Showing 45001 words to 48000 words out of 56324 words

Chapter 16 - USTAZIYA KO YAR DUNIYA BY AUNTY MAMIE.doc

ya rufe leemah da duka tako'ina yana kuka harda majina yana mata Allah ya isa, kallon su Malam liman keyi yana durkushe kafun a Ankara shima ya zube bakinshi dauke da salati nan asibiti aka rikice da surutai yaran Malam liman ne duka Ukun suka taruma leemah da duka ta ko'ina Alkawari sukai saisun kashe ta tunda tayi sanadiyyan kashe musu iyaye bazasu barta ba, dakyar aka kwata leemah a hannun su wacce ko motsi batayi jini sai ambaliya yakeyi ta kasanta Asibiti ya cika makil kowa na ganin abun Al'ajabi kassncewar Malam liman sananne hakan yasa harda yan'jaridu da TV stations anata kokawan daukan labarai, cikin hanzari aka karayin gaba da leemah inda saida tarasa hakora Uku biyu a saman baki daya a kasa ta gefe duk yanda akaso ankasa daidaita numfashnta inda ake shirin sakata a coma.


AK kuwa gaba daya chanzawa yayi yayinda abun yafara ba Aisha tsoro ganin dama AK ya iya magana haka, kwana daya yayi a Asibitin dakyar Wanda daran jiya yadamu Aisha da roko da magiya akan tayafe mishi ganin duk abunda yake mata bai hanata jinyar shiba dukda babu yanda baiyi da ita akan ta kwanta akan gado ba amma kememe taki inda ta raya daran nata wurin Rokan Allah akan ya daidaita rayuwarta ko'itama zata samu jin dadi tun AK na kallonta Yayinda take burge shi har bcci yayi awon gaba dashi, washe gari Dagewa yayi akan bazaici abinci ba wai hannun shina ciwo a cewarsa mahuta ya bugan masa hannu sosai yanama tunanin har'yayi targade hannun yayi tsami inda Aisha baki bude take mamakin yanda Yaya AK ya kware a karya idan bata mance ba baima ba mahuta damar dukansa ba amma ji yanda yake gilma karya babu ko kunya, kiri kiri yakicin Abinci dukda yanajin yinwa a cewarsa indai Eesha bata bashi a baki ba tohfa saidai ya mutu da yinwa ko jiyama haka yayi inda madara kawai yasha Aisha kuwa ta murzama idonta toka dukda Tausayin shida takeji bataso yasamu weakness dinta, ana cikin haka ne kaninshi Abdulhakeem ya shigo inda AK yahade rai tareda kunkuni, "wai nayau ma kawai baza'a bar mutum ya sake da iyalinsa ba? Mtseww, Zama Hakeem yayi tareda murmushi, Daddy ne yace inzo in kwana dakai a Asibiti Anty ta koma gida itama ta huta.......ka kwana dawa? Badai niba? Wace Antyn? Badai my Eesha ba? Yafadi fuska a hade kamar zai mangare Hakeem, Allah ya kyauta in kwana da katon kato a daki daya bayan inada matata wacce zata kula dani, my Eesha ko bakyaso ki samu ladan jinyar mijinki ne? Ya fadi murmushi akan fuskarsa, mikewa Aisha tayi yayinda tajawo hijab dinta tareda shirin tafiya dukda tanaso ta kasance da Mijinta, kallon Hakeem tayi, 'yauwa ka bashi Abinci a baki yace bazai iya Amfani da hannunsa ba Nina tafi saida safe, 'wait Wait???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? Hakeem ya furta cikeda dariya yana tafa hannu tareda nuna AK da yatsa, Badai Bros kike nufi zanba abinci a baki ba tsofai tsofai dashi? Nooooo it can't be possible kuna wasa ne wlh bazanba wani kato abinci a baki ba look ki ciyarda mijinki, 'nine katon? AK ya Tambaya sounding so serious fuska a harde, " am sorry bro but u and ur wife are very funny, 'Nina tafi Aisha ta furta tana shirin bude kofa inda AK yayi wani mugun tsalle daya tareda damko ta saikace bashi ke jinya ba, rungume ta yayi sosai da hannuwa duka biyu ta baya har'saida tasaki yar'kara sai kokarin kwace jikinta takeyi ina yaki barinta ihu tafarayi kasa kasa tana bubbuga kafarta cikin shagwaba, Kallon Hakeem yayi Wanda yasaki baki da hanci yana kallo da mamakin salon yayan nashi, toh magulmata sai abamu wuri koh jeka waje ka nemo mun lemun bawo mai zaki, 'Allah ya Baku hakuri ni ina zan iya kallon abun kunyar nan? Dama fita zanyi ko'bakace ba yafadi yayinda ya Mike, but Bros wannan uban lemun fa? Yafadi tareda nuna tarin lemun zakin dake jibge a gefe daya, 'look Malam basu nakeso ba kana bata mana lokaci, ko kunya baiji ba ya juyo da Aisha tana fuskantar Sa fuska sharkaf hawaye inda yake kokarin zame mata hijab ita kuma ta kunkume taki bari, Kofa Hakeem ya kulle tareda mamakin dama haka yayanshi yake baida kunya?
"Kuka Aisha keyi maidan sauti tunowa da irin wulakancin da azabar da AK yake gana mata a ganinta rainin hankali ne kwana daya rak yadawo wai yana Santa yana Santa kodai yana Sha'awar ta? Kuka takeyi sosai.....'nooo my Eeasha please please not again banaso in Zama sanadiyyar zubowar hawayanki insha Allah daga yau har'abada please my wife karki horani ki tausaya mun.......'daka rasa swt 18 dinka koh? Daka rasa matar so? Ni banza yar'tasha Mara tarbiyya kazar kowa yar'duniya wacce batada gata wacce tagama rabarda duk wani mutincinta a titi wacce batada Amfani a gidanka face taci takuma cika maka Masai da kashi mai wari a gida....." Nooo Eeasha please please karkice haka ki fahimce AK dinki nasan naso kaina dayawa na cutar dake Wanda bazaki iya yafemunba wlh kiyimun duk hukuncin daya Dace I deserve please wife but ki kasance tareda ni karki gujeni wlh dakin San wanene ni da kinsan halinda nashiga a kanki da kinsan mahaukacin Soyyar da nake miki saikin tausaya mun.....'oh yes, tafadi tana shirin kwace jikinta daga nashi amma yaki sakinta, Soyyar da babu komai sai azaba da bauta? Soyyar tozarci da duka? Soyyar bauta? Mara yan'ci? Ko zamanin jahiliyyah bantaba jin labarin irin soyyar nanba, 'girgiza mata kai AK keyi kamar zaiyi kuka kwalla tafara cika masa ido cikeda nadama tareda tsanar kanshi akan abunda ya aikata, Aisha kuwa kuka takeyi tuno da azabar daya gana mata eye? Gayamun gayamun haka ake soyya a duniyar ka? Inko haka soyyar ka take tun wuri kaje ka nema wacce zakayi irinshi da ita badaini ba not again nagama wlh nagama kokuma idan matar so tadawo....rufe bakinta yayi danashi jin zuciyarshi tana shirin fashewa tumomai da abunda leemah tayi Wanda bazai iya sauraran taba tun ana na hankali tana kokarin kwacewa dakai masa bugu ina dorata yayi akan gadon Asibitin inda yayi Mata rumfa da jikinsa sunkai minti goma a haka har'karfin Aisha yakare inda ya sake bakinta yafara lashe hawayan dayayi Alkawarin bazasu Kara zuba a sanadiyyar saba saidai tayi hawayan dadi insha Allah, runtse ido Aisha tayi jikinta na rawa tana wasiwasi Anya ba mafarki nakeyi ba? Yaya AK kecewa yana Santa? Ashe dama zataga ranan nan a zahiri ba'a mafarki ba? 'Likita dake tsaye a kansu Wanda baiyi minti daya da shigowa ba shine yayi gyaran murya tareda kauda kansa gefe yana murmushi duba jikin AK yazoyi inda yake shirin aiko masa dawasu maganin, 'Ranka shi Dade da Alamar sallama kawai kake bukata Dan naga jiki yayi kyau Alhmdlh da Allah bai kawoni ba kila da'a dakin nan za'a sama mana tsarabar dan'baba, Hakeem neya shigo jin maganar da doctor keyi aikuwa ya tuntsure da dariya inda AK ke zaune a gefe sai kame kame yakeyi tareda gyarama Aisha dankwalinta daya cire mata, fusge dan'kwalin tayi ta cusa kanta ciki cikeda kunya shikuwa sai hade rai yakeyi a dole bayasan Raini, "bari in rubuta muku takardar sallama mu ai haka mukeso Lallai uwargida Maganinki yafi asibiti tasiri wannan aiki haka hmmm, likita yafadi cikin barkwanci tareda barin dakin aikuwa mikewa AK yayi yafara hada kaya, 'Bros ya haka? Ina kuma zaka? Inji Hakeem dayake faman dariya, 'ban saniba koba a gabanka aka sallame niba look bansan munafunci uban maiya dawo dakai bayan na sallame ka? zo kayi gida Malam, yafadi har yana hankade Hakeem waje harda Danna sakata a dakin inda Hakeem keta sheka dariya, wooooo soyyah masu gari dole inba su Mamie da Daddy labarin nan hahahaa love on point Gskia nima dady ne zai nemo mun matarda zan Aura naga alaman baya zabin banza, 'Allah ya isa indai akayi gulmata Dana matata, Ak yafadi da karfi sounding so serious Aisha kuwa Yanzu abun yadaina bata mamaki sai tsoro.








*Mrs Saddiq Rumah???b*


??Z烙?_??Z烙?_??Z烙?_
*Ustaziya ko Yar'duniya???W0???_%??]?j??W0???_%??]?j??W0???_%??]?j*




*Written by Anty Mamie*


*Afuwan jiya nayi mistake a wurin page number, 36 zansa nasa 37 yanzu zan cigaba da 38 kawai gudun rikicewa.*



38




Dole hakeem sukabi yakaisu gida yayinda ko takardar sallama bai jira ankawo ba suna isa gida mai'gadi ya bude gate tareda gaishe shida jiki yanaso ya gaya musu zuwan yan'sanda neman AK amma ganin rashin dacewar hakan Ga Wanda yadawo daga Asibiti yasashi tsuke bakin shi inda Aisha ta kira bilki batareda bata lokaci ba tazo yayinda suka Kara kimtsa gidan tas ko'ina sai kamshi yakeyi Mamie ceta kira Aisha tareda shaida mata kada tayi girki za'a kawo musu daga gida tahuta na kwana biyu hakan yasa suka koma daki itada bilki inda take bata labarin sabon salon AK dariya bilki ta dinga yi inda ko kadan bataji tausayin Shiba saima cewa datayi kadan yagani, "idan ankawo abincin ki daure kibashi a baki kada ki sakar masa fuska, a haka suka tsaida maganar, aikuwa ana kawo abincin AK ya shigo dakin da sallama "hmmm maza kenan ji yanda yayi ladabi cikin kwana biyu" yayinda yayi wanka ya chanza cikin farin jallabiya kallan bilki yayi yana murmushi, " kanwar mu sannu da zuwa yasu mama? 'Lafiya kalau suke sunce a gaida ka, tafadi dukda ada ta tsani AK amma koba komai zaici darajar Auran yayarta da yakeyi kuma tsakanin miji da mata sai Allah, my Eeasha am hungry please Dan Allah Kibani Abinci Eesha yafadi a dole so yakeyi Aisha taji tausayin shi, 'Bata Musa masa ba suka fito gaba daya harda bilki inda jalof rice ce tasha hadi sai kamshi takeyi ga hadaddan Pepe chicken awani kula hakan yasa Aisha ta zuba abincin yayinda ya zauna akan dining bilki na tsakiyar parlor tana kallo kusada kujerar shi Aisha ta zauna yayinda ganin baida niyyar ci yasa ta juyo da kujerarta sosai tana fuskantar sa tafara ciyar dashi batareda tabari sun hada ido ba inda yakecin abincin cikin natsuwa so yakeyi ta dinga sakewa dashi amma taya? Taya zai fara? Maiya kamata yayi domin gyara kuskuran daya tafka? Yah rabbi ka kawomun mafita a gidana, ya furta a zuciyar Sa inda saida yaci ya koshi sannan ta diba nata awani plate din tareda dauka tabar wurin parlor takoma inda bilki take nan suka zauna sunaci suna fira harga Allah baiso ta tashi ba dukda baida abunda zaice mata amma yanaso taita Zama kodan ya dinga kallon ta, waito taya ake lallashin mace ne? Ooh gskia lamarin mata sai a hankali dukda kukan dayayi mata a gabansu daddy Yanzu maiya rage? Oooh GOD wazai gayamai abunda zaima matarsa ta huce? Ba ance mata nasan goyo ba toh kodai tsugunawa zaiyi yace tahau bayansa yaita zagayawa da ita? Nooo nooo Goya wannan katuwar saita karyani ai, murmushi yayi tunowa dayayi da jikin Aishar, ita kuwa Aisha Rashin sabo yasata barin wurin ganin yanda ya kafeta da ido bazata iyacin abinci a gabanshi ba hakan yasa ta tashi.



A' Asibiti kuwa Ansamu Malam liman da mama sun farfado amma an rikesu a cewar likitoci sai sunyi kwana biyu saboda tabbatar da lafiyar su Wanda Malam din bai damu ba ko kadan baisan dawani ido zai kalla jama'a ba, taya zaifara? Taya? Tabbas yasan hakan na cikin jarabawar shi dukda ganganci da sakaci irin nashi dasai yanzu yake ganin gudunmawar da suka bada wurin bata tarbiyyan diyarsu nan yaita kuka yana neman gafarar ubangiji Wanda ya jarabceshi ya nuna masa duk tarin ilimin shi ba shine zai Hana Allah jarabtar bawansa ta inda bai zato ba, nan ya kudiri Aniyar idan komai ya daidaita zai karbi halima da hannu biyu baya cikin iyayan dake gudun kuskuran su zai Amsa kuskuransa da hannu biyu tareda kulada cikin jikinta har Allah ya sauke ta lfy koda kuwa jama'ar gari zasu koreshi akan yana rainon cikin shege duk zaginda za'ai mishi zai toshe kunnan Sa barna ce anriga an tafka hannun ka baya rubewa ka yanke, inda labari yagama bin gari duk inda ka waiga maganar diyar Malam akeyi karya da Gskia haka mutane keta ruruta lamarin har kasashan ya'da labarai saida akasa domin yazama iznah ga iyaye Wanda wasu da biyu sukeyin hakan domin tozarta malamin masu zagi da takaicin leemah nayi, masu ganin ganganci da Laifin su Malam nayi, harda masu Allah Kara, nidai nace kanku akeji.




Ta fannin mahuta kuwa Lauyoyin Dadyn shine suka bashi shawarar janye karar da yake shirin makawa kotu ganin duk yanda ake daukan lamarin tohfa ya wuce nan, Ranka shi Dade wannan ba maganar kudi akeyi ko matsayi ba duk abunda akace akwai idon mutane a ciki gaba daya Al'ummah sun karkata akan case dinnan kasancewar ta diyar babban Malami a ganina fa barin sha'riar nan itace hanya mafi sauki kada Allura ta tono garma babu abunda mutane ke jira illah iyaka Susan Wanda yaima halima ciki ya kake ganin za'ai idan muka fito da kanmu tareda tona kanmu har a'kasan Dan gidan babban dan'siyasan da yayi suna shine ya banka ma diyar babban Malami ciki ya kake ganin makomar siyasar ka? Goge zufa daddy yayi dukda baiso hakan ba amma Yaji dadin Sha'awar nan Allah yaso shi dayayi tabargaza garin neman gira arasa ido hakanan yanaji yana gani aka rufe case din Inda sukayi luf sukayi shiru suna kallon yanda Abun zai kasance.

Mahuta kuwa tuni aka saka mishi hakorin Roba a wawulan bakin shi inda ya kudiri aniyar nanda wani lokaci zaibar kasar domin haduwa da manya manyan likitoci asan yanda za'ai dashi bazai yiwu babban guy kamarshi ba Dan kudi yakarasa Kuruciya babu hakori a bakinsa ba, yawa ne indai kudi na aiki tohfa komai yazo da sauki tuni yakoma kan network inda ya hada duka kawayan leemah meenah da feenah ya ajiyesu gida na musamman babu ko kunya aka dasa daga inda aka tsaya a cewarsa Gari dayawa maye bazai taba cin kansa Sa Ga mata jaga jaga wasu ma koda kudinka saida rabon ka, sukuwa ko kishin kansu basayi tunda rufin asiri suke nema kuma mahuta ya sake musu kudi wani Kishin namijin bariki zasuyi Wanda baida tabbas?

AK ne zaune a parlor sai safa da marwa yakeyi misalin karfe goma na Dare Wanda tuni Aisha tadade da Danna ma dakinta sakata, sai sake sake yakeyi yarasa abunyi, dakin limah yashiga nan yafara jido akwatinan lefenta daya hada mata kaf saida ya hadasu akwati dozin da manyan jaka guda biyu, dukda ta dinka wasu bai damu ba, akwatin dankunne yabude tareda Addu'ar Allah yasa gold dinda yasa mata a lefe yananan, aikuwa yana dubawa saiga dankunne da sarka da zoben gold nan yaita kinkimar kayan yana jerasu tsakiyar parlon dakyar ya karasa dukya gaji, kai tsaye dakin Aisha ya nufa yaita buga mata kofa sanin bazai taba dainawa ba harsai ta fito yasata bude kofar fuska a hade sanye da Riga da wando masu taushi blue color sunyi kyau sosai sai kamshi takeyi tana yamutsa fuska, "yadai? Bcci nakeyi lafiya ka tasoni cikin daran nan? My Aeesha magana zamuyi ki sameni a parlor, yafadi tareda Kare mata kallo yakoma parlon, kai tsaye ta bishi kanta babu Dan kwali tsayawa tayi trus tana mamakin uban hadaddun sababbin akwatin da suka cika parlon nasu kallonta yayi, " zauna mana sarautar mata, yayinda yake nuna mata kusada shi, kan hannun kujera tadan zauna nesa dashi yayinda ta kalle shi tareda kauda ido, ehm ina jinka tafadi Alamar kosawa, "Aiishaa, yafadi in a husky voice, duk kayanda ke nan wurin ki kwasa na mallaka miki idan akwai abunda bai miki ba kibada idan akwai abunda kike bukata ki gayamun, kallon kayan tashiga yi daya bayan daya cikin Al'ajabi da mamakin jin furucin shi cikin tsohon daran nan wannan kyautar dukta mecece? Shin maiya kamata tayi? Ta Amsa kokuwa? Mai zatayi da uban kaya haka?, "ya mai karatu kuba Aisha shawara shin ta Amsa kyautar da AK yaimata kokuwa??

Gogan kuwa Rokan Allah yakeyi yabashi Hanyarda zai lallashi Eeashar Sa, " Shin wazai ba AK shawarar yanda zai lallashi uwargida?.

Ina jiran comments dinku domin samarma ma'auratan mafita ku taimaka ma AK da kalaman Soyyah kunsan fa sai a hankali ta fannin Soyyah a play class yake???a???_%??]?j???b???_
Eh:- "Kodai yace yake mintin zuciyata na tuba ki yafemun idan bake ba sai lahira??C0???i






*Mr's Saddiq Rumah*???b???_


??Z烙?_??Z烙?_??Z烙?_
*Ustaziya ko Yar'duniya???W0???_%??]?j??W0???_%??]?j??W0???_%??]?j*


*Written by Anty Mamie*


*Tun jiya nasoyin posting wlh am having a very bad network ne, duk naga comments dinku OMG naci dariya please ina fatan ba haka kukeba iga hakuri ba idan kunyi laifi tabbas wata rana zaki Iya tsintar hakoranki a kasa hajiyata??C0???i???i???i Masoyiyata nine Ak dinki???i.*




*Dedicated to Sister Husnah.*


39


My Eeasha kinyi shiru, yafadi tareda karasowa inda take ya tsuguna da guiwoyinsa duka biyun hannun ta yarike yayinda ya kafeta da ido Aisha kuwa banda bugu babu abunda zuciyarta keyi, "kana tunanin kayan nan zasu siyeni ne? Mai zanyi da kayanka? Au wato saboda babu matarso kwalliya bata biya kudin sabulu ba shiyasa ni banza ka dauko kayan dabada sunana akayi ba kakawo munko? Bana bukatar su maisu zata dawo ta dauki abunta 'hawayan da take kokarin boyewa suke zubowa, " Aaaisha ki bude kunnanki dakyau kiji abunda zan furta miki sannan sai kiyimun duk hukuncin daya Dace dani na Amince na yarda ban chanchanci yafiyarki ba, kayan banza bayan dakai da kaya duk Mallakar wuya ne, da kayan dani kaina duka naki ne a karkashin ki muke saikuma yanda kikayi damu Allah yasani Aisha zan gaya miki sirrin da babu Wanda yasani saike da zakiji a yanzu Wanda duk abunda zan furta miki shine ainihin gskiar magana, "mikewa yayi daga tsugunnan dayayi tareda Zama kusada ita harda Kara juyo da ita suna fuskantar junan su hannun su rikeda juna, gyaran murya yayi Alamar duk abunda zai fadi yanada muhimmanci "tun kafun ki mallaki hankalin kanki Aisha tun ana mun wasa ana kiranki da sunan matata harga Allah tun a lokacin banida burinda ya wuce in tattalaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login