Showing 75001 words to 78000 words out of 123822 words

Chapter 26 - WATA KADDARA Complete book By (Yar gatan mama).doc

22 Sep 2025

2596

jiyo ana bugun ?ofar parlorn.

Kallon ta ya yi, ya ce "Bari na duba na ga waye" da sauri cikin zumuWi ta ce "Ah ah Yaya ni ce zan duba saboda na san wata?il su momyna ne" da gudu ta wuce cikin farin ciki, ta na buWewa ta ce "Oyo yo my Momys" sai kawai ta yi turus ta tsaya.

Daga can ya ce "Ya dai na ga kin tsaya ko ba su Momyn ba ne?"

Juyawa ta yi cikin parlorn ta ce "A ba su, ba ne gurin ka aka zo" nan ta bar shi tsaye ta shige kitchen.

Cikin mamakin sauyawar ta lokaci Waya, ya je gurin ?ofar sai kawai ya ga ashe ?an uwan sa ne tsaye.

Cikin farin ciki ya rungume su sai can kuma ya sake su ya ce "Wane kalar renin hankali ne kuma wannan ku zo amma ku?i shigowa? dalla ku shigo malumai."

Samir ya ce "Ta ya za mu shiga gidan ango da amarya kai tsaye? ai kai ma ka san dole sai da izini."

Salim ya ce "Kai ma dai ka ce haka, wa ya sani ma ko bai so zuwanmu ba yanzu."

"Ka ji wani sabon wula?anci, Allah na yi matu?ar kewar ku sannan na yi farin ciki ganin ku yanzu."

"To mu dai ba wani dogon surutu muka zo ba, dama su Momy ne, na ce a kawo maku breakfast."

"Allah sarki kamar kun san yanzu muke shirin haWawa, bari na je in dakatar da ita."

Da sauri ya shiga gurin ta ya ce "Kar ki Wora komai su Momy sun aiko mana da abinci" sannan ya kalle ta da kyau ya ce "?anwata wace irin tarba ce wannan ki ka, yi wa ?an uwan ki kamar ba ki san su ba? ko fa gaida su, ba ki yi ba."

"Ka yi ha?uri Yaya, dama bari na yi su shigo tukunna mu gaisa, kuma na ga kana nan shi ya sa, na bari ka tarbe su tun da kai ne, na miji Wan uwan su."

"Shi ke nan koma dai mene ne yanzu mu je, ku gaisa sannan mu yi breakfast"

Haka suka fito a tare suna isa gurin su ta ce "Ina kwana nan ku, kun zo lafiya?"

Cikin sakin fuska suka amsa da lafiya ?alau ?anwarmu, mun same ku lafiya koh?" Ta ce "Ummm" daga haka bata sake magana.

Zuwa ta yi ta zubawa ko wannen su abinci, ita kuma ta koma kan kujera tare da Waukar fruit ta zauna tana shirin yankan apple, da sauri Sufiyan ya ce "Me hakan ke nufi ?anwata, abincin kuma fa?"

"Ba yanzu zanci ba sai anjima saboda bana jin yunwa yanzu fruits kawai nake son na sha."

"Hakan ba zai yuyuba ko fa jiya haka ki ka kwana ba kici komai ba sai ruwan lemu, yanzu kuma ki ce, ba kijin yunwa? kinga malama ta shi mu je kici abinci kin ji koh."

Cikin yana yin ta kamar na mai shirin kuka ta ce "Na ro?eka ka bari har ajima, dama kuma yanzu ba lokacin cin abincina ba ne kai ma ka san da haka, na yima al?awarin zan ci anjima."

Haka ba dan ya so ba, ya dawo kusa da ?an uwansa suka fara cin abinci, can sai Salim ya ce "?an uwa sati mai zuwa muke tunanin zuwa Dubai in sha Allah, kuma za mu Wan Wauki lokaci a can."

Da sauri ya kalle su ya ce "Me zai kai ku Dubai har kuna tunanin jima wa a can? dukanmu dai doctors ne masu zaman kan su balle na ce ko kun samu sauyin gurin aiki ne."

"Sannan duk kasuwancinmu bamu ke kulawa da shi ba akwai wakilai, to mai zai sa kuce za ku yi tafiya haka, kuma har kuna tunanin tafiya ba tare da ni ba? sannan ina ce nan da sati uku za mu je raka ?anwarmu makaranta koh?"

Samir ya ce "Wannan tashin hankalin na mene ne kuma haka Wan uwa? tafiya ce kawai fa muka ce, za mu yi ba mutuwa ba, zancen za mu tafi ba tare da kai ba karka manta yanzu fa kai mai aure ne wasu tafiye tafiye dole ka rage su, in kuma har za ka yi tafiya to ba tare damu ba sai dai da matar ka."

"Sannan zancen raka ?anwarmu makaranta Momys sun gama yanke shawarar ku biyu kawai za ku fara tafiya, daga bi sani muda su sai muzo."

Sufiyan zai sake yin magana ke nan suka jiyo ?arar Sufayya daga cikin parlorn hakan ya sa, ya fasa maganar ya yi gurin ta da sauri...

WATA ?ADDARA
ANOTHER DESTINY
BY
SUWAIBA M AMIRU
(?ar gatan mama)
' PAGE 4?? 6??

~?OYON SIRRIN ZUCIYA SABODA BIYAYYAR AURE~

Cikin hanzari su ma Yayunta duk suka ?araso gurin ta, suna isa suka tarar hannunta yana ta zubar da jini, ga duk'kan alama ta yanke ne gurin yankan apple, cikin ruWewa kamar an ce masu za ta mutu yanzu yanzu suke jefa mata tambayoyi kala kala.

Me ya faru, ya aka yi kika yanke, garin ya hakan ya faru?" amma kuma ba amsa sai faman yarfi take da hannun.

Da sauri Sufiyan ya Wauko first aid box suka fara gyara mata gurin, bayan sun gama Sufiyan ya dube ta arauna ne ya ce "Don Allah ki daure kici wani abu kinga sai ki sha magani."

"Wai Yaya na ga duk ka yi wani damuwa, bafa wani babban rauni ba ne kuma ka ga hakan da idonka don haka karka da mu don Allah."

Har ta yun?ura za ta, ta shi sai kuma ta koma ta zauna ta kalli Sufiyan ta ce "Sannan kuma Yaya ina son in sanar da kai wani abu Waya, a duk lokacin da wani ya ce zai fita daga rayuwarka ko kuma zai yi ni sa da kai, to kabar shi ya tafi karka yi ?o?arin tsayar da shi, idan da hali ma ka buWe ma shi ?ofa da kanka ka raka shi, koma waye shi kuwa."

Tana gama faWar hakan ta shige Waki da sauri saboda ta ji alamun idanunta za su zubar da hawaye.

Da kallo duk suka bita sai yanzu suka fahimci dalilin yan ke warta, ke nan jin labarin tafiyar su ne, ya Waga mata hankali.

Idanun Sufiyan suka yi wani irin ja sosai hakan ya sa, ya yi saurin rufe idon saboda kar ?an uwansa su fahimci halinda yake ciki na damuwa, ya jima a haka sannan ya jiyo ya kalle su ya ce "Mu je mu ?arasa cin abincin koh."

Duk'kan su jikin su ya yi sanyi sosai don sun fahimci komai take nufi, ko wannen su zargin kan sa yake, yana ganin kamar shi ne sanadin faruwar hakan, don me za su yi wannan maganar tana ku sa.

Haka dai suka bar gidan kowa da irin tunanin sa a zuciyar sa.

***********************
Haka rayuwar su, ta cigaba da tafiya ba laifi duk'kan su suna kulawa da juna, Sufayya na ?o?ari wajen ganin ta danne duk wata dumuwar ta, sai dai Sufiyan kar yake kallon ta.

Amma yana jin daWin zama da ita sosai saboda tana iya yin ta wajen faranta ma sa rai, shi ma kuma haka, bai taSa tunanin za ta kwantar da hankalinta haka ba, ganin yadda aka yi auren.

Amma dai har yanzu kowannen su Wakinsa da ban, tun tana fargabar zai sauya ra'ayi har ta daina ta ?ara sakin jikinta da shi.

Yau ta kama saura kwana biyu su wuce Germany hakan ya sa, suka shirya tafiya gidajen iyayen na su sallama, sun zagaya ko wane gida kuma duk in da suka je sai an yi masu nasiha da jan kunne sosai.

Sun je gida uku gidan su Sufiyan ne ?arshe ko da suka je suka tarar da Salim da Samir a gidan, Sufiyan ya ce dama na ce tun da bamu ganku ko ina ba kuna gidan nan, nan dai suka ?arasa wunin sai dare suka tafi.

******************
Yau kam duka families sun zo raka su airport Sufayya ta yi kuka sosai kamar wace za'aje siyarwa, ta ro?esu karsu jima basu zo ba don Allah, sun bata tabbacin zuwa a kan lokaci in sha Allah.

Su kuma iyayen sun yi hakan ne don su basu damar samun lokaci da juna sosai, sun gama yarda cewa idan suna su biyu ba sa ganin kowa ku sa dasu za su fi samun lokacin juna, a Sangare Waya kuma ba su san wane kalar zama suke ba.

Haka dai suka tafi yau ga Rahma a Germany tun da ta tuna abun da ya kai ta ?asar, sai kuma ta nemi duk wata damuwar ta ta rasa, shi ma ya ji daWin ganin ta walwale hakan ya sa, ya samu natsuwa sosai.

Kwana biyu da zuwan su ya je rakata makaranta sai da ya tabbatar ya gama mata komai, amma yau ya sha faman lallashi har sai da yakai ga kiran gida su Momy suka ta ya shi bata ha?uri, a kan ta yi ha?uri ta cigaba da amsa sunan Sufayya ita kuma ta ce wallahi RAHMA MALAN MUSA ta sani, shi ne sunan ta.

Shi kuma ko da suka je duk ya sauya mata komai da asalin sunan ta wato SUFAYYA ALHAJI MUNIR, har suka dawo gida tana mita shi dai ko ?ala baice ba tun ya samu ta daina kukan ma hakan ya yi mai daWi.

Haka dai ya zama direban ta sam bai yarda wani ya kai ta ba, kuma ita ba ta gama iya motar ba tukunna, shi ke kai ta ya dawo da ita, ba ya da wani lokacin kansa sai na ta, duk asibitocin su ya rage zuwa in ba wani babban daliliba, wani lokaci har tausayi yake bata, a kan yadda yake fama da ita a kan komai.

Yau watan su Waya da zuwa ba zato ba tsammani sai jin saukar families su suka yi ?asar, bayan ya je Wauko ta daga makaranta suna shigowa da motar su gidan suka ga motocin iyayensu, aikuwa da sauri suka shiga gidan cikin farin ciki.

Sufayya ta rungume iyayenta Waya bayan Waya sannan ta gyada su, Sufiyan shuru ya yi yana ta dube dube can dai ya gaza ha?uri ya ce "Wai ni kam ina ku ka baro man ?an uwana?"

Dady Munir ya ce "Ba su sanar da kai za su tafi dubai ba? ai suna can tun sati uku da suka wuce."

Cikin damuwa da Sacin rai ya ce "Wai yanzu me ya sa suke yi man haka? nafa sanar da su bana son tafiyar nan, tun da ban ji wani babban dalili ba amma shi ne suka tafi ba tare da sanina ba, duk tsawon lokacin nan na yi tunanin suna tare da ku, a she shi ya sa suka fi son mu yi chat da mu yi waya saboda sun san zan iya fahimtar duk in da suke" ransa a Sace yake magana.

Dady Suraj ya ce "Kai dai ka sani, mu dai ka san bama shiga maganar ku don yanzu sai ku bamu kunya, dan haka kun fi ku sa sai ka kira su can ka yi ma su faWan."

Sai dare sannan kowanne su, ya fara shirin tafiya gidansa, da yake gidajen ba su da, ni sa da juna layin ma one family ake kiran sa, saboda zaman su yafi ?arfi a nan shi ya sa suka yi hakan.

Su kuma Salim Samir Sufiyan, gidan su a haWe yake guri Waya sai dai ko wanne da part Win sa, sun gama shirin da sun yi aure guri Waya za su haWa matan su don su ma, su zama ?an uwan juna, sai kuma wannan ?addarar ta gifta ta son mace Waya.

Wannan dalilin ne ya ?ara sanya suka ji ba sa son zuwa ?asar saboda sun san halin Sufiyan ba zai bari su sauka wani gurin, da ban ba.

Dole a gidan za su sauka, su kuma ba za su juri ganin ?anwarsu a matsayin matar aure ba, kuma wai har tana fushi da su.

Sufiyan ya kira ya yi faWan shi har ya ga ji dole ya ha?ura, kuma shi dai yanzu ba zai iya zuwa gurin da suke ba saboda kai Sufayya makaranta ban da haka da tabbas sai ya je gurin su.

Yanzu kam Sufayya ta zama marar zama guri Waya, da ta dawo za ta fara zirga ni ya bata wannan gidan bata wancen gidan, gurin aunty ce kawai ba ta fiye shiga ba saboda yawan yi mata faWan da take na cewa ta zauna gidan auren ta, shi ma Sufiyan hakan yake biye mata su yi ta yawon, shi har farin ciki yake ganin yadda ta saki jikin ta take walwala.

Wata huWu ke nan da zuwan su ?asar su Salim suka sauka ?asar cikin farin ciki Sufiyan ya tarbe su, har su Dady na tsokanar su, "Wai Sufiyan ba kai ba ne wanda kake fushi da su ba? ai mun yi tunanin idan ku ka haWu ko kallo ba su ishe ka ba, sai kuma muka ga saSanin haka."

"Dady faWan yana nan amma ba yanzu ba sai mun gama gaisawa tukunna" Samir ya ce "Ah ah Wan uwa ka daure ka yafe mana, ka san fa abu kaWan suke jira ya faru tsakaninmu su yi mana dariya."

"Shi ke nan na yafe maku amma don Allah karku sake yi man haka na yin ni sa, da ni sam bana so gaskiya" sun yi mai al?awarin in sha Allah ba za su sake ba.

Duk wannan diramar Rahma na gurin amma tun da ta gaida su, ba ta sake bin ta kansu ba, har tsawon wannan lokacin ba wanda ya san kalar zaman da suke, sai su ?an uwan na su don har magana sun taSa yi ma sa, a kan ya yi ?o?ari ya gyara zaman da suke, shi dai ya dai ce masu, to kawai.

***********************
Wata biyar ke nan da auren su amma ko alama ba ta da niyar sauyawa zuwa yadda Sufiyan yake so ma'ana ta nuna ta yarda da shi a matsayin miji, shi kuma ya yi al?awarin ba zai taSa yi mata magana ba, sai dai kulawar da take ba shi har mamaki yake, yanzu har ya fara zargin.

"An ya ban yi mata kuskuren fahimta ba kuwa, ko dai gaskiya take faWa tun da jimawa cewa tana so na? amma ko idan haka ne zuciyata ta yi man ?arya ke nan a kan ?anwata? kai gaskiya ba zai yuyuba sam bana tunanin cewa zuciyata za ta ?i sanar da ni gaskiya" shi kaWai yake ta tunanin sa, da maganar zuci.


Da yamma suna gidan Momy Nafisa ya kalle ta ya ce "?anwata mu tafi gida yanzu kin shirya ko, saboda yau na gan ki duk sai a hankali kamar marar lafiya?"

"Yaya lafiya ta ?alau magana dai nake son mu yi don haka ta shi mu je gida kamar hakan zai fi man sau?i."

Ya yi matu?ar mamaki ganin nan a take ta yarda su tafi gida, ita da idan ta zo gidajen iyayen na su bata son bari har sai an yi mata magana.

Ganin hakan ya sa ba shiri ya mi?e tsaye ya ce "Ta shi mu tafi to" saboda shi dai duk tunanin sa bata da lafiya ne, duk wannan maganar da suke ba wanda ya ji me suke faWa saboda sun yi ?asa muryar su, haka dai suka dawo gidan su.

Kallon ta ya yi, ya ce "Ina jinki sanar da ni, me ke da mun ki ?anwata?"

Gyara zaman ta, ta yi a kan kujera ta du?ar da kanta sannan ta fara rawar murya tana faWin "Yaya dama umm amm sai kuma ta yi shuru jin wayarsa na ?ara alamar kira ya shigo, yana Wagawa aka ce don Allah ya zo da sauri ana bu?atar shi asibiti akwai babbar matsala, ba shiri ya mi?e tsaye ya ce.

"?anwata ki gafarce ni don Allah idan na dawo za mu yi magana saboda yanzu marar lafiya yana bu?atar taimakona, ki kulaman da kanki don Allah sai na dawo, kuma ki yi man addu'a."

Haka ya fice da sauri, ta ce "To Yaya Allah ya taimaka ya bada sa'a" jiki a sanyaye ta kwanta a kan kujerar ta fara tunanin yau fa ku san kwana huWu ke nan tana son magana da shi mai mahimmanci amma ta gaza samun wannan damar.

Ga kuma yawan faWuwar gaba da take ji kwanan nan, a bayyane ta ce "Allah dai ya sa, ba rashin faWar abun da ke raina ba ne, ke shirin haifar da wata matsalar idan ko haka ne ya zama dole na yi hanzari magana da Yaya."

Sai dare sosai ya dawo ku san ?arfe 10:pm lokacin har ta yi shirin bacci amma ta gaza sai kuma ta tsaya jiran dawowar shi, yana shigowa ya ganta zaune da sauri ya ce "?anwata me kike yi har yanzu ba ki kwanta ba?"

"Yaya dama na ji ka shuru kuma na kira wayar ka bata shiga shi ya sa na zauna jiran dawowar ka."

Kallon ta ya yi sosai a ransa ya ce "Ina ma da gaske kina so na, shi ya sa kike nunaman wannan kulawar" a zahiri kuma ya ce "Mu je muci abinci na Wan yi wanka."

Bayan ya gama komai ta ce "Yaya to yanzu kana da lokaci mu yi magana?"

"A. ina da lokaci amma da safe saboda yanzu nafi son ki je, ki samu bacci sosai don ina son gobe ki ta shi a kan lokaci akwai abun da za mu yi duka wannan families, kuma umurni suka ba ni a kan na sanya ki bacci da wuri don haka zo, ki kwanta."

Ta ce "Amma Yaya maganar fa ita ma tana da mahimmanci sosai."

"Na san tana da mahimmanci tun da har kika dage haka, amma kin san shi ma bin umurnin iyayenmu abu ne mai matu?ar mahimanci, don haka mu bari har safe, kar ki manta yau da gobe duk Waya ne, in sha Allah gobe za mu yi magana."

Ba dan ranta ya so ba, ta ce "To Allah ya kaimu Yaya" haka ta shige ta kwanta, shi ma ya wuce na shi Wakin, yana mamakin shin wai wace magana ce take son sanar da shi haka duk tabi ta da mu sosai? tabbas ba dan umurnin iyayen su ba, da yanzu nan sai ya ji koma meye, A haka har bacci ya zo ma shi.

Tana ta shi daga bacci bayan gama addu'ar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login