya,ajiye ya ajiye na kausar .

"Kinyi ƙoƙari sosai wannan waye ce da makin din mu yazo ɗaya da,ita tayi ƙoƙari sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login