Showing 18001 words to 21000 words out of 78516 words

Chapter 7 - FEERYAL Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.doc

sai ya karaso ganin Sahla ma bata fito ba,
suka toko da kafa har zuwa kofar get d'in side in Mommy.
anan suka tsaya harya d'au Sahla Miemie yazo ya d'au Nabila
ya karaso.
dai-dai lokacin kuwa su Ameerah suka fito.
Farida da Sumayya duk suka d'auke kai kamar basu gantaba,
bare ta sa ran samun gaisuwa daga gare su.
dan dama basu da wannan tarfiyyar ganin babba su gaishe shi.
Aunty ta ce
"Ameerah Nabila Sahla, me yasa kuke dukan Feeryal kurika yadda ita a kasa tana jin ciwo? 'yar'uwar ku ce fa itama, ku da zakuga wani yana yi mata ku hana amma ku kuke dukanta, kar ku sake dukanta kanwar ku ce kun ji."
maganar Farida tajiyo daga bayan su
"Ah mu ba kanwar mu bace kada ki danganta mu da ita, meye had'in aljana da mutum."
Aunty ta juyo tana kallon yadda Farida take wani yamutsa fuska.
"Kuma mayya ba mai idon mayu."
cewar Ameerah tana hararar Feeryal.

Ganin yaran suna shirin yi mata rashin kunya ta ce
"Kul ingaya muku ni ba sa'arku bace, zan farfasawa yarinya baki, idan tace zatayi min rashin kunya, wata a cikin ku tasake tab'ata ta ga yadda zanyi da ita."

Gajeren tsaki Farida tayi taja hannun Sumayya ta ce "Zo mu tafi kar mu tsaya b'ata lokacin mu anan."
tawani murgud'a baki cike da fitsara, suka shige motarsu da yanzu ya karaso gurin.
Aunty ta ce
"Dukan tsiya zanyi wa yarinya idan tace zata zage ni fitsararrun banza kawai,
kuma wlh wata a cikin ku tasake tab'ata ta gani."
Isa direba yashiga bata hakuri, kana yabud'e wa Feeryal gaba Aunty ta sakata tana musu Allah ya tsare..
kana ta juya ta koma side d'in ta...

Duk da gargad'in da Aunty tayi musu baisa sun ji ba, yau ma sai da suka tara yara sukayi ta jifanta,
ta dawo da jikin ta fusu-fusu.
kullum kuwa haka suke yi mata, su tara yara suyita jifanta suna ce mata aljana mayya.
abun su Ameerah sai gaba ya ke, lura da yadda suka sako ta gaba, ranar malaman su suka tarasu suka zanesu gaba d'ayan su da yaran da suke tarawa.

Kasancewar ranar juma'a ne da wuri a ka taso su a makaranta,
a mota Ameerah nata jan hanci sabo da ba kad'an ba dukan ya shige ta,tarika hararar Feeryal tana kwafa.
suna isa gida, Ameerah aka fara saukewa kofarsu kafin Nabila, sai Feeryal.
Miemie ta leko ta jikin gilashin mota ta ce
"Feeryal gobe weekend zakizo garden muyi wasa?."
ido Feeryal ta d'an waro cike da jin dad'in abun da Miemie ta fad'a, dan tana son wasa sosai.
tabud'e d'an karamin bakinta tana d'an wawware idanunta irin abin yazo mata a bazata.
ta ce
"A Garden d'in Ammah in ki? zan zo da baby na ma, ke ma zaki zo da naki?"
Miemie ta ce
"Ke ba garden in Ammah na ba, a babban garden na bayan sede d'in su Ya Ajeemal, zaki zo?."
kai ta gyad'a mata, duk da bata tab'a sanin da wannan garden d'in da take fad'a a cikin gidan ba,
ya ma za'ayi ta sani ita da ba ko ina take zuwaba a cikin gidan.
daga makaranta sai side d'in su.
ko side d'in su Miemie'n ma baifi a kirgaba zuwanta side d'in,
shima d'in da Ammie'nta suka je.
Miemie ta koma ta zauna kan sit, direba yaja suka nufi side d'insu.
Feeryal ko ta zuba a guje tayi cikin nasu side d'in tana fad'in

"Ammie na dawo Ammie na dawo."
da sauri Aunty dake shirya abinci kan dinning ta bud'e mata hannu ta taho da gudu ta fad'a jikin ta.
Aunty ta rungume ta tana cewa
"Oyoyo 'yammatan Ammie an dawo ya karatu."
sai ta cirota a jikin ta tana kallon fuskanta da mamakin ganin yau babu hawaye kan fuskar nata.
"Yau ba'ayi kuka ba ke nan?."
kai ta gyad'a
"Ai yau su Ameerah basu bigeni ba, Uncle da Aunty sun ce zasu zane su in suka kuma duka na."
"Ah gaskiya Uncle da Aunty sun kyauta, daga yanzu bazasu sake dukan ki ba."
murmushi tayi sai kuma ta ce
"Ammie gobe weekend zamuyi wasa a garden da Miemie."
d'an shiru Aunty ta yi tana kallon ta,
tasan dole su Ameerah suna gurin.
dan duk ran Saturday and Sunday yaran gidan manya da kananun su suna had'uwa a babban garden d'in gidan, ayi ciye-ceye da shaye-shaye da tand'e-tand'e.

Kafa tashiga bugawa kasa tana ce wa
"Ammie zanje Ammie zanje."
"Feeryal su Ameerah fa zasuje suma, kiyi zaman ki kawai a nan."
d'an karamin bakin ta ta turo gaba tana shirin yin kuka, Aunty ta ja kumatun ta ta ce
"To naji zakije shi ke nan, taho muje a cire Uniform."

Washegari da safe Miemie tabiyo wa Feeryal sutafi,
badun Aunty taso ba ta barta suka tafi.
kaf yaran gidan sun hallara, masu wasa suna yi masu ciye-ciye suna ta kai.
tun daga can Sahla ta hango su Miemie da sauri ta matsa in da Ameerah take, ta nuna mata su da hannu.
Ameerah tawani taune baki tuno da bulalar da tasha jiya akan Feeryal.
da sauri ta tafi ta sha gabansu Miemie, ta ware kafafunta ta bud'e hannayenta.
"Baza ta shiga ba ai nan ba gidan su bane gidan mu ne."
cewar Ameerah tana hararar Feeryal.
Miemie ta ce
"Wasa zamuyi kibari Ameerah."
da gudu Sahla da Nabila suka zo in da suke.
Nabila ta ce
"Yauwa Ameerah kin tuna dukanmu da jiya akayi akan."
"Ai rama kayanmu zamuyi."
cewar Sahla tana gyara hannun rigarta.
ai ko kan kace me suka rufu a kanta duka ta ko ta ina suke kai mata.
Miemie tarika jansu tana fad'in
su daina.
ganin bazasu bari ba tayi gudu taje gurin su Farida
"Aunty Farida Aunty Bilkisu ku hana su Ameerah dukan Feeryal, gafa yadda suke dukanta."
Farida ta waigo ta kalli in da suke ta ce
"Suci ubanta dan uwarta wayace tazo nan ko an gayyace ta ne."
Bilkisu ta ce
"Su faffasawa shegiya aljana baki ko zata b'ace mana a gida."

Da gudu Miemie ta juya ganin ba taimakon ta zasuyi ba,
tayi gurin Ajeemal da ta hango yafito daga b'angarensu, zai fita damuwar sa.
"Ya Ajeemal Ya Ajeemal gasu Ameerah can suna dukan Feeryal."
da sauri ya yi in da suke yana fad'in
"Kai bakuda hankali ne."
aiko suna ganin sa suka ruga da gudu suka bar gurin.
ya karaso da sauri ya d'aga Feeryal dake yashe a kasa tana kuka, sun mata lilis sun farfasa mata baki.
karkad'e mata jikinta ya yi ya ce
"Yi hakuri kiyi shiru ki tafi abin ki zan rama miki."
ta tafi tana kuka Miemie na biye da ita tana bata hakuri har side d'in su.

Aunty na ganin Feeryal da kuka ta taso da sauri
"Lafiya Feeryal ke Miemie me ya same ta haka?
ai sai da nace bazaki je ba kika matsa sai kin je."
"Ameerah da Nabila da Sahla ce suka taru suka bigeta."
cewar Miemie kamar zatayi kuka.
rai b'ace Aunty ta ce
"Irin wannan duka haka sai kace jakarsu, ai ni da ma nasan za'ayi haka shiyasa tun farko banso ki je in da suke ba."
ta janyo hannun Feeryal tana dudduba jikinta.
duk a kwakkwarjane sun jijji mata ciwo har yana fidda jini.

Mayafinta ta zara ta janyo hannunta ta ce
"Zo muje idan ba layi na ja wa yarannan ba bazasu barki kisha ruwa ba."

Suna isa garden ta cafko hannayen Ameerah da Nabila da Sahla.
ta ce
"Haba ku kuwa Ameerah Sahla Nabila, me yarinyar nan tayi muku haka,
zakuyi mata irin wannan dukan?
babu kyau cin zali fa, ku duba kuga yadda kuka jijji mata ciwo har jini yake fiddawa
haba ku kuwa,
ai ba ita ta sa a bige ku a makaranta ba jiya,
ku da kuke dukanta kullum ta tab'a ramawa?
kar ku sake mata irin wannan dukan idan kuka kara kuma sai na zazzane ku da bulala,
yanzu ku da girman ku Farida Sumayya Bilkisu Saddiqa,
kuna kallo suyi wa yarinyar nan irin wannan dukan bazaku hana su ba, haba ku kuwa"

Hanci sama duk suka d'aga kowa ta kawar da kanta kamar basa ma jin abin da take fad'a,
Farida kam uwar 'yan rashin kunya sai da ta had'a mata da kallon banza.
bata bi ta kansu ba,
ta jajja kunnuwan su Ameerah tanai musu gargad'in kada su kara.
"Kada ku kara idan kuka kara zan d'auki bulaba, idan tayi muku laifi kuzo ku fad'a min, ni zanyi mata hukunci dan bata isa ta raina ku ba dan kune yayun ta."

Daga bayan su tajuyo muryar Umma Karima tana tafa hannaye da fad'in.

"Iyee da kyau mana bashakka, sakar musu kunne kada ki tsinke dan baki da asara,
akan wannan aljanar ruwan zaki ni mi ki tadawa ya'yan mu hankali, har da wani kabaibaye su kina shirin b'alla musu hannaye da kunnuwa;
to maza sake su,
ke kenan ma da baki san kalar nishin haihuwa da wahalarsa ba kika ji zafin ta, bare mu da muka san wuyar sa,
tsintacciyar cikin ruwa mara galihu aljana-aljana mayya-mayya akan ta ne zaki saka mana yara gaba,
to ko da bakin wasa ki tsaya matsayar ki, dama duk juyar mace sai ka same ta da bakin mugunta kan ya'yan mutane,
dan bata san wuyar d'aukar ciki da haihuwa ba,
shi yasa baki san zafin ya'yan ba, ko wacce kalar mugunta ma zaki iya yi musu, batare da kinji ko d'arrr a zuciyar ki,
kibar 'ya'yan gida su sakata su wala suyi yadda suke so, kada ki sake kice zaki takura musu akan wata agola tsintacciyar cikin ruwa aljana mai idon mayu."

Ta iso fuuu ta fizge hannayen su ta kad'a keyarsu ta ce
"Maza kuje ku sakata ku wala babu wanda ya isa ya takura muku ku da gidan uban ku,
wlh sai yarinyar nan tabar gidan nan, ba'a isa a takurawa 'ya'yan mu a kanta ba."

Murmushin takaici Aunty ta yi sannan ta ce
"Bazan tsaya bata bakina ina musayar yawu da wanda baisan girman ikon Allah ba, taho muje Feeryal mugun ji mugun gani Allah ya tsare mu da shi,
zaman gidan nan kuma yanzu kika fara sai dai bakinciki yakashe mai hassada,
duk wani yaron daya kuma tab'ata wlh sai na rama mata tun da abun ba mutunci."

"Kee ni zaki gwadawa Allah tun kan a haife ki nasan Allah, munafurcin banza,
ai munsan irin ku da yawa masu nuna kamar sunfi kowa tsoron Allah alhalin sunfi kowa tab'ara a bayan fage,
duk wani bita da kullen ki babu wanda ba'a sani ba,
kice wa malamin ki ya kasa, wlh sai ta bar gidan nan tun da ba na uban ta bane,
kada ki kuskura kice zaki tab'a mana 'ya'ya akan wannan aljanar idan kuma ba haka ba sai na sa sunyi mata dukan mutuwa a cikin gidan nan,
dan kin asirce miji baki isa ki asirce 'yan gida ba,
shima ki zuba ido ki gani alkadarin ki yana daf da karyewa, dani Karima kike zance Fatima."


Aunty bata kuma bi ta kanta ba, dan tasan Hajiya
Karima abin kunya gaba ta bashi ba baya ba,
ba mutunci gare ta ba sai ta iya warewa tace
zasuyi dambe, kamar 'yar bariki haka take.
ta janyo hannun d'iyarta suka kama hanya.

Direct bathroom d'in d'akin Feeryal d'in ta wuce ta da ita, ta tub'e mata kayan jikinta da ya yi
fusu-fusu, tayi mata wanka da ruwa mai zafi.
sai kuka take tana fad'in ciwo na mata zafi.
cike da tausayawa Aunty ta ruko ta suka fito.
ta saka mata wani kaya ta kwantar da ita a kan gado.
kan kace me jikin ta ya yi zafi rau sai rawar sanyi take zazzab'i mai zafi ya rufeta.
hankalin Aunty ya yi masifar tashi tarasa me
zatayi sai daga baya tunanin kiran Dr ya zo mata.
da kyar Feeryal ta tsaya akayi mata allura sai da
Aunty ta rirriketa, ya basu maganin da yazo da shi ta bata ta sha.
Dr ya yi musu salla Aunty tayi masa
godiya babu jimawa kuwa bacci ya yi gaba da ita.

Dr na fita Hajiya Safiyyah ta shigo da sallama,
Miemie na biye da ita suka shige d'akin Feeryal.
Aunty da ke zaune a bakin gadon Feeryal tana shafa katan.
ta amsa sallamar tana cewa
"Sannun ku da shigowa."
ta karaso bakin gadon ta zauna gefen Aunty tana duban Feeryal da bacci ya tafi da ita
"Ashe dai da gaske ne yanzun nan Miemie ta je take fad'a min wai su Ameerah sun taru sun bigi Feeryal,
kajimin shegun yarannan marata hankali,
ga yadda da suka sa jikin yariya duk ya yi ja."
Aunty tayi murmmushi ta ce
"Ai yarannan basu da hankali wai dan jiya an zane su, a makaranta sabo da sun bigeta shine suka rama a kanta."
"Ammah ai rannan ma sun bigeta har suka ji mata ciwo."
Miemie tayi maganar kamar zata zubda kwalla cike da tausayin Feeryal d'in.
Hajiya Safiyyah ta ce
"Idan suka bige ta ki rika rama mata, kinga jikinta ba irin naku bane, jikinta bazai yure azabar nan ba, bakiga duk ya yi ja ba,
in kuma sun taru duka bazaki iya da su ba, kiyi gudu kije ki kirawo wani babba ko a school d'in ne ma."
kai ta gyad'a tana cije baki alamun abin ya yi mata zafi.

Sun jima a sashin nasu kafin suka tafi.


Sai da Feeryal ta kwana uku tana zazzabi kafin ya sake ta.
kullum kuma Dr na zuwa duba ta.

A b'angaren su Ameerah ranar da zazzabi yasake Feeryal su kuma ya kamasu dukansu mai mugun bala'in zafi.
kowa na zaune a b'angaren iyayensa, sujaji tambar an tsikare su da kifiya ko allura a ciki, a tare duk suka zabura, suka rike cikin su.
musabbabin ciwon nasu ke nan.
hankalin iyayensu duk ya tashi, sai amai ta hanci ta baki.
wuni d'aya suka fed'e duk suka fita hayyacin su.
Ameerah Nabila Sahla ko iya tsayuwar kirki basa yi sabar zazzab'i.
a bujajan aka kirawo family Dr su
yazo.
side d'in su Ameerah ya fara zuwa,

Dr ya had'a ruwan allura a sirinji, ya ce wa Mommy ta gyara ta a mata allurar da zai d'an lafar musu da zazzabin kafin ayi musu test agano me ke damun su.
gaba d'aya Mommy ta rud'e autarta ba lafiya.
ta rike Ameerah Dr ya soka mata allura, kan allurar tana shigewa cikin jikinta, ji kake fass robar sirinjin ta fashe ruwan allurar ta watse,
da sauri ya yi kokari zaro allurar aiko ya ciro robar zalla allurar ta karye a jikinta.
Ameerah ta saki uban kara jin kamar ana dad'a nitsa mata allurar cikin jikinta.
hankali tashe Mommy ta ce
"Nashiga uku likita yi sauri ka cire mana."
da kyar likita ya samu ya zaro sa.
Ameerah sai ihu tana dafe da d'uwawunta.
kan kace me gurin ya tsunduma suntum.

Ya d'auko wani allurar yana kuma shirin mata tasa ihu, Mommy ta ce
"Gaskiya Dr a barta haka dubi fa kaga yadda gurin yanzu-yanzu har ya kunbura, aje kawai a taho mata da magani."
yaja jinin ta ya ce sai an mata test asan ciwon dake damin ta kafin a kawo mata magani.

Side d'in Umma Karima ya tafi, nan ma allura ya had'a yasa Umma karima ta rike Nabila
yasoka mata allurar,
yana matsa ruwan allurar da mamaki yake kallon sa. baya shiga jikinta a iya guri guda yake taruwa.
Nabila tashiga kurma ihu tana ji tamkar garwashi ake tura mata a dai-dai inda ruwan allurar ya tsaya.
haka ya zare allurar ruwan kuma na nan aguri guda bai bi jikinta ba, ita ko sai ihu take kurmawa.
itama ya d'auki jinin ta ya tafi.

A b'angaren su Hajiya Nafisat ma daya je yiwa Sahla nata allurar yana yi mata ruwan allurar ta tsiyaye kasa daga jikin ta, haka itama tarika kurma ihu.

Bakaramin damuwa da faruwar hakan Dr yashiga ba, yashiga yiwa kansa tambayar me ke damun sa ne yau.

bai kawo musu result d'in test d'in ba sai washegari da safe.
kafin wayewar gari kuwa dukkanin su d'uwawun su ya sussunduma, Ameerah da allura ya karye mata, dai-dai gurin ya d'ura ruwa ko zama bata iya yi.
Nabila kuma inda ruwan allurar ya taru, a hankali a hankali ya tsiyaye sai gurin yayi baki ya kuma yi rami.
Sahla kuma gefen kafar gaba d'aya ya yi tsami bata ko iya d'aga kafar.
Dr da iyayen su sun shiga matukar damuwa sosai.
result d'in kuma bai nuna suna d'auke da ko wani irin ciwoba ko maleriya da taipot basu da shi.
shi dai magani kawai ya kawo musu wan da zasuji d'an saukin abinda ke damun su.

Umma Karima ta ce itafa gaskiya bata yadda da ciwon nan nasu ba, an sa musu hannu ne kuma tana zargin mayyar yarinyar can Feeryal.
Mommy da Hajiya Nafisat duk suka haukan maganar nata suka zauna.
suka rika d'ebawa Feeryal albarka suka kuma ce wlh sai ta bar gidan,
dan ya'yan su basu tab'a ciwo azo ayi musu allura irin haka ta faru ba.
sai da Daddy yayi musu jan ido tukun.

Tsawon sati guda suka share suna ciwo ana shan magani kamar ba'a sha.
kullum abu sai gaba-gaba yake.
sai da suka cika kwanaki goma cur-cur kafin suka fara dawowa hayyacin su.

Makaranta kuwa Feeryal da Miemie kad'ai direba ke kaisu,
su Ameerah kam sai da sukayi sati biyu kafin suka fara tafiya makaranta.......!





Mommyn Twins ce








??/\??/\ *FEERYAL* ??/\??/\


*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*


( _Book 1_)


~Free page~


*____________________________________*

*???[???VAINUWA ???VRITER'SA??]Fq??*
*???VSSOCIATION??B惙?_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???a???_

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


??T???7



Har kuma yanzu jikin su bai gama dawowa normal ba,
suna nan dai da sauransu.
suna tafe a mota a hanyarsu na zuwa school, kamar ko da yaushe Feeryal na gaba su suna baya.
wata babbar titi gosule ya tare su.
Isa direba ya zuge gilashin gaba,sabo da yana yin zafi dukda kuwa AC da ke cikin motar.
da sauri aka zuge gilashin motar da ke gefen nasu.
sosai direbar motan yakura mata ido.
kamar ance ta juyo ai ko suka had'a ido.
murmushi ya sakar mata tare da d'aga mata hannu
"Hi Baby welcome to Nigeria."
murmushi ta masa.

Da d'an sauri ya b'alle marfin motar ya fito, yazo jikin motar su ta gefen da take.
ya mika hannu ta saman glashi ya ruko hannun ta.
fuska d'auke da murmushi cikin harshen turanci ya ce
"Ina Mama da Baba suke tare da su kuka zo, Nigeria akwai dad'i ko?."
nan ma murmushi tayi masa, taji abin da yake fad'a sai dai bata gane matufarsa ba.
caraf a kunnen Ameerah da sauri ta ce
"Ba daga wani kasa ta zo ba tsintarta akayi a.."
da sauri ta had'iye ragowar maganar jin yadda cikinta yawani tsikarar ta tamkar an tsikara mata kifiya.
gurin allurar ta da haryanzu bai gama warkewa ba taji kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login