Showing 15001 words to 18000 words out of 123822 words

Chapter 6 - WATA KADDARA Complete book By (Yar gatan mama).doc

22 Sep 2025

2588

sa ta yi, ta ce "Me zan zuba maka Yaya?"

Cikin zumuWi ya ce "Duk abun da kika ga ya dace ina so."

Bayan ta gama aikin san yawa kowa abincin, ta nufi hanyar komawa Wakin ta, cikin sauri Momy ta ce yau dai don ALLAH 'yata ki zauna damu ki ci abinci kin ga koba komai ya yi yawa ba za mu iya cin yewa ba."

"Ki yi ha?uri Momy bana?i ta yinki bane amma idan ya yi saura kubawa ma bu?ata kamar dai kullun saboda yau litanin ina azumi."

Sufiyan na jin hakan har ya Wau chokali sai kawai ya ajiye, "Momy na man ta ni ma azumin nake yi fa."

"Yaushe wannan tunanin yazo kuma?"
Momy ke tambaya.
Dama can da tunanin na kwana Momy."

Dady ne ya ga tana son ji?awa Wan sa aiki da sauri ya ce "To ALLAH yaba da lada my son,
A nan Momy ta gano bakin zaren ita ma, ta ce "ALLAH ya karSi ibada."

Girgiza kai Rahma ta yi, ta wuce Wakin ta da tunani iri iri a ranta,
Anya kuwa su Momy basu san Sufiyan na son ta ba?"
******************
Daren ranar haka kawai Sufiyan ya gaza samun sukuni, zuciyar sa, na rayamasa akwai abun da Rahma ke shiryawa, amma kuma mene ne abun?

Yana cikin wannan tunanin kawai sai ya jiyo tafiya cikin sanWa fitowa ya yi da sauri ya kunna fitalar parlorn Rahma ya hango har ta kusa ficewa daga gidan da ?arfi ya ce Rahma.

Rahma tsayawa ta yi cak amma ba alamar zata koma ko kuma ta ji tsoro,
Gurinta ya ?arasa ya ce "Rahma ina za ki je haka cikin daren nan don ALLAH?"

Cikin dakewa Rahma ta ce "Tun da kace don ALLAH to zan sanar da kai, Barin gidan zanyi kuma saboda kai,
Duk kabi ka addabi rayuwa ta, shi ya sa nayi tunanin tafiya idan na tafi basai naga yadda za ka takura man ba."

Hankalin Sufiyan ya yi matu?ar ta shi, amma sai ya daure ya ce "Yanzu don ALLAH Rahma sai kibar gidan nan saboda ni kawai?"

"Sosai makuwa ko kana tunanin ba zan iya ba?"
"Ya ce ko da can baya banyi tunanin za ki iya ba, yanzu kam na yarda gaskiya, amma kin san wani abu kuwa?"
Cikin murguWa baki da harara ta ce "Sai ka faWa sannan." har da wani girgiza take shi abun ma dariya ta so ba shi.

"A. gaskiya na yi matu?ar mamaki ace wai baki san wasaba, ni fa wasa kawai nake yi maki amma ba wani zan can soyayya a tsakinmu inma akwai to bata wuce ta Yaya da ?anwa ba."
Watsa ma sa wata irin harara ta yi, da manyan idanun ta sannan ta ce "Ni zaka mai da ?aramar yarinya ko kuma sakarya ban san abun da nake yi ba kenan?"
"A cikin idanun ka na hango gaskiyar maganar ka sannan kwana biyun nan har da rashin cin abinci da shiga damuwa duk a kan baka samu amsa daga bakina ba, yanzu shi ne za ka ce, da ni duk wasa ne hakan?"

"Wannan duk gaskiya ne amma nasan kafin na dawo ?asar nan kin samu labari na, daga ciki har da yadda na tsani soyayya, wannan shi ne dalilin."
"Bayan zuwa na dana ganki sai naga kamar irin ra'ayin mu Waya amma saboda na tabbar da hakan shi ne na gwada ki ta wannan hanyar kuma tabbas kin ci jarabawa amma don ALLAH ki yi man afuwa da Sata maki ran da na yi."

"Kallon sa ta yi cikin kar yar da kai murya a sanyaye ta ce kuma don ALLAH gaskiya kake sanar da ni?"
"Sai kuma na ga kamar su Momy sun san kana so na?"
"I ya gaskiyar kenan ?anwata kuma da su Momy sun san komai ba zakiji gidan nan haka tsit ba yadda suke jiran na kawo masu wacce nake so."
"ALLAH ko yaya?"
"ALLAH kuwa ?anwata."

Amma me ya sa bazaka samu wace kake so ba tun da shi ne labarin da suke so a yanzu."

"Ni ma zan so hakan ta faru amma matsalar bana soyayya saboda a duniyar nan bana tunanin akwai sauran son gaskiya."
Shuru ta yi, na Wan lokaci idanun ta suka cika da hawaye ta ce "Kuma maganar ka gaskiya ce a wannan duniyar ba soyayyar gaskiya,
Amma kataSa wata soyayya ne wacce ka chutu?"

Ah Ahh. gaskiya har yanzu ban taSa yi ba saboda ina tsoron yaudara ina son wacce zata so ni bawai wani abun nawaba."
"Wannan kuma gaskiya ne, ina yimaka fatan ALLAH ya baka mace ta gari."
"To ameeen ya ALLAH."
Amma dai yanzu mun shirya koh, kin yarda za ki zama ?aunata kuma ?awata ko?"
"In sha ALLAH mun shirya ka dawo da matsayin ka na yayana har da ?arin zama abokina amma fa da sharaWin ba zaka sake yiman wannan wasar ba."

"In sha ALLAH ba zan sakeba, yanzu dai yi sauri kizo na raka ki Wakin ki kar su Momy su ganmu a nan dare ya yi, gobe idan ALLAH ya kai mu sai mu ?arasa maganar."

"To matsoracin yayana tsoro kake Momy ta fito ta ganmu ta Wauka zance muke, ta ce ka shirya aure satin nan ba fashi."

"Aiba ni kaWai ba ne matsoracin ba harda ke, dan nasan idan aka faWi hakan har suma sai kinyi."
"Tabbs kuwa zan iya, sai dai ta wani fannin ni kam bazan damuba saboda guduwa aguna abune mai sau?i."
Na yarda za ki iya yanzu ma, ba dan ALLAH ya fito daniba nasan watakil da tuni kin gudu,
A haka dai suka ?arasa Wakin ta, shiga ta yi sannan ta yi masa sai da safe
Shi ma ya wuce part Winsa cike da damuwa a ransa....

WATA ?ADDARA
ANOTHER DENSITY
By
SUWAIBA M AMIRU
('Yar gatan mama)
' 08160726558
PAGE 1?? 2??

Bayan shigar sa Waki zuciyarsa ya ji tana yi ma sa zafi sai wani bugawa take sosai wasu hawaye ne masu zafi suka sauka a kan fuskarsa sai faman faWin yake me ya aikata haka yanzu na rasata a matsayin matar aure kenan?
Alwalla ya Wauro ya fara sallah har bacci Sarawo ya yi awon gaba da shi.

A Sangaren Rahma kuwa farin ciki kawai take tana yi wa ALLAH godiya da ya sa ashe yaya wasa yake mata, ita ma a haka ta yi bacci cikin matu?ar farin ciki.
Da safe iyayen na su sunyi matu?ar mamakin ganin yadda komi ya sauya musamman ta Sangaren Rahma ganin cewa har da gaida Sufiyan kuma cikin sakin fuska sosai.

Rahma na tafiya Wakin ta da sauri Momy ta kalli Sufiyan tare dayi ma sa tambayar meke faruwa?

A nan dai ya kwashe duk abun da ya faru tsaninsu a daren jiya ya sanar da su, ko da ya ?arasa faWamasu idanunsa sun cike da ?walla.

Cikin kulawa Dady ya ce "amma meka aikata haka, kenan ka yi ha?uri da ita?"

A rauna ne ya ce "Dady wasu lokutan muna barin abun da muke so saboda wanda muke so,
Ita soyayya bawai tana nufin mai da wanda kake so ya zama naka ba, ah ahh tana nufin saudakar da duk abun da kake da shi domin wanda kake so ya yi farin ciki."
"Dady a jiyar nan da ban sanar da ita abun da take son ji ba, da tu ni ta bar gidan nan, tambayar a nan ita ce idan ta tafi ina za ta faWa kuma awane hali za ta kasance duk'kan mu ba mu sani ba."
"Dady da'ace yau mun wayi gari bata gidan kuma saboda ni, ta bar gidan da ba zan taSa yafewa kaina ba kuma zanfi cutuwa sosai a kan yanzu."
"Amma yanzu kadubi magana ta Waya yadda ta sauya komai sai farin ciki take ni kam wannan kaWai ya isa na yi farin ciki ni ma, idan har ALLAH ya yi ita Win matata ce in sha ALLAH sai na aureta."

Dady ya rungume shi sosai ya ce "Ina alfahari da kai, ina ro?on Allah ya baka ikon cinye jarabawa kuma ya sanyama Rahma son ka kamar yadda kake son ta."

Da sauri ya amsa da "Ameen Dady na gode sosai."
Wunin ranar haka suka zauna kamar waWan da aka yi wa mutuwa.
********************
Lokaci na tafiya cikin kwana biyu zuwa uku wata sabuwar sha?uwa ce tsakanin su komai za ta yi sai ya yi ?o?arin ta ya ta duk'da bawa ni iya aikin ya yi ba sai dan yana samun kulawa da taimakon Rahma, har mamaki suke yi dama haka Rahma keda sau?in kai.

A yanzu dai sun gano kaWan daga cikin abun da bata so kuma idan mutum ya ki yaye to za su zauna lafiya, sun lura bata son zancen sanin wace ce ita kuma bata son zancen soyayya da kuma zancen ta dena Waukar nauyin kanta,
Tun da kuwa suka fahimci hakan shi kenan suke ki yayewa.

Ita ma yanzu tana jin cewa Yaya shi ne abokin ta ko'ina ka gansu a tare idan sun gama aikin to suna parlor ko lambun gidan.

Kamar kullun bayan sun gama girkin sun jera ?o?arin zubawa kowa take Sufiyan ya ce "Ni dai kar ki zuba da ni saboda yau ba shi zanci ba gaskiya."

"Lalle ma Yayan nan ka san da hakan me ya sa baka sanar da ni a kan lokaci ba, na haWa maka wani abun?"
"Ko yanzu hakan za'ayi saboda duk abun da za ki ci yau ni ma shi zanci."

Ware idanunta ta yi, ta ce "Kamar yafa ban gane ba?"

"Ina nufin za mu rin?a cin abinci juna idan yau munci na ki gobe kuma sai nawa."

Rahma ta ce "Dady don ALLAH ka sanar da shi gaskiya ba zai iya cin abun da nake ci ba."

"Yau kam 'yata ba zan goyi bayan ki ba,
Saboda idan har aboki ba zai iya cin abincin abokinsa ba saboda wani dalilin to bai dace akira shi aminiba kuma ke kinsan da haka."
Shi ke nan na yarda amma ni kam ba zanci na shi ba saboda ban saba ba."

Kawai faWuwa ya yi a ?asa yana ta birgima yana buga ?afa kamar dai wani ?aramin yaro sai faWin yake "Momy ki sanar mata ban yarda ba dole ta koya kamar yadda zan koya."

Momy ta ce "Rahma yau dai ki na son Yayanki ya tuna halin na sa, na yarinta koh?"
Kusa da shi Rahma ta je, ta ce shi ke nan zan yi yadda kake so."

HaWa masu garin kwakinta ta yi, ta sanya duk abun da ya kama ta gyaWa sukari, dama dai sune mahaWin na ta, ko madara babu, kofi Waya ta ba shi ita ma, ta Wauki nata, hanyar shi ga Waki ta nufa
Da sauri ya dakatar da ita da cewa "Ina kuma za ki tafi?"
"?aki mana na ci abinci koh."
"Me ze hana ki zauna tare da mu."
"Wai kana nufin sai na yi ta buWa baki ana kallona."

Sai da yayi dariya sosai sannan ya ce "Na yi maki alkawarin ba wanda zai kalleki har da ni ma kaina."
"Wai da gaske kake don Allah?"

Da gaske na ke, kuma zo ki zauna ki ga ni idan kinga wani na kallonki ki sanar da ni kawai zan Wauki mataki."

A haka dai ya samu ta zauna shi ma ya fara shan nasa amma kana ga ni kasan bai sababa da ?yar yake tura shi, sai dai ya lura ita lafiya ?alau ta ke shan na ta amma duk ta, takura saboda rashin zama cikin mutane irin haka.

Momy kuwa har hawaye ke zubo mata ga nin yadda Wan nata ke faman koyon shan wannan abun, duk soyayya ta sauya masu rayuwar Wansu.
*********************
Lokaci na tafiya a yanzu Sufiyan ya koyi abubuwa sosai daga Rahalma kama daga kan azumin litanin da alhamis da zuwa kasuwa rakata siyayya duk'da idan sunje sai dai ya zauna mota ita ta je siyo abun da ya kaita, ita ce ta ba shi wannan umurnin saboda ganin bai saba ba.

Kamar ko yau she suna firarsu a lambu Rahma ta ce "Yayana yau ne zuwa kasuwa ta kuma ya dace mufita a kan lokaci saboda ina son mubi ta gurin masu Win ki."

Sufiyan ya ce "Ah ah ki ce yau ?anwata har da sabon Win ki, za ta yi?"

A. haka ne, amma fa idan kana ganin da takura kabari kawai na je, ni kaWai saboda za mu jima awajen gaskya."

"Wace magana kike yi haka, wai kuwa kin Wau kan yadda na Wauke ki ?anwata?"
"Sosai ma kuwa yayana."

To idan haka ne, ki ta shi kawai mu tafi kar yamma ta yi."

Cikin gida suka koma sanar da Momy gurin da za su je, Momy taWau kuWin Rahma kamar kullun ta ba ta, sh ima Sufiyan ya ce yau ba inda za shi sai ta ba shi na shi kuWin ai shi ma yanzu tare suke aikin.

Rahma ta ce to yazo suraba na ta amma ya dage shi Momy yake so tun da ita ce mai biyan, shi ne bai bar gurin ba sai da Momy ta ba shi na shi kuWin tukunna suka tafi.

Sun je kasuwa ta gama duk siyayyar ta sannan suka baro kasuwar ta dinga yi masa kwatancen hanyar shagon Winkin suna isa mai shagon ya ce, "Rahma yau har da Wan rakiya kika zo?"

"Yayana kuma aminina" amsar da ta ba shi ke nan, ranta a hade babu alamar wasa a tare da ita
Ya ce "Shi ke nan ba damuwa yau ma Winki za ki yi?"
"Ka taSa ganina gurin nan idan ba Winki na zoba?"
"Ni fa wallahi na tsani yawan tambaya kuma na sha sanar da kai hakan."

Ganin yadda ran ta ya Saci shi ne ya yi saurin cewa don Allah ki yi ha?uri."
"Na ji, yau dai nawane kuWin hayar keken ?"
Sai a nan Sufiyan ya yi magana "Wai ?aunata me kike shirin yi a nan, na yi tunanin bada aikin Winkin za ki yi gobe sai muzo karSa?"

Ah ahh Yaya ni dai bana bada Winkina, ni ke yin kayana da kaina, yanzu dai ka zo mu shiga ciki na fara saboda yamma na yi kuma ka san su Momy na can suna jiran mu."

Haka Sufiyan ya bita baki sake, shagon babba ne sosai Sangaren maza daban mata daban.
Kallon sa ta yi, ta ce "Yaya ka zauna gurin maza ina zuwa yanzu in sha ALLAH."
Cikin awar da bata wuci Waya zuwa da rabi ba har ta gama.

Bayan ta fito mai gurin, ya ce "Wai don Allah ba za ki fara aiki a nan ba duk kika zo sai na yi wannan ro?on amma har yanzu kuma ro?ona bai samu kar Suwaba ina son zaman ki gurin nan saboda wallahi duk shagon nan ba wanda ya yi saurin Winkin ki Rahma."

Rahma ta ce "Malan karSi kuWinka kuma wallahi duk na sake zuwa gurin nan ka sake da mu na, da yawan magana Allah ba za ka sake ganina a nan ba."

Tana zuwa kusa da Sufiyan ta ce "Yaya mu tafi kawai, sun zo kusan fita sai ga SALE shi ma yana ?o?arin shigowa shagon cikin sauri,
Cikin sauke ajiyar zuciya Sale ya ce masoyiya yanzu don Allah ta ya, za ki zo gurin nan har ki tafi baki neman ba."

BuWe idanu Sufiyan ya yi kamar za su faWo ?asa jin ankira Rahma da masoyiya kuma inji wani na mijin.....

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' 08160726558
PAGE 1?? 3??

Sale matashi ne yana aiki ne a shagon shi ma, sannan yana Wan shaye shaye amma a duniya ba wace Sale ke so kamar Rahma tun ranar da ta fara zuwa shagon, kuma duk ta zo sai ya takura mata dan ma ita Win ba kanwar lasa ba ce,
Yau ma kamar kullun suna kusan fita ne ya shigo, tare ta ya yi kamar mai shirin faWa mata a jiki.

Kauce ma sa, ta yi tana neman wucewa sai kawai ya ri?o mata hijab da ni yar tsayar da'ita hakan ya faru a kan idon Sufiyan kafin ya yi wani yun?uri har Rahma ta wanke Sale da wani wawan mari kafin ta kai na biyu har Sufiyan ya kai ma sa, na shi marin haka yarin?a jibgarsa yana faWin "Da wannan ?azamin hannun na ka, za ka ri?ar man hijab Win Rahma ta kai Win Wan waye?" da ?yar aka raba su.
Amma Sufiyan ya yi wa Sale mugun duka wanda har ya gaza guduwa ya, faWi nan ?asa kwance.
Ogan gurin ya ce "Don Allah ku yi ha?uri wallahi kullun ta zo sai na yi mai kashedi amma ba ya ji, kuma ita ma tana jamasa kunne amma duk a banza, ban san wanda ya ce, da shi haka ake yin so ba."

"Sufiyan ya ce daman kin san hakan na faruwa amma kike zuwa nan gurin?"
Tun da mu kazo na ji gurin bai kwanta man ba, to yanzu ai sai ki wuce mu tafi koh."

Tun da suka shiga mota ba wanda ya yi magana a cikin su kana ganin idanun Sufiyan ka san ransa a Sace yake a haka suka iso gida.
Suna shiga ya wuce Wakinsa ko gurin su Momy bai shigaba, ita ma Rahma a sanyaye ta shiga ta sanar sun dawo daga haka bata sake magana ba sai kawai ta wuce Waki,
Tun daga ganin haka Momy ta san cewa akwai matsala.

Ita da Dady suka je gurin sa yana yin da suka tarar da shi shi ne, ya ba su damar sake yar da cewa akwai matsala, da ?yar suka samu ya Wan natsu har ya yi masu bayanin abun da ya faru bayan fitarsu.

Momy ta ce "Haba Sufiyan yanzu saboda Wan wannan abun za ka Sata ranka kai da ya dace ace katsaya ka kwantar wa Rahma hankali saboda ita ma ranta a Sace yake, kai ne babba kai ya dace ace naka fushin ya sauka."

"Momy ta san fa gurin akwai mai takura mata amma ta ke zuwa don ALLAH yau da bama tare me kike tunanin zai faru?"

"Ba abun da zai faru sai alkhairi karka manta ka ce har marinsa ta yi, ka ga ke nan Rahmar mu jaruma ce."
"To yanzu Dady ya zan yi ke nan?"
Ya yi maganar yana duban Day cikin rauni.

"Ka je ku shirya da ?aunarka sannan ka yi maganin zuwa gurin masu Win kin."
"Kamar ya fa Dady?"
"Ka siya mata keken Win kin ka ga shi ke nan ta dai na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login