Showing 33001 words to 36000 words out of 78516 words

Chapter 12 - FEERYAL Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.doc

tab'a fahimta ba.
ta zame jiki tayi d'aki.


Tana shiga bathroom ta isketa tana ta wasa da tsalle cikin ruwa tana fad'in
"Ku zubo mana ruwan gidan ku muyi wankan yafi dad'i."
"Anya Feeryal bata sami matsalar kwakwalwa ba kuwa?."
tayi maganar a kasan ranta.
"Idan har ba matsala ta samu a kwakwalwa ba to kuwa akwai wani abin akasa."

Haka ta daure tayi mata wanka, tana mata tana fad'in
"Ammie kiyi wa kawaye na suma."

Bayan ta gama mata wankan tafice da gudu, tana fad'in
"Ayi rige-rige."
Aunty ta tsaya ta gyara in da suka b'ata, koda ta fito d'akin.
can saman wardrobe ta hango ta d'ororo a tsaye da kafafunta, tana ta kyakyata dariya.
tsoro ne ya ziyarci Aunty, ko ita tsawonta baya kai saman wardrobe d'in nan.
ko abu zata d'auko a saman sa sai ta samo abin hawa takara tsawo kafin hannunta ya iya kai wa saman sa,
sai ga Feeryal d'ororo a saman wardrobe.

Hannu ta mika tana fad'in
"Ammie ki saukar da ni sun gudu sun barni."
da sauri Aunty ta yi waje, jikinta na b'ari.
ganin yadda ta fito yasa Daddy fad'in
"Lafiya Fad'imatu?."

Kofa tashiga nunawa tana fad'in
"Feeryal a saman wardrobe."
Daddy ya mike yana cewa
"Me kuma ya kaita saman sa, kin d'aura ta ne kika kasa sauke ta?."
kai ta girgiza da sauri ta ce
"Bani na d'aurata ba a kai na ganta."
da d'an sauri Daddy ya nufi bedroom yana fa d'in
"Shine zaki fito ki barta idan kuma ta fad'o taji ciwo fa?."

Yana shiga ya ganta tsaye a cikin d'aki.
Aunty da ke biye da shi ta
tsaya cike da mashahuriyar mamakin ganin ta a tsaye cikin d'akin.
Daddy ya dubi Aunty yana cewa
"Bansan me yasa kike kin amfani da magani da hayakin can ba,
bari nayi waya a karb'o miki wani."
"Daddy ka maida ni mai tab'in hankali ce ko?."
tun kafin yakuma cewa wani abu, ta b'ata fuska ta koma parlour tayi zamanta.

Yakama hannun Feeryal da kansa ya saka mata kaya ya shiryata tsaf yaruko hannunta suka fito.
Aunty na ganin sa takuma had'e fuska.
murmushi ya yi ganin yadda ta cika tam.
ya kad'a keyar Feeryal ya ce
"Je kichin maza Baba Rabi ta had'a miki breakfast."
tace tom.
da gudu tayi hanyar kichin.

Ya karaso ya zauna gefen Aunty yaruko hannunta tare da kiran sunan ta
"Fad'imatu."
da sauri ta tari numfashin sa.
"Daddy gizo ne yanzun d'in ma kada ka ce komai, amma ni bana da wata matsala a kwakwalwa ta, wlh ina son Feeryal ban tab'a jinta a wata daban ba, ina jinta ne tamkar jinin jikina, wacce ta fito daga tsatsona;
abubuwan danake gani tare da ita ne kawai yake sani shiga fargaba a kanta,
ina tsoron kada wataran na rasata, bayan nayi sabo da ita."

Hannuta ya dad'a rike wa cikin nasa ya ce
"Insha'allah bazaki rasata ba, sai kin kaita har d'akin aurenta, kin ga jikokin ki."
ido ta d'an lumshe ta bud'e tana jinjina kai.

Kullum abin Feeryal karuwa yake salon yau daban na gobe da ban ita da Kawayen nata da babu mai ganin su sai ita.
zuwa yanzu Aunty tafara tunanin kodai mayu ne ke bibiyar ta, tana tsoron kada su bata maita ko su cinye ta.
kullum a cikin addu'a take ba dare ba rana, Allah ya kare mata ita daga sharrin miyagon da ido baya iya ganinsu.

Kimanin wata biyu ke nan ana cikin wannan halin kuma kullum abin gaba ya ke ba baya ba..

Aunty ce zaune cikin bedroom tajiyo hayaniya cikin parlour.
jin muryar Mommy tana fad'in
"Wlh sai kin bar gidan nan tun da bana ubanki bane, baki isa kice zaki takurawa 'yan gida ke kina agola ba, wacce ta tsaya mikin ma bata isa ba bare kuma ke."

Da sauri Aunty ta fito parlour'n.
Mommy Ameerah Feeryal Miemie Sahla Nabila. tagani cikin parlour'n.
Mommy na damke da hannun Feeryal, kamar wacce ta kamata tayi mata sata.
Ameerah tsaye baki na fidda jini gefen goshin ta ma haka.
Mommy na ganinta takuma d'aga murya tana cigaba da fad'in
"Wannan annobar 'yar da kika kawo mana gida take kokarin kashe mana 'ya'ya wlh in akan buzu kike kwana karshen tsafi, sai nayi duk yadda zanyi naga tabar gidan nan,
kina sane da cewa dai nafiki fawa a gidan nan, da uban Alhaji Abubakar da ubana uwarsu d'aya ubansu d'aya, kinsan dai na d'are miki nesa ba kusa ba,
d'an'uwa na jini kuma mijina nice nan kuma uwar manyan 'ya'yansa,
kinsan ina da hanyoyin da zanbi cikin sauki na fidda wannan aljanar mayyar a cikin gidan nan, ba ita ba hatta ke wlh ina da yadda zan bi kibar gidan nan tacikin ruwan sanyi, kibi a sannu na gaya miki ke nan;
ina dalili ina mafari da zata sako mana 'ya'ya gaba,
jiya ta fasawa Nabila baki an kyaleta shine yau bari ta komo ta kan autata, to wlh bata isa ta ci bulus ba, baki isa ki takurwa 'yan gida kina tsintacciyar agola zub???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?in mayun aljanu ba,
a gaban uwar tsintuwar taki zan ci uban ki."

Ta tsulawa Feeryal bulalar da ke rike a hannunta, har sau uku.
Feeryal tasaki kara tana tsalle da yarfe hannu.

A guje Aunty ta karaso inda suke ta kwace ta a hannunta tana fad'in.
"Haba Hajiya Halima kiyi hakuri dan Allah, kin san sha'anin yaro, sai a hankali, Allah dai ya shiryar mana da su kawai,
ke Feeryal me yasa zakiyi mata haka, ku dai na fad'a sakanin ku mana,
kuda 'yan'uwan ku kurika fad'a kaman masu ganin hanjin juna,
duk yaron da nasake ganin ya sake fad'a da d'an uwan sa sai na zane shi."
"Dalla rufamin baki munafukar banza munafukar hofi,
idan da mai ganin hanjin wani ai wannan mayyar aljanar da kika kwaso mana ita gida ne,
idan maita kuke ke da ita sai dai kuci kanku,
munafuka al'gunguma, ke kuma Feeryal kike ko ferfela sai na ci ubaki idan kika kara dukar min 'ya shegiya mayya kawai,
sai kin bar gidan nan."
ta kuma kai mata bugu da hannu a kan baki, aiko bakin ta ya fashe sai jini.

"Ya ishe ki haka Hajiya Halima, ita sau nawa suke dukanta suji mata ciwo, natab'a zuwa na sameku kan batun,
sai dai nayi musu fad'a,
sabo da nasan d'a na kowa ne, ina abin duka a jikin wannan yarinyar in banda rashin imani, ai ba'a ki kimata hukunci ba amma ba irin wannan ba,
tun da kuma bakwa yadda a kan naku nima bazan zuba ido ina gani a cutar min da ita ba,
Feeryal zama daram a gidan nan kije kiyi duk abin da zakiyi."

"Ai haka kika ce ko? ai kuwa zaki ga abinda zanyi."
ta janyo hannun Ameerah ta ce wa sauran yaran
"Ku zo mu tafi, zan nuna miki kasawar ki kuwa,
sai na nuna miki karfin dangantakar datake sakanin mu da Alhaji, yafi wacce yake sakanin ku."

Baki Aunty ta tab'e dan tajima tana jin wannan kalmar daga bakin ta, kulllum Mommy gorin ta da kowa ke nan tana da dangantaka mai karfi sakanin ta da Daddy, shiyasa take tsiyarta son ranta babu mai iya takata.
ta ce
"An dad'e ana ruwa kasa tana shanyewa, in banda bazan iya jurar rike wad'annan sangartattun 'ya'yan naku da kuka gama baud'ar da su kuka sangartasu, basusan girman nagaba da su ba,
kuka kasa basu tarbiyya mai kyau ba,
da kuk nasa an sallame ku kuje ku koyo darasin rayuwa, kusan yadda ake daraja mutane kafin ku dawo, kucigaba da rainon su."

"Sai dai ke ki bar gidan nan ba dai mu ba,
juyar banza juyar hofi kawai,
in banda Alhaji ma da niman kalen jan raini wa mutane, har ke kin isa ki tsaya a gabana ina fad'a kina fad'a, wacce a haihuwar akuya nakai na haife ki."
"Sai dai in a haihuwar akuyar kam, amma ke baki isa ki haife ni ba, ai girma batayi rana ba tun da har yanzu hankali bata ishe ku ba."

Mommy tayi bakin kofa fuuu tana zazzaga buhun masifa.
tana isa bakin kofa zata d'aga kafa ta wuce kafa taki gaba taki baya, tayi-tayi ta d'aga kafar ta kasa,
nan da nan zufa yashiga ke to mata, sai ga Mommy tana salati da sallallami.
Aunty ta tab'e baki ta juya tana kokarin komawa bedroom rike da Feeryal.
takuma jiyo salatin Mommy
"La'ilaha'illahu, wayyo Allah kafata nashiga uku,
ke Sahla Nabila kuje ku kira min Ajeemal da Daddyn ku."
Aunty na tsaye tana kallon ta, ganin dai da gaske kasa d'aga kafar tayi, tana ta faman jansa yaki gaba.
zuciya irin na Aunty nan da nan jikin ta ya d'anyi sanyi, ta tako in da take tana fad'in
"Me ya sami kafar taki, subhanallah sannu mugani ko kin taka wani abun ne."
ta sunkuya tana kokarin dubawa,
da sauri Mommy ta ce
"Kada ki sake ki tab'a min kafa, bakar munafuka, waya sani ma ko takan sihirin ki na bi na taka."
"Ashsha me yasa kuke son mu'amala da shirka ne, laifin da Allah baya yafewa bawa har idan yamutu yana aikatawa bai tuba ba,
kawai daga kafarki ya kama ciwo sai ki d'aura alhakin hakan a kan wani,
komai ya faru da bawa da sanin Ubangiji."
"Dalla gafara can bance ki tsaya kawo min aya da hadisi ba, narigaki sanin Allah,
matsa daga nan kada ki sake ki tab'a min kafa ki shafa min wani abin."

Kai Aunty ta girgiza ta mike daga durkushen da take.
da sauri duk suka jiyo jin Feeryal ta fashe da dariya.
san da Mommy ta kuma yunkurin d'aga kafarta tana cewa
"Wayyooo Allah jama'a kuzo ku kawo min d'auki Fatima zata kashe ni."
Feeryal dariya har tana fad'uwa da rike ciki, idan ta nuna Mommy da hanu sai ta kuma tuntsirewa da dariya.

Aunty tayi saurin karasowa in da take ta finciko ta tana fad'in
"Kinci kaniyar ki sa'arki ce da zaki rika yi mata dariya, kar na sake ganin kina yiwa babba haka."
baki ta kunshe da dariya ciki, aiko dariyar ta tsub'uce, cikin muryar dariyar ta ke kuma nuna Mommy dake kurma kururuwa ta ce
"Ammie Chulu zata rike d'ayan ma."

Da sauri Aunty ta kalli inda take nuna mata gurin Mommy kana ta maida dubanta gareta ta ce
"D'ayan me zata rike Feeryal? ki dai na wannan dariyar."
"D'ayan kafar Mommy wanda Chuchu bata rike ba."
ido Aunty ta waro ta ce
"Waya rike kafar nata da?."
"Chuchu ce ba gata can ba tana caccaka mata kaya akan kafar, laaa Ammie kin gani Chulu ma ta rike d'ayar."
takuma fashewa da dariya.

Aiko nan Mommy ta saki wani uban kururuwa ta zube kasa warwas, tana birgima da rike kafa kamar zata fice a hayyacin ta.

Tsawa Aunty ta bugawa Feeryal
"Ke Feeryal kice su sake mata kafa yanzun nan."
cikin muryar dariya ta ce
"Chuchu Chulu ku sakar mata kafa Ammie na ta ce ku barta."
ai ko nan take Mommy ta saida kururuwar da take, jin tamkar an zare gashi cikin fura, cikin dakika d'aya ta nimi cuwon ta rasa.
a bujajan ta mike tayi waje bata ko bi takan autar tata ba Ameerah da take tsaye a kanta tana tayata ihu.
ganin uwar nata tayi waje itama ta bita a guje.

Ido Aunty ta zubawa Feeryal cikin sanyin jiki da sanyin murya ta ce
"Feeryal ki dai na hakan ba kyau."
ita kam Feeryal gaba tayi abin ta taje ta sunkuya wasan ta.

Aunty ta shige bedroom ta zauna bakin gado tare da d'aukar wayarta ta lalub'o lambar,
Hajiya Fara wato mahaifiyar ta, wacce suke kira da Hajja Umma.

Jin mahaifiyar tata ta d'aga tayi saurin fad'in
"Assalamualaikum ina wuni Hajja Umma ya gida."
"Lafiya lau alhmdulillah Fatimah ya kuke, ya mutan gidan?."
ta ce "Duk suna lafiya, ina Maryam yau ba school ana gida,
ta ce min zata zo tayi ta shafamin romo a baki shine taki zuwa ko."
"D'azun nan taje gidan kawun ku Idris, sai da ta isa ta bugo min waya wai a can zata kwana."
Aunty ta ce
"Lallai kuwa a gaida Maryam shine ni taki zuwa min shekaru nawa rabon da ta kawo min ziyara,
Hajja Umma ki ce mata ta zo ni zan biya kud'in jirgi ni ban ce ta taho a mota ba,
basai ma Abba ya biya mata ba."
"A'a ba yanzu ba dai kubar min autata kusa da ni, Zainab ma tana ta masawa sai ta je mata,
na ce ba yanzu ba."
"Kai Hajja Umma shine kike hanata zuwa mana."
"Zata je muku amma dai ku bari sai an yi hutu mai tsawo tukun,
wai ni kam ina kawata ce banji d'uriyar ta kusa ba,
Alhaji kullum sai maganar ta yake, na ce ban gane ba daga ganin farar fuska sai ka rud'e, tun tale-tale muna zaune baka tab'a batun wata ba sai akanta,
ki bani ita na fad'a mata mu bibbiyu da ni da ita ta rabu min da miji."

Dariya Aunty ta yi ta ce "Amaryar Abba ai shekaran jiyan nan ma ya kira ya ce a bata,
ke kam dai Hajja Umma an barki a gefe baki sani ba, kullum Abba sai ya kira sunyi hira da ita."
"Ai ko zamu gamu da ita, tazo ina jiran ta duk sai na kora ma'aikatan gida na,
nakafa sabon murhun itace a waje ita zata rika min girki sai fatar nan nata ya canza kala.
amma Fatimah lafiya dai ko ya naji kamar bakya
yanayin nutsuwa,
ba na ce kiyi ta hakuri nasan ki
da ita,
ki kara kirika mai da komai ba komai ba,
kada ki yada addu'a makarin mumini ne,
me zai dame ki mijinki na son ki,
da har da ke cikin jerin wad'an da Abban ku zai biyawa kud'in hajjin bana,
mai gidan ki ya ce, shima a barshi ya sami lada, sau biyu kad'ai shi yatab'a kaiki hajji,
Abba'n ku kuma sau hud'u, shima yana da bukatar samin karin lada,
me zai d'aga miki hankali mijin ki na biye da ke, kada damuwar wasu ya tada miki hankali kin san dai Abba'n ku bazai jure jin ki cikin matsala ba,
idan ni na jure shi bazai jure ba."

Numfashi Aunty ta sauke ta ce
"Umma ni damuwar mutanen gidan mu baya gabana yanzu, dan nagama gane cewa jahilci ke damun su, ina da ilimi na bazan zauna biyewa jahilai wad'an da basu san abin da suke yi ba,
Hajja umma matsala ta yanzu d'aya Feeryal,
natab'a fad'a miki tun tana jaririya abubuwan da narika gani a tare da ita,
sai gashi a 'yan kwanakin nan ina kuma ganin wasu sauye-sauye a gurin ta,
Hajja Umma ita kad'ai zakiji tana magana kuma bil'hakki da wani take, yanzun nan kamma tayi wani abinda ya shanye min ruwan kai,
wlh Hajja Umma ta dad'a jefani cikin kokonto daban-daban,
anya yarinyar nan ba miyagu suke son kulla alaka da ita ba,
d'ayan biyu ko hakan ko kuma da gaske ita d'in ba mutum bace........!





Mommyn Twins ce


??/\??/\ *FEERYAL* ??/\??/\


*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*


( _Book 1_)


*~Free page~*



*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*

*____________________________________*

*???[???VAINUWA ???VRITER'SA??]Fq??*
*???VSSOCIATION??B惙?_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???a???_

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*





??T???11




Shiru Hajja Umma tayi tana sauraran bayanan da Aunty take kora mata,
na duk abinda ya faru a baya da kuma abin da ya faru da Mommy yanzu ba da jimawa ba.
Aunty tad'aura da fad'in
"Nakanji tsoro wani lokacin na tsinci kaina cikin fargaba, wlh Hajja Umma ina son Feeryal bana son rabuwa da ita,
ni ko aljana ce ma ita ina son ta zan rayu da ita a haka,
abin da nake tsoro d'aya kada ta cutar da ni ko wad'an da nake tare da su, bana so na rabu da Feeryal, wlh ina son ta a haka."
Aunty ta karasa maganar cikin sanyin murya.
Hajja Umma ta jinjina kai sannan ta ce
"Yanzu ina Feeryal d'in?."
"Tana parlour tana ta kan wasa wai da kawayen ta, da ni bana ganin su, ni tsoro na ma d'aya kar ta faje da wasu tarika cutar da mutane."
d'an shiru Hajja Umma ta yi kana ta soma magana.
"Akwai wani malami a can jahar Bauchi awani gari da ake kira Duguri,
Allah ya basa baiwar fahimtar irin wad'an nan matsalolin,
ki kaita can koma mene ne zakiji, in har ba mutum bace bama kafin ku isa zaki nime ta ki rasa, dan bazan mance ba, lokacin jinyar Yayan ku da muka gama karad'e kasashe da dama bamu dace ba, a can gurun sa muka dace,
lokacin da mukaje wata mata tazo da kwatankwacin irin wannan matsalar sai dai ita haifar d'iyar tayi aka canza mata,
ya ce taje ta zo da yarinyar, 'yar tana goye a bayan ta a hanya ta b'ace, bata sani bama har sai da tazo zata kunceta ta shafa taji wayam babu komai a bayan ta,
ganin yadda hankalin ta ya tashi malamin yace ai dama ba 'yarta bace nasu ne ta koma gurin iyayenta,
shi da kansa yaje ya karb'o mata asalin d'iyarta a gurin su,
idan zaku tafi ki sanar mata da in da zakuje, in har Feeryal ba mutum bace baza ta soma dumfarar gabansa ba zata gudu, tun kafin ku isa,
zan bincika ko yana nan har yanzu dan shekarun da dama tun Yayan ku na d'an shekara uku."

Aunty ta ce "Amma Hajja Umma ba dai irin mushrikai d'in nan ba ko? yanzu sai susa ka kauce hanya."
"Haba Fatima ni da kaina bazan kaiki in da zaki halaka ki rasa imanin ki ba,
kin san ba irin wannan tarbiyyar na baku ba, haka nima ba irin wacce iyayena suka bani shi ba ke nan,
idan da yana shirka da tun zuwata ta farko bazan kara zuwa ba,
bare kuma har na tuna da shi a yanzu har nayi miki sha'awar zuwa gurin sa,
malami ne mai aiki da ilimin addini, ba irin masu fad'e-fad'e da karyace-karyacen nan ba,
zan bincika ayau d'in nan idan yana nan sai kubi jirgi kuje."

Aunty ta ce to. nan sukayi sallam.


A b'angaren Mommy kuwa, tana fita ta had'u da Ajeemal dasu Sahla suka kira sa.
da sauri ya tare ta yana fad'in
"Mommy lafiya? su Nabila sun ce min wai kin fad'i kina ihu."
"Biyo ni kawai Ajeemal kar ka tsaya anan da alama kaf yankin side d'in ta ta zagaye shi da kafin asiri."
kai ya girgiza shi sam baya son irin wad'an nan abubuwan da Mommy da Umma Karima suke yi,
baisan me ya kaita sashin Aunty'n ba da take maganar wani asiri.
su komai sai sun dangantashi da asiri.
sam baya jin dad'in yadda iyayen nasa suke zama da abokiyar zamar tasu.
yabi bayanta.

Suna shiga parlour'n ta Mommy ta zube a kan carpet tana dudduba kafafunta, da d'azu take jin sa tamkar za'a finceke su sufice daga ganganr jikinta.

"Kai Fatimah bakar munafuka ce, wannan zata iya kashe mutum da bakin asiri take aiki."

Fuska Ajeemal ya b'ata ya ce
"Mommy to me ya kaiki side d'in Aunty Mommy

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login