Showing 114001 words to 117000 words out of 123822 words

Chapter 39 - WATA KADDARA Complete book By (Yar gatan mama).doc

22 Sep 2025

179

shiga motar su ya ce "Mu je ku kai ni airport yanzu don Allah."

Suna son su yi magana amma yana yin sa sam ba mai kyau ba ne hakan ya sa suka yi shuru suka nufi gurin da, ya ba su umurni, har suka ?arasa ya shiga jirgi magana Waya ce ya yi masu ita ce "Don Allah ku kula da kanku sannan ku kula man da ?anwata, yara kuma na san ko ban ce ba, za ku kula da su sosai na yarda da wannan, sai mun yi Waya."

A kan idanunsu jirgin ya ta shi sannan suka nufi gida su ma...

Sufayya na shiga Waki kuka sosai ta fara tambayar kanta take "Wai me na yi ma sa, me ya sa yake yi man haka, wane laifin na yi kuma, har sai yaushe zai yarda ina son sa, waya Sata ma sa rai yake hucewa a kaina?" Tambayoyin da ba amsa su take yi kanta.

Salim da Samir gidan Momy Nafisa suka wuce dama duk iyayen na can gidan, su Momy Saratu kawai ba sa nan, ko su don sun wuce da Sufayya ne gidan su ganin za'a takura ma ta, da masifa.

Samir ya kalli Momy Nafisa ya ce don Allah duk yadda za ki yi Sufayya ta zo gidan nan yanzu ba tare da Momy Saratu ba ki yi yanzu Momy."

Har za ta yi masu tambaya amma ta fasa ta Wauki waya ta kira Momy Saratu bayan sun gaisa ta ce "Allah dai ya sa ?ata ba wani abun take ba yanzu saboda ina son ta Wan zo ta gyara man kan nan nawa?"

Momy ta ce "Ba ta komai yanzu za ta zo in sha Allah" lokacin da ta sanar da Sufayya har zazzaSi ya fara kama ta, duk jin jikinta take ba daidai ba, haka dai ta daure ta fita don ba ta son Momy ta fahimci ba lafiya ba.

Tana shiga gidan ganin duk mutanen a guri Waya har da su Kaka hakan ya bata tabbacin ba lafiya ba, sai dai ita kam a zahirin gaskiya yanzu bata son ace duk wata matsala ta faru tsakanin ta da Yaya har sai duk families sun yi magana, ita yanzu tafi son su rin?a shirya tsakanin su ba tare da sanin kowa, amma sam ya ?i bata wannan damar.

Jiki a sanyaye ta gaida kowa sannan ta zauna ?asa tana jiran ta ji dalilin kiran ta, duk da jikinta har rawa yake a kan sanyin zazzaSi.

Samir ne ya fara magana "Dalilin wannan taron shi ne Kaka kun jima kuna son mu yi aure to yanzu mun shirya tsaf sai dai bamu tsayar da kowa ba, don haka idan kuna ganin akwai waWan da suka dace da mu, za ku iya aura mana su, kuma mun yi maku al?awarin ba za mu, ba ku kunya ba za mu nuna masu soyayya iya iyawar mu in sha Allah."

Ganin yana yin da, ta shiga shi ya basu tabbacin shirin su zai yi aiki saboda jikinta har kyarma yake, a tunanin su maganar su ce sanadin shigar ta wannan halin.

Ita kuma tunanin ta "To a kan wannan maganar za'a ta so ni nazo har nan? ga shi ni ina cikin damuwar rashin mijina kuma ko lafiya bana da, to ni ina ruwana da wannan maganar saboda Allah dai" tana cikin tunanin ta jiyo muryar Momy Aisha tana cewa.

"Wace irin magana ce wannan kuma? to ku sani ba za mu taSa barin ku yi aure a haka ba, don mun san duk wace za ku aura ba don kuna son ta ba, sanadin hakan kuma zai iya sanya ku wuta dalilin hak?in iyali."

Mu kuma sam mun fi farin ciki mu ganku a haka da ace ranar ?iyama kun fuskanci hukuncin Allah saboda cutar da iyali, sannan duk'kanmu nan mun san al?awarin da, ku ka Waukarwa kanku, don haka kuma sauya wannan tunanin."

Salim ya ce "Momy ai mun karya wannan al?awarin kuma kin san ba haramun ba ne don mun karya al?awari irin wannan, to shin me ye amfanin ri?e al?awarin, mu muna ta ?o?arin cikawa amma wace muke saboda ita ta gaza yi mana alfarma Waya tak a rayuwa, shin wai kun san cewa Wan uwanmu baya ?asanar yanzu haka, kuma ita ce sanadi?"

Da sauri ta Wago kai murya na rawa irin ta marar lafiya ta ce "Yaya ni kuma me na yi, ma sa don Allah?"
Kan ta ?arasa ta ji saukar mari a kan fuskarta tana Wago kai ta ga mahaifinta ne Dady Munir, abun da bai taSa yi ba ko a sauran yaran da suka girma a gaban sa, saboda shi ya ce bai yarda duka na hukunci ba, sai dai kuma yau ransa a matu?ar Sace yake.

Cikin Sacin rai ya ce "Su Win sa'annin ki ne, da suke magana ke ma kina ?o?arin yin maganar, ?arya za su yi maki ne, duk families nan sanar da ni mutum Waya da zai Sata ran Sufiyan har ya bar ?asar nan, ba tare da ya yi wa, mu iyayen sa sallama ba idan bake ba?"

Ganin yadda ran kowa ke Sace shi ya sa ta sha jinin jikinta guri Waya kuma ta Wauki al?awarin komai za su ce, ba za ta sake magana ba saboda ta fahimci ba za su taSa saurarar ta ba.

Dady Ahmad ya ce "Ku yi mana baya nin abun da kuka sani ga mai da tafiyar ta shi."
Dady bamu san cikakken abun da ya faru ba, amma jiya mun je kiran su lokacin da ku ka ce, mu kira su za mu je gida, a cikin asibiti muka tarar da su, yana yin ba mai kyau ba ne kamar akwai abun da ya sanya ta, ita kuma ta?i yi, shi ya sa ransa ya Saci har ya bar ?asar nan, amma a zaharin gaskiya mun san ba ?aramin abu ba ne, ta yi ma sa wanda har zai sa ya Wauki wannan matakin."

Hakan ya nuna man ?arara ba mu san abun da take yi ma sa ba, a bayan idonmu, Allah ne ka Wai ya san kalar cutuwar da take yi ma sa."

Momy Nafisa ta ce "Wai kina nufin duk abun da suka faWa gaskiya ne, wai ke wace irin zuciya ce dake, wace kalar soyayya kike ne ma a duniya wace Sufiyan baya nuna maki? ki yi magana ina jikin ki" cikin tsawa ta yi maganar sai da ta?ara razana.

"Momy wallahi ba laifina ba ne" da ?arfi Salim ya daka ma ta tsawa sai da cikin ta ya murWa "Sanar da mu laifin waye, kar ki yarda ki ce mana sharrin sheWan ne, ko ?addara don laifin ki ne, ke kika gaza koyawa zuciyarki son Wan uwanmu."

"To bari ki ji na faWa maki wani abu Waya, idan har kika yarda wani munan nan abu ya samu shi, ki sani ba za mu taSa yafe ma ki ba, wallahi kin ji na rantse."

Ita dai sauraren kowa take, ita yanzu idan so samu ne subar ta, ta je ta kwanta saboda kanta da ke ta juya ma ta, cikin tsananin ciwo.

Haka duk aka watse Waya bayan ita ka Wai aka bari a gurin, Waki ta shiga ita ma ta samu magani ta sha sannan ta Wan jingina da jikin gadon tana tunanin yanzu ko ta kira Yaya ba lalle ya Waga ba, a haka dai har ta samu bacci saboda maganin da ta sha.

Sai yamma ta farka ko shi hayaniyar mutanen gidan ta ji sun dawo parlour har da Yayunta ai kuwa da sauri ta fito ta zo gurin su, da ?yar suka amsa gaisuwar da ta yi masu.

Kallon Yayunta ta yi, ta ce "Yaya don Allah ina ne man alfarma a gurin ku" duk'kan su ba wanda ya kalli gurin da take, ban za suka yi da ita kamar ba su ji, abun da take faWa ba.

Kaka ya ce "Wace alfarma kike nema a gurin su, wai kina son ki ce kar su yi aure ne ko kuwa"

Girgiza kai ta yi ta ce "Kaka sanin kanku ne aure lokaci ne idan Allah ya nufa ba wanda ya isa ya hana faruwar hakan, to ni wacece da zan hana ikon Allah faruwa? kawai dai ina neman taimakon su ne gurin gyara kuskurena."

Kallon ta suka yi lokaci Waya ganin yadda fuskarta ta kunbura sosai ya basu tausayi, da yake duk da ita Win ba fara ba ce sosai, amma duk ta yi kuka sai ya nuna ta.

Cikin tausayawa da taushin murya suka ce "Wane kalar taimako kike ne ma a gurinmu?"

Murya na rawa idanu cike da kwallah ta ce "So nake don Allah ku kai ni gurin da Yaya ko ku sanar da ni, ni na je ina son magana da shi a zahiri ba wai ta waya ba, na tabbatar kun san ina ya je."

Samir ya ce "Ohh so kike mu sanar dake gurin da yake ki je, ki ?ara tura ma sa wata damuwar Koh?"

Girgiza kai kawai take alamar ba haka ba ne, ta ce "Me ya sa zaka faWi hakan Yaya, wallahi na yi maku al?awarin zan gano gurin da matsalar take kuma na gyara, ba za ku sake samun damar yin ?orafi kaina ba, zan tabbatar na bawa Yaya farin cikin daya kamata ya samu daga gurina, ba zan taSa barin ya shiga damuwa ba ta dalilina in sha Allah."

Salim ya ce "To idan ko haka ne mu kuma za mu ba ki duk ko wace kalar gudun mawa, don ganin kin samu damar cika mana wannan al?awarin da kika Wauka in sha Allah."

Samir ya ce "Amma ba za mu kai ki gurin sa ba, sai dai mu sanya shi dawowa, amma mun san ba abu ba ne mai sau?i saboda ransa a matu?ar Sace yake, don haka sai da taimakon ki hakan za ta faru, shin ni kam ba saura wata Waya anniversary Win ku, na cika shekara takwas ya za gayo ba?"

Shuru ta yi, ya ce "Da ke nake fa" sannan ta ce "A haka ne idan muna da rabon ga ni in sha Allah."
"To shi ke nan faWuwa ta yi daidai da zama, kinga yanzu abun da za ayi ki Wauki waya ki kira shi."

Shuru ta yi tana tunanin to me za ta sanar da shi a gaban mutane, wayar ma ba za'a ba mutum damar shiga Waki ya yi ba cikin sirri" turo baki ta yi ta ce "To Yaya me zance ma sa idan na kira?"

A kausashe Samir ya ce "Wai ke wace iri ce don Allah, yanzu har da abun da za ki sanar da shi sai mun faWa maki?"

Salim ya ce "Bi ta a hankali, shi ke nan bari mu sanar dake" nan dai suka fada ma ta duk abun da suke son ta sanar da shi, wanda suka san zai Wan ji sanyi a ransa.
*************************
Kwance yake a parlor tun da ya shigo yake kwance a kan kujera ya gaza ta shi daga gurin yafi awa uku tunanin ta kawai yake, kamar daga sama ya jiyo ?arar wayar sa, ya san ita ce saboda nata ringtone na daban ne a wayarsa, kamar kar ya Waga sai kuma ya tuna yanzu fa kira ya kai 20 ke nan tun da, ya ta so take kira bai Waga ba, hakan ya sa yanzu ya daure ya Waga.

Da sallama ya Waga bayan sun gaisa sai kuma duk suka yi shuru, can bayan wani Wan lokaci ta ce "Yaya ka kai lafiya?"
A ta?aice ya ce "Lafiya ?alau."

"Yayana don Allah yaushe za ka dawo? idan kuma kana ganin za ka Wauki lokaci a can to ka yi man izini na zo gurin ka, tun da ka tafi nake jina ba daidai ba har yanzu na gaza shan ko da ruwan tea ne, Yaya a gaskiya ba zan juri rashin ka aku sa da ni ba, don Allah ka dawo ko ka bar ni, na zo da kaina."

Murmushi ya yi mai ciwo sannan ya mi?e zaune ya ce "Sanar da ni ke da waye a gurin da kike yanzu?" shuru ta yi.

"Humm ba za ki iya sanar da ni gaskiya ba saboda ki san cewa bake ka Wai ba ce, duk wannan dogon baya nin, na san sanya ki aka yi, don haka don Allah idan ba ki da wani abu mai mahimmanci ki bar ni ina Wan aiki yanzu."

"Yaya ka yarda da ni, tabbas na san a halin yanzu ba ni, ka Wai bace amma ka sani abun da nake faWa babu ?arya a ciki please ka yarda da ni" kafin ta ?arasa ta ji ya kashe wayar, kallon wayar ta yi wasu hawaye suka zubo ma ta.

Salim ya ce "Duk abun kika yi ma sa, ba ?arami ba ne, kuma yanzu bama bu?atar sanin ko meye shi saboda tsakanin ku ne, ya rage naki ki gyara, sannan ki shirya gobe da safe misalin ?arfe 7:am za mu bar ?asar nan, mu kai ki gurin da yake daga nan dubara ta rage naki, mu dai munyi iya namu."

Cikin sanyin murya ta ce "To Yaya amma kuma yaran fa, ya zan yi da su?"
Momy Nafisa ta ce "Yaye su za'a yi kuma nan za ki bar su daga manyan har ?ananun."

Kamar ta yi kuka tana son yin musu amma bata ga fuska ba, tun da yaran ta suka zo duniya bata taSa ko wuni Waya ba tare da su ba, yanzu kuma ace za ta yi tafiya har wata ?asar tabar su, sai dai haka za ta daure dole don ta samu damar gyara komai.

Tun asuba suka gama shiryawa rungumar duka yaran nata ta yi tare da yi masu addu'a, sannan ta ce "Jawad ka kula da ?annenka sosai karka bari su takura wa kowa, ku zama masu kir ki kun ji koh?"


Haka suka bar ?asar sai Saudia kai tsaye gidan da yake suka sauka dama sun tabbatar nan zasu same shi, kallon ta suka yi sannan Salim ya ce "Ki shiga yana ciki in sha Allah, mu za mu wuce Waya gidanmu kuma gobe za mu bar ?asar nan, idan kin gama daidai ta komai sai ku dawo mu dai za mu koma gurin yaran mu, kar ki damu kuma in sha za mu kula da su."

Rungume Salim ta yi tana kuka sosai ta ce "Don Allah ku yi ha?uri na Wauki duk laifina kuma zan tabbatar komai ya gyaru in sha na gode da ?o?arin ku a gurina."

"Kar ki da mu komai ya wuce duk wani bawa da kika ga ni a duniyar nan da kalar jarabawar sa, Allah ya ba ki ikon cinyewa" shi ma Samir haka ta rungume shi ta ce "Ameen ya Allah Yaya ku ma ubangiji ya baku ikon cinye taku jarabawar" duk suka amsa da Ameen.

Cikin tausayawa suka bar ta nan tsaye tare da fatan Allah ya daidai komai tsakanin su...

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
*PAGE* 60

Sufiyan gama karatun sa ke nan na Qur'anic saboda yanzu shi ka Wai yake rage ma sa damuwar sa, ?araurawar gidan ya ji tana ?ara, cikin mamaki yake tunanin waye kuma, waye ya san yana nan? da wannan tunanin ya je yana le?awa da sauri ya buWe ?ofar yana ?are ma ta kallo.

Cikin mamaki yake kallon ta tare da tambayar ke ce a nan, ta ya kika san ina nan, wa ya kawo ki?"

Shuru ya yi can kuma ya ce "Ohh Yayunki ne ko? yanzu na fahimta dama na san su ka Wai suka san gidan da zan sauka kai tsaye, me ya sa ban yi tunanin hakan ba na sauya gida ba, yanzu ina suke su Yayun na ki?"

Kallon sa take cikin tsananin mamaki murya a karye ta ce "Yaya ba ka yi farin cikin ganina ba, ke nan guduna kake Yaya da har kake fatan sauya gida saboda ni, shigowa gidan ma ba za ka bar ni, na yi ba?"

Hanya ya bata ta shigo, zama ta yi a kan kujera shi ma zaman ya yi yana kallon ta, ta gaji da shurun ta ce "Yaya fatan na same ka lafiya?" a ta?aice ya ce "Lafiya."

Nan ma wani shurun ne ya biyo baya na Wan lokaci, komai ya tuna da sauri dai ya mi?e tsaye ya shiga kitchen ruwa ya kawo ma ta, sannan ya koma kitchen Win be jima da shiga ba wayar sa ta yi ?ara alamar kira na shigowa daga can ya ce "Kina fa ji ana kira, ki Waga kafin nazo."
Har za ta kai ma sa amma jin ya ce ta Waga hakan ya sanya ta Wagawa, muryar wata ta ji tana faWin "Baby kana jina, dear ka yi magana mana wai har wane lokacin za ka sanya ni zaman jiran ka, please come soon."

Duk sanyin gurin gume ne ya fara zubar ma ta a jiki, shi kuma ?arasowar sa gurin ke nan ya ce "Ya za ki Waga waya kuma ki yi shuru? ba ni nan."
Wayar ya karSa ita bata ma san lokacin da ya cire wayar daga kunnenta ba, sai jin muryarsa ta yi yana faWin "Ok don't worry am coming now, sarkin rigima ke nan" cikin murmushi ya ?arasa maganar."

Kallon Sufayya ya yi "Ga abinci nan da tea ki samu ki ci zan Wan fita yanzu sai na dawo" da sauri ya shiga Waki ba jimawa ya fito cikin shigar manyan kaya ya yi kyau sosai, haka ya fita yana ta faman sauri, tare da yi ma ta sallama, yana fita a nan gurin ta zube ?asa zaune ta yi zaman ?an bori kukan da take ri?ewa nan take ya fara zuwan ma ta kuka take sosai, kuma ba mai lallashi.

Shi kuma yana fita kai tsaye gidan da ya san zai samu ?an uwansa ya fara tsayawa, suna ganin sa da sauri suka rungume shi cikin farin amma shi Sangaren sa sun ga saSanin haka, kallon sa suka yi tare da tambayar "Lafiya kuwa Wan uwa?"

Murmushi ya yi mai ciwo ya ce "Hmm ai ku zan yi wa wannan tambayar, lafiya ?alau kuwa, har tsawon wane lokacin hakan zai cigaba da faruwa, yanzu ma na yi nisa da ita kun sake bata wani umurnin na zuwa gurina, ko ba haka ba ne, ko kuna son cewa ba shirin ku ba ne zuwan ta ?asar nan?"

Salim ya dafa shi ya ce "?an uwa duk ka sauya don Allah ka sanar damu damuwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login