Showing 6001 words to 9000 words out of 56324 words

Chapter 3 - USTAZIYA KO YAR DUNIYA BY AUNTY MAMIE.doc

biyu, ta manna daya a goshin ta daya sace amma yabar karamin ciwo, daya kuma a gefen bakinta ta manna, blue material Mara nauyi ta dauko wacce akai mata simple dinkin doguwar Riga ba hayaniya simple make-up tayi tareda feshe jikinta da turare nan tafito Ras abunta dinkin ya amshe ta sosai dukda Zainab masha Allah kamar yanda AK yace she fat for back she fat for front tohfa haka yake a cike take taf tareda taimakon shafaffen cikinta dake tona asirin kyawun halittarta ya kwanta ya lafe kamar ba hanji a ciki, irin dogayan matan nanan ne amma ba fara bace bakuma baka sidik ba black beauty ce skin dinta mai tsada tanada kyau mai tsayawa a rai hmmmm *'nasan zakuso kuji wacece Zainab ku cigaba da kasancewa da Yar mutan katsinawa*


Saida ta kyara ko'ina na cikin gidan dukda girman gidan amma yauda gobe tasaba bata wani ganin wahalar hakan kasancewar tun Dare ta wanke kwanukan da akai Amfani dasu tareda goge kitchen din, hakan yasa turaren wuta kawai tasa ko'ina yadau kamshi masha Allah, ragowar ferfesun jiya ta dumama tareda Juyewa a cooler sai sandwich datayi tareda dafa ruwan tea Wanda Yaji kayan kamshi kan dinning ta jera komai da komai cikin rawan jiki tafito makeken harabar gidan nasu wurin jerun motocin AK ta nufa guda Uku masu kyau, 'dattijon mai gadin gidan nasu ne ya matso wurinta tana hango shi ta gaishe shi nan ya Amsa mata cikeda fara'a da mamakin ranarda zata daina wankema AK motoci kusan shekara Uku Abu yakici yaki cinyewa ba karamin tausaya mata yakeyi ba hakan yasa har Addu'a yake mata Allah yakawo mata karshe wahala wurin uban gidan nashi, a iya sanin shi baitaba jin AK ya dagama wani murya ba kokuma ya zagi wani sai matarshi hakan yasa yake cikeda zumudin San jin tarihin rayuwar su dukansu idan da Hali, sanin babu halin shiyasa ya hakura yaja kafarshi tareda komawa bakin aikinsa, 'motocin ta shiga wankewa sauri sauri gudun fitowar shi, hakan yasa tagama dawuri ta wanke su duka tas tareda gogesu ciki da waje a gajiye take lis ko wankin motocin wani katon aiki ne sanin ko kura yagani cikin motar tohfa ta shiga Uku, tana gamawa ta dauki abun gyaran flowers ta nufi flowers dinda ke zagaye da gidan nasu, dukda ada akwai masu aikin gyaran flowers din harda mai wanke mai motan tun farkon Auran suya sallame su duka a cewarsa kudinsa ya huta an kawo mishi jakar mai Aiki, cike da sabo da kwarewa tashiga gyarawa tagama komai nan ta hau sharar tsakar gidan nasu dakyar ta gama saboda girman gidan, shiganta cikin gidan yayi daidai da fitowar shi daga dakin shi sanye da dakakken suite milk color yasha necktie black da zanan milk ya tsuke fuskar nan a murtuke dukda haka yayi matukar yin kyau gawani bakin gashi daya zagaye fuskar nashi hakan yakara fito da madarar kyan shi, dogon Namiji ne fari tas Tubarkallah masha Allah, shagala tayi da kallon Sa kaunarsa na Kara ruruwa a ruhinta ji take kamar tayi tsalle ta makalkale shi, ganin batada niyyar daina kallon nashi yasa shi watsa mata Wata shegiyar harara a cewarshi kada ta shafa mai bad luck da sanyin safiya, russunawa tayi tana gaishe shi, 'ina kwana ka tashi lafiya? Kamar kullum wuceta yayi kamar tana magana da dutse kallon dining yayi yaga ta jera abinci kotakan abincin baibi ba, dama baci yakeyi ba sai ranarda tayi matukar Sa'a idan kuma batayi ba wani sabon tashin hankali ne, duk Randa tayi gigin mai tayin abinci kuwa a jikinta yake Juyewa duk zafin shi.
Tanajin fitar shi gidan a gurguje tashiga daki Kara gyara jikinta tayi tareda chanza kaya duk sun takura ta, ta matse cikin kananan kaya gajeran wando jins blue da farar vest, masha Allah ita kanta tasan Allah ya kawata surar ta, shiyasa ta dinga fuskantar matsaloli ada saboda hakan kan dining ta nufa nanta kwasa girkin ta yayinda ta koshi daki ta koma ta zumbula dogon hijab sauran abincin ta juye awani cooler Wanda yake mallakin mai gadi ne, mika mai tayi tadawo tareda kunna TV takamo Arewa24 kwantawa tayi akan doguwar kujera tanata kallo har wurin 11 taji tsamin jikinta ya dame ta baya mata dadi ko kadan, tashar ta chanza aikuwa ta kama Wata tashar wakan turawa sai karkada jiki sukeyi, nan danan ta Mike wai itama zata gwada kozata danji karfi karfi a jikin nata idanta jijjiga jinin jikin ta dukda maganin datasha a banza, rawan ta shigayi tana botsarewa sai bankare bankare takeyi tana juya cikin ta kamar yanda taga sunayi , tayi Akalla kusan minti 10 cikin nishadin data dade batayi ba ganin takoma saikace yarinya yar shekara sha Tara, karan Abu taji hakan yasa ta waigo da sauri abun mamaki AK tagani tsaye kamar gunki ya sankare yana Kare mata kallo ko kyaftawa bayayi baki a bude aikuwa a 360 tabar wurin tareda garkama makulli a dakin nata, wayarshi daya Saki ya kalla a kasa domin tunda tafara rawan ya shigo da niyyar Amsa waya haryasa a kunne yanaji ana mai magana cikin wayar amma yakasa tabuka komai............yanzu abun Aisha harya kaiga haka? Tuno wani littafin sanin sirrin mata daya taba karantawa idan bai manta ba malamin cewa yayi duk macen datake yawan mika ko bankarewa toh tana cikin tsananin bukatar Namiji, *Innalillahi wa inna ilaihir raji'un* ya furta cikin sanyin jiki.


*Shin wakesan yasan labarin ma'auratan nan masu ban Al'ajabi?* duk maiso ya daga hannu???b???_%??]?j




*Mrs Sadik Rumah???b???_*
[14/11, 00:13] %???+234 814 511 8251%???: ??Z烙?_??Z烙?_??Z烙?_
*Ustaziya ko Yar'duniya?*
??W0???_%??]?j??W0???_%??]?j??W0???_%??]?j

*Written by Anty Mamie*

*Gskia sai jiya na tabbatar da masoyan littafin nan Nada yawa fiyeda tsammani na wayata har daukewa takeyi saboda ruwan comments da Addu'a a gareni nayi matukar farinciki tareda mamakin yanda kuka karbe shida hannu biyu biyu, bazan daina fadi ba comments dinku nasani matukar nishadi tareda karfin typing, Godiya mai tarin yawa Ga makaranta???i???i*
Sorry nayi mistake a last page inda zansa Sunan Aisha nasa Zainab, Afuwan typing error ne.

*Dedicated to sister Husnah*


9

*Shin wacece Aisha? Wanene kuma AK?*

Ya'u shine Mahaifin Aisha tareda mahaifiyarta Ramata Asalin yan cirani ne daga Damagaram dake jahar Nijar, inda suka shigo Nigeria lokacin da yaransu biyu, namiji da yar'karamar yarinya mace wacce mahaifiyarta Ramata ke rike da ita a hannu, a lokacin bazata wuce shekara biyu a duniya ba, namijin suna kiransa da garbati, yayinda macen suke cemata shatu, Sanye suke da bakaken kayan buzaye yayinda sukasha nadi a kansu daka gansu kaga bakin haure, daga Ya'u har Ramata irin dogayen buzayen nanne sosai wankan tarwada kyawawa Tubarkallah, yayinda cikin ikon Allah suka sauka garin Kaduna a unguwan shanu kai tsaye gidan mai unguwa sukayi inda suka gayamai kudirin suna San fara sana'a yanda zasu tallafa rayuwar su, cikin ikon Allah mai unguwn yabasu daki daya Wanda ke zauran cikin gidajan shina unguwan aiko ba karamin murna suka dinga yiba tareda godiya da Addu'a a gareshi, dakin karami ne baida girma sai window kwaya daya rak, inda Allah ya taimake su zauran nada dan fadi hakan yasa Ramata keyin sanwa a lungun zauran, yayinda suka hada bayi da mutanan dake cikin gidan dukda gidan bawani Babba bane dakuna Uku ne a cikin gidan sai bayi guda daya da kitchen dinda kowa ke Amfani dashi, batareda bata lokaci ba Ya'u ya kafa Karamar teburin shayi a gaba da gidan nasu nan danan yafara Tara customer's bakaramin ciniki yakeyi ba darana kuma saiya kasa rake duk anan wurin yayinda Garbati ke tayashi Zama a lokacin yanada shekara goma a duniya akwai tazarar shekara takwas tsakanin shida Aisha, Ramata kuwa baa barta a baya ba, wankau tafara a cikin gida, itama babu laifi tana samu hakan yasa tace barita gwada shiga cikin gidajan masu kudin unguwan kila zata Dace su dauketa wani aikin, cikin ikon Allah nan saman layin su sosai inda gidaje masu kyau suke nanta tunkara duk gidan data shiga bata dacewa harta fara gajiya ga zafin rana Ga Aisha dake bayanta sai kuka take tsalawa, ganin sauran wani gida daya Wanda yafi duk Wanda take zuwa tsaruwa tana shirin komawa gida hakanan tace bari ta gwada sa'ar ta, tun daga kofar gidan mai gadin gidan ya dakatar da ita, 'hajiya lafiya? Yana Kare mata kallo sama da kasa, kafun takaiga bashi Amsa sukaji karan horn din mota Alamar masu gidan ne suka dawo, matsawa tayi gefe tareda rusunawa, koda suka shigo hajiyar gidan ce dayara guda biyu tareda ita, babban shekaransa goma sha biyar mai suna Abdulkareem yayinda dayan bazai wuce sha'daya ba, shikuma Abdulhakeem kallo daya zakai musu kaga kallar kamarsu da mamar tasu wacce take fara kar, 'a'a lafiya? Wacece wanchan? Hajiyar ta tambaya tareda nuna Ramata daketa zuba zufa cikin tsakiyar rana, Kafun mai gadin yabata Amsa ta karaso tareda Kara dukawa gaban hajiyar tana gaishe ta, 'amsawa tayi cikin sakin fuska, 'hajiya Dan girman Allah ki taimakeni kibani aikin yi, ta furta cikin rawar murya, achan kasan layinku gidanmu yake Mijina ne mai saida shayi da rake a kasan layi, 'shigo mu shiga ciki hajiyar ta furta ganin yanda Aisha keta tsala kuka kamar zata suma, samarin kuwa tuni sukayi cikin gida hannun su rikeda Leda da Alamar siyya sukayi da mamar tasu.

A babban parlon dake kasan gidan sukai masauki kassncewar gidan gidan sama ne, parlon ya tsaru sosai, a gefen kujera Ramata ta zauna yayinda hajiyar tayi tayi ta zauna kan kujera taki, Wata dattijuwa ceta shigo parlon rikeda farantin ruwan sanyi da lemu tanama hajiya sannu da zuwa, amsawa tayi tareda mika ma Ramata ruwan aikuwa ta Amsa ta sha sosai tareda kwanto Aisha tabata tasha nan tayi shiru tana Ajiyar zuciya da Alama zafi neya dameta dama.

Basu bar gidan ba saida hajiya taimata Albishir din bata aikin wanke wanke da gyaran kitchen da tsakar gida, tunda sunada mai musu girki sannan ba abincin kowa suke ciba, cikin Ikon Allah tafara zuwa tareda samun Alheri mai tarin yawa inda kusan anan take saman musu abincin da sukeci a gida, kassncewar idan abinci ya kwana basa ci, nan hajiya taba Ramata izinin dauka tunda dama Almajirai ake dunduma ma, dukda ranar juma'a ana girki na musamman da yamma Almajirai na layi amsar sadakan abinci mai rai da lafiya, nanfa duniya tadawo masu ya'u da Ramata harma da yaransu sabuwa sunyi fes sunyi kyau sosai sun murmure Aisha kuwa sai wayo takeyi tayi bulbul da ita gwanin ban Sha'awa takawa takeyi ko'ina.




*Mr's Sadik Rumah???b???_*
[14/11, 00:13] %???+234 814 511 8251%???: ??Z烙?_??Z烙?_??Z烙?_
*Ustaziya ko Yar'duniya???W0???_%??]?j??W0???_%??]?j??W0???_%??]?j*


*Written by Anty Mamie*


*Dedicated to sister Husnah*


*Woooo page biyu harda Read more har biyu??I0dukda haka some one must complain???i???ilemmi c*???i

10




Alhaji muktar babban Dan kasuwa ne kuma ma'aikacin gwamnati inda yake aiki a NGO yayinda yake zaune a unguwan shanu, tareda matarsa hajiya Bilkisu wacce sukai Auran saurayi da budurwa cikeda soyya, Alhaji muktar Dan Asalin jahar katsina ne matar shi kuma yar Yola ce bafulatana kyakyawar mace sun hadu dalilin wani zuwa Yola dayayi cikin ikon Allah har sukai Auran soyya tareda Arzikin yara biyu duka maza, Abdulkareem shine Babba Wanda akafi Sani da AK, sai Abdulhakeem tun akansu haihuwa ta tsaya musu chak dukda a duniya babu abunda suke Sha'awa kamar Tara yara masu yawa Wanda burin hajiya Bilkisu wacce suke kira da Mamie bai wuce ta ganta da diya mace ba, hakan yasa kullum Addu'ar ta kenan samun mace,
Alhaji muktar mutum ne mai tausayin talaka hakama matar tasa, ba karamin kyautata ma talakawan unguwan yakeyi ba hakan yasa a karo da dama yaso barin unguwan talakawa na hanashi ganin yanda suke karuwa dashi matuka dukda yanada gidaje masu dumbun yawa a garin kullum arzikinsa karuwa yakeyi saboda yanda yake wanke dukiyar shi inda yaso yakoma GRA cikin manyan gidajan shi nachan ya koma da iyalan shi amma yan'unguwa sunyi kememe sun hanashi, babu yanda basuyi dashi ba akan yashiga harkar siyasa yaki, a cewarshi bata burge shi.
zuwan su Ramata gidan yasa hajiyar sakewa da Aisha a cewarta yarinyar na burge ta gata kyakyawa gata yar'duma Duma bakaramin gashi Aisha keda shiba inda tayi gadon shi wurin dangin uwa harna uba, kyawaw??n halin Ramata neyasa Mamie takara janta a jiki itada diyarta domin tasha gwadata ta hanyoyi da dama kuma cikin ikon Allah bata kamata dawani laifi, soyyar da Mamie kema Aisha yasa AK shiga lamarin ta indai yana gidan tohfa tana hannun shi har fita kofar gida yakeyi da ita yanai mata wasa kassncewar kullum zaka ganta fesfes an tubke mata gashi gwanin ban Sha'awa, hakan yasa Ramata na zuwa Mamie ke amsarta taita mata wasa itama, shakuwa sosai ke tsakanin AK da Aisha, inda a yanzu a'kalla takai shekara hudu a duniya wayau da surutu kuwa ba'a magana komai Yaya AK, hakan yasa Mamie ke tsokanar AK Take cemishi Angon Aisha, na Aisha wasa wasa shima yafara kiranta da matarshi, inda babu Wanda yayi zargin wani Abu, shakuwar AK da Aisha ba'a magana inda hajiya har kaya siyan mata takeyi hakan yasa Alhaji ma yafara sake mata ganin iyalin Sa na kaunar yarinya shima ta shiga Ranshi, nan Ramata tasa Aisha awata islamiyya anan unguwan tana zuwa safe da yamma, A'nanan har babanta yasata awata makarantar gwamnati tafara zuwa Boko cikin lokaci kadan takara wayau sosai, a kwana a tashi saiga wani cikin ya kuma bullowa a jikin Ramata nan taita rainon abunta har Allah ya sauke ta lfy ta haifi diya mace inda a wannan karan hajiya Bilkisu akaima takwara a cewarsu basuda kamarsu a kaf unguwan bayan mai unguwa, bazasu manta Alkairin su a garesu ba, sunji dadin karan da akai musu nan suka Kara rike juna da Amana.

Abunda masu karatu basu Sani ba shine ya'u Nada wani mugun hali tun a kasarsu nijar babban mashayi ne kuma dan'chacha ko bayan daya Auri Ramata babu abunda yafasa a halinshi talaucin daya mamaye sune yasa ya ajiye shaye shayen a gefe ganin baida kudin dazai siya tareda ma Ramata Alkawarin dainawa yayi gaba daya tunda yara sun fara girma baiso yabar musu abun kunya, ganin yanda kudi ke shigo mishi yanzu gakuma matarshi kusan ta dauke mai hidimar ci Dasha na gida hakan yasa yadawo da tsohon halin shi, tun yanayi a boye har Ramata ta farga hankalinta ba karamin tashi yayi ba, inda zata tasa shi a gaba taita masa magiya tana rokon Sa tana kuka, haka zaikara mata Alkawarin daina wa, Wata rana idan ya bugu tana magana zai lakada mata duka a daki tanaji tana gani zai jibge ta haka zata hadiye kukanta a cewarta bataso kukanta ya tona asirin uban yaranta, haka yaran zasu makure a bango suna kuka ganin yanda ake jibgar mamarsu, washe gari haka zaizo ya tsugunna yana bata hakuri da nadama, amma hakan bazata chanza zani ba. babu yanda batayi dashi akan su nema hayan gida kusa dasu koda wani daki dayan ne tunda garbati ma yafara Zama saurayi, dakin yamusu kadan ga Aisha tafara girma rai biyar dakin bazai dauke suba amma kememe ya shafa ma idon shi toka dukda yanada kudin yin hakan a yanzu ganin biyan kudin hayan dakin da zai kama kamar barnan kudi ne gara yasha kudin shi yayi tatil haka zai shigo yana rangaji tareda zage zage tun yan unguwa basu farga ba har aka fara ganewa inda sanaar shayin ma yadaina garbati keyi yanzu shi saidai ya kwanta a gida idan Ramata tatafi aikatau yaita baccin Asara, wasa wasa abun nashi yai tsanani inda akaita kaima mai unguwa karar shi, hakan yasa ya kirashi yai masa nasiha sosai, hakuri yaita badawa, inda har cewa yakeyi asiri akai masa daga kasarsu a cewarshi wai sun sami labarin rufin asirin shine, Jama'a saidai suce Allah shi kyauta, Daya daina na kwana biyu zai dawo ruwa tsundum harma yafi Nada.





Shakuwar AK da Aisha ba'a magana, inda AK bai hadata da komai ba hidima yake mata baji ba gani a lokacin ya mallaki hankalin kanshi yazama kyakyawan saurayi sosai, babu abunda yafi kauna kamar ka danganta shida Aisha tun bare idan kace mai mijin Aisha hmmm har kowa yagane hakan ita kanta Aisha dadin hakan takeji komai Yaya AK bakinta baitaba rabuwa da sunan shi, a lokacin yafara shirye shiryen barin kasar zuwa Egypt yin jami'ar shi dukda baiso hakan ba a cewarsa wazai kula maida Aishar Sa, dakyar iyayan suka lallaba shiya tafi, inda Aisha ta rikice lokacin tafara Zama budurwa itama har abinci saida ta daina ci dukta rame nanfa iyayan suka fara tsoran shakuwar dake tsakanin su. A kwana a tashi babu wuya komai na tafiya daidai banda halin ya'u dake Kara birkicewa dukya rikice yakara tsufa abun na damun iyalan Sa tun bare Aisha da a makaranta har gori ake mata haka zatai ta kuka tun bata saba ba harta saba mai unguwan yaso korarsu a karo da dama tuno Laifin wani baya taba shafar wani saboda darajar matarshi da yaran shi Wanda suka samu shaida mai kyau a unguwan shiyasa ake daga mai kafa, inda Aisha tazama Silent kasancewar batada kawaye a cewar su babu Wanda zaiyi harka da diyar mashayi, nan kewar yayanta yakara cikata saidai ta kwanta a daki taita kukan kewar AK Wanda a lokacin tagama yarda shine farin cikin ta, tagama yarda idan bada shita rayu ba toh rayuwar Tata batada wani Amfani, tagama yarda sanshi takeyi soyya Mara iyaka inda Ramata tun tana biye mata suna labarin harta fara tausaya ma diyar Tata ganin dala da gwauron dutsen data dauko ma kanta ko'a duniyar mafarki AK ba sa'an ta bane hakan yasa Ramata tadage dayimata Addu'a Allah ya yaye mata larurar data Dora ma kanta.
Ta fannin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login