Showing 9001 words to 12000 words out of 56324 words

Chapter 4 - USTAZIYA KO YAR DUNIYA BY AUNTY MAMIE.doc

mamie kuwa komai na tafiya daidai duk sanda zasuyi waya da AK baida abun tambaya sai Aisha, tun bata damuwa abun yafara damun ta nan ta taka mai birki bataso zargin da takeyi yazama gaske, ganin yanda Ranta baisan hakan yasashi daina tambayar badan Ranshi naso ba, Mamie babu abunda suka Fasa yima Ramata da yaranta dukda sanin halin ya'u saidai mommy taita bata hakuri da tattausan kalamai.



A kwana a tashi lokaci na ta tafiya tun Aisha nasa ran dawowar AK harta dangana saidai soyyar shi nanan daram a Ranta tareda Alkawarin bazata taba mai kishiya a Ranta ba, yayinda ta bangaran shi kuwa iyayanshi kekai mishi ziyara a cewar su gara ya zauna wuri daya saiya gama komai da komai tas na karatun shi domin yana hada Degree gara ya karasa gaba daya zasu dinga zuwa tareda kanin shi Abdulhakeem Wanda a yanzu shima yake shirin komawa chan karatu.

A lokacin ne makerin budurwa yagama kawata halittar Aisha fiyeda tunanin mai tunani tahada duk abunda ake bukata a wurin mace, Allah ya wadata tada zaunannan baya 'duwawu' ga tudu kamar ka Dora Kofi ya zauna daram??M0 ga hips masha Allah ga kirjin nan ya cika yayi dam Tubarkallah, da taimakon shafaffen cikinta shape din halittar ta yakara baiyana, ko hijab tasaka idan tana tafiya komai na jikinta saiya dinga kadawa, kiban jikinta a wuri biyu yake hakan ba karamin tsokale ma samarin unguwan ido yakeyi ba uwa uba Allah ya zuba mata natsuwa ta musamman kullum cikin dogon hijab zaka ganta hakan yasa yan iskan samari saka fara samata ido, inda Ramata ta farga Kullum cikin yimata Addu'a da nasiha takeyi hakan yasa take Kara suturta kanta kokadan bata shigan banza.


*Bakar rana........coming soon*










*Mr's Sadik Rumah???b???_*
[14/11, 00:14] %???+234 814 511 8251%???: ??Z烙?_??Z烙?_??Z烙?_
*Ustaziya ko Yar'duniya???W0???_%??]?j??W0???_%??]?j??W0???_%??]?j*


*Written by Anty Mamie*

*Dedicated to sister Husnah*


11


Tunda Aisha tazama cikakkiyar budurwa a lokacin tanada ilimin Addini Daidai gwargwado, Boko kuma tana SS1 Makarantar gwamnati, nanfa samari suka yo mata chara, yawancin marasa jin unguwan ne duk Wanda yasan unguwan shanu yasan ba laifi akwai marasa ji saidai Allah ya shirya kawai, hakan yasa bata kula kowa ganin duk babu na kwarai koma akwai babu hurumin shi a gefen zuciyarta, nanfa suka Kara samata ido wasu harda zagi idan tafito, tana diyar mai shayi da rake amma tana girman kai, wasu suce rufa mata Asiri zasuyi danta samu ana Santa diyar Dan kwaya, hakan yasa tasa katon audiga tareda toshe kunnan ta, Ramata kuwa Kullum cikin hannunka mai sanda take mata yayinda yayanta garbati abun yafi damun shi fiyeda kowa amma ya zaiyi? Wasu yan'iskan ma cewa sukeyi darajar shi takeci mai akai da diyar mashayi dan cha-cha?
Ya'u kuwa ko'a kwalar rigarsa hidimarsa yakeyi.
Cikin masu takura mata akwai wani Saurayin dake zaune a cikin gidan su Wanda yake dan'sara suka ne yayi suna a unguwar wurin rashin ji, duk inda ka ambaci *Virus* tohfa harta yaro yasan da zaman shi a unguwar, maguwar Sha'awar Aisha yakeyi tunda ya kyalla ido yaga surarta, hakan yasa yaita mata tayin soyyar Sa babu yanda baiyi ba ko darajar magana baya samu dukda yana aiko mata da kananan kyauta kozata kula shi saidai ta kori Dan sakon tareda sakon, Wata rana da yamma tadawo daga islamiyya Virus na zaune a kofar gida ganinta yasa yatare karamin kofar shiga cikin gidan, tsayawa tayi dataga bayida niyyar matsa mata kallan shi tayi, 'zan wuce, 'kallon ta yakeyi sama da kasa tareda lashe baki kamar tsohon maye, 'ki wuce mana, tareda Dan bude mata hanya kadan, rabawa tayi ta gefen shi cikin natsuwa ta manne da bango gudun kada jikinsu yataba juna Virus kuwa dayake bahaka yaso ba yaso yadan ji dumin ta koda Dan gogarshi ne tayi hakan yasa kafun takarasa wucewa taji PA's ya bugan mata gefen duwawu har yana Danna hannun shi, wooooooooo kafun yarufe baki aiko Yaji saukan Mari a gefen fuskarshi, karamai wani tayi tana huci Ranta yayi mugun baci ta kudiri aniyar duk abunda zai faru saidai yafaru tagaji da rainin wayaun su, hannun ta aka kama daga baya, 'zoki wuce, inji Ramata wacce tafito duba sanwar data Dora a zaure, babu musu tabi bayanta sukabar Virus na hucin ganin babu namijin daya isa yayi mishi haka amma yau saboda ya latsa duwawun mace yasamu mari biyu abun takaici kuma a gaban yaransa dake zaune a gefe, aikuwa masu dariya damai kirari nayi masu bashi hakuri nayi nan yakara kulewa tareda Alkawarin daukar fansa.

Kuka takeyi da takaicin rayuwar data tsinci kanta a ciki bakowa yakara jamusu abun gori ba I'lla baban su daya kasance mutumin kwarai babu Wanda zai watsa musu shara, nan tayi mai isarta yayinda Ramata batabi ta kanta ba itama dazata samu mai lallashin nata so takeyi, Aisha kukan fili takeyi itako tadade tanayin na zuci, batada yancin shiga cikin mata sa'an ninta iyaye koda kuwa sha'ani ne na cikin unguwan inko taje an dinga ya'da mata habaici kenan saikace itace keyin cha-cha ko shaye shayen??W0???_%??]?j gidansu AK ne kawai basu chanza mata ba.



Bayan an kwana biyu, zaune suke a'dan tsukukun dakin su cikeda jimamin rashin dawowar ya'u gida kusan kwana biyu kenan babu shi babu labari, shiba wayaba bare a kira duk inda akesa ran ganinshi bayanan hakan yasa suka dangana tareda zubama sarautan Allah ido, garbati ne ke zaune gefen mamar tasu da Aisha yana cin tuwon masara miyar kuka Auta kuwa tana gefe daya tazuba uban tagumi sai tausar su yakeyi akan baban nasu zai bayyana gobe da sassafe zai Kara dubashi ko za'a Dace, dakyar ya lallaba sukaci tuwon suma tareda musu sallama zuwa makwancin shi a lokacin yabar dakin su ganin rashin dacewar hakan shiyasa yakoma dakin abokinshi dake unguwan yana kwana, sallama yayi musu yayinda yawuce a lokacin sunada matsalar wuta gashi lokacin zafi ne babu halin kulle kofa dukda sunsan akwai hatsari barin kofar a bude tohya zasuyi? Gashi kofar gidan nasu dan kwano ne akeja ake kullewa.

Wurin sha'dayan Dare dukansu sukayi bcci ga azabar sauro da zafi hakan yasa Ramata ke daure da zani a kirji Auta ma haka, Aisha kuwa vest ce sai underwear a cewarsu zafi bazai kashe suba.

Kafarta yake shafawa a hankali, nan yafara kokarin tube mata Riga,cikin bcci taji ana shirin cire mata kaya gashi ana shafa mata jikin ta, aikuwa kwanciya yayi sosai a jikinta jin nauyin shi yasata sakin ihun da Ramata ta farka, nanta dinga zuba ihu daduk karfin ta aikuwa kafun kace kwabo muryarta ta karade ko'ina, magana yafara cikin maye, meeeeyeee......ha.ka, Raaaa.. a'a
Mikewa tayi ganin ana shirin keta ma diyarta haddi akan idonta Kwanan samiran dake gefenta ta kwada masa akai, sannan ta tuna da tuchlight dinda ke gefen katifar su, ihu Ramata keyi akan akawo musu dauki kwarto ya shigo aikuwa tana kunna tuchlight din idonta ya sauka akan Ya'u dake shirin cirema Aisha underware harya fara yaga mata vest din jikinta, bin bango tayi tana salati tareda dafe kirji tuchlight din hannun ta yafadi kasa hakan yayi daidai da karasowar virus da ihunsu ya tashi kowa na gida, ihu yasaka jama'a uba kecin diyarsa shiyasa aka hanamu dandane ashe cikin zafin nama ta tattaro duka karfin jikin ta tahau buga mai duk wani Abu dake kusa da ita, virus kuwa ihu kawai yakeyi yana shela a unguwa ya gansu turmi da tabarya, diyata? Duk karuwan gari sai diyata? Wlh kashe ka zanyi Ya'u Allah ya la'ance ka Allah ya hanaka farinciki Aisha sumewa tayi ganin ubanta neya yaga mata suturar jikinta yayinda Auta bilki tayi mutuwar tsaye numfashi na sama da kasa.........




*Mrs Sadik Rumah???b???_*

[14/11, 00:14] %???+234 814 511 8251%???: ??Z烙?_??Z烙?_??Z烙?_
*Ustaziya ko Yar'duniya??W0???_%??]?j??W0???_%??]?j??W0???_%??]?j*


*Written by Anty Mamie*



*Dedicated to sister Husnah.*


12



Kafun kace kwabo mutane sun yanyame zauran gidan, nan aka damki ya'u dukanshi sukeyi Kota ina matasan unguwan, suna cewa duk iskancin su bazasu taba naiman jinin suba karshan iskanci yakare uba ya nema yarsa ya'u tuni yadan dawo hankalin Sa saboda bugun daya kesha jini ta hanci ta baki babu kyan gani kanshi a fashe duk jikin shi ciwo, 'wlh na dauka Ramata ce, Allah na tuba shegiya, shegiyyaaa giya giya Allah ya tsine miki yar iska ta kassarani Allah ka dauki raina Dan girman Allah ku kashe ni banda Amfani nadauka Mamarta ce taya zan naima abunda na Haifa? Bantaba zina ba ya za'ai infara akan diyar cikina? Allah ka shiga tsakanina da giya kaimana hisabi Kin gama dani kinji dadi giyaaaaaaaa, Babu Wanda ya saurare shi, Ramata kuwa kirjinta ta dafe nanta sulale kasa sharaf, matan makota ne suka suturta ma Aisha jiki dukda ba'a tsirara take ba nan aka Kara rikicewa a tunanin su mutuwa Aishar tayi danko motsi batayi, ruwa aka shiga watsa musu yayinda Ramata taja Ajiyar zuciya mai karfi Aisha kuwa ko Alamar motsi batayi ba, Auta bilki kuwa tana manne da bango kamar mutum mutumi itama ruwan sanyin aka shiga yayyafa mata domin batada banbanci da wacce ta suma, ana haka ne Garbati ya karaso a rikice dagashi sai gajeran wando saboda rudewa, dakyar aka iya bambare ya'u daga hannun matasa, nan Abokanan garbati suka shiga lallaba su, kememe sukace sai sun kashe shi mutumin da akace an ganshi turmi da tabarya shida diyar cikin Sa ina maganar sassauci? Karku raina mana hankali mana malam, cikin dabara Abokanan garbati sukaja hankalin su da sunan bada hakuri yayinda Garbati yaja ya'u batareda sun Ankara ba saboda garin yayi duf kowa da tuchlight yake rike, ya'u kuwa babu abunda yakeyi sai tsine ma giya da cha-cha tareda yima kanshi Allah wadaran sai a lokacin yasan illar shaye shaye wato duk abunda musulunci zai Hana toh bakaramin Rahama bane a garemu muddun zaka kusance shi kuwa sai Allah ya nunama kyakyawan jarabawa akan haka, Allah ya tsine miki giya, kabarsu su kashe ni, 'suna barin wurin Virus ya karaso da abokansa yan Sara suka harda fetur da taya wai zasu kona ya'u bakaramin takaicin rashin samun Sa sukayi ba, yayinda wasu sukace a fito musu da Aisha, nan virus yace su kyale ta batada laifi, Laifin baban ne dayake mata mugunta hartaki yin Aure Ashe shike kwasar romon tunda budurwa ce su barta kawai, a zuciyar shi kuwa wani kudiri ne na daban akan hakan dayayi tunda yaga Aisha da underwear yasa ma Ranshi koda gawarta cefa saiya dandana.


Watsewa akayi babu Wanda yabi takan Ramata da yaranta kowa ya koma gida ana ruruta abunda ya faru dama Wanda bai faru ba kowada kalar labarin Sa akan lamarin, dakyar bilki ta tattaro jarumtar ta yayinda ta dibo ruwa a Roba da tsumma taita shafama Ramata da Aisha a jiki saboda rashin mafitan abun yi shiyasa tace bari ta gwada kila a Dace, Saida gari yafara wayewa Ramata ta farfado nan akai jugum jugum Aisha kuwa babu ko Alama, saida tayi yini daya Sannan aka samu kanta, babu mai iya magana cikin su kamar kurame yayinda zaman gida yagama Auran dukansu babu mai iya leka waje, unguwa kuwa anyi gulma harta takashi??M0 a'haka Rayuwa ta kasance musu babu labarin ya'u babu kuma Wanda yadamu yasani cikinsu bare ya tambaya ko maganar basu Kara tadowa ba, hidimar gidan garbati ne ya dauka gaba daya harta gidansu AK Ramata ta daina zuwa inda Mamie ta tako takanas tazo musu jaje rareda Alkairi mai yawa inda Alhaji muktar ma yabada kudi masu yawa akan abasu.


Aisha kuwa saida aka dade sannan tafara fita hijab dogo har kasa take sawa kamar da nan za'ai ta mata habaici da gori a unguwan, nan aka Sa mata suna *Ustaziya ko Yar'duniya* yayinda ta dauki kaddarar tada hannu biyu bata taba tankawa ba makaranta daina zuwa tayi Boko da islamiyya akan dole inda ko Kare baya naiman ta samari kuwa ko'yan iskan ma sun daina zuwa a cewarsu ita kakarsu ce a bariki dakyar da sidin goshi mai unguwa yabarsu sukara Zama tareda kashedi mai girma idan makamancin hakan yakara faruwa za'a hukunta su tareda koransu gaba daya, sanarwa yabada duk Wanda yaga ya'u a unguwar azo a gaya mai baice kowa ya dauki hukunci a hannu ba.









Mr's Sadik rumah???b???_
[14/11, 00:15] %???+234 814 511 8251%???: ??Z烙?_??Z烙?_??Z烙?_
*Ustaziya ko Yar'duniya???W0???_%??]?j??W0???_%??]?j??W0???_%??]?j*


*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husnah*


13





Bayan shekara Uku da faruwan hakan ne cikin Ikon Allah da Al'ajabi tayi wani Saurayi daga sama wai yazo kuma ba wasa ya kawo shiba Aure yazoyi bayasan bata lokaci, sunan shi Musa yanada mata daya da yara Uku baida Wata Sana'a I'lla iyaka shago dayake dashi yana saida kayan masarufi harga Allah baimata ba amma hausawa sunce da babu gara ba dadi hakan yasa batareda dogon nazari ba ta amince a lokacin tanada shekara ashirin a duniya nan Ramata taita farinciki baki yaki rufuwa kashi sittin na damuwarta ya yaye domin tagama sama Ranta Aisha bazata taba samun mijin Aure ba kila Aure kuma sai a lahira idan anayi saboda bakin fentin da Ya'u ya goga musu ita kanta Aisha bata taba tunanin samun mijin Aure ba koma zata samu batasa ran anan kusa zata samu ba harga Allah tacire Auran AK a Ranta tasan kozata mutu tadawo ita dashi har abada saidai babu na biyun shi zatai Aure bana soyya ba.
???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?

Mamie ce ke kaiwa da kawowa bakinta yaki rufuwa yayinda da kanta take shigo da farantan abincin da suka gaji da haduwa domin tarban dan'lelen ta, farin saurayi sosai kakkarfa mai kwantaccan bakin gashi dake daukar ido yayinda gefen bakin shi bakin gashin ke zagaye da karamin bakin nashi Wanda Ake kirada *Quarter mullion* hancin shi siriri masha Allah idon shi basu cika girma ba yan daidai sannan basuyi fari kar ba duk inda ake naiman Handsome indai kaga Saurayin nan tohfa an Dace, fara'a ne kwance a fuskar shi Rabon shida Nigeria harya manta he feel Alive gashi cikin gidansu yayinda ya matsu yaci abinci akwai tarin tambayoyin da yake shirin yima mamin nasa, zaune suke gaba daya harda Dadyn su anata cin abinci tareda basu labarin nasarorin daya samu a tafiyar dayayi yasha Addu'a babu adadi wurin iyayan nashi cike daso da kauna nan Dadyn su yai mishi Albishir din fara Aiki a ma'aikatar su NGO tareda mukami mai girma saboda darajar kwalinshi saidai muce masha Allah, gakuma kasuwancin shida yakeyi Abubuwa sunmai yawa yana naiman mataimaki tunda tsufa yafara kamashi ba kamar daba, duk AK ne zai amshe su a'haka firar nasu na ranar ya Kare batareda yasamu damar yima Mamie tambayar da yakeso ba.

Washe gari Allah Allah yakeyi a hadu cin abinci cike yakeda da zumudin dahar mamakin kanshi yake, wanka yayi cikin kananan kaya misalin karfe Tara ya sauko breakfast lokacin Daddy ya Dade da tafiya office, tsakurar abincin yayi sama sama yayinda yake Jan Mamie da fira har akazo inda yakeso, 'wai Mamie ina mai muku wanke wanke ne Ramata Kota daina zuwa dawuri ne Yanzu? Aisha fa nasan tazama budurwa yanzu, 'hmmmm bari kawai son abun ne saidai muce Allah shi kyauta rabona da Ramata kusan shekara Uku kenan baiwar Allah oooh Duniya, tafadi cikin jimami, nanta bashi labarin Abunda yafaru bakaramin tashin hankali ya shiga ba sai zufa yakeyi of all people why Aisha? Eye Mamie Anya ba sharri akayi musu ba kinsan fa mutane? AK kabar mutum kawai Allah kadai yasan abunda yafaru nidai bazance yar'iska bace kamar yanda ake fadi a unguwa saboda ban gani da idona ba, inadai musu aike jefi jefi saboda samun lada, Allah yasa ta Auru shine kawai wlh na tabbata babu mai Auran yarinyar nan, why mum? Meye Laifin ta? How sure are u bazata auru ba? Yafadi tareda mikewa a fusace yabar wurin, ikon Allah konice Ya'u kokuma nice yan'unguwa dasuke kiranta yar iska? Ihu fa kakemun AK, ita kadai take maganar ta AK kuwa ya Dade da barin gidan cikin tashin hankalin da baisan dalili ba.


Saida yayi kwana biyu babu inda yaje sai tarin wasiwasi da yakeyi taya ma za'a cemai Aisha yar'iska ce? Dukda ya Dade bai ganta ba amma ya tabbata ko cikin duhu zai iya gane ta, why? Toh kodai gskia ne kamar yanda aka Kara bashi labarin abun a unguwa dukda masu bada labarin suma sun Kara gishiri da Maggi a ciki.

Ramata keba Aisha labarin dawowar AK yi tayi kamar bataji taba saboda rashin abun cewa zuciyarta kuwa idan banda bugu babu abunda takeyi inda har Ramata ta farga da hakan taja bakinta ta tsuke,
Hijab ne kamar koda Yaushe katoto a jikin ta bayan sallar Isha'e Ramata ceta aiketa bayan Layin su kai kayan wankin da taima wasu gida kusan kwana biyu kenan basu aiko sun Amsa ba gashi ya cika mata daki gashi suna bukatar kudi basuda ko abunda zasuyi Karin safen gobe, bilkisu ta aika Aisha tace zata bataso ana aikan bilki sannan tafisan fitan Dare yanzu babu maisa mata ido kamar rana dukda Yanzu anfara sakar mata Mara ba kamar daba dadan dama dama, ta bayan layinsu tabi inda tunda Vairus yaga fitowarta da inda ta dosa Yaji kamar anmai bushara da Aljannah yayinda takai sakon tareda amso kudin wankin Naira dari Uku da hamsin, siririyar hanya yar karama ce ba'a cika wucewa ba kasancewar ba'a gama ginin gidajan dake wurin ba koda rana hanyar shiru zaka jita bare da Dare dukda haka mutane nabin ta sosai saboda shortcuts ne mai sauki indai zaka zagaya bayan Layin kana bulla ka huta dogon tafiya, touch light ne hannun ta tana tafiya sauri sauri Addu'a dauke a bakinta bata San maiyasa ba gabanta ke matukar faduwa sosai, ji tayi an buga mata wani Abu akai yayinda aka toshe mata hanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login