Showing 90001 words to 93000 words out of 123822 words

Chapter 31 - WATA KADDARA Complete book By (Yar gatan mama).doc

22 Sep 2025

2600

ta ce "Au ashe har labarin ya zo maka ka ji sanyi a ranka, to ka zauna nan ka yi tunanin ta da kyau idan ka gama sai ka same ni gidan Momy a can zan yi maka girki saboda ban girka komai ba a nan" kan ya yi magana har ta bar gurin ta fi ce daga gidan.

Cikin sauri shi ma ya yi wanka ya shirya sannan su ka fito shi da ?an uwansa sai gidan Momy Nafisa, suna shiga Samir ya ce "Ni dai yunwa nake ji sosai Momy."

"Yau ?anwar ta ku bata yi maku girkin ba ne halan, ko har yanzu bata dawo daga makarantar ba ne?"

Da sauri Sufiyan ya ce "Ban gane ba Momy tun Wazu ta zo nan gidan"
"Gaskiya bata zo ba saboda tun Wazu ina cikin parlor nan banga shigowar ta ba, kuma ni ma nan ita nake jira za ta yi man kitso yau."

A take suka mi?e tsaye suna faWin "Hakan ba zai yuyuba Momy tafa kai awa biyu da fitowa kuma nan tace za ta shigo."

Shin wai mene ne abun Waga hankali haka wata?il bayan ta fito ta sauya ra'ayinta ta shiga wani gidan, ku kira sauran iyayenku ko tana gurin su."

Cikin hanzari suka rin?a kiran iyayensu amma duk inda suka kira sai ace bata zo ba, kuma sun bincika ko ina cikin gidan bata nan, hankalin su ba?aramin ta shi ya yi ba har ita kanta Momy'n.

Ba'a Wauki wani dogon lokaci ba sai ga duka iyayen sun zo gidan, Dady Ahmad ya ce "Kun binciki mai gadi kuwa ko yaga shigowar ta?"

Sun je sun binciki mai gadi ya ce gaskiya bai ga shigowar ta ba amma Wazu ya Wan shiga ban Waki wata?il bayan tafiyar sa ta shigo.

Cikin sar?ewar murya Sufiyan ya ce "Ko dai har yanzu tana cikin fushi da abun da Rashida ta sanar da ita?" daga bi sani kuma ya ce "Gaskiya ina da tabbacin komai Sacin ran da take ciki ba za ta bar gida ba har ta yi ni sa, ya Allah ina ro?on ka kasa ?anwata bata cikin hatsari."

"Karka Waga hankalin ka Wan uwa in sha Allah tana lafiya kuma bata yi ni sa ba, za mu ganta" Salim ke maganar.

Shuru duk suka yi suna tunanin ta ma ina za su fara neman ta, Samir ya ce "Ku Wan dakata mun duba duka gidajenmu bamu sameta ba amma kuma bamu duba gidan gona ba."

Dady Nura ya ce "Duk da ban san abun da zai kai ta gidan gona ba yanzu amma ya dace mu shiga mu ga ni."

Aikuwa suna dosar gurin suka jiyo muryarta tana faWin ?anena ka daina tsinko wanda ya nuna, na sanar da kai Wanye nake so."

Da sauri sun ka ?arasa gurin ta amma bata ma lura da su ba sai faman wanke mangworo tana sha har wani lumshe idanu take, can saman icce kuma Wan mai gadin gidan ne ta sanya yana ta tsinko ma ta, da sauri Sufiyan ya ?arasa gurin ta ya fizge na hannunta ya jefar.

Tana buWa idanunta ta ga duk families a kanta sai kawai ta fara kuka kamar wace aka yi wa duka, Aunty ta ce "Au ke nan kuka kika samu damar yi bayan kin gama Wagawa mutane hankali ana ta neman ki."

Cikin kuka ta ce "To ba na sanar da Yaya cewa nan gidan zan zo ba, to meye kuma zai sa a neman, kuma ai dole na yi kuka kina fa ganin yadda ya jafar man da mangwaro."

"Amma da kika zo meya hana ki fara shiga gidan Momy ta san kin shigo kafin kizo nan, kuma kin san cewa wannan Wan yan ne zai cutar dake amma shi ne kike sha, idan kina so ai kin san akwai mai kyau cikin ko wane gida a fright to me kike yi da wannan" Sufiyan ke maganar ran sa a Sace.

"Ni kam bana son na gidanmu saboda duk sun nuna sosai kuma gidan gonar mu ?ananu ne shi ya sa na zo nan, kuma ma nafi son wanda aka tsinko yanzu."

Zai sake magana Momy Saratu ta hana ta ce "?ata ta shi mu shiga cikin gida sai ki sha cikin natsuwa."

"To Momy" har ta mi?e tsaye ta kalli Yayunta "To ku taimaka ku kwaso man ku shigo da shi ciki."

Kallon ta suka tsaya yi sai da Momy ta ce "Ba ku ji abun da ta faWa ba ne?" ransu a Sace suna ta faman hararar ta, ita ma mayar masu da hararar ta yi ta ce "Ai sai ku yi kuma ko duka na za ku yi sai na sha tun da ba a cikinku na saka ba ehee" har da wani murguWa masu baki...

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
By
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' PAGE 5?? 2??

Kwana biyu da faruwar hakan su Kaka na sauka ?asar a gidan Dady Munir suka sauka bayan sun huta duk sun haWu a parlor Sufayya kuma tana zubawa kowa abinci ta gama da kowa ta zo kan Sufiyan za ta zuba ma shi sai jin Kaka suka yi yana faWin ku san fa zancen auren yaran nan ne ta kawo mu Salim da Samir wai shin har yanzu ba su samu waWan da suke so ba ne?"

A take jikinta ya fara rawa abincin da ta Webo da niyar za ta zuba ya zube ?asa idanunta suka ciko da hawaye, da sauri Sufiyan ya ri?eta ganin yadda jikinta ke ta faman rawa ya ce "Lafiya kike kuwa ?anwata ya naga Jikin ki haka?"

Da ?yar ta ce "Lafiya ?alau Yaya amma idan ba damuwa ina son na je na Wan kwanta saboda jiri nake ji sosai."

"Ba damuwa ki je ki kwanta, ko dai na raka ki?"
"Ah ah Yaya zan iya in sha Allah."

Tana barin gurin Yayunta suka kalli Kaka Salim ya ce "Don Allah ku daina zancen nan, na ga dai ko a musulunci aure ba dole ba ne, sannan idan har Allah ya nufi za mu yi aure a cikin duniyar nan to kuna zaune za mu, zo maku da zancen da kanmu, amma yanzu ba wannan tunanin a ranmu don Allah ku cire wannan tunanin a ranku."

"Kuma ai naga dai muWin maza ne, sannan in sha Allah za mu iya kulawa da kanmu tare da addu'ar ku, a matsayin ku, na magabatan mu."

"Shi ke nan ba damuwa Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhari kuma Allah ya yi maku albarka, cewar Kaka Alhaji."

*********************
Aunty ce ta shiga gurin ta tarar da ita kwance duk da ta rufa da blanket amma rawar sanyi jikinta yake Aunty ta ce "Me kike yi haka ne kina ganin abun da kike yi dace? ba za ki yi tunanin halin da Sufiyan zai shiga ba idan ya fahimci abun da kike."

Da ?yar ta koma zaune ta ce "Yanzu kuma Aunty me na yi don Allah, me kike tuhuma ta a kai?"

Tambaya ta kike me kika yi, kina fa jin abun ya kawo Kaka kika shiga wannan halin ga shi nan har yanzu ba ki dawo daidai ba, to ki sani za ki karya zuciyar Sufiyan saboda yanzu ya gama yarda kina son sa."

Aunty na san ba lalle abun da zan faWa ki yarda ba, amma wallahi ba ina cikin wannan halin ba ne saboda maganar Kaka ba, da gaske bana jin daWi, kawai dai yana yin nawa ya sauya ne daidai lokacin shi ya sa kike tunanin haka."

"Aunty me zai sa na ji ba daWi don an yi maganar auren su, to idan ba su yi aure ba ni zan aure su ne?" Aunty idan har da gaske ina son su ai dole na so, su yi farin ciki."

Cikin kulawa Aunty ta ce "Kin tabbatar da abun da kika sanar da ni gaskiya ne, kuma idan gaskiya ne me ya sa ba ki sanar da kowa ba musamman Yayan ki, ko dai shi ya san ba ki lafiya?"

"Aunty gaskiya nake sanar da Ke, kuma ban sanar da kowa ba har shi Yayan saboda na san halin sa yanzu idan ya san bana da lafiya har sai yafi ni jinya wata?il har na ji sau?i shi bai gama ta shi jinyar ba, ni dai kar ki da mu, ni ma yanzu na Wan san wasu abubuwan na doctor zan kula da kaina ba tare da na Waga hankalin kowa ba in sha Allah" ta ?arasa maganar cikin murmushi.

"Au Wan nawa kike cewa haka kina nufin ragon namiji ne kon? to bari na fita na sanar da shi abun da kika faWa ya zo ya yi man maganin ki" ita ma da murmushin ta ?arasa maganar.

"Ni dai rufa man asiri ban ce shi ragon namiji ba ne, amma dai na san a kaina abun da ya fi zama ragon ma zai yi, shi ya sa na faWi hakan, amma na daina" duk dariya suka yi lokaci Waya, Aunty ta ce "To kwanta ki huta Allah ya ba ki lafiya kuma ya yi maki albarka."

*******************
A parlor kuma Sufiyan ne ya haWa kayan abinci sannan ya kalli ?an uwansa ya ce "Don Allah ku ri?a man sau ran kayan nan mu kaiwa ?anwarmu duk yau bata ci komai ba, ko ma nace ku san kwana???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? uku ke nan tana rashin cin abinci."

Suna shiga gurin ta a kwance suka tarar da ita Sufiyan ya ce "?anwata ta shi ki Wan ci wani abun"
"Ka yi ha?uri Yaya amma ba zan iya ba bana jin cin komai yanzu."

"Ko ka Wan ne ki Wan ci sai mu duba ki muga abun da ke da mun ki don Allah kar ki yi gardama kin ji ?anwata?"

Da ?yar ta ta shi zaune Sufiyan ya fara bata tana ci, ba tafi cukali uku ba ta ce "Don Allah ku bar ni haka nan wallahi ya ishe ni, komawa ta yi ta kwanta da sauri kuma ta mi?e tana ?o?arin sauka daga kan gadon, ba shiri Sufiyan ya a jiye kayan abincin ?asa ya ri?eta yana faWin "Ina kuma za ki je haka?"

Jikinta ya ji ya yi zafi sosai kuma sai rawa yake kamar mai jin sanyi, ?o?arin kwace kanta ta fara tana yi ma sa, nu ni da hanyar restroom amma duk sun gaza fahimtar me take nufi, ?o?arin ture shi take amma ta gaza a haka har aman ya zo ma ta, ta wanke su da shi, sai lokacin suka fahimci dalilin rashin buWa bakinta ta yi magana.

Haka ta rin?a yin sa tun tana yi da ?arfinta har ya kai babu ?arfin a jikinta duk ba wanda bai same shi daga cikin su ba Salim ne ya Wauko ruwa yana yayyafa ma ta a kanta jikinta duk ya yi week, haka ta koma baya ta kwanta tana mai da numfashi.

Sai faman faWi take "Don Allah ku taimakeni wallahi ina ga mutuwa zan yi idanuwana sun yi man duhu bana ganin komai."

Duk sun ruWe sosai ga kuma tausayin ta da sauri Samir ya kira Momy's, su ma ganin ta haka ta a ba su tausayi, suka ce kai Sufiyan ka je ka gyara ma ta jikinta, ku ma ku je ku gyara kanku."

Bayan an gyara ko ina Samir ya sanya ma ta ruwa tare da allurar bacci sannan suka Wauki jininta suka fita da shi Sufiyan ka Wai suka bari a gurin ta.

Sun fi awa Waya sannan suka dawo cikin parlor suna ta faman kiran sunan iyayensu, suna zuwa gurin su Kaka suka ri?a hannun su suna ta juyawa suna rawa, Momy Saratu ta ce "Wannan farin cikin fa na mene ne?"

Lokacin Sufiyan ya fito shi ma daga Waki ya zo gurin su yana faWin "Wai don Allah kun manta ?anwarmu bata da lafiya ne halan?"

"In dai irin wannan rashin lafiyar ne muna fatan duk shekara ta yi irin ta" Samir ya faWa cikin farin ciki.

Baki Sufiyan ya saki ya bisu da kallo ya ce "Ban fahimta ba, kuna son ku ce man za ku yi farin ciki idan duk shekara ta shi ga wannan wahalar, to me ta yi maku haka da kuke yi ma ta wannan fatan?"

To yanzu za ka fahimta, kaga mu Win nan mun ku sa zama iyaye, ma'ana ?anwarmu na da juna biyu" mi?a ma sa gwajin suka yi, ya ga ni, duk families suka mi?e tsaye cikin tsantsar farin ciki suna ta yi wa Allah godiya.

Duk Wakin suka shiga gurin ta hakan ya yi daidai da farkawar ta daga bacci cikin tsananin farin ciki Sufiyan ya rungume ta ba abun da yake faWa sai na gode na gode sosai ?anwata, Wago ta ya yi yana kallon ta ya ce "Ba ki san dalilin wannan farin cikin na mu ba ko? to kin ku sa zama uwa ?anwata in sha Allah."

Duk sai suka zuba ma ta ido su ga irin farin cikin da za ta yi amma sai suka ga akasin haka, cewa kawai ta yi "To maa sha Allah" sannan ta koma ta kwanta."

A nan take jikin su ya yi sanyi musamman Sufiyan, kallon ta ya ?ara yi sannan ya ce "?anwata ba ki farin ciki ne halan, naga sam ba alamar mamaki a tare da ke sannan kuma ba wani farin ciki a fuskar ki?"

"Yaya don Allah me ze sanya ni wani mamakin kuma? bayan na san da wannan maganar tun wata Waya da ya wuce, sannan zancen farin cikina na yi shi tun lokacin kuma ina cikin yin sa ako da yaushe, don Allah yanzu dai ku bar ni na yi bacci, har yanzu ban ji baccin ya ishe ni ba."

Da ?arfi cikin tsawa Sufiyan ya ce What, ?anwata kina nufin kin san da wannan albishir Win har tsawon wata Waya amma ba ki sanar da ni ba, me ya sa kika yi man haka, ko ba ni da dalilin sanin na ku sa zama uba ne, shin wai ma tsaya a yaushe kika san da hakan kuma ta ya?"

Shuru ta yi tare da sunkuyar da kanta ?asa ba alamar za ta yi magana, ga kuma tsawar da ya yi, ta razana ta sosai, aikuwa kafin ta gama dawo wa daidai ta ji tsawar Aunty na cewa "Shin ba ki ji tambayar da ake yi maki ba ne?"

Jikinta ya fara kyarma ta ja baya ta haWe da jikin gadon sannan ta ce "Ku yi ha?uri wallahi ban za ci ranku zai Saci ba har haka, dama wata Waya da ya wuce ne na rin?a jin yana yi na duk ya sauya ba yadda na saba ba amma ban wani damu ba saboda naga ba abun da bana yi, hakan ya tabbatar man lafiya ta ?alau, wata rana na je makaranta sai na ji ana yi mana baya nin alamomin da, idan mace na jin su to abu na farko da za'a fara bincikar ta shi ne juna biyu musamman idan matar aure ce."

"Hankalina ya yi matu?ar ta shi saboda ku san kamar duk abun da nake ji ne aka bayyana, shi ya sa na yi saurin zuwa na Wauki abun gwaji dan na tabbatar, sai ga shi hakan ta tabbata."

"Ka yarda da ni Yaya tun a lokacin nake neman hanyar da zan sanar da kai amma na kasa, hakan ya sa na ha?ura tare da ro?on Allah ya kawo man hanyar da za ku sani cikin sau?i."

Da fe kansa Sufiyan ya yi sannan ya Wago kai ya Kalle ta ya ce "Amma kin san cewa rashin sanar da ni zai iya zamewa abun da yake cikin ki hatsari kuwa? a matsayina na mijin ki ya dace kibi ko wace irin hanya don sanar da ni domin zan iya taimaka maki wajen kula da shi."

"Haka ne kuma, to don Allah ka yi ha?uri na tuba" Aunty ta ce "Ai indai bayar da ha?uri ne ta kware nan, kuma baya hana ta sake wani laifin nan ku sa."

Kaka ya ce "Kai ya isa haka nan ke Sufayya abun da kika yi bai dace ba, amma ku kuma ya dace ku rin?a tunawa har yanzu ita Win yarinya ce, sannan duk mai hali irin nata ta kunya zai yi wahala kai tsaye ta iya tun karar ku tace wai tana da juna biyu, don haka komai ya wuce, Allah ya raba lafiya kawai."

Duk wanda ke Wakin ya ce kuma fa haka ne wannan gaskiya ne, Dady Suraj ya ce "To ni ban ma ga abun Waga hankali ba a nan, yanzu dai ba ga shi kun sani ba, to ai shi ke nan."

"Ai duk wula?anci ne wallahi salon su Sata ma ta rai ne kawai shi ya sa, kin ga ?ata kwanta ki hutawar ki" Momy Saratu ta faWa.

Sufiyan ya ce "?anwata ki yi ha?uri na Sata maki rai a ranar da ya dace ace muna cikin farin ciki"
"Ah ah Yaya ni ce mai laifi kuma ina ro?on ka gafarceni sam ban kawo illar hakan a raina ba."

"Shi ke nan ba komai mu yafi juna, yanzu dai sanar da ni me kike son kici ko ki sha tun jiya ban ga kin ci wani abun ba sosai?"

"Me take so kuwa bayan mu je gidan gona mu hau ita ce kamar wasu birai mu tsinko ma ta Wanyen mangwaro" Cikin sigar zolaya Salim ya yi maganar.

Dariya duk suka fara sai lokacin suka fahimci dalilin yawan shan Wanyen mangwaron ta bayan ada sam ba haka take ba.

Cikin murya mai kama da ta mai son yin kuka ta ce "Dady kuna fa jinsa koh?"
"Barmu da shi za mu yi maganin sa kar ki da mu."

*******************
Haka dai rayuwa ta cigaba kowa a families ya tattara kulawar sa a gurin ta, ta na samun kulawa ta ko ina...

Salim Sufiyan Samir ne a cikin parlor suna tattauna wasu abubuwan da suka shafi cigaban rayuwar su, Samir ya yi shuru kamar ma hankalin sa baya kansu, Sufiyan ya gama fahimtar shi ma Salim yana cikin irin wannan yana yin.

Cikin Sacin rai ya daki jikinsu suka dawo cikin tunanin su sannan ya ce "Wai don Allah wannan wace irin rayuwa ce haka, me ya sa, ba za ku sanar da ni damuwar ku ba? bayan kun san idan abu na damun mu tsakaninmu muke neman mafita, amma yanzu na ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login