Showing 9001 words to 12000 words out of 78516 words

Chapter 4 - FEERYAL Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.doc

ga Alhaji Abubakar Fiya haifaffen d'an jahar plateau state ne awani gari da ake kira da Yelwan Shandam,
Alhaji Shitu Fiya shahararren manomi ne wanda yake noma gonaki sama da hamsin a ciki da wajen Yelwan Shandam.
yana da mata d'aya da ya'ya biyu Abubakar da kuma Sulaiman.
yana da manya-manyan gonaki da girman su yakai girma, a kalla sama da guda hamsin, yana noma nau'ikan abubuwan da akafi amfani da su sosai a kasarmu.
Auduga, Shinkafa, Masara, Gero, Dawa, Maiwa, Rid'i, Agushi Gyad'a, farar Wake, Waken soya, Doya, Dankali, na hausa da kuma na surawa Rogo. da dai sauran nau'o'in kayan masarufi nayau da kullum.
ba a iya noman damina ya tsaya ba har da noman rani.
idan amfaninsa tayi bayan ya cire zakka.
zai aje wanda gida zai ci na tsawon shekara, kana ya cire wanda zai raba kyauta wa danginsa da y'an garinsa, san nan a kai sauran kasuwa.

Cikin kankanin lokaci yazamo shahararren mai kud'in da babu kamarsa a yankin.
a lokacin yakara iyali matansa suka zamo biyu, in da aka kuma samin karuwa bayan d'an wani lokaci amarya ta haifo d'anta na miji yaci suna Tukur.

Dukiyar Alhaji Shitu Fiya sai dad'a hab'aka take tamkar kullum dare ninka masa ake.
ya yi shaharar da kaf fad'in kasar nan ansan da zamansa a wannan gari na Yelwan Shandam.
dan yanzu manya-manyan y'an kasuwa ne suke shigowa cikin garin Yelwa suke sayan kayansa suna fita dashi zuwa jahohin kasar nan.

Amaryar Alhaji Shitu wato Luba batayi tsawon rayuwa ba, ta koma ga mahaliccin ta ,
tare da tsohon ciki na biyu a jikin ta, lokacin d'anta Tukur yana da shekaru uku.
nan fa mutane masu fama da cutar gulma suka shiga kai kawo suna yad'a jita-jita, aka d'aura alhakin mutuwar ta kan kishiyarta, wai ita ta kasheta dan ta zauna cikin daula ita kad'ai, dama da kyar ta bari akayi auren.
nan fa dangin Luba suka rungume zancen a kirjinsu suka yarda kan cewa ita ta kashe musu 'yar'uwar su, dan yanzu taga dukiyarsa ya ninka na da.
suka d'auki karar tsana suka sakawa uwargidan Alhaji Shiru, suka masa sai dai a basu Tukar kar shima ta kashe shi.
Alhaji Shitu Fiya bai yarda ya basu shi ba, ya ce yana da ransa da rufin asirin da Allah ya yi masa d'ansa bazai je agolanci wani gida ba.

Dayaki basu shi sai suka shiga zuwa suna d'aukarsa yana wuni a gurin su.
lokacin da yakara wayo kuma yashiga zuwa da kansa,
duk san da ya je, haka zasu zaunar da shi suna tambayarsa, me matar ubansa take masa, duk abinda ta bashi idan bai yarda da shi ba kada ya ci dan ita ta kashe masa mahaifiyarsa.
da ire-iren wad'annan abubuwan suka rika cusa masa ra'ayi suna dad'a masa hud'uba kan cewa,
ita abokiyar gabansa ce dan ita ta kashe mamarsa kada ya yarda da ita, da kuma ya'yan ta.
a lokacin Hanne wato uwargidan Alhaji Shitu takuma haihuwan 'ya mace taci suna Bishira.
ai kuwa gari yakuma d'aukawa dama ta kasheta ne dan ta tara ya'ya tasami gado.

Hannatu ta toshe kunnuwanta da jifan da magauta suke mata, baisa tayi wasi da rukon d'an mijinta ba, bata tab'a nuna masa bambanci sakanin sa da ya'yan da ta haifa ba.


Ya'yan Alhaji Shitu Abubakar Sulaiman Tukur da kuma autarsu Bishira.
sun fara datawa, in da babban d'ansa Abubakar yafi mai da hankalin kan sana'ar mahaifin nasu, a duk in da Alhaji Shitu ya ke to zakaga Abubakar.

Wani aminin Alhaji Shitu ya janyo ra'ayin sa kan sana'ar man fetur da shi ya ke yi, nan yakuma fad'awa tsundum cikin harkar man fetur, bai kuma sake harkar noman sa ba,
sai ma abin da ya karu.
dan yanzu yasabunta sana'ar ta hanyar amfani da hanyoyin zamani.
yanzu shi da kansa yake sarrafa duk abinda ya noma, akasin da da sai masaya sun shigo sun sayi kayansa, su su fita dashi suje su sarrafashi ta hanyoyi daban-daban.
Alhaji Shitu Fiya ya kafa manyan kamfanoni a manyan jahohin mu, wan da yasashi dole barin garinsa yakoma Lagos da zama, in da babban kamfanin sa na sarrafa auduga ke gurin.
gonakin da yake noman auduga shi ake kaisu kamfanin ake sarrafasu baya sayan auduga daga ko ina shi yake noma kayansa, yaku sarrafa shi ta hanyoyi daban-daban.
har wasu ma suzo su siya.
duk kayan amfanin da yake nomawa ko wanne sai da ya bud'e masa kamfani na musamman a ko wata jahar dake cikin fad'in kasar nan.

Tuni Abubakar ya yi koyi ga mahaifinsa domin kuwa shima harkar noman yarike, baji ba gani, ba karamar karb'arsa noma tayi ba, har mutane suna cewa makoyi zaifi gwani.
sosai ya maida hankali kan karatu kan fannin noma daya zab'a.
akasin 'yan'uwansa da kowa ke karantar wasu abubuwan daban.
lokacin da yakai munzalin aure takanas Alhaji Shitu yaje Yelwan Shandam yanimawa Abubakar auren 'yar d'an'uwan sa, wan da dama maganar had'in take aje dun da jimawa.

A Yelwa aka gudanar da duk shagulgulan bikin kana aka d'auko amarya Halima aka kawo ta Lagos.

Bayan wani lokaci kwasam Alhaji Shitu yakwanta jinya,
daya fahimci rayuwar sa tazo karshe sai ya tarkaso kan takardun kadarorin sa, kana ya tara ya'yan sa da matarsa, ya ce Alhaji Abubakar ya sayi kamfanonin sa da gonakin sa, dan bazai siyarwa wani bare ba.
da arziki a garin wani gara a garin ka.
ya yi hakan ne badun komai ba sai dun yadad'a karfafawa Alhaji Abubakar gwuiwa kan harkokin noma daya gaje sa.
Alhaji Shitu Fiya ya sa hannu cikin takardun mallakawa babban d'ansa Alhaji Abubakar Fiya gonaki da kuma kamfanoni, shikuma ya damka masa kud'ad'ensa.

Bayan rasuwar Alhaji Shitu aka rabawa magada makudan kud'i da sauran kadarorin da ya bari, irinsu gidaje da filaye da kuma gidajen man fetur, ban da gonaki da kuma kamfanoni da yanzu suke a matsayin mallakin Alhaji Abubakar Fiya.

Sosai Alhaji Abubakar yake gudanar da harkokin noman sa, Allah kuma ya sanya masa albarka, arziki yacigaba da hab'aka.

Alhaji Abubakar ya kammala gina wani katafen gida unguwa guda, wan da girmamsa yakai girman wani karamin gari guda a cikin garin Lagos.
manya-manyan part-part ne da akalla zasu kai guda goma shabiyar ne a gidan, kuma ko wani side yana d'auke da get da parking lot mai d'aukar motoci uku, had'e da garden na musamman.

Katafaren katanga mai matukar girmar tsawo ke zagaye da gidan gaba d'aya, wan da saman ginin aka sanya wayoyin shokin domin tsaro aka zagaye garun gaba d'aya da shi.

(A.A FIYA STREET)
sunan da unguwar take amsa wa ke nan.

Lokacin da zasu tare a gidan Alhaji Abubakar yakara aure ya auro Hajiya Karima, iyayen Umma Karima asalin 'yan Kano ne mazaunan Lagos.
lokacin yana da 'ya'yan sa biyu maza da suka haifa da Hajiya Halima, Abdurrahim da Ajeemal.

Sai a lokacin Alhaji Sulaiman da Alhaji Tukur suma sukayi aure, bai bar su sun tare a gidajen da sukaci gadon sa ba, ya ce duk suzo su zauna a gidan da ya gina, suka d'auko mahaifiyarsu suka koma da ita sabon gida,
in da ko wannensu ke zaune da matarsa a side guda guda.

Shekara biyar da dawowan su sabon gida Alhaji Abubakar yahad'u da Fatima a gurin taron bud'e kamfanin mahaifinta a birnin tarayya Abuja. mahaifin Fatima abokin kasuwancin Alhaji Abubakar ne, yana siyan kayan kamfanin sa yakai nasa kamfanin.
ya gayyaci Alhaji Abubakar ne shagalin bud'e sabon kamfanin sa, a nan yahad'u da y'arsa Fatima ya yaba da nutsuwa da kamalanta, ya nimi yardar mahaifinta atake kuwa ya aminta yakuma yi masa alkawarin aura masa ita.
ba'a d'au lokaci ba akayi bikin.
Fatima ta fuskanci kalubale da dama a tun ranar da ta sanya kafarta cikin wannan gida.
do min kuwa Hajiya Halima da Hajiya Karima sun had'e kansu a tun ranar da suka sami labarin auren da mijin nasu zai kara.
wan da a da sam basa zaman dad'i sakaninsu, tun da sukaji zaiyi aure suka had'e kansu.

Cikin kankanin lokaci family'n ta soma hab'aka suka fara tara iyali.
Hajiya Halima uwargidan Alhaji Abubakar ya'yan ta biyar bayan maza biyun data haifa kafin sudawo sabon gida, takuma haihuwar mata uku, Farida Sumayya Amira.
Hajiya Karima ya'yan ta hud'u dukansu mata.
Bilkisu Saddika Rahama Nabila.
Hajiya Fatima kuwa har yanzu Allah baibata haihuwa ba, wan da hakan yazame mata abin gore a gurin abokan zamanta..

Alhaji Sulaiman shima 'ya'yan sa biyu da matarsa Hajiya Safiyya, Faisal da Miemie

Sai kuma Alhaji Tutur y'ay'an sa uku da matarsa Hajiya Nafisat, Shamsuddin Zaraddin Sahla

Family ya had'u cas da su??
Wannan shine takaitaccen labarin Family'n Alhaji Abubakar Fiya.

Mutane na kudai ku biyo ni yanzu wasan yasoma??X0??




Mommyn Twins ce





??/\??/\ *FEERYAL* ??/\??/\



*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*


( _Book 1_)


*~Free page~*


*____________________________________*

*???[???VAINUWA ???VRITER'SA??]Fq??*
*???VSSOCIATION??B惙?_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???a???_

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*



*Bismillahirrahmanurrahim*


??T???4





A b'angaren su Mommy tun da suka fita daga side in Daddy suka koma part in Mommy.
suke kitsa ta yadda zasuji da lamarin,
Umma Karima ta gyara zama ta ce
"Hajiya Halima ga wani shawara, muje mu d'auki yarinyar nan mu nimi ruwa nan kusa ko na kwalbati ne mujefa ta ciki, ta koma gurin danginta,
kowa ma ya huta,
idan fa muka zuba ido muka barta daga karshe mu zata zame mana karfen kafa, tazo ta shafe mana ya'ya ko jinya kad'ai tabarmu da shi ai ta cutar da mu, Fatima bata da asara tun da ba d'a take da shi a gidan nan ba,
sai dai tayi farin ciki da hakan, ina tunanin ma wani makircin take son kitsa mana, idan muka zuba ido kuwa mu zata kaimu ta baro mu,
kinga ta dad'a mallake Alhaji gaba d'aya ta in da dolen mu mubar gidan nan, bakiji yafara fad'a da bakinsa tun yau ba."
Mommy ta jijina kai tare da fad'in
"Kwarai kuwa akwai abin da Fatima take son kitsawa wata kila bokanta ne yabata wani sa'ar, dole aljanar nan ta bar gidan nan,
to amma yanzu ta ya zamuyi mu d'auke ta daga gidan nan, kinsan fa wannan Fatima mai taurin kan ba bari zatayi ba."
"Ai dama ko ta karfin tsiya sai ta bar gidan nan, yanzu dai shammatar ta zamuyi,
mu d'ake ta mu fita da ita,
idan bamuyi sa'a ba sai mu nimi masu d'auko mana ita."
Mommy ta girgiza kai cike da gamtsuwa da maganar Umma Karima.

Kusan raba dare sukayi suna kitsa yadda zasuji da lamarin, Umma Karima ta koma side d'in ta, da shirin gobe zasu je su d'auke ta sufita da ita a gidan.

Washegari da sassafe Mommy da Umma Karima suka fito da shirinsu na d'auko Feeryal, dan sun san yau talata iwar haka Daddy yana masallaci yana sauraran wa'azi.
koda suka iso side d'in Aunty, ganin babu kowa cikin parlour kai tsaye bedroom d'in ta suka wuce.
batare da ko d'ard'ar ba dan sun lashi takwabin sai tabar gidan ko ta alin kaka, ko kwana bazata kuma yi a gidan nan ba.
Feeryal ce ita kad'ai a d'akin kwance a kan gado Aunty na cikin bathroom.
da sauri suka isa bakin gadon cikin kasa da murya Mommy ta ce
"Yi sauri mu d'auke ta kafin ta fito."
Umma Karima ta mika hanu zata d'auketa, wani irin dirrr taji tamkar jan wutar lantarki, da karfi ta janye hannunta jiki na rawa.
a d'an tsorace Mommy ta ce
"Mene ne kuma?."
batakai ga rufe baki ba sukaga ta wani irin waro ido tana jujjuya shi, ya yin da kwayar idanunta suka fara sauya kaloli daban-daban.
kwan wutan cikin d'akin yashiga kawowa yana d'aukewa.
tare da sauya kaloli daban-daban kamar yadda kwayar idanunta suke sauyawa, izuwa fari baki ja kore, da sauran kaloli daban-daban.
tuni jikinsu yakama b'ari zufa yashiga keto musu,
kowa ya shiga neman ceton rayuwar sa.
da gudu sukayi bakin kofa tun kan su karaso kofa ta rufe.
sai ga Mommy da Umma Karima suna kwalla kururuwan niman taimako.


Aun???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ty da ke gyaran cikim bathroom tafito da sauri, nan take wutan nan ya tsaya yadawo dai-dai.
da mamaki ta tsaya kallon su Mommy dake cikin bedroom d'in ta sunata kururuwa.
kallon kan gado tayi in da Feeryal ke kwance, da sauri taga idon Feeryal ya rufe sai kuma kofar d'akin ya bud'e.
aiko da gudu su Mommy suka fice har suna ture juna.
shiru Aunty tayi idanunta akan Feeryal sai dai har lokacin bata kuma motsi ba.
kirjin ta ne yad'an buga tayi saurin fad'in
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un."
acikin zuciyar ta, nan take taji zuciyarta ya yi wasai.
numfashi ta sauke a fili ta furta
"Lallai Hajiya Halima Hajiya Karima kun d'ebo da zafi amma muzuba mu gani."
gaban gadon ta isa tana mai dad'a karfafa zuciyar ta, kan cewa Feeryal mutum ce ba abin da zuciyar ta ke bijiro mata da shi bane ayan da taga yarinyar yanzu.
ta gyarawa Feeryal rufuwa kana ta juya ta koma ta cigaba da aikinta.


A guje suka karaso parlour'n Mommy suna haki, ganin yadda suka shigo a hargitsi 'ya'yansu duk suka mike suna tambayar su me ke faruwa.
"Kada wani a cikinku ya sake yaje side d'in Fatima!."
cewar Mommy tana zama kan kujera gaba d'aya a firgice ta ke jikinta sai rawa yake..
Ajeemal ne yakaraso in da take yana fad'in
"Mommy wai mene ne kam naga duk kun firgice?."
"Ajeemal aljana wlh aljana ce ba mutum ba, mun shiga uku ankawo mana annoba cikin gida, wlh yarinyar can ba mutum ba ce aljana ce, Fatima takawo mana aljana gida, Hajiya Karima kinga abin da nagani kuwa?."

"Ni kuwa naga sihiri aljananci maitanci ido da ido, ko shakka babu 'yannan ba mutum ba ce."
Umma Karima da tsoro yakusa kasheta taja 'ya'yanta, suka koma side d'in ta, suka rufo kofa a kansu.

A b'angaren Mommy kuwa har ta d'aga waya zata sanarwa Hajiya abin da ke faruwa, ta tuna da gargad'in Daddy ta aje wayar jiki a sanyaye
tana ciza yatsa.

A b'angaren Umma Karima ma taso kiran Hajiyar sai dai tana gudun abin da zaije ya dawo, dan bata kaunar abin da zai gutsire mata igiyar aurenta, takan bi ko wace hanya wajen dakile faruwar hakan.


Bayan wata 5

Tun daga wancan ranar su Mommy basu kuma wani yunkuri a kan Feeryal ba,
Aunty kuwa ta dage wajen kula da rainon d'iyarta yadda ya kamata.
yarinya tana ta murjewa fatarta na dad'a kyau babu alamar maraicin uwa tare da ita, ta sami ruwan nono mai kyau da inganci.
tayi wayo sosai tayi mul-mul da ita.
har ta fara iya zama.
sosai Aunty ke kula da ita Daddy na bata gudumawa yadda ya kamata.
bata fita da ita ko ina ko side d'in Daddy zataje ba sosai take zuwa da itaba, takan barta wa Baba Rabi.
kaf fad'in gidan kuwa dama babu inda take shiga side d'in Hajiya Safiyyah ce kad'ai take d'an lekawa.
kowa na harkar gaban sa a gidan.

Yanzu duk wanda yazo gurin ta bata bari yaga Feeryal,
b'oyeta take a d'aki har sai ba'in sun tafi kafin tafito da ita.
sabo da gujewa maganganun da ake akan ta, dan duk wanda ya ganta sai ya ce wuuu a'ina ta samo wannan mai kalar aljanu sam batayi kama da mutane ba.
kyawun ta ya yi yawa.


Aunty ce tsaye cikin kichin bayan ta gama shiryawa Daddy abincin sa dan yau zai dawo gurin ta.
baba Rabi tana ta goge-gogen in da suka b'ata.
Aunty ta dubi Baba Rabi tana fad'in
"Bari naje nayi wanka kafin rikicacciyata ta tashi, idan kazarnan ta kara zafi a ciro ta kada ta kone."

"To Hajiya." Baba Rabi ta amsa tana maida komai wajen zaman sa.

Aunty ta fito daga kichin ta nufi bedroom d'inta, a hankali ta tura kofa cikin kasa da murya take fad'in
"Allah yasa bata tashi ba har sai na gama komai."
ta maida kofar a hankali ta rufe.
idanunta a kan inda bed d'in Feeryal yake,
tana fata Allah dai yasa bata tashin ba.
da d'an mamaki take kallon cikin d'akin, ganin babu gadon nata gaba d'aya a cikin bedroom d'in.
"Ta ina tayi ko ta tashi garin rarrafe ta fad'o a gado ne, to ina ma ganon yake?."
ta had'a tambayoyi wa kanta tana rarraba ido.
da sauri ta d'aga kafa tana kokarin karasawa cikin d'akin.
wani irin tsinkewa gaban kirjinta ya yi tayi baya da sauri, jikinta na wani irin cirawa tsoro da firgici suka dirar mata lokaci guda. gaba d'aya jikinta ya d'auki b'ari.

Hango gadon Feeryal ya tashi sama tamkar ana lilata gadon yana juyawa shi kad'ai sai kyakyata dariya take.
kamar yadda take mata wasa take b'allewa da dariya haka nan take yi, har tana mika hanu alamun a d'auke ta.

Cikin kad'uwa da firgici Aunty takuma yin baya da karfi ta furta
"Innalillahi'wa inna'ilaiihirraji'un!."
ai ko kamar jira ake tayi magana.
a hankali godon yashiga saukowa har ya diro kasa tamkar an dai-dai ta zamansa a gurin zaman sa.

Karaf Feeryal ya saukakan Aunty,
ganin Aunty tafara mika hanu ta d'auke ta, Aunty kuwa cikin hanzari ta bud'e kofa jiki na b'ari tayi waje cike da d'inbin tsoro.

Tana jiyo kukanta bata ko waiga ba,
a parlour ta tsaya tana maida numfashi, tare da dafe kirjinta dake dukan tara-tara!.
addu'a tafarayi wanda duk yazo bakinta yi take tana saukewa.
a matukar tsorace tashiga kwad'awa Baba Rabi kira.
"Baba Rabi Baba Rabi!."
da sauri Baba rabi ta fito tana amsa kiran, ganin yadda gaba d'aya ta rasa nutsuwarta Baba Rabi tashiga tambayar ta ba'asi.
bata iya magana ba sai nuna kofar bedroom d'inta take da hannu.
da sauri Baba Rabi ta nufi kofar bedroom d'in jiyo kukan Feeryal daga ciki.
dan tagama tsinkewa wani abun ne ya sameta, ganin yadda gaba d'aya Aunty ta firgice.

Tana shiga d'akin ta hangoto zaune a kan gadon ta tana kela kuka da mika hanu tana niman mai d'aukarta.
da sauri ta karaso gareta ta sa hanu ta d'auke tana fad'in
"Me ya same ki Feeryal Ammie'n ki ta shiga firgici? kuma dai gaki lafiya lau nagan ki, to ko wani abun tagani cikin bayi?."

Tayi waje da ita tana jijjigata.
ta taho in da Aunty take tsaye zuwa yanzu nutsuwa yafara shigarta da taimakon addu'o'in da take ta yi.
ta mika mata ita tana fad'in
"Hajiya wani abin kika gani ne cikin band'aki akirawo security suzo su cire?
dama da an fara zafi wad'an nan muggan igiyoyin kasan zasu fara niman gurin sanyi su rika fitowa daga mab'uyarsu suna shigewa ramuka ta baya suna shigowa mutane ta cikin toilet."

Ido Aunty ta kurwa Feeryal da tsoron ta ya kamata
batare da ta karb'e ta ba, itako sai zillo take tana mika hanu tana so ta taje gurinta.
"Rike ta naje na kirawo su suzo su kashe kada ya shige wani gurin a rasa shi."
Baba Rabi ta kuma fad'i tana dad'a mika mata ita.
Ja da baya tayi idon ta a kan ta tana kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login