Showing 36001 words to 39000 words out of 71593 words

Chapter 13 - Matar Dr Saiyadee Complete Book by Mhiss B~hal Ce.pdf

of the Readers}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 All My groupies indai kina cikin group d'inah kowanne toh page d'innan nakune, Ina
Alfahari daku dah kaunar dakuke nunamin Ngd sosai ANATARE Insha Allah�

2days Later
Tun daga wannan lokacin dah Abusaiyeed yatafi Ummulkhair batah k'ara ganin sabah yau
kwana biyu kenan, adaren nafarko bataji shigowar sah dah fitan sabah so batah tabbatar koh
agida ya kwana bah amman tamishi uziri sabida yamata bayani cewa schedules d'insa are very
tight sai adare nah biyu taji shigowar shi wajajan 2am midnight lokacin tanayin sallan nafila
bayan tah idar tah tashi takoma tah kwanta akan gado tayi tunanin Abusaiyeed zaizo wajan tah
amman sam tunda taji shigewar sah part d'inshi bai k'ara fitowa bah haka tah kwanta zafafan
hawayen bak'in ciki nah tsiyayo matah bacci dai takasa haka tah dinga tunanin koh wani abun
tayi masa, toh wai haka auren yake neh koyaya?, haka tadinga wannan tunanin har saida bacci
ya sace tah, abu kaman wasa yau kwana hud'u tanaji yanah shigowa amman part d'inshi yake
wuce wa kuma tanajin fitar shi dah Asuba amman still baya zuwa wajanta har tayi kuka tah
k'oshi idan abin yadame tah saita kaiwa Ubangijin mu kukanta tareda karatun Alkur'ani dan
samun nutsuwa, yau dai tah tashi dah wani mugun kasala dah zazzabi jitake idan bataji muryan
Abusaiyeed bah mutuwa zatayi dan takasa yin komai kullum part d'inshi take zuwa dazaran
yafita tah d'auki kayan sa tasa ahanci tanah shak'ar k'amshin jikinsa dahaka take d'an jin dama2
toh Amman yau hakan ba zaiyi sustaining d'inta bah dan har turaren nashi tah dinga feshewa
ahannu tanah shinshina wa Amman kamar dad'a haukacewa take dasan rungume shi dah jin
muryan shi hakan yasa tah ajiye mulkin tah agefe tayi deciding tah kira shi taji muryan sah koh
zatah samu nutsuwa, waya tah dauka without wasting of time tashiga dailing numban shi kira
take ajere babu adadi ita burin tah yadauka koh sallama yamata taji muryan shi tasamu biyan
buk'ata amman sam baya picking, kasa hak'uri tayi tacigaba dah kuka har saida yayi matah msg
kamar haka,
Ummu ina meeting let's talk ltr pls, on receiving the text tayi collapsing akan gado tah rushe dah
sabon kuka, yanzu yazata yi Abusaiyeed yadaina sonta neh or what, what actually happened to
the 'nah' dah yake attaching asunan tah, juz Ummu ya kira tah yanzu? Why? kasa bawa kanta
amsoshi tayi hakan yasa tah kira Mummyn tah dan tasamu nutsuwa k'ok'ari take tah saita kanta
sabida kada mahaifiyarta tah fuskancin komai, Mummy tanah picking tayi Sallama, Ummulkhair

dajin muryan Mummyn tah taji wani nutsuwa ya ratsa tah tun daga saman kanta har k'asan tafin
k'afafun tah, Allah Sarki UWA, gaskiya UWA daban Ce, kowacce UWA tafi k'arfin Wulak'anci,
UWA bakida kama, UWA kinfi komai dad'i kice MOWA azuciyoyin wanda sukasan darajar ki,
Allah yasaka miki dah Gidan Aljanna UWA, Allah mungode makah dakayi UWA, duk mai zagin
UWAR wani rashin sanin darajar tasa Ce, toh kusani wlh Allah Iyaye koh wanne sunfi k'arfin
wulak'anci ta'ba IYAYE jawowa kai targad'en rayuwa ayi hattara musan abinda mukeyi, IYAYE
koh banaka bah IYAYE neh ai sunan UWA dah UBA baya canzawa kuma idan dah kara
IYAYEN wance IYAYEN wance neh, wani ma maraya neh gaba dah baya baida IYAYEN wani
kuma UBAN neh babu Wani Kuma UWA, kai\ke da kike\kake dasu dukkah kin\ka kasa sanin
darajar su, toh wallahi Allah idanma bakya\baka kyautata masu karki\karka wuce yau baki nemi
yafiyar su bah domin Wlh indai babu kyautata wa IYAYE musamman UWA tofa mutum bazai
ta'ba ganin daidai Arayuwar sabah, Idan kazagi IYAYEN wani wallahi Allah naka kazaga, sai ayi
hattara idan kunne yaji jiki ya tsira, Allah yashige manah gaba! Cigaban labari, kukan dah
Ummulkhair take k'ok'arin dannewa neh ya ku'buce matah batasan sanda tafashe dah kuka
bah, itama Mummyn dajin hankalin Ummulkhair atashe tafashe dah kukan tareda tambayar
dalilin kukan dah take, Ummulkhair saida taji hankalin Mummy ya tashi sosai sannan tace,
"Mummyn mu kiyi hak'uri ki yafe min Dan Allah nasa kin zubda hawayen ki akaina, "Khairiya
nah" Mummy tafad'a cikin kuka, menene kifad'a min kinji, Mummy bkomai Missing d'inki nayi
kuma nayi nayi yace bazan zo bah sai nayi wata d'aya, Mummy sam bata gamsu dah amsar
bah tace, "Khairiya nice nah haife ki kuma babu abinda zaki b'oye min, kigaya min menene
matsalar"?, Mummynah nifa sonake naganki nayi missing d'inki dayawa jinake kamar zan mutu,
a'a bar fad'in haka kinji, kin tabbatar min dah iya matsalar kenan? Uhm Mummy ni kawai sonake
naganki! toh maza share hawayen ki bazan ta'ba barin Khairiya tabah, mahaifiyar ki tanah
kaunar ki haryau har gobe har kullum harta mutu har alahira, kidena kuka Dan Allah khairat kina
d'aga min hankali sai naga kamar zaman auren neh baya miki dad'i, a'a Mummy bahaka baneh
kiyi hak'uri daman ni sonake nah rungume ki mundad'e bamu had'uba, toh shikenan tunda kin
d'an kwana biyu zan tambayi Abbanku Insha Allah zanzo naduba ki kinji koh?, kuma har goya
kima zanyi! Dariyan murna tafara yi tanah share hawayen tah, Mummy dagaske? Eh manah
Khairiya ke Alkhairi ce arayuwa tah, toh naji Mummynah nagode Sosai Allah yabiya ki dah
gidan Aljanna, Ameen toh yanzu hankalin Khairiyan Mummy ya kwanta koh? kuma bazata k'ara
kuka bah koh? Eh Mummy bazan k'ara damuwa bah ina sonki sosai rayuwa tah, murmushin
farin ciki sukewa junansu kamar suna ganin juna, nan suka d'an ta'ba hirar su kafin suyi sallama
inda Mummy take ce matah Allah ya Albarkaci rayuwar itah dah mijin tah yabasu zaman lafiya,
koda Ummulkhair tah ajiye waya saida tayi wani kukan sabida tsananin missing Mummyn tah
datayi wani kaunar mahaifiyar tah neh yake d'auwainiya dah itah, tashi tayi tayi sujjada cikin
kuka tah godewa Allah daya batah Mummy had'e dah Daddy, Gaskia IYAYE NAGARI KAT
NEH Muna tafe Sweet Fans Next Episode @Pg.39


Mhiss B~hal Ce
[15/10 07:22] 'Yar Gatan SadNaf Ce��: NoVelWriTter
☣Mhiss~B~hal‍♀☣

⏳39⌛

‍♀‍♀ ‍♀‍♀
☘Matar DR. Saiyadee☘

‍⚕ ‍⚕




(Love&Pain Story Based On Reality)

PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
✍[P~M ~L]✍
{We don't just Entertain & Educate,we Touch the Hearts of the Readers}

www.mhissbhal.WordPress.com

Dedicated 2 All MATAN AURE gaskiya kuna k'ok'ari Allah dai yabada lada Allah yaraya yaran
Albarka masu nema Allah yabasu, Ina yabo matan aure Allah yasaka dah gidan Aljanna
Mhiss~B~hal tanah gaisuwa�

ATTENTION!!!
Agaskia tunda har attention danah rubuta Asama yaja hankalin ki\ka toh ya kamata ku nutsu
kuji abinda yake tafe dani, ak'arshe page 38 idan bazaku manta bah nasaka IYAYE NAGARI
KAT NEH! Toh wanda bah NAGARI bah fah? Ai akwai su koh? Toh jiya naci karo dawani
mumunar labari daya hanani sukuni ku aramun kunnuwan ku Mhiss B~hal tanah neman
alfarman hakan pls, Wata baiwar Allah Ce wacce batah wuci shekara sha bakwai bah aduniya
tayi aure kuma auren soyayya tayi ahaya suke zaune dah mijinta bayan tah haihu tasamu namiji
mijin yafara canzawa kusan meh? sai Allah yad'aura wa d'ansu rashin lafiya yanayin jijjiga
sannan kuma wai jini yahaura brain d'inshi sai yaron yafara acting abnormal zance yasha
banban Asibiti suka buk'aci kud'i dayawa, shikenan aka nemi miji aka rasa yagudu yabar itah
dah yaro kuma gidan haya suke, kunsa mesa yagudu?, an nemi shi sama dah k'asa babu shi
duk inda ake tunanin za aganshi anduba babu shi sai awajan wani abokin shi akaji wai baya
kano kuma dalilin guduwar sah shine sabida haya yacika za abiya sabo kuma yaro Allah ya
jarrabe shi dah cuta, meh gida yak'ara matah hak'uri zuwa d'anwani lokacin kad'an chan kuma
yace subar mishi gida saita d'auko yaro tafito bakin titi tazauna tanah rusa kuka nasan
kowannen ku zaice toh batada GIDAN UBA, anan inda take kuka wani mai adaidaita yazo
yasame tah yake tambayar tah damuwar tah, nan tafad'a masa komai, sai yace toh gidan ku fah
kinje gida? Kusan menene masu karatu? Eh taje gida UBANTA yace bazata zauna agidan shiba
dah d'anta shi bazai ajiye d'an mara mutunci agidan sabah, saidai taje tasan yanda zatayi dah
yaron tah dawo amman sam inda dah yaron nan bazata zauna agidan shiba sabida bashida
wajan ajiye yaron, sai wannan bawan Allahn yace "toh ina UWAR KI?" Sai tace banida UWA,

MAHAIFIYA tah tarasu, Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun! Wallahi Mata muna shan wahala dole
muce zamuyi karatu kafin muyi aure, ai it's because we want to be independent, tsakani dah
Allah wasu mazan basa kyautawa matan su, akwai labaran dasuka fi wannan muni, wallahi
akwai k'awar Yayata mijin tah sai yaje yasha giya ya k'oshi yake dawowa gida yanah zuwa zaiyi
amai ya'bata waje kafin tah tashi tah gyara yajawo tah yayi matah fiyad'e, kuma auren soyayya
neh kuma bata sanshi dah halin nanba kafin suyi aure, toh ni agani nah rashin bincike neh daga
b'angaran mata sabida zaiyi wahala kaga mace batason namiji tsakani dah Allah tah aure shi,
idan kinawa namiji so tsakani dah Allah sai kiga ai bashida aibu toh kina tafka babban kuskure
wallahi, ai Allah neh ya Umarce mu muyi bincike, toh mesah bazaki yi bah? Subhanallahi, wlh
Allah bai yarda namiji ya kusanci matar shi batare dah amincewar tabah, MAZA MAZA MAZA
kuji tsoron Allah dah ranar dazaku bar duniya yanzu macen dah kuke sha'awa itah kuke aure,
tabbas auren yanzu nah Sha'awa neh kuma bayan aure dazaran ankauda wannan Sha'awan
sai kiga zance yasha banban, toh kusani abinda ka shuka shi zakah girba itah rayuwa haka
take duk kunbi kunsa muna tsoron aure sabida bamusan abinda zaibiyo baya bah zakuzo
manah dah farin fuska bayan aure muga bak'ake kuke wulik, toh kuma kunada k'anne kuma
zasuyi aure kuma Kunasan ar'ike su dakyau kumesa bazaku rik'e k'annan wasu dakyau bah,
Another problem dah ake facing shine RAYUWAR K'AUYE ADAA anayi wa matah auren wuri
wanda har yanzu awannan zamanin akwai masu aurar dah 'ya er shekara goma shad'aya
wallahi wannan kwata kwata baidace bah karma kucemin Sunnah domin daa dah yanzu bah
d'aya bah kuma Shugaban halittun duniya daban yake shi, sannan U guys are after sex not the
real sunnah, yarinya er shekara goma shad'aya tsakani dah Allah metah sani?, saikaga yarinya
batasan ciwon kanta bah balle left and right d'inta amman tasan d'aa namiji, tasan meh
akecewa SEX, dole acutar dah itah gaskia adaina cutar dah k'annen mu mata, wata matar
auren dakayi matah Addu'an Allah yabarta dah mijin tah gwanda kah shak'e tah sabida tsananin
azabar dah take fama dashi agidan miji, shiyasa mafi akasari nidai Mhiss B~hal nafi yiwa matan
aure Addu'ar Aljanna domin indai daman soyayyar su dah mijin su tsakani dah Allah neh, kuma
mazajen masu tsoron Allah dah rik'on amana dah gaskia neh toh indai suka samu Aljanna sun
samu mazazen su, MATA suna shan wahala agidan aure amman dayawa suna amfani dah
kalman HAK'URI suna zama sabida Allah dah yaran su, Ya Salam�, MATAN AURE
sannun ku dah k'ok'ari Allah ya shige muku gaba ya kauda fitina wlh Inayin ku, Allah yabarku
dah yaranku dah IYAYEN ku kuma UWA kam daban take
Ya ALLAH INA ROK'ON KAH KAH SAKAWA UWA DAH GIDAN ALJANNA, wallahi wallahi duk
mai UWA baisan gatan dah Allah yayi masa bah, UWA tafi k'arfin Wulak'anci ku daraja UWA
koh wacce UWA d'aya Ce sunan baya canzawa, kuyi biyayya ga kowacce UWA Allah zai baku
ladan yin hakan kuma taku UWAR dah nagari Allah zai dinga had'a tah ako ina, yanzu wannan
baiwar Allahn daa tanada UWA wlh dah rayuwar tah tayi kyau! Toh wannan matsalan daya faru
meya jawo shi, Gurbatattun IYAYE sune SILLA, kamar yanda mukeda yara nagari dah wanda
bah nagari bah haka mukeda IYAYE nagari dah wanda bah nagari bah, toh IYAYE sune suka
haifi YARA dan haka matsalar daga wajan su take, itah tarbiya nagari yad'uwa take haka zalika
wanda bah nagari bah itama yad'uwa take, toh IYAYE kusani wallahi Allah YARA AMANAR
Allah Ce, kuma tunda kuna dashi kund'au AMANAR Allah, wasu Iyaye basu san darajar
yaransu bah kuma wannan bai dace bah koh kad'an, saikaga 'yar rik'o tafi wacce take gidansu
jin dad'i wata agidan su ma karuwanci ake sakata takawo kud'in aci abinci, tarbiyan yara yanah

hannun Iyaye maza dah mata aman kuma UWA tafi sanin ciwon kan 'ya'yan tah akan UBA toh
yake UWA kisani daga ranar dah kika samu ciki Wallahil Azeem kin d'auki AMANAR Allah,
domin yara AMANAR Allah neh kuma AMANAR Allah bah abin wasa baneh ranar dazai
tambaye ki yanda kikayi dah AMANAR sah acikin d'unbin jama'a nanan tafe, wasu matan suna
neman haihuwa wasu kuma suna tsiyaye CIKI abakin makwarara, kai mata muji tsoron Allah,
wallahi masu d'aukan cikin shege daku nake idan har kinsan kin riga kinyi wannan stupid
mistake d'in (ZINA) arayuwar ki har kika samu ciki toh kada ki sake ki b'arar wallahi koda kuwa
ke karuwa ce bakida hajjar zubar dah wannan cikin, domin kin k'ara wa kanki azabar Allah, gata
ZINA bata KISA, dah yaron dah aka Haifa tah hanyar zina dah yaron dah aka Haifa tah hanyar
Sunna wallahi duk Amanar Allah neh sabida Allah yafi kowa san kowani bawan sah aduniya,
banbancin kawai idan kikayi zina tofah keda Allah dole ki horu tun daga duniya har izuwa lahira
saidai idan tuba kikayi, kuma yaron dah kika Haifa tah hanyar zina shima zai fuskanci k'alubalen
rayuwa, dan haka masu b'arar dah ciki kuji tsoron Allah abinda yake bani mamaki wai harda
matan aure, wai saikaga macce dah auren tah dah mijin tah tasamu ciki tah b'arar, watama mijin
tah baisani bah U can Imaging yanda kike kai sahunki hanyar wuta, idan kah tambaye tah hujja
sai tace makah ai batasan tayi Konica sabida babu tazara tsakanin d'an dah take goyo dah ciki,
toh yake hajiya Konica idan kece kike bada haihuwar saiki bawa wanda suka dad'e suna nema
mugani, wai har Allah zai miki kyauta kinuna bakya so sabida jama'a zasuga rashin tazara
hhhhh kai kajimin wannan jahilcin har ina, waye yace ki b'arar? Ke kika sakawa kanki d'aa
aciki? Yaushe Allah yayi miki alk'awarin zai k'ara miki wasu yaran bayan wanda kika b'arar? kin
d'auka SEX is all about getting pregnant? Idan hakan neh mesah wasu matan sun dade suna
neman haihuwar basu samu bah? ai idan hakane dah babu wacce bata haihuwa(barren)
aduniya kenan koh? toh tunda bakida amsoshin nan bakida damar b'arar dah ciki indai banah
lafiya bah sabida akwai cikin dah ake cireshi sabida asamu lafiya, CIKl, HAIHUWA, YARA DUK
KYAUTAR ALLAH NEH, kuma AMANAR ALLAH, wacece keh dazaki wulak'anta abu nah
Allah?, sabida kin tabbatar bazaki mutu bah balle ki had'u dah ALLAH? Shugaban hallittun
duniya baiyi k'arya bah dayace matah sunfi yauwa acikin wutan jahannama Innalillahi wa Inna
ilaihi rajiun, wai azamanin daama kenan balle wannan tabararren zamanin namu nah yanzu,
Mata Mata Mata! Wallahi Mata kurage buri duk wacce tamutu duniya batayi asaran komai bah
sabida akwai dubun ki acikin sah kuma dubun ki suna kan hanyar zuwa, toh wlh yake mace ki
kula masu aikata mugayen halayya batare dah sanin mazajen subah ku kula wallahi Allah yana
ganin komai fah dan baya bacci kuma Aljannar ki tanah k'ark'ashin tafin kaf'an mijin ki, ki kula
dah dukiyar sah dah halin dah yaranku ke ciki, domin kece agida tareda su koda yaushe UBAN
mafi Akasari yanah wajan aiki,
Anyway iyayen daa kenan, iyayen yanzu kud'i yarufe masu ido UBA yanah fita aiki UWAR ma
hakan kai awani gidan ma UBAN yanah riga UWAR dawowa daga aiki, abin haushi anan shine
kwata kwata basuda lokacin yaransu daga an aika su Boko sai Islamiyya sai abasu abinci
amusu wanka, shikenan? INJIWA? kin tabbatar babu abinda yake damun yaranki at school koh
Islamiyya? kin tabbatar babu targad'e atarbiyyan su? kin zauna kin basu wadatattan tarbiyan
dah UWA take bawa yaran tah? Ohh ashe fah kinanan kina neman kud'i koh? toh abinda yake
bani mamaki shine duk wanda ya tambaye ki neman kud'in mekike yi? sai kice sabida yara nah,
kinga matsalar koh? dan yaran ake neman kud'in amman in the same process ana gurb'ata
masu tarbiya iyayen yanzu bakwa bud'e littafan yaranku balle kuga irin Asignments d'insu harku

taimaka masu dashi of which baidace bah koh kad'an amakaranta idan anbawa yara news letter
wanda school management take calling iyaye for Parents• Teachers •Association Meeting (PTA
Meeting) wlh iyayen yanzu 10% neh suke zuwa 90% suna wajan Neman kud'i Alhalin Iyayen
daa they are challenging they voice out their opinions akan yaransu idan abu beyi masu bah
they call for PTA Meeting themselves, they care about their children they watch all their moves
and activities, kuma adaan ma suma suna zuwa aiki amman sun ware special time for their kids,
I Mhiss B~hal call on all parents to be conscious akan yaran su for Future Reference!
Kafin nan idan kinada Uwa TaGaRi kitashi kiyi sujjada kigode wa Allah, dan wallahi yayi miki
baiwa sosai, sannan kiji tsoron Allah kid'aura yaranki akan tarbiya nagari dah aka d'aura ki akai
kema, d'aya daga cikin hallayar uwa tagari shine Hana erki zuwa kowani biki dah suna sabida
ita 'ya mace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login