Showing 69001 words to 72000 words out of 123822 words

Chapter 24 - WATA KADDARA Complete book By (Yar gatan mama).doc

22 Sep 2025

2597

yayun na ki a matsayin masoya na aure, sai dai a matsayin yayunki kuma abokai."

Da sauri ta kalli Dady sannan ta kalli yayunta hawayenta ba su dai na fita ba kamar ba, za ta yi magana ba, da ?yar ta ce "Idan har za su iya dai na kallona da wannan manufar su sadaukar da ni, ga Wan uwansu, to ni me ze hana ni yin hakan, don haka na amince."

"Idan ba wata damuwar zan iya tafiya Waki kenan yanzu?"

Dady ya ce "Allah ya yi maki albarka ta shi ki tafi mun gode sosai ?armu."

Duk ?arfinta ta haWa guri Waya ta fara ?o?arin ta shi duhu ta fara ga ni bata ganin komai, amma haka ta cigaba da ?o?arin ta shi, sai dai sam ta gaza nan ta faWi a sume babu alamar numfashi a tare da ita.

Da sauri duk suka yo kanta hankalin kowa a ta she musamman Yayunta, girgiza ta suke ta yi amma sam babu alamar motsi a tare da ita...

*WATA ?ADDARA*
*ANOTHER DESTINY*
By
*SUWAIBA M AMIRU*
(?ar gatan mama)
' *PAGE* 4?? 3??

Hankalin su duk a ta she Salim ne wanda ya yi jarumtar tunawa da ruwa, da gudu ya Wauko ruwa ya fara zuba mata a fuska da ?yar suka sa mu ta farfaWo tare da jan numfashi, jiki ba ?wari amma haka ta fara ?o?arin ta shi.

Kaka ne ya ri?a hannunta ya ce "An ya za ki iya kuwa Sufayya?"

"Me zai hana in iya bayan kun gama yarda zan iya Win, karku da mu burinku zai cika in sha Allah ba zan ba ku kunya ba."

Maganar take da ?yar numfashi na fita a wahale, hawayenta kuma ba alamar za su dai na fita, ta bawa kowa a gurin tausayi sosai.

Ganin ba za ta iya kai kanta Waki ba hakan ya sa, su Momy taimaka mata suka kai ta har Wakin, sannan suka fito, duk'kan su da tunanin an ya kuwa sun yi mata adalci, domin neman rayuwar Wansu su sadaukar da farin cikinta.

Rahma kuma tunani take shin ita daga cikin waWan nan Yayun na ta biyu wa tafi so, wa tafi jin zafin rabuwa da shi, sai kawai ta sake sakin wani sabon kukan har sai da zazzaSi ya rufe ta.

Cikin rawar sanyi da jikinta ke yi, take magana tana faWin "Zan iya bin umurnin Yaya Salim na yi jarumta da dauriyar zama da Yaya Samir, amma zama da Yaya Sufiyan sam zai yi man wahala sosai wallahi" cikin kuka sosai take magana, "Wai ni kam me ya sa ?addarata bata zuwa da kyau a ko wane lokaci?" tambayar da ta yi wa kanta ke nan.

A haka ta kwana cikin tsananin zazzaSi sosai, da safe ta gaza fitowa a kan lokaci ko aikin haWa breakfast bata ri?aba yau, sai da ta misilta cewa yanzu sun gama breakfast sannan ta fito.

Tana tafiya hanya na haWe mata har ta samu ta kai parlorn sama, nan duk ta tarar da kowa, gaidasu ta yi sannan ta nemi guri ta zauna.

Kaka ya kalle ta ya ce "Ya naga kamar kina son magana Sufayya ina dai fatan komai lafiya, shin kin ma ci abinci kuwa?"

Cikin ?asa da murya ta ce "Ji yadda yake magana kamar bai san aikin da suka ba ni ba, wai har da tambayar Allah ya sa dai lafiya, to ina lafiya kuwa kuna son tarwatsa man rayuwa da zuciya, amma yanzu ba ni da wani zaSin wanda ya wuce na yi abun da suke so, idan kuma ba haka ba komai ya faru zasu ce, ni ce sanadi."

Kaka ya gaji da shurun ya ce "Magana fa nake maki, amma ga duk'kan alama kin tafi ba?in tunanin na ki."

"Ku yi ha?uri Kaka dama ina da magana ne sannan zancen abinci yanzu ba zan iya ci ba har sai na gabatar da maganata" shuru ta yi na Wan lokaci kamar ba, za ta yi magana ba sannan ta ce "Don Allah ku gafarce ni a kan abun da zan faWa yanzu, ba ni da wani zaSin da ya wuce wannan."

"A can baya Kaka ya ba ni damar zaSar wanda nake so na aura daga cikin Yayuna amma na gaza har na bar maku zaSi a tunanina za ku zaSa man wanda nake tsammani, amma sai hakan bata faru ba."

"To yanzu na fahimci cewa ina cutar da kaina kuma zan cutar da shi wanda ku ka zaSa man hakan ya sa na yanke shawarar faWar gaskiya yanzu."

"Ni dai a gaskiya Yaya" sai kuma ta gaza ?arasawa sai da Kaka ya muntsine ta, da ?arfi dama shi ne a ku sa da'ita, aikuwa da sauri ba shiri murya na rawa ta ce "Sufi Sufiyan nake son na aura, ta sunkuyar da kanta saboda hawayen da ke zubar mata.

Duk wanda ya ji maganar ya san ba shiri ta yi maganar.

Da sauri Sufiyan ya mi?e tsaye ya ce "Kina cikin hayyacinki kuwa, kin san me kike faWa?"

Kaka ne ya dakatar da shi ya ce "Ya isa" sannan ya kallin Sufayya da har yanzu bata sake Wago kanta ba ya ce "Dama na san akwai wanda kike so daga cikin su, amma ina yi wa Allah godiya da ya sa kika yi magana tun da sauran lokaci don haka yanzu sa ranar ta koma kan Sufiyan ma'ana nan da sati huWu."

Cikin firgita ya ce "Don Allah Kaka karka yanke wannan hukunci ba tare da bincike ba, ku ba ni dama zan yi magana da ita."

Kaka ya ce "Wa ne bincike kuma kake son mu yi bayan da bakinta ta faWa, sannan zancen a baka damar magana da ita, ai yanzu kafi kowa wannan damar tun da matar da, za ka aura ce."

Da sauri ya ja hannunta suka bar parlorn, su na fita ya ce "Kalleni da kyau ?anwata, kar ki ji tsoron komai don Allah ki sanar da ni waya sanya ki wannan maganar ki sanar da ni, in sha Allah zan daidai ta komai."
Ya yi maganar a rauna ne, idanunsa duk sun sauya lau ni zuwa ja.

Idanunta suka kawo ruwa har ta fara tunanin sanar da shi gaskiya, ta buWa baki ke nan za ta yi magana sai kawai ta hango iyayen su tsaye suna kallon ta, gefe Waya kuma Yayunta ta hango suna ta girgiza mata kai alamar kar ta aikata abun da take son yi yanzu.

Ba shiri a tsorace ta sauya zancen ta ce "Shin Yaya ina son na sani ka dai na so na, ke nan? idan har baka so na, ka sanar da ni zan koma in janye maganata, shi ke nan ni ban da damar faWar ra'ayina sai an zargi wani abu."

Ta haWa hannunta guri Waya ta ce "Na ro?eka in har kana so na kuma kana son farin cikina to karka sake yi man irin wannan tambayar" tana gama faWar hakan ta wuce Wakinta da gudu.

Yana juyawa da nufin bari gurin, ya ga ?an uwansa tsaye su Momy kuwa har sunyi saurin barin gurin bai hango su ba, kallon ?an uwan na shi ya yi, ya ce "Na tabbatar zuciyata ba za ta taSa sanar da ni ?arya ba a kan ?anwata idan har akwai abun da ke damun ta tabbas zan sani, na yi imani kuna da, sa hannu ga wannan abun dake faruwa."

"Amma bari na yi maku tambaya shin ko da sau Waya kun yi tunanin illar da hakan zai haifar kuwa? za ku cutar da ita sannan ku cutar da ni, sannan ku ma za ku cutar da kanku, don Allah ku sanar da ni gaskiya ?an uwana."
Cikin muryar tausayi yake yi masu maganar.

Su ka ce "Wai me kake faWa ne haka? yarinya ta yanke shawararta to don Allah ta ya kake son mu dakatar da ita? sannan kuma ai mu da kai duk Waya ne" Samir ya ce "Don Allah daga yanzu karka sake yi mana wannan zancen komai ka ga, ya faru haka Allah ya nufa don haka komai ya wuce haka nan please."

Tsayawa ya yi ya zuba masu idanu yana mamakin yadda lokaci Waya suka manta cewa ko da kallo suna fahimtar zancen juna, yau shi za su yi wa ?arya, girgiza kai ya yi, ya wuce Waki ya barsu nan tsaye.

Kwana biyu da yin wannan maganar Momy Aisha da Momy Nafisa suka ce za su wuce da Sufayya gurinsu domin su fara shirya ta, tun da ga lokacin na ta tafiya, su kuma mazan su tsaya gurin Momy Saratu da Aunty.

Yau sati Waya ke nan da zuwan su gidan Momy Nafisa komai aka ce, ta yi sai dai ta ce to kawai, gyara suke yi mata sosai duk gurin da ta wuce ?amshi take daman can masoyiyar ?amshi ce, ta ?ara haske sosai sai dai fuskar nan ba walwala ko kaWan.

?an murmushin ma da ake samu tana yi yanzu duk ta dai na, yanzu ko magana bata yi, ta koma halinta na baya sak, su Momy kuwa ko da yaushe cikin yi mata huWuba suke.

Daga Camaro suka Wauko mai gyaran jikin amma yau Sufayya ta ce ita wallahi ta ga ji kawai ta koma za ta iya yi wa kanta, ba yadda su Momy ba su, yi ba amma ta dage ita ba ta so dole suka sallame su suka koma.

Yau tana kwance a parlorn Momy, sai ga Yayun na ta sun zo gidan, Momy na ganin su ta ce "Me ya kawo ku gidan nan kuma yanzu?"

Salim ya ce "Zance mu ka zo gurin amaryarmu."

Ku san a tare suka ce "Ai kuwa ba za ku ganta ba yanzu sai lokacin biki."

Samir ya ce "Don Allah dai ataimaka mana wallahi abu kawai muke son mu tambaye ta kuma a kan bikin ne tana bamu amsa za mu wuce yanzu in sha Allah."

Momy Aisha ta ce "To na ji, ku shiga amma karku cika ta da surutu."

Tun da suka je bakin ?ofar suke yin sallama amma ba amsa har suka shiga cikin parlorn bata san sun shigo ba, kuma ba bacci take ta dai kwanta tana kallon sama, sai da Salim ya daki kujerar da take kai kwance sannan ta Wago kanta da sauri ta kalle shi ta ce "Sannunku da zuwa" sannan ta gaida su, suka amsa.

Duk'kan su kallon ta suke saboda ganin wannan ramar da ta yi duk'da tana cikin hijab amma fuskarta ta nuna sosai, sai kawai suka kawar da wannan tunanin a ransu.

Salim ya yi gyaran murya ya ce "?anwata dama mun zo ne domin mu ji abubuwan da kika tsara wanda kike son ayi a bikin nan?"

Kanta ta mayar ta jinginar a kan kujera sannan ta rufe idonta kamar ta fara bacci sai can ta ce "Ni ina ganin ba sai an yi komai ba kawai taron ranar Waurin aure ya isa, tun da kunga ni bama wasu ?awaye ne da, ni ba."

Samir ya ce "Amma sai nake ganin tun da akwai sauran lokaci to ya dace ko abu uku ne, mu yi kinga fa wannan shi ne aure na farko da, za mu yi a families mu, na tabbatar ko su Momy za su ji daWin a ce an yi wani abun, don haka za mu yi, ko da walima kamu da kuma dinner, ko me kika ce?"

Ya yi maganar yana duban ta amma yadda take tana nan haka nan bata Wago kanta ba, ta ce "Dama can shawara ku ka zo nema a gurina kuma na sanar da ku ra'ayina don haka za ku iya yin duk abun da ya yi maku."

Sai lokacin Sufiyan ya yi magana murya a sanyaye ya ce "?anwata to zancen zuwa haWa kaya fa yaushe kike ganin ya da ce mubar ?asar nan zuwa haWa kayan? ki duba abun da kike ganin shi ne ra'ayin ki, saboda kinga su momy har sun gama haWa maki na su yanzu mu kawai suke jira."

"Allah sarki aikuwa da ba su wahalar da kansu ba kuma kai ma ba sai ka wahalar da kanka ba saboda bana bu?ayar komai, sannan karka manta a wannan zamanin ba komai ake barin mutum ya zaSi ra'ayi shi ba, don haka karka da mu, saboda gaskiya idan ka ga, na bar ?asar nan to ka tabbatar makaranta zan tafi in sha Allah."

Ta Wago kanta ta kallesu sannan ta ce "Idan abun da ya kawo ku, ke nan ni zan wuce Waki na kwanta saboda ina jin bacci sosai" kafin su yi magana ita har ta bar gurin.

Sufiyan da kallo ya bita har ta shige Waki, shuru duk suka yi na Wan wani lokaci, sannan Sufiyan ya yi, a jiyar zuciya ya ce "Humm ai sai ku ta shi mu tafi koh."

**********************
Haka abubuwa suka cigaba da faruwa yau gamu har mun shigo satin biki, yau ake walima kamar yadda aka tsara amma da ?yar aka samu amarya ta cire hijab ta sanya mayafi sai dai ko poda ta?i barin a shafa mata.

Haka ma ranar kamu ta yi, shigar jikinta ce kawai za ta nuna maka cewa ita Win amarya ce.

A daren ranar kamun ne Aunty ta zaunar da ita cikin Waki, sannan ta ce "Na san irin damuwar da kike ciki ba sai kin sanar da ni komai ba, kawai ina ro?on ki, ki rage wannan damuwar saboda za ta cutar dake, kuma matu?ar kika cutu to ni ma tabbas zan cutu, haka ma mahaifinki, ba za mu juri wani abun ya sake faruwa dake ba."

"Ina son ki yarda cewa wannan ita ce ?addararki in sha Allah ba za ki taSa da na sani ba ?ata."

Jikinta ta kwanta ta rin?a kuka sosai mai ban tausayi, kuma sam Aunty bata hana ta ba, saboda ita ma hawayen take, sai da ta yi sosai sannan ta Wan samu natsuwa.

Ta kalli Aunty ta ce "In sha Allah zan yi iya ?o?arina na rage duk wata damuwa ke ma, ki yi man addu'a ubangiji ya ba ni ikon yi ma shi biyayya."

Tana maganar cikin muguwar damuwa jikinta ya yi zafi sosai alamar zazzaSi.

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
PAGE 4?? 4??

~LOKACIN SHA GALIN BIKIN AURE~

Aunty ta ce "?ata" da sauri Rahma ta kalle ta cikin mamaki saboda ba ta saba kiranta da wannan sunan ba, sai dai ta kira ta da, ?ar su Momy saboda kawaici irin na ta.

Kamar yadda su ma suke kiran yaran na su, da ?a ?an Aunty.

Jin hakan ya sa Rahma duk ta haWa natsuwar ta guri Waya don ta ji mai za ta ce, ita ma cikin zumuWi ta sake faWawa jikinta ta ce "Na am Momy ki sanar da ni abun da ki ke son na yi."

Cikin magana irin ta uwa ta ce "Ba umurni na ke son ba ki ba, alfarma na ke son nema a gurin ki."

"Kin ga Iyayenki maza da mu mata da Yayunki, duk mun yo gayyata ta ko ina ?asashe da ban da ban za su zo kuma duk gurin dinner suke, sa ran ganin amarya da ango."

"Kin ga har yanzu ba kowa ya san ki ba, don haka na ro?e ki kar ki bari mu ji kunya ko kuma shi angon na ki, don Allah ki bari a yi maki kwalliya ki fito a amaryarki kin ji ?ata?"

"Kar ki da mu Aunty na yi maki al?awari in sha Allah ba zan bari ku samu abun yin ?orafi a kaina ba, ba zan taSa ba ku kunya ba."

"Zancen kulliya kuma kar ki da mu, ni zan yi wa kaina, kar ki manta ni ma wannan yana cikin aikin da na iya kuma har sana'ar na yi, don haka ba na so ki samu damuwa da wannan."

"To sai zancen ?unshi kuma, na ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ga shi ma har yanzu ?in?i barin a yi maki, sannan ba ki sanar da ni a kan rigar da aka kawo maki ba, kin san fa Yayunki ne suka sanya a yi maki ita daga England, fatan ta yi maki kyau koh?"

"A ta yi man kyau sosai aunty kuma na yi farin cikin ganin ta saboda favorite color ta ce, sannan kuma gyaran kai ?unshi kwalliya duk zan yi ?o?arin yin su da kaina in sha Allah."

"Ke dai Aunty ina son ki yi man wani aiki Waya, jibi ranar dinner duk yadda ake nema na kar ki bari a zo a takura man, ni kuma in sha Allah zuwa lokacin zan fito tsaf, a amaryata yadda kike so" cikin murmushi ta yi maganar.

Aunty ta yi ajiyar zuciya ita ma cikin farin ciki ta ce "Wallahi har kin sanya na ji natsuwa ubangiji Allah ya yi maki albarka" ta amsa da ameen.

Haka dai Aunty ta sanar da su Momy cewa su hana kowa zuwa Wakin Sufayya, wannan umurninta ne.

"Sai dai kuma har sai da lokacin fara Waukar mutane ya yi ba alamar amarya, har an fara tunanin ko dai a karya umunirta a je duba ta.

Sufiyan shi ne wanda ya fara ganin isowar ta, ba shiri ya mi?e tsaye kuma ya gaza Wauke idonsa a kanta, hakan ya sa hankalin sauran mutanen gurin ya kai kanta, su ma duk suka mi?e tsaye.

Duk a takure ta ke saboda rashin sabo da zama ba hijab ga shi kuma ta sanya wadding gowns duk sai ta ji wani iri, amma dole haka ta ke dauriya saboda families ta.

Momy Aisha da sauri ta rungume ta sannan ta ce "?ata ba dan na san ki ba, da ba zan gane ki ba, kin yi matu?ar kyau Allah ya kawar da mugun ido a kanki."

Murmushi ta yi, ta ce "Na gode Momy" Momy Nafisa ta ce "Da ace bake ba ce amarya yau kam dake za ki yi man kwalliya ?ata."

Kaka ya ce "Ai ni har kishina ya motsa, na fara jin an ya kuwa sufiyanu ba zan fasa ba ka ita ba."

Duk mutanen gurin sai da kowa ya yi dariya amma ban da Sufayya murmushi ka wai ta yi dama can shi ne Wabi'ar ta.

Sufiyan ya matsa kusa da ita ya ce "Kin yi kyau sosai ?anwata" su ma ?an uwan su haka suka faWa.

Murmushin ?arfin hali ta yi sannan ta ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login