Showing 111001 words to 114000 words out of 123822 words

Chapter 38 - WATA KADDARA Complete book By (Yar gatan mama).doc

22 Sep 2025

2602

yanzu na Wan samu natsuwa sosai ganin yadda Sufayya ta saki jikinta sosai da Sufiyan, ina tunanin yanzu kam Sufiyan ya samu gurbi a zuciyarta, yanzu kam na fara yarda cewa ba zaman biyayya kawai take yi ba."

Momy Nafisa ta ce "Kin san Allah ?ar uwa a lokacin bikin su ko da yaushe a tsorace nake kar ta yi wani abun da shirin mu zai wargaje, ganin irin tashin hankalin da ta shiga."

"Du bi fa lokacin da muka ce muna bu?atar ta sanar a gaban kowa cewa shi take son aura har sumewa ta yi a kan tsananin damuwa, kin san Allah a lokacin sai da na so cewa mu fasa wannan shirin saboda tsoron kar muzo ayi gawa biyu, garin neman gira a rasa ido."

Dady Ahmad ya ce "To yanzu dai ba ga shi komai ya wuce ba, dama can sune ?ADDARAR juna, ita ce ?addarar sa, shi ne ?addarar ta, ba wanda ya isa ya sauya hakan, fatan mu dai ubangiji ya ?ara sanya natsuwa da farin ciki, a zukatan su" duk suka amsa da Ameen.

Salim ya ce "Ina matu?ar jin kwanciyar hankali idan naga Wan uwa cikin farin ciki, hakan ya nuna yana samun kulawar matarsa, sai dai ban san me ya sa ba, har yanzu na?i yarda cewa ?anwarmu ta faWa son Wan uwa 100%, duk da tana yawan yi mana zancen aure amma nafi tunanin tana yin hakan ne saboda ku iyayenmu ku yi farin ciki, a tunanin ta farin cikin ku zai ?aru idan muka yi aure."

Samir ya ce "?an uwa idan ko haka ne tabbas ya dace mu gano gaskiyar abun da ke ranta domin musan wane matsayi Wan uwanmu yake da shi a zuciyarta."

Aunty ta ce "Amma fa sai nake ganin kamar yanzu tana farin ciki da Sufiyan sosai, ina tunanin gaskiya tana son shi, duk da ba wai magana take da ni ba musamman abun da ya shafi rayuwar gidan auren ta, wannan tunanina ne kawai."

Dady Nura ya ce "Ko ma dai mene ne ubangiji ya tabbatar da alkhari shi ne fatan mu."

Sufiyan dake tsaye jin ya yi ?afafunsa sun gaza Waukar sa a nan gurin ya faWi zaune gumi ne, ke ta zubar ma sa a jiki kamar wanda aka zuba wa ruwa, jikinsa duk ?yarma yake kansa nata juya ma sa, mai mai ta sunan Sufayya kawai yake yana faWin "Har suma ta yi a kan ta tsane ni" wayarsa ya Waga ya fara ?o?arin kiran ta.

Ita kuma a wannan lokacin tana can asibiti aikin yi ya samu ta gaza zama idan ta je nan ta je can, cikin shau?i ta ce "Yaya Sufiyan ke nan a ko da yaushe burin ka, ka rin?a yin surprise Wina ko? to ni ma a ka shirya zan yi surprise Win ka yadda ba za ka manta ba in sha Allah, amma hakan zai fi k?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? yau ranar anniversary party Win mu."

Tana cikin wannan tunanin kiran wayarta ya shigo tana dubawa ta saki wani murmushi ta ce "?an halak kamar ya san shi nake tunani" tana Wagawa bai tsaya amsa sallamar ba ya ce "Ki na ina yanzu?"

Asibiti, shi ne amsar da ta ba shi a ta?aice kafin ta sake wata maganar har ya kashe wayar, da kallo ta bi wayar tare faWin "Lafiya kuwa Yayana yake?"

Bai fi minty uku ba ta hango shigowar sa, da sauri ta ?arasa gurin sa ganin yana yin sa ya bata tsoro, hannunsa ta ri?a ta ce "Lafiya kake kuwa Yaya me ke damun ka, ko kai ba ka farin ciki ne yau?"

Da idanu ya kafe ta, ya Wauki Wan lokaci kafin ya ce "Ba komai ?anwata ina cikin farin ciki ni ma, kamar yadda na lura ke ma kina cikin farin ciki sosai shi ya sa, nake son don Allah ki ?awata wannan farin cikin na mu, da cika man burina a yau kuma yanzu."

"Buri kuma Yaya, wane irin buri ke nan? ban fa fahimci ina zancen ka ya dosa ba."
Daurewa ya yi, ya ja dogon numfashi don ya kawar da damuwar sa kar ta fahimta ya ce "Shi ke nan bari na yi maki ba ya ni, dama ina son don Allah mu koma cikin families mu yanzu ki furta man kalmar kina so na sannan kuma ki faWi hakan har cikin zuciyarki ba wai ki faWi hakan ba don ki faranta man ba, ko families mu."

A zuciyarta ta ce "Lalle ma wannan Yayan ke nan shi ka Wai ya iya surprise, shi ne yake son Waya daga cikin surprise Wina ya Sata man, chabWijam walahi baka isa ba, sai ranar zan haWa duk surprise Wina guri Waya, ba tare da ka yi tsammani ba kamar yadda kake yi man."

Cikin Wan sakin fuska kamar na mai son yin dariya ta kalle sa ta ce "Dama can baya Yaya ban yi cewa ina son ka, a gaban kowa ba?"

"Kin yi faWan hakan, amma sai dai zuciyata na sanar da ni cewa tabbas ko wane lokaci kika furta wannan kalmar to fa kina da dalilin yin hakan ba wai don ra'ayin ki ba, na fara cutuwa ?anwata da rashin jin wannan kalmar ta fito daga ?asan zuciyar ki, don Allah ki taimaka man ki fara so na ?anwata."

Dariya take Soyewa bata son ta yi ya gano so take ta yi ma sa yawo da hankali, cikin sigar shagwaSa ta juya baya tare naWe hannunta a ?irji ta ce "Yaya ni fa na san cewa ina son ka, kuma na sha faWan hakan a gaban mutane, don haka sai dai ka kawo wata sabuwar idea wannan tsohon ya yi ne kawai."

Fizgota ya yi da ?arfi, ya juyo da ita suka fuskanci juna ya ce "Ni a haka nake son tsohuwar idea Win bana bu?atar komai bayan wannan."

Duk ta gama tsorata da yana yin sa, ya sauya ma ta lokaci Waya, ita dai za ta iya rantsuwa ba ta taSa ganin shi a wannan yana yin ba, murya na rawa ta ce "Yaya kwantar da hankalinka me yake faruwa da kai haka? in dai a kan wannan kalmar ne, zo mu je, na shirya zan faWa, ba a gaban families ba, ko a gaban mutanen duniya kake so zan faWa, amma don Allah karka sauya man kana tsoratar da ni."

Kafe ta da idanu ya yi har sai da ta ji duk ta tsargu sosai da kallon, ta sunkuyar da kanta da sauri.
Idanunsa nan take suka fara zubar da hawaye ya ce "Ko da rantsuwa na yi tabbas ba zan yi kaffara ba cewa ba ki taSa so na ba a matsayin mijin ki, ni babu ma abun da yake ?ara Waga man hankali, idan na tuna nake jin zafi a zuciyata irin yadda ba wani burina da ya cika a rayuwar aure."

"Na sha burin cewa idan har na yi aure duk yaran da zan haifa su ne shedar soyayyar da muke wa junanmu, sai ga shi yanzu mun kai ga yara biyu amma sam ?in?i ba ni damar cika wannan burin nawa."

"Ina son ace muna nuna wa junanmu so a gaban kowa, duk wanda ya ganmu ya ga cikakkin masoyan da ke matu?ar ?aunar junansu, amma ina sam ba ni da wannan sa'ar."

Girgiza kai kawai take ita ma da hawayen a fuskarta izuwa yanzu zuciyarta ta fara karye wa sosai, murya na rawa ta ce "Yaya me kake faWa ne haka ni fa wallahi ina son".....

Kafin ta ?arasa ya daka ma ta wata uwar tsawa sai da ta razana, tare da Waga ma ta hannu ya ce "Don Allah ki yi man shuru bana son kina ?ara laifi ga ubangiji, don haka ki yi shuru kawai, don na san duk kalmar da za ki faWa ba gaskiya ba ce."

Da sauri ya bar gurin, tana ta kiran sunan sa amma ya?i ko da juyowa, cikin tsananin tashin hankali ta bi bayan sa amma ina ya yi ma ta, ni sa sosai kuma ga Yayunta da ta hango suna nufo su, da sauri ta tsaya don ba ta son su fahimci da matsala a tsakin su, yanzu nan sai duk families su shiga zancen.

Ita kuma yanzu sam ba ta son hakan, tafi son idan matsala ta tun karo su yi maganin ta da kan su, ba sai kowa ya shiga tsakani ba.

Yana zuwa ku sa da ?an uwansa kallo ya ?are masu sannan ya wuce bai ce da su uffan ba, su ma ganin yana yin sa sun gaza yi ma sa magana.

Ta jima a gurin tana tunanin me ya Sata ran Yayanta haka lokaci Waya, haka ta koma gidan cikin mutane a sanyaye.

Tana ?arasawa gurin iyayensu Aunty ta yi ma ta kallon tuhuma sannan ta ce "Me kika yi ma sa har ya bar gurin nan a wannan yana yin, bayan hakan ba halin sa ba ne? duk yadda muka zo tare haka za mu koma tare, amma sai ga shi yau ya bar gurin nan ba tare da ya yi wa kowa sallama ba, kuma muna ta kiran sunan sa amma ya?i sauraren kowa, hakan ya nuna baya ma cikin hayyacin sa."

Momy Saratu ta ce "Wai don Allah me ya sa duk abun da ya faru ba wanda kuke ganin laifin sa sai yarinyar nan, halan shi Win waliyi ne da baya laifi?" Hannunta ta ri?a ta ce "Mu je gidanmu ki huta ba wanda zai biyo mu balle a takura maki a hanaki suku ni."

Ita dai Sufayya abun duniya duk ya ishe ta, tunanin ta Waya ina Yayanta yake shin ko yana lafiya kuwa?...

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
PAGE 59

Sufiyan kuma yana barin gurin kai tsaye gidan Dady Munir ya wuce, yana zuwa be tsaya ko ina ba sai Wakin Sufayya a kan gadonta na yarinta ya faWa a kife rub da ciki ya yi, da yake komai na yarintar ta yana nan ba abun da aka cire, bayan ta dawo kuma aka raba Wakin biyu aka sanya ma ta wasu kayan na manya saboda Wakin babba ne sosai shi ya sa duk ya Wauke komai har aka bar sauran fili sosai.

Daga kwancen ya runtse idanunsa hawaye suka biyo a kan fuskar, ya fara tunanin irin yadda yake mutuwar son ta tun suna yara.

Idan ya wuni be ganta ba, ba ya da sukuni, sannan idan ta tun karo ga guri ko be ganta ba, bugun zuciyarsa ke sanar da shi cewa tana gurin.

Tun lokacin da, ta Sata kuma be sake jin irin haka a kan ko wace mace ba sai ranar da ya fara ganin ta a gidan su, a take ya ji duk yana yin da yake ji a kan ?anwarsa ya dawo ma sa sabo a kanta shi ya sa, ya iya furta ma ta kalmar so lokaci Waya.

A lokacin da suka fahimci cewa ita ce ?anwar su, ya yi ta, yi wa Allah godiya burin sa na tun yarinya ta zai cika zai auri ?anwar sa abar ?aunar sa.

Ya tuna wata rana suna zaune su biyu a Wakinta sai faman rigima take ma sa wai mp Win ta, ta tsaya ta daina karatu kuma ita kam ba za ta iya bacci ba sai ta ji karatu, daya ga ji da rigimar ta da kuma lallashi, ya Wauko ma ta, ta shi ya ce "Kin ga ki yi amfani da tawa zuwa safe sai Dady ya duba maki ta ki Ko."

Cikin farin ciki ta ce "Yayana na gode sosai" shi ma a nan take ya ji ya shiga farin ciki ganin ta daina kuka ya ce "?anwata zan iya ba ki komai dana mallaka daga ciki ko har da rayuwata."

"Amma yanzu ina ne man alfarma a gurin ki, ki yi man al?awarin cewa za ki zama tawa har abada sannan za ki so ni kamar yadda nake son ki, ba za ki taSa bawa wani namiji damar shiga zuciyarki ba, sai ni ka Wai."

A rashin sanin ina maganarsa ta dosa, da maganar ta ta yarinta ta ce "Yaya na yi maka al?awari hakan" ranar a jikinsa ta kwana sai da Aunty ta shigo neman sa saboda ta duba Wakin su baya can Salim da Samir ne kawai a gurin, duk yadda ta so raba su sun ?i rabuwa hakan ya sa ta kyalesu.

************************
Da ?arfi ya daki gadon yana faWin me ya sa kika Waukar man al?awarin da, ba za ki cika ba, me ya sa kika yi man haka kika karya man zuciya, me na yi maki ne dana can can ci hakan a gurin ki?" kuka yake sosai kamar wani ?aramin yaro.

?an garen Sufayya ita ma sam bata cikin natsuwar ta, su Momy ma sun fahimci hakan saboda ta je part Win sa yafi sau goma, ta kira wayar sa a kashe duk suke, haka kawai ta ji kuka ya zo ma ta.

Tana ta faWar "Ni kam na yi dana sanin wannan jinkiran da na yi lokacin da ya ce, mu je na faWi abun da yake son ji a cikin mutane, da na je kai tsaye da duk hakan be faru ba."

"Amma a zahirin gaskiya bana tunanin wannan ne dalilin wannan fushin na shi" Waga kai ta yi sama hawaye na zuba ta ce "Ya Allah ka kulaman da Yayana karka bar damuwa ta yi ma sa illah."

********************
Sufiyan a nan gurin ya kwana tun da asuba ya fice daga gidan ya nufi gidan su, a kan hanyarsa na tafiya ya kunna wayoyinsa wanda suke a kashe tun jiya, kamar jiran ake ya kunna wayar kiran ?an uwansa ya shigo, bayan ya Waga har sun fara masifar ina ya shiga haka kuma duk ya kashe wayoyinsa, muryarsa da suka ji ba daidai ba shi ya sa suka yi shuru su ji me zai ce.

Ya ce "Me ye matsalar ?an uwa bayan kun san ba zan kashe kaina da hannuna ba, dole na jira lokacina ya yi, yanzu dai ku same ni airport zan tafi Saudia wani aiki, daga nan kuma ina son zan yi umra in sha Allah."

Salim ya ce "?an uwa ya kake magana haka, kuma Umra yanzu ba tsammani, Wan uwa sanar da ni yanzu kana ina?"

"Ina kan hanyar zuwa gidan Momy Saratu yanzu in sha Allah" da sauri suka ce "Ok don Allah ka jira mu a can gamu nan zuwa gidan."

************************
Ya rigasu ?arasowa Wakin ya shiga kai tsaye ya Wauko wata ?ar ?aramar jaka ya zuba wasu takardu a ciki, ?o?arin fitowa daga Wakin yake ya ji, ya yi karo da mutum yana dubawa ya ga Sufayya ce idanunta har sun sauya saboda kuka da rashin bacci, kamar yadda shi ma yana yin sa yake.

Suna haWa ido ta sunkuyar da kanta sannan cikin sanyin murya ta ce "Ina kwana Yaya, don Allah ina ka shige haka tun jiya?"

Sai da ya ?are ma ta kallo ya ga kamar da gaske ta shiga damuwar rashin sa, kawar da wannan tunanin ya yi tare da cewa "Lafiya ?alau, ya kike, ina yarana?"

Ganin cewa har yanzu bai dawo daidai ba hakan ya sa jikin ta ya ?ara sanyi a sanyaye ta ce "Ni ma ina lafiya, yara kuma suna gurin Momy."

"Ok bari na duba su" ya wuce ya barta nan gurin tsaye, yana zuwa iyayensa na guri Waya ya gaidasu a tare sannan ya ce yazo ne ya yi masu sallama, tafiya ta kama shi yanzu zuwa Saudia kuma yana son ya yi umra daga nan.

Dady Suraj ya ce "Maa sha Allah ke nan yanzu iyalin naka ka zo Wauka ku tafi tare Koh?"

Ya kalli gefen da Sufayya take a tsaye ya ga ta rufe ido da sosai, tunanin sa bata son ta bi shi, shi ya sa, ta rufe ido haka, wani irin zafi ya ji a zuciyarsa, shi ma Wan rufe idon ya yi na lokaci.

Ita kuma hakan da ta yi addu'a take Allah ya sa, ya amince su tafi tare wata?il su samu damar fahimtar juna kafin su dawo, kuma ta samu damar sanin me ke damun sa haka tun jiya, amma sai ta ji saSanin hakan ta jiyo yana faWin.

"Ah Ah ni ka Wai zan tafi saboda ba wani jimawa zan yi ba, sannan kun ga akwai yara idan na fita aiki kulawa da su zai yi ma ta wahala tun da dai ba yaye su, ta yi ba, amma idan kuna tare na san daga ita har su, za su samu kulawar da, ta dace in sha Allah."

Momy ta ce "To doctor Allah ya tsare, amma fa karka jima ba ka dawo ba don Allah saboda kabar iyalinka a nan" ta kalli Sufayya da tun Wazu ta yi suman tsaye, tun da ta ji cewa wai ba tare za su tafi ba, Momy ta ce "Ke kuma je ki raka shi ku samu yin sallama."

Sufiyan ya yi gaba Sufayya ta bi bayansa sai da suka yi, ni sa daga gurin iyayensu sannan ya kalleta ya ce "Zan iya jure ?iyayar da kike yi man, amma don Allah ki kulaman da yarana kar ki bari ?iyayar da kike yi man ta sha fe su, sam ba zan juri hakan ba, na san ba wanda ya kai ki son su a matsayin ki na mahaifiyar su, to don Allah ina son ki cigaba da nuna ma su wannan kaunar ta UWA, wannan alfarmar ka Wai idan kika yi man kin gama man komai."

Ta Wan jima kafin ta yi magana, ganin haka ya sa ya juya ya nufi mota har ya bude ?ofar yana ?o?arin shiga da sauri ta rufe ?ofar ta kalle sa idanunta cike da hawaye ta ce "Yaya Allah ya tsare ya kai ka lafiya, kuma don Allah ka kula da kanka sosai ko dan yaran ka, tun da dai ni har yanzu ba ka yarda cewa ina son ka ba" hawayen da take ?o?arin Soyewa suke son zuba da sauri ta bar gurin ta shige cikin gida.

Ya jima a gurin yana nazarin maganarta a zuciyarsa yake cewa "Ko dai da gaske ta fara so na, ni ne ban fahimci hakan ba? wata zuciyar kuma ta ce "Kai ina ba zan bari na sake kuskuren tunanin tana so na ba kamar yadda na yi a can ba ya, ba za ta taSa so na ba."

Yana nan tsaye ya hango ?an uwansa shigowa da sauri ya Wauki jakarsa ya nufi gurin su ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login