Showing 51001 words to 54000 words out of 71593 words

Chapter 18 - Matar Dr Saiyadee Complete Book by Mhiss B~hal Ce.pdf

fad'awa kowa ga dubu goma nan kiyi
kud'in mota Allah yayi miki Albarka, saida Hajiya Humaira tayi dakyar ZeeSarki tah amshi kud'in,
zuwa k'arfe d'aya ZeeSarki takoma gida tareda alk'awarin zata dawo, numban Amrah takarb'a
dan tadinga jin how far, sai bayan tashiga adaidaita takula wayan Ummulkhair nah hannun tah
atake takashe tah B'oye, bayan tah tafi Hajiya Humaira tasoma yiwa Amrah bayanin abinda
yafaru shuru tad'an yi sannan tace, Umma yayanmu bai kyauta bah wlh Antynmu batada
matsala koh kad'an yanzu Allah kad'ai neh yasan halin dazata shiga wlh, idan tafarka Allah yasa
kada tah manta dah komai, rai ahad'e Hajiya Humaira tace, Allah yasa dai tamanta dah
Abubakar dah rayuwar shi, mara kirkin yaro kawai, Umma kiyi hak'uri kada kijefe shi dah
magana cikin fushi mantawa dashi ba shine mafita bah, Amrah kota mance shi koh bata mance
shiba nariga nah yanke hukunci abinda zanyi ina jira neh tafarka kawai nayi mata wasu 'yan
tambayoyi dazaran nasamu ansan su zan d'au mataki, naji dad'i dah Abban ku baya gari hakan
zaibani damar yankewa Abubakar hukunci daidai dah laifin daya aikata, kuma banaso kowa yaji
shiyasa ma nace kada kibari Amal koh Bilal susan kinfito cax sunfi kusa dah Abubakar kuma
zasu iya batamin plans, kin taho dah kayan shayi? A'a mom, tashi ki koma kihad'a kayan shayin
kitaho dasu make sure no one see's U, "alright mom" tace sannan takoma gida tahad'a kayan
shayin juz as instructed, ahanyar tah tadawo wa tah tsaya siyan fruits sannan tawuce clinic
straight har suka k'arasa tunanin Ummulkhair take, toh ina yayanmu yaje, toh dah Antynmu tah
mutu fah, bayan takoma take cewa Hajiya Humaira, "Umma kuma yayanmu babu abinda
yasame shi kina gani zai iya barin tah cikin wannan yanayin dah gangan?" rufemin baki sakarai
meze sameshi inbanda aikin shi daya d'aura asaman komai tun kafin yayi auren ance miki baya
kwana a Asibitin neh?, for some reasons I have to punish him, bcax of his carelessness I lost
my 1st grandchild ga pneumonia ajikin er mutane ance miki k'arramar cuta ce?, ido Amrah
tazaro tareda saka hannu biyu tarufe bakin tah, this is serious tah furta shocked and
disappointed, so mom how's it goin to be yanzu from the view of things the situation is very

critical, bara tah farfad'o aini nah gama tsara komai kuma my plans goes withu be careful and
keep ur mouth dead! Next On MDS @Pg.53 Ku kyalemin Saiyadee o sai murna suke za ad'auki
mataki� God dey O


Mhiss B~hal Ce
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf Ce��: NoVelWriTter
☣Mhiss~B~hal‍♀☣

⏳53⌛

‍♀‍♀ ‍♀‍♀
☘Matar DR. Saiyadee☘

‍⚕ ‍⚕




(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍[P~M ~L]✍
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the Readers}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 Hassyluv Maiduguri, God bless U sweetheart Allah yabiya miki buk'atun ki duniya
dah lahira, Do Stay Blessed #OneTrueFan#���

Abusaiyeed neh yafito daga Asibiti motar shi naga yashiga sannan yafidda waya yafara kiran
layin Ummulkhair, akashe yaji layin, mamaki neh yakama shi bcax this is very unusual, kuma
dailing yayi yaji shi akashe, amman ai tanada charge, I Unplugged her phone myself jiya dah
asuba kuma Ummunah bata fiye misusing phone bah, God of Earth yace, yanah jingina kai
ajikin mota, yanzu yazan san abinda takeso bayan springrolls, mota yatada ya tsaya wani waje
yamata siyayyan kayan ciye2 iri2 harda springrolls, shawarma dah Samosa, sannan yakama
hanyar gida, yanah zuwa gida yatarar dah main gate abud'e, lamenting yafara yi tun daga mota
akan cewa it isn't save yanda tabar gidan abud'e tunda bayanan, yanah shiga yakuma tarar dah
wani shock of his life k'ofan ciki ma wanda zaiyi leading to main parlour abud'e yake wide open,
ga d'igon jini ako ina, kamar wani dull baby haka yabi wannan d'igon jini har zuwa kitchen inda
yaga jini sosai ak'asa yanah mashi maraba, kalle~kalle yasoma yi yaga flesh d'in samosa datayi
preparing ga kayan lambu datayi greating shima abud'e, convincing kanshi yayi dacewar she's
inside her room, kamar wanda ka d'aurewa k'afa haka yataka zuwa d'akin Ummulkhair, nanfa

tashin hankali ya riske shi babu ita babu alamun tah, kamar wani mara hankali haka yafara
duba koh ina acikin gidan yana cewa Ummunah banasan irin wannan expensive jokes d'in
please come out I've missed U badly, shuru har saida ya zagaye koh ina agidan babu itah babu
alamun tah, one more time yakuma komawa d'akin tah with the hope of tana ciki, ahankali yake
bud'e k'ofan hoping that it will reveal her, bayan yabud'e for sure yaga she's no where to be
found hakan yasa yazauna yabuga uban tagumi yafara salati yanah kuka, Ina Ummunsah take?
Is she save? Is she ok? Meya sameta? mesah bata fad'a masah bah? Is this a joke or what?
Someone please tell me it's a dream, afirgice yafita daga cikin gidan, yanah fita yaci karo dah
Maman Hanan dah mijin tah sun dawo suna k'ok'arin shiga cikin gida dah mota, Baban Hanan
naganin shi yasauka ya mik'a mishi hannu suyi musabaha, maimakon sugaisa saiya rik'e
hannun kawai yanah hawaye, "matata" yace yanah kallon Baban Hanan kamar wani yaro, toh
Subhanallahi meya samete, Maman Hanan saurin fitowa tayi daga mota jin ya ambaci Matata,
"jikin natah neh" cewar Maman Hanan, fitowa tayi tah dawo gefen mijin tah, batada lafiya neh
Saiyadee ya tambaya cike dah damuwa? Eh jiya her body was almost critical dan batasan
abinda yake damun tabah, nan ciwo chan ciwo ga zazzabi daya rufeta, nashiga naduba tah
nabata magani saina kwantar dah itah tah huta akan zanje nadawo toh Abban Hanan kuma
yazo yatafi damu gida chan dawowan mu kenan yanzu mu achan muka kwana, buh gaskia
jiyan nan I felt pity for her, she's sick, kunya ce tarufe shi sosai akan yanda zai fara masu
bayanin shima shigowar shi kenan, hakan hawayen bak'in ciki suke tsiyaya daga idanun shi
yace, it's so unfortunate my wife is missing, I juz arrived not more than 10mins back, jiya kwana
nayi a asibiti inada patient she's pregnant and kuma cikin bai zauna dakyau bah inata k'ok'arin
kada ayi asaran shi I couldn't come back home, I was there at the hospital with My pregnant
patient and still the baby had to pour out, ni bansani bah ai, Madam dakin kirani, cewar
Abusaiyeed, gaskia dai maybe dataga nah jima ban shigo bah tah tafi gida, sabida kanta yanah
ciwo har tanah shafa k'ank'ara dan tad'an ji dama~dama, amman kaje gida tukunnan kaji koh
tanah gida ai bazata wuce gidan bah, jini neh duk acikin gidan yafad'a dah sabbin hawaye
wanda suke zuba kamar anbud'e famfo, tsoro neh yakama Maman Hanan dah Baban Hanan,
muje mugani cewar Baban Hanan, Bismillahn ku yafad'a leading them to his house! Next on
MDS@Page.54�


Mhiss B~hal Ce
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf Ce��: NoVelWriTter
☣Mhiss~B~hal‍♀☣

⏳54⌛

‍♀‍♀ ‍♀‍♀
☘Matar DR. Saiyadee☘

‍⚕ ‍⚕





(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍[P~M ~L]✍
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the Readers}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 ZeeSarki, Deejah Nakundu, Miss Biey cholli, Hassyluv, Maman Sadeeq Lagos,
Mama Sky, Sahla, Asmeey Husnert, Ayeesha, and D rest I Love U Ol Tag#TrueFans#�

Ciki suka shiga Maman Hanan tanah daga bayan mijin tah dan itah abin ma tsoro yake bata,
sai asannan yaga cewar jinin ma ai har tsakar gida hankalin shi sosai yakuma tashi haka
yakaisu ciki yana cewa, "kunga fah Ummunah batah d'akin tah, kumama bah wayan tah yak'i
shiga bah" wlh sun d'auke min farin ciki nah yafad'a yanah ja dah baya kamar wanda baisan
abinda yakeyi bah, cikin sauri Baban Hanan yarik'e shi sai faman salati yakeyi, cikin nutsuwa
yakalli Abusaiyeed wanda duniya tah sauya masa yace, "shi musulmi anaso idan yabu yafi
k'arfin shi yadaure yadinga fad'in, Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, Dan Allah kah nutsu kafara
dubo gidan su tukunnan, muje nakai kah, kallon Maman Hanan yayi wanda taci kukan tah
tak'oshi gabad'aya lefin kanta take gani, gani take data koma dah Ummulkhair abu bai sameta
bah, tashi ki shiga gida bara muje mudawo! Kai tafara girgiza wa Baban Hanan cikin sauri tana
fad'in nidai ban iya zama tsoro nakeji, muje tare koh ka kaini gida gurin hajiya, hannun tah
yakama cikin nashi yaji sai rawa hannun nata suke janta yayi jikin shi yana cewa, "haba dear
nah yanzu baki yarda dah kaddara bah harkina cewa baki iya zaman gidan ki akwai inda yakai
d'akin mijin ki rufin asiri neh?", kije ni nace kije babu abinda zai sameki Insha Allah, toh tace
tanah dad'a k'ank'ame shi, muje kinga Hanan tanah bacci cikin mota kada tah tashi, juyowar su
keda wuya sukaga Abusaiyeed yab'are baki sai kuka yakeyi kamar yaro, duk abinda sukeyi neh
yadad'a tuna masa dah Ummulkhair Saboda itama haka takeda tsoro, tashi yayi jiki asanyaye
yafita waje, mukullin mota Maman Hanan takarb'a gurin mijin tah ta shigar dah motan shi cikin
gida, sannan sukuma suka tafi amotan Abusaiyeed, Baban Hanan neh yayi driving sabida
condition d'in Saiyadee, basu wani dad'e bah suka iso k'ofar gidan su Ummulkhair, saita kanshi
yayi dan kada afuskanci komai yanda Baban Hanan yabashi shawara, suna zuwa Affan yana
fitowa daga gida, laa yayanmu sannu dah zuwa dariyan k'arfin hali kawai yakeyi, Yasu Mummy
please d'an kiramin Ummunah nabata sak'o, ai batazo bah kaganni nan yanzu nah bud'e
gidanma tun jiya zand'an je chan, Ok bara nakira tah naji koh wajan hajiya taje, faking call yayi,
sannan yace, ashe tanah kabuga daman yauda sassafe nace tah tafi konan koh chan, toh nayi
tunanin nan zatazo sabida nasan tayi missing Mummy, A'a kuwa batanan yayanmu tayi maka
kara chan taje, toh shikenan nagode bara naje yanzu bazan iya gaida su Mummy bah it's to
early, haka sukayi sallama yanah shiga motan yace wa Baban Hanan yi sauri mubar nan gurin,
suna barin wajan gumi yafara keto masa yafara kuka mai sauti tamkar yaro, yanah fad'in
"Ummunah kina ina bazaki dawo bah sai Zuciya tah tafashe" gida Baban Hanan yamaida su

yace, "kah kira chan gidan ku kaji" aikuwa take yakira Hajiya Humaira cikin normal muryan tah
suka gaisa, kuka yafara matah akan waya, kazo gida yanzu kawai tace masa takashe wayan,
Asibiti tabari bayan tah Umarci Amrah tazauna karta bar side d'in Ummulkhair koda wasa, gida
tawuce straight kusan tare suka isa dah Abusaiyeed, ciki suka shiga, yace ashe Umma
bakyanan, aw bazaka gaisheni bah saidai kajefe ni dah tambaya, am sorry Umma Ina kwana,
anyway daga gidan frnd d'ita nake batada lafiya, menene kake kuka akan waya kuma, wasu
sabbin hawaye neh ke gangaro masa, cikin tsananin tashin hankali yace, "Umma banga
Ummunah bah" wlh bata gidan su Umma nashiga uku ya zanyi dah rayuwa tah, take tah had'e
rai tace, "bangane bakaga Ummulkhair bah", batare kuka kwana bah, tashi kayi bakagan tah
agefen kaba koyaya, A'a Umma inada patient ban kwana agida bah dana dawo dasafe bah ita
bah wayan tah sai jinin tah koh ina agidan, Umma wlh bata gidan koh ina naduba, Umma ki
taimake ni, Abubakar tafad'a atsawace, nutsuwa yad'an yi yanah kallon idanun tah dah fuskan
tah dasuka canza, kana jina? Kai ya girgiza mata alamun Eh, wlh duk inda Khairiya take saika
nemo min itah kafin nan zuwa dare idan bahaka bah idan kazo gidan nan kasa aranka bawaje
nah kazo bah kuma Wallahil azeem kafito min dah ita koh nah kaika kotu, Innalillahi wa Inna
ilaihi rajiun, Umma banida kamar ki kada kiyimin haka ki taimaka min, taimako kace komai? Kai
bakasan darajar aure bah bakasan what it takes mace tah tare gidan kah tafara sabon rayuwa
dakai bah?, tun kafin kayi aure nayi maka fad'an kwana a asibiti, sannan nace maka bayan aure
kada kasake katab'a kwana awaje idan kuma takama dole kah kwana toh kah kawomin
Ummulkhair danko gidan su baida ce kah kaita bah kuma barin tah kwana ita d'aya agida is not
save, amman saika watsar dah magana tah, kaga da ace agida kah kwana komin banza
zakasan what actually happened even if U can't help, amman.......... Bai bari tah idda maganar
tabah yace, "Umma wlh jiya patient d'inah me ciki ce cikin ke k'ok'arin zubewa sabida bai zauna
bah I had to stay with her at the hospital to save her life and the baby's, dole akwai alluran
dazan dinga bata akai akai ina monitoring d'inta, Hajiya Humaira hankalin tah atashe jin abinda
yace, wato Ummulkhair tanah gida nata cikin ya b'are shi yanacan wai yanah ceto wani cikin
dan kada yab'are, is that ur excuse tah tambaya cikin tsananin b'acin rai? Wlh Umma dagaske
nake, wani wawan mari tah tsinka masa tace, "tashi kaje kah nemo min Ummulkhair kuma wlh
idan baka nemo tabah daganan zuwa gobe, zan sanar dah iyayen tah nakaika kotu, fita mara
mutuncin yaro kawai! Next on MDS @ Page 55. Stay Blessed‍♀


Mhiss B~hal Ce
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf Ce��: NoVelWriTter
☣Mhiss~B~hal‍♀☣

⏳55⌛

‍♀‍♀ ‍♀‍♀
☘Matar DR. Saiyadee☘

‍⚕ ‍⚕




(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍[P~M ~L]✍
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the Readers}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 berries ZeeSarki, Deejah Nakundu, Miss Biey cholli & Hassyluv stay blessed I
cherish U guys alot�


"Ummah" Wallahil azeem bawasa nakeyi bah banganta bah wlh daga gidan su nake batanan,
Umma ki taimaka min Dan Allah, tashi kafita Abubakar kuma wlh kanemo tah koh kuma kasha
mamaki nah Hajiya Humaira tanah kaiwa nan tawuce d'akin tah, tashi yayi bayan wajan minti
goma gwiwa asanyaye yabar cikin gidan, cikin mota yasamu Baban Hanan wanda shima
yashiga duniyar tunani, yanah ganinshi yace "tana gidan neh" reaction d'in Abusaiyeed neh
yasa yasan cewa batanan, "kaini dutsen goron dutse" Abusaiyeed yafad'a yana kallon gabanshi
gawani zafafan hawayen dake tsiyayo mishi, bangane nakaika dutsen goron dutse bah cewar
Baban Hanan looking confused, eh kaini zanje nahau sainaga inda Ummunah take nah rok'e
tah tadawo, ajiyar zuciya Baban Hanan yasauke sannan yaja motan suka wuce gida straight!
ZeeSarki ce zaune takira layin Amrah, bayan tah d'aga neh take tambayan Amrah jikin
Ummulkhair, wlh Zee jikin Alhamdulillah tunda akayi mata k'arin jini sai godiya dan tama motsa
saidai haryanzu the oxygen is supporting her in breathing! ajiyar zuciya ZeeSarki tayi tace, "toh
Allah yabata lafiya, Insha Allah nima zan shigo zuwa jimawa" Allah yakaimu Amrah tace kamun
suyi sallama, zama Amrah tayi gefen Hajiya Humaira tace, "waini Umma fah tun safe kike
tunani kuma babu kyau" hmmm badole bah Amrah yanzu fisabilillah yayanku yakyauta wannan
yarinyar inba gani nayi tah mik'e kalau bah banida nutsuwa, nan tah labarta mata zuwan
Abusaiyeed gida wai yanah neman matarsa, Umma kiyi hak'uri Dan Allah Insha Allah zata tashi,
toh amman Umma meza kiyi idan tah tashi komawa gidan yaya zatayi, sam babu wannan
zancen, Maryam Abacha American University nah nijar zantura ku keda ita, ke kiyi degree itah
tayi masters, Umma auren nasu fah? Dan Allah Umma kiyi hak'uri hukuncin nan yayi tsauri
dayawa, babu wani tsauri hakannan yake yanda nah tsara tanah warkewa sosai zaku wuce dan
ba zaman aure takeyi bah kawai tanah mishi gadin gidansa neh,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login