Showing 54001 words to 57000 words out of 78516 words

Chapter 19 - FEERYAL Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.doc

cewa
"Fita Seena an fad'a miki nafara hauka ne, ki koma gidan ku kije ki kwana a can."
zata kuma magana yabuga mata tsawa
"get out please."
kina dad'a tsayar da ni dare yana da d'a yi."

Ta bud'e ta fita tana tura baki, taso su kwana tare koba a nan ba ko a gidan nasu ne.
yaja motar a guje yafiya a Club d'in yana maganar zuci
"Yanzu haka wancan tsohon yana nan idanunsa biyu ka dawo yasoma tuhumar ka in da ka fito, mtsst."
yaja tsaki yana kara gudun motar ya d'au hanyar A.A FIYA STREET.

Yana isa bakin get d'in gidan su, ya yi hon har sau biyar ba'a bud'e masa get ba.
a kufule ya fito daga cikin motar, ya tab'a karamar kofa yaji ta a kulle.
rai b'ace yashiga bubbugawa da karfi.
security suna ji basu ko kalli kofar ba, duk da suna da tabbacin Zaraddin d'in ne ya dawo, dan shine yake dawowa a'irin wannan lokacin ko fin irin lokacin ma.
tun da karfe goma na daren al'a'dar Daddy ne sai yaje ya duba matasan gidan shin kowa ya dawo kafin ya je ya kwanta.
bayan ya duba yaga kowa na nan shine kawai baya nan har wajen karfe 12 yakuma zuwa da kansa ya duba yaga bai dawo ba,
ya sanarwa security idan ya dawo kar su bud'e masa kofa tun da ba yau ya saba yin hakan ba.

Zaraddin yakai minti goma tsaye yana buga kofa, babu security daya taso bud'e masa.
dogon tsaki ya ja, ya juya ya koma motar sa ya d'au wayoyin sa da tun zuwan sa Club d'in rabonsa da d'aukar su.
nan yaga missed calls sun cika wayar.
na Ajeemal ya fara cin karo da shi, sai na Dad da Mom d'in sa.
a karshe kuna 1 missed call na Daddy.

Tsaki yakuma ja
"Sai kace mutum zai b'ata sun wani cika min waya da kira."
ya dannan no d'in Ajeemal.
har kiran ya yanke bai d'aga ba, yakuma mai da kiran har ya kusa yankewa kafin ya d'aga.

A b'angaren Ajeemal kuwa kiran wayar ne ya tashe sa daga bacci.
ya janyo wayar tare da d'aga kiran cikin muryar bacci ya yi sallama batare da duba mai kiran nasa ba.
jin ya d'aga Zaraddin ya ce
"Ajeemal zo kasa wad'an nan banzayen security su bud'e min kofa, nakai 20min a tsaye suna jina ina hon sunki bud'ewa sai kace gidan uban su!."

Ido Ajeemal ya mustsike cike da jin bacci ya mika hannu ya kara hasken Night Shining Bulb in da ke kan bedside, ya dubi agogon dake like jikin garun d'akin karfe 2 har da mintuna 15 ya ce
"Zaraddin har this time kana waje baka shigo gida ba?."
"Dalla kazo ka bud'e min kofa ko ma meye kabari na shigo ciki tukun."
kai Ajeemal ya girgiza ya janye blanket d'in da ke rufe a jikin sa ya sauko a gadon yafita ya nufi bakin get.

Kasancewar tazaran da ke sakanin babban get da side d'in nasu, sai da ya yi tafiya mai d'an tsawo kafin ya isa bakin get d'in.

A zaune a waje ya tadda security guda biyu, da alama hon da bugun kofar Zaraddin d'in ne ya ta sosu.
Ajeemal ya ce
"Ku bud'e masa get ya shigo."
suka ce
"Alhaji ne ya ce kada a bud'e masa ko da ya dawo."
Ajeemal ya ce
"Kar ku damu ku bud'e masa babu komai."
nan d'aya daga cikin su ya karasa ya bud'e get d'in.
Zaraddin ya ja tsaki ya dannu hancin motar da gudu kamar zai d'auke security'n.
ba shiri ya matsa gefe.
ya d'an tafi can ya tsaya Ajeeml ya karaso ya bud'e d'aya gefen ya shiga yana binsa da kallon tuhuma.
Zaraddin ya d'auke kai ko a jikin sa ya ja motar zuwa side d'in su.
gudun kar Ajeemal ya tsare shi da surutu ya sauka da sauri ya je ya bud'e get d'in side d'in su ya dawo ya shiga motar suka karasa parking lot d'in su,
ya gayara parking gefen motocin su Ajeemal d'in.
yana kashe motar ya fita.
Ajeemal ya bi bayan sa, har suka shige parlour'n su.
yana kokarin shigewa bedroom d'in sa Ajeemal ya ce
"Zaraddin yanzu abinda kakeyi kana kyautawa kan ka ke nan,
har wani irin dad'i zakaji karaba dare a waje baka dawo gidan iyayen ka ba, ba wani aiki kake ba bare ace aiki ne ke tsaida ka ka kai har dare irin haka,
ya kamata kayiwa kanka karatun tanatsu, ka dai na abunda kake yi d'in nan, babu riba cikin ta sai fad'uwa,
har sau nawa na kiraka a waya baka d'aga ba,
karigada ka san Daddy kullum sai yazo ya duba duk muna nan ko ba ma nan,
d'azu yazo baka nan karka mance shekaran jiya ma yazo baka nan, kuma na fad'a maka,
madadin ka kiyaye shine ka sake aikatawa."
"Kai bafa wani guri naje ba mittin muke da abokai na."
"Aiki kuka somayi kai da abokan naka da kuka zauna yin mittin, wace irin aiki ce arasa lokacin yin mittin sai tsakar dare, maita ce ko sata shine dai nake da tabbacin ake yin sa a tsakiyar dare,
wlh Zaraddin kayi wa kanka fad'a nadai fad'a maka."
hararar Ajeemal ya yi ya ce
"Idan ina maita ko sata ku zaku fara sani, dalla karabu da ni malam kaje ka kwanta."

Hayaniyar su ne ya tashi Shamsuddin da Faisal, suka fito daga d'akunan su.
dai-dai lokacin da Zaraddin yake shigewa cikin bedroom d'in sa.
Shamsuddin ya dubi Ajeemal ya ce
"Ka tsaya b'ata lokacin ka a cikin daren nan dalla rabu da shi, yaje ya yi ta yi tun da hakan yafi masa."
Faisal ya girgiza kai yana fad'in
"Bansan me ke damun Zaraddin ba, d'azu da naga wannan abokin nasa Ziyad d'an gidan Ministan nan nasan cewa da in da suka kulla zuwa yau,
wlh wannan Ziyad d'in ba mutumin arziki bane, baima kamata ace wani d'an gidan nan yana harka da shi ba, har ma a gansa yana shigowa cikin gidan nan."
"Ba shi yaja ba duk wani kare da doki sune abokan sa, yaran da suka fi karfin iyayen su, sai abin da sukaga damar yi suke yi."
ce war Shamsuddin, yana hararar kofar sa.
Zaraddin ya leko yana fad'in
"To munafukai idan kun gama sai kuje ku kwanta,
ni nayi kwanciya ta abina."
ya turo kofarsa ya rufe.

"Zaka gamu da Daddy gobe ai."
Shamsuddin ya fad'a ya juya ya shige bedroom d'in sa.
Faisal da Ajeemal ma suka wuce nasu d'akunan.

Washegari tun karfe 9 da rabi na safe Zaraddin ya tashi ya nufi sashin Daddy.
kamar yadda suka saba ko wacce rana da safe karfe 10 suke bin kan iyayen nasu duk su gaishe su.
acikin su kuwa shine mai lattin zuwa gaisuwa, yakan kai goma da rabi wani binma har 11, idan yagama baccin gajiyar yawon daren sa kafin yafita zuwa gaishe su.
sai gashi yau yariga kowa zuwa sashin Daddy.

A parlour ya tadda shi fitowar sa daga bedroom kenan, yana kokarin zama Zaraddin d'in na shigo wa.
ya karaso tsimi-tsimi kansa a kasa, ya zauna kasan carpet kusa da kafar Daddy.
cikin kwantar da murya ya shiga gaishe sa.
Daddy ya zuba masa ido batare da ya amsa gaisuwar tasa ba kana ya ce
"Ina ka kwana Zaraddin?."
da sauri ya d'ago ya ce "A ina na kwana kuma Daddy a gida na kwana wlh."
"Karya ka ke har karfe 12 ina tsaye da kafafu na ina jiran dawowar ka, har nayi bacci baka dawo gidan nan ba."
da sauri ya mike yana cigaba da marairaice murya ya saka gwuiwowin sa a kasa kamar mai niman gafara yana wani kwantar da kai
"Wlh wlh Daddy a gidan nan na kwana Ajeemal ma shaida ne, shi ya zo yasa security suka bud'e min kofa,
nafi awa uku a waje tun 11 da wani abu nake bakin get suka ki bud'e min, sai da na kira sa kafin yazo yasa suka bud'e,
ni Daddy ina zanje na kwana batare da izinin ku ba idan ina son zaman lafiya da sanyawar albarka."

Shiru Daddy ya yi yana kallon sa, shi dai a sanin sa sai da 12 tayi jiya kafin yaje ya ce da security kada su bud'e masa get. amma gashi shi yanzu yana fad'in
wai tun 11 da wani abu yake bakin get.
gaba d'aya Zaraddin ya marairaice tamkar iya gaskiyar sa yake fad'i.
har kuwa Daddy ya yarda yake ganin wata kila basuji hon d'in sa bane yasa basu bud'e da farko ba, bayan kuma yaje yace dasu idan yazo karsu bud'e shiyasa suka ki bud'e masa daga baya.

Daddy ya ce
"To naji amma dai kasan dokan karfe goma ne kowa ya kasance a gida ko, duk abinda kuke ku bari ku dawo gida,
duk abin da kake koma mene ne ka barshi ka dawo gida, kada ka kuma ketare karfe goma daga yau na fad'a maka."
"To insha'allahu Daddy bazan karaba jiyan ma akasi aka samu, a gafarce ni."
Daddy ya jinjina kai yana cewa
"Tashi ka je, kadai kiyaye kaji na gaya maka."

Zama ya gyara ya tsunkuyar da kai yana d'an sosa bayan keyar sa.
Daddy ya dube sa yana fad'in
"Ya akayi kuma?."
dad'a tsunkuyar da kai ya yi yana shafo keyarsa sannan ya ce
"Am dama Daddy wani d'an kud'i ne nake da bukatar su."

Sallamar da su Ajeemal sukayi ne ya katse shi daga abin da yake son fad'a.
Daddy ya amsa suka karaso suka zazzauna kasan carpet suna gaida Daddy'n.
ya amsa yana tambayarsu sun tashi lafiya?.
duk suka amsa da lafiya lau.

Suma zaman suka gyara da alamar akwai abin da ke tafe da su.

Daddy ya dubi Zaraddin ya ce
"Uhum ina jin ka Zaraddin me ke tafe da kai?."
Zaraddin yabi su Ajeemal da kallon kasa-kasa duk ya harare su kana ya muskuta ya ce
"Da ma Daddy kud'i nake so, abokin mu ne zaiyi aure yau, ina kuma niman izini ba a garin nan za'ayi bikin ba, zamuje mu kwana d'aya gobe zamu dawo."
Daddy ya ce
"Nawa ne kake bukata?."
kai ya d'an sosa sannan ya ce
"2 million ne Daddy."
Daddy ya d'aga ido ya kalle shi kana ya ce
"1 million za'a baka sai ka lallab'a, ka koyi yadda ake maneji."

Faisal ya zubawa Zaraddin ido da mamakin karyar da ya sharara yanzu,
wanda yana jin sa sanda ya fito zai zo gurin Daddy yazo zai wuce ta kofar bedroom d'in sa yaji yana waya,
yana sanarwa wani abokin sa yau da karfe 12 na dare akwai birthday party na girl friend d'in su.
"Wato acan zaije ya kwana ke nan."
ya girgiza kai

Maganar Daddy ne yasashi maida hankali gurin sa
"Ku me ke tafe da ku?."
Ajeemal yad'an gyara zama sannan ya ce
"Daddy muna so ka cika mana kud'i ne mu siyi sabon computer, muna son mu samu babban namu saboda yanayin karatun mu."
Daddy ya jinjina kai ya ce
"Nawa ne cikon kud'in naku?."
Shamsuddin ya ce
"2-2 millons ne kud'in computer amma 1 million muke so a cika mana."
Faisal ya karb'i batun da cewa
"Mun samu irin wanda muke so a Germany zamuyi odar sa can."
"To madalla hakan abune me kyau."
Daddy ya fad'a yana d'aukar d'aya daga cikin wayoyin sa.

Ya yi wa ko wannensu transfer d'in million d'aya da rabi.
sannan ya dube su yana fad'in
"Miliyan d'aya da rabi-rabi na sa muku sai ku aje 500k ko wata bukatar zata taso muku,
kai Zaraddin sai kayi hidimar bikin da zakuyi, amma kai banji kace zaka sayi computer ba, ko kana da ita ne?."

Gefen kansa ya sosa ya ce
"Am eh.eh..idan na dawo ne zan yi maganar ni ma."
"To shike nan sai ku tashi kuje Allah ya yi jagora,
amma Shamsuddin Ajeemal Faisal wazai yi muku odar daga can bazakuyi wa d'an'uwanku magana, tun da yana can,
ya sako muku a jirgi ba, ko kun yarda da wanda zakuyi harkar da shi ne?."

Ajeemal ya ce
"Daddy shine ma zamu tura masa, munyi magana da shi ne kan muna son sabon computer shine ya ce,
mu turo da rabin kud'i sai ya cika ya siya mana."
Daddy ya ce
"Inji sa ya ce sai kun bada rabin kud'i kafin ya siya muku abu?
to duk ku maido min da kud'i na kuce masa nace ko sisi bazaku bada ba shi zai siya muku da kud'in sa,
ya baku sana'ar yi ne da zaku sami kud'i da har zaice ku bada rabin kud'i? a ina zaku sami kud'in kuna 'yan makaranta yabari idan kuka gama karatu kuka kama aiki shine zaiyi wannan maganar,
maza-maza kuce dashi na ce ko sisi bazaku bashi ba shi zai saya muku da kud'in sa."

Duk suka zaro wayoyin su suna kokarin maida masa kud'in da ya tura musu.
ya ce "Ku bar shi ku adana idan kuna da bukatar wani abin sai kuyi da shi, kada ku kuskura ku tura masa ko sisi cikin kud'in nan."
suka amsa da to sukayi masa godiya suka mike suka fito.

Suna fita Faisal ya dubi Zaraddin da yayi kicin-kicin da fuska, yana harararsu ya ce
"Yanzu kayiwa Daddy irin wannan karyar alhalin party zakaje kace zakayi tafiya,
ina jin kafa d'azu kana waya zakuje birthday party 12 na dare."
baki Shamsuddin ya bud'e ya rike hab'a ya ce
"Kasan da wannan Faisal shine kana ji ya yi wa Daddy karya,
ya ce zaije bikin abokin sa, ashe party zaije ya kwana a can,
to wlh sai na fad'awa Daddy tun da har abun naka yakai ka fara kwana a Club."
ya juya zai koma parlour'n Daddy.
Ajeemal ya ruko sa yana fad'in
"Rabu da shi karma kaje ka barshi yaci gaba tun da hakan ya zab'ar wa kansa."
"Munafukan banza, je ka fad'a mana,
in banda tsabar bakin ciki za'a bani 2 million,
kuka wani kwaso kafa kuka zo wai kuma a baku,
kuka sa a ka rage kud'in da za'a bani,
munafurcin banza kawai bansan me na tsare muku ba kuka bi kuka samin ido,
tun da Dad da Abbieh suna gida zan sami cikon miliyan d'ayan da kuka yi bakin cikin acika min,
'yan sa ido kawai."
Ya juya ya wuce.
Ajeemal ya ce
"Mujen ku kurabu da shi dan Allah Allah ya bashi sa'a."



Su Ajeemal suna fita Daddy ya gyara zaman shi bayan ya tura kira a wayarsa.
har kiran nashirin yankewa kafin aka d'aga.
Daddy ya amsa sallama had'e da gaisuwar da yake masa, sannan ya d'aura da fad'in
"Ya aikin dan naga alama aiki na shirin ya fimu a gurin ka, yanzu sai kayi kwana hud'u biyar sati baka neme mu ba,
mu in mun neme ka ma sai munyi da gaske muke samin ka,
yanzu ma har na cire rai da samin ka, watakila kana gidane yanzun ma yasa na same ka akan lokaci."
daga cikin wayar ya ce
"Kayi hakuri Daddy yanayin aikin namu ne, kwana biyun nan ina yawan shiga CS ne shiyasa bana samin time d'in d'aukar wayar, ya cikin gidan duk kuna lafiya?."

Daddy ya ce
"Kowa lafiya, kaifa kana lafiya?."
d'an gajeren tsaki ya sake cikin yanayin gajiya da kosawa ya ce
"Daddy bana samin bacci kwana biyu, kusan a tsaye nake kwana,
majinyatan Israel yawancin nan ake shigowa da su,
I'm busy this moment, nagaji kaina yana yawan ciwo,
I will go back to Nigeria very soon,
in ba haka ba zan iya samin bp."

Murmushi Daddy ya yi yasan shi sarai baya son damuwa da yawa, shi yasa ma tun farko yaki aikin likitanci sai da Daddy'n ya matsa masa sosai,
dan shi ya taso da burin gadar kakan sa Alhaji Shitu Fiya da kuma shi kansa Daddy'n,
wato harkar noma yafi bukata.
duk da Daddy'n yahanashi sai da ya sami digiri a harkar noma, bayan ya kammala karatun likitancinsa.

Daddy ya ce
"Haka kake cewa last year ma haka kace min zaka dawo amma baka dawo ba,
ya kamata ka dawo gida Nigeria dan kasarmu ma tana da bukatar ka,
duk d'inbin kud'in da suke biyan ka a can, ko da kasarka bata biyaka rabin sa ba,
yafi ka zauna a can kana musu aiki kadawo ka ceci al'ummar kasarka."

"Daddy ni fa aje aikin zanyi gaba d'aya, nagaji da shi,
zan dawo gida na huta."
"A'a bazaka aje aiki ba, aikin lada ai ba'a gajiya da shi, yanzu kasan ladan da kake samu na ceton rayukan da kake,
ko iya musulman Israel d'in da ka ceta ai lada me yawa ka samu,
duk da gwamnatin kasar ce ke biyan ka ai kana samin lada, dan wannan aikin Allah ne kad'ai ke iya biyan bawa bawai kud'in da ake biyan sa ba."

"Hmm."
kawai ya ce dan shi fa aikin ne baya so, baya son hayani ko kad'an.

Daddy ya ce
"Dr Omar, High Doctor of General Hospital, ya kirani da kansa ranar,
jiya ma yasake kirana yana min tuni,
mai girma gwamnan jihar nan Lagos ya tambaye ka da kansa, ana bukatar ka a kasarka a jihar nan,
me yasa bazaka dawo ka koma bakin aikin kaba, ga asibitocin ka ma kana ganin ma'aikatan ciki sun wadatar,
ka sa rana ka tattaro ka dawo kasar ka."

Shiru ya yi batare da yakuma cewa komai ba.

Daddy ya ce
"D'azu su Ajeemal suka zomin da batun wai ka ce su kawo kud'i ka cika musu ka siya musu computer,
to nace kar su tura ma ko sisi,
ka siya musu da kud'in ka,
suna sana'a ne da zasu sami kud'i."
"Daddy ai na ce musu surika zuwa d'aya daga cikin Company duk ranar weekend's,
na tambaye su suka ce min suna zuwa suma sun fara karb'ar salari, ina son sanin hazakarsu ne yasa nace su kawo kud'in."
Daddy ya ce
"Sun ce zasu fara zuwa ni na hanasu zuwa na ce su nutsu da hankalin su da karatu tukun, har su kammala."

Kai ya jinjina sannan ya ce
"To shike nan Dadd???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?y saura 10 minute na shiga CS idan na fito zamuyi waya."
"To Allah ya bada sa'a."
sukayi salla ya kashe wayar duka ya turashi gefe.
ahankali ya maida bayan sa jikin lafiyayyen kujerar office d'in sa, ya lumsahe idanun sa, masu d'auke da gashin ido zara-zara luf-luf kamar an zizara masa.

Kyakkyawa ne dogo mai murd'ad'd'in jiki,
yana da tsananin kwarjini da cikar haiba mai cika ido.
akan kyakkyawar fuskarsa zagaye da saje mai kyau da ya karawa fuskarsa kyau, zuwa gyemunsa da baiwuce kamu d'aya ba.
dogon hanci lips mai kyau da taushe,
kwantaccen gashin gira mai yelwa da zara-zaran gashin ido.
gashin kansa baki sutuf a nannad'e yasha gyara sai sheki yake.
yana da faffad'an kirji mai shinfid'e da gashi luf-luf,
daya dad'a kawata faffad'an kirjin nasa.
sai dai shi sam ba fari bane kuma baza'a kirashi da baki can ba, sai dai mu iya cewa wankan tarwad'a wato chocolate kolo.

Dr Abdurrahim Abubakar Shitu Fiya kenan.
inkiya (A.A FIYA)

A hankali ya bud'e lumsassun idanunsa.
ya sauke sa kan tsadaddin agogon diamond d'in da ke d'aure a hannun sa,
d'an gajeren tsaki ya ja ganin time d'in shiga CS d'in sa ya yi.
da gaske ya ke jin ya gaji da damuwar aikin nan,
gaba d'aya sun d'aure shi da jijiyoyin jikin sa.
a gida Nigeria ana fitinarsa ya dawo.
a nan kasar suma gwamnatin kasar sun ki su barshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login