Showing 63001 words to 66000 words out of 78516 words

Chapter 22 - FEERYAL Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.doc

hango police da ma'aikacin asibitin mai gidan sa.
ya bud'e karamar kofa yana rarraba ido da son jin ba'asin abin da ya kawo su tsohon daren nan.
Inspector Nasir ya ce
"Sannun ka da aiki, mun zo gurin mai gidan ne."
ido mai gadi ya gwalalo ya ce
"Yallab'oi Allah dai yasa lafiya, wlh shi kam ma yau ya shigo kasarnan yana can kasan turawa,
yana rayuwar shi babu ruwan shi da kowa."
"Bamu hanya dai yanzu mu wuce."
da sauri mai gadi ya matsa gefe.
suka shigo ciki Nasir ya dubi mai gadin yana fad'in
"Kayi mana sallama da shi yanzu dan Allah."
mai gadi ya isa da sauri jikin garun d'akin sa, in da wayar tafi da gidan ka take sakale a gurin.
ya daddanna ya kara a kunnen sa.

Aci kuwa nan take wayar ta soma kara ta karad'e cikin parlour.
yana kwance idanunsa a lumshe da sauri ya kai hannu ya toshe kunnuwan sa,
"Ya salam."
ya furta yana mikewa zaune.
kai ya dafe da hannunsa biyu, jin yadda kiran yake kuma shigowa babu kakkautawa.
ya mike a fusace ya fito parlour.
ya fincike wayar ya kai sa kunne cikin tsawa ya ce
"Kai wani irin hauka ne wannan zaka cika min kunne da kira!."
mai gadi ya durkusa kaman yana gaban sa ya ce
"Allah baka hakuri oga hankali na ne a tashe ganin police a tsohon daren nan wai yazo niman ka."
tsaki yaja ya saki wayar Allah ya kare bata isa kasa ba da sai dai wata ba dai ita ba,tana ririto ajikin igiyar ta.

Kugu ya rike tare da furzar da huci mai zafi daga bakin sa.
ya yi da na sanin zuwa kasar shi da ya gudo domin ya huta ashe wata musifar aikin zai kuma gamuwa da shi a nan.
a hankali ya ke takawa yana mammatse idanunsa da bacci yake cike tam a cikin su,
Allah ya sani ba karamin bacci yake ji ba.
ya isa in da takalman takawan cikin parlour'n suke ya zura d'aya a kafarsa ya fito da gajeren wandon jikin sa da singileti.
yana aikin jan tsaki fuskarsa a had'e kamar tun da yake bai tab'a dariya ba.
tun kan ya karaso in da suke Nasir yashiga takowa gare sa shima suka had'e a tsakiya.

I'd d'in sa ya ciro a aljuhu ya nuna masa yana fad'in
"Inspector Nasir B Suleja, barka da dare Dr Abdurrahim A.A FIYA."
Nasir ya mika masa hannu, da kyar ya miko masa nasa hannun suka gaisa.
Nasir ya gyara tsayuwar sa ya ce
"Nasan baka sanni ba, nima dai bana ce nasan ka a ido ba, amma ina jin sunan ka,
akwai kuma kyakkyawar alaka sakanin Alhajin ka da hukumar mu."
fuska ya dad'a had'ewa dan ya kosa da jin bayanan sa, katse Nasir ya yi da fad'in
"I'm okay me ya kawo nan?."
Nasir ya yi murmushi ya ce
"Dole zan sanar maka abin da ya kawo mu ai bayan gabatarwa,
kayi hakuri mun katse maka baccin ka,
dole ne yasa hakan, muma bamu samu mun rumtse ba cikin daren nan,
aikin mu da naka yana kamancece niya so dole bacci zai zamo mana short saboda taimakon al'ummar mu,
muna tafe da patient tana asibitin ka, amatsayin mu na jami'an tsaro mun sami nasarar kwato ta daga hannun 'yan tadaddan da suka saceta suke kokarin guduwa da ita,
mu munyi aikin mu saura naka,
kai kuma a matsayin ka na likita yanzu sauran aikin naka ne, tana bukatar taimako dan Allah kaje ka duba ta."

Fuska ya dad'a had'e wa, ina gashi nan kalar aikin da yakin aka matsa masa sai ya yi, shi kullum bashida lokacin kansa sai na mutane.
d'an baccin ma baza'a barshi ya yi ba.
juyawa ya yi yana kokarin barin gurin tare da fad'in
"Ku barta a gurin gobe Doctor's zasu shigo su duba ta."
da sauri Nasir ya sha gaban sa ya ce
"Haba kai kuwa yarinyar da take cikin halin mutuwa ko rayuwa, idan ka taimake ta kaima Allah zai dad'a taimakon ka, bata cikin hayyacin ta gaba d'aya please ka taimaketa dan Allah, daure dai muje ka duba ta,
ai duk irin aikin namu ke nan muna son baccin nan muke hakura da shi."

Gajeren tsaki yaja, kana ya zura hannayen sa cikin aljuhun gajeren wandon jikin sa, ya juya suka nufi kofa.
Nasir yana ta bashi baki har suka fice a gidan suka ketare titi suka shiga asibitin.

Ma'aikatan da suke kwana asibitin suna ganin sa kowa ya mike tsaye da kafafunsa, suna mika masa gaisuwa, ba wanda ya amsa gaisuwar sa ya wuce ICU Nasir na biye dashi.

Har lokacin Major Sadam yana tsaye da kafafunsa yana ta kai kawo cikin room d'in.
yana shiga room d'in ya zare hannayen sa daga aljihu ya nad'e su a kirji yaja ya tsaya.
inspector Nasir ya dube sa, ya yi murmushin gefen baki, a ransa yake fad'in
"Wannan fa d'an zafin kai ne, dube shi kamar wani boss yawani b'ata rai, ya juye tamkar shine sojan."
a fili kuwa cewa ya yi
"Yauwa Dr bari mu baka guri ka gudanar da aikin ka, Major muje ta waje ko."

Sadam ya watsa masa mugun kallo cikin kakkausar murya ya ce
"A kiraka kana wani ji da kai who are you! idan kayi wasa sai Kayi sallen kwad'o a nan,
yarinya tana cikin wani hali kazo ka duba ta,
kana gayawa mutane magana,
mu da muke hana idanun mu bacci domin baku tsaro bamu ce mun gaji ba sai kai ne zaka wani ce wai lokacin baccin ka ne,
kai dole ma na baka wani punishment idan ka gama dubata ka biyo ni office!."
wani kallo ya bisa da shi sannan ya ce
"Go ehead for the punishment in zaka iya,
ku d'auke ta ku fita da ita a nan bazan duba ta ba!."
a fusace Sadam ya bud'i baki zaiyi magana
Nasir ya yi saurin ruko hannunsa.
"Please Major barshi ya yi aikin sa dan Allah babu tima.
ya janyo Sadam dayake nuna Dr A.A Fiya da hannu yana fad'in
"Who are you be careful."
ya jashi suka fito dan yaga Dr nan ba sauki damasan sa sai wani bud'ewa suke babu tsoro ko d'igo a gare shi.
za'a iya yin ba dai-dai ba,
karshe ya nimo masu taya shi rabon fad'a dan bazai iya shi kad'ai da wannan murd'ad'd'en Dr ba.
duk da kuwa kasancewar sa hukuma shi da yake likita yafisu zubin kakkarfan zaratan jaruman maza.

Dogon tsaki yaja a fili ya furta
"See this guy mttss."
yakuma jan tsaki akan wata patient sun d'aga masa hankili sun hanashi bacci, daya sani ma da baizo kasar ba, shi da ya gudo yazo dan ya huta amma daga zuwan sa an wani takurawa rayuwarsa, shifa wannan aikin in da yasan yadda zaiyi ya yakace shi a gareshi daya kakkab'e shi,
domin babu komai cikin aikin sai takura a hana mutum sakewa da hutawa kullum mutum bashi da lokacin kansa sai na mutane,
da Daddy zai duba masa da ya barshi ya jingina aikin nan gefe baya son damuwa.
kwafa ya yi a fili.
tare da sauke idanunsa kan bed in da take kwance flat kamar babu rai a jikin ta, tana sanye da riga da wandon bacci.
a hankali yashiga d'aga kafarsa yana takowa inda take.........!





Mommyn Twins ce




??/\ *FEERYAL* ??/\




*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*




( _Book 1_)

~Free page~


( _Bismillahirrahmanurrahim_)




*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*


*____________________________________*

*???[???VAINUWA ???VRITER'SA??]Fq??*
*???VSSOCIATION??B惙?_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???a???_

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*




??T???19



Dipp! karar sautin bugun zuciyarsa dai-dai san da idanunsa ya sauka a kanta.
babu zato yaji bugun zuciyar da baisan musabbabin abin da ya haifar da shi ba.
da karfi ya rumtse idanunsa yana sauraran sautin bugun zuciyarsa.

"Why!."
ya furta a file sai kuma ya yi gajeren tsaki.
ya na bud'e idanun nasa,ya janye shi daga gareta ya matsa gefe, yasoma had'a abubuwan da zai yi mata amfani da su wajen bata taimakon gaggawa.
ya taho dasu bakin gadon.
tsayuwar sa ya gyara, a hanlali ya kamo tsinsiyar hannunta, da yatsunsa biyu kamar baya son tab'awa, idanunsa yana kan na'urar da yake ta kokarin saita shi.
2 seconds yana rike da hannun nata, tsaki ya ja sai kuma ya saki hannun,
ya dad'a matsowa yakai hannunsa ta saman wuyan rigar baccin jikinta yad'an jashi kasa,
ya saka yatsarsa a jikin jijiyar gefen wuyanta,
2 seconds nan ma yatsarsa yana gurin, kana ya janye.
ya d'an juyo ya dubi nurse d'in da ke tsaye a gefen sa ya ce
"Je ka kirasu suzo su d'auke ta ta mutu."
da sauri ya juya ya fita yaje ya sanar musu.
a razane duk suka mike suka had'a baki wajen fad'in
"What!."
Major Sadam da ya ji kansa na juyawa ya nufi kofar ICU Nasir na biye da shi.
ya tura kofar da karfi yana fad'in
"No bazai yuwu ace ta mutu ba! ya za'ayi kace ta mutu no bazai yuwu ba!."
gefe Dr A.A Fiya ya matsa yana zura hannayen sa cikin aljuhu, tare da mara baki ganin yadda Major Sadam yawani birkice ya yi kanta yana fad'in
"FEERYAL please ki tashi no bazai yuwu ace kin mutu ba!."
ya jijjiga hannunta yana kiran sunanta.
sai kuma yayi wani irin juyowa yana duban Dr A.A Fiya da jajayen ido
ya ce
"Kar ka sake kabari ta mutu, wlh idan ta mutu da kai da b'arayin can, tare zakuyi freezing sannan na harbe ku da kaina, kayi mata abin da zaisa ta tashi!."
Sadam ya fad'a da karfi yana jijjiga kafad'ar Dr A.A Fiya.
ture hannunsa ya yi daga kafad'arsa ya ce
"Kai ka dawo da ita mana kayi mata abinda zaisa tatashin,
ka d'auke ta ku fita min a asibiti ni na gama nawa sai kaje kayi yadda zata tashin a can waje."

Inspector Nasir ya matso da sauri yana fad'in
"Please let me know Dr da gaske ta mutu!?."
kafad'a ya d'aga kana ya ce
"Ina tunanin hakan."
da sauri Nasir ya rike hannunsa ya ce
"No! tunani kake, bai tabbata ba, ka taimaka ka sake gwadawa insha'allah zata tashi, aikin ka ne mu bamusan yadda zamuyi da ita ba, dan Allah Dr dan Allah ka taimaka dan Allah dan Allah please help."
ya jijjiga hannunsa yana magiya da rokon sa.
hannu ya d'aga musu yana jifan Major Sadam da mugun kallo kana ya ce
"Ku jira a waje."
Nasir yaja Sadam da sauri sukayi waje.

Gajeren tsaki yaja ya matsa bakin gadon,
ya rike kugu yana dad'a jan tsaki.
sannan a hankali ya kai hannunsa kan cikinta ya janye rigar baccin jikinta da yatsu biyu,
ta d'an sama har zuwa saman cibiyarta, yadda yake yi kamar mai tab'a wani abin kyama da baya son hannunsa ya tab'a.
ya d'au defibrillator yana had'asu, kana ya dad'a matsowa ya manna shi kan cikin ta.
da karfi ta zabura ta kuma komawa tana kokarin kuma shiga dogon suman.
yakuma manna mata sau biyu a jere tawani irin zabura da karfi tare da jan numfashi,
mai had'e da ihu a firgice ta yunkura ta fad'a jikinsa ta tsakalo wuyansa ta kankamesa da karfi tare da fasa kuka,
tana b'oye fuskarta cikin kirjinsa.
cikin fizgar munfashi mai nuni da zallar tsoro wanda a yanzu kwakwalwar ta ke tsaye cak baya nanata komai sai kasantuwarta da b'arayin nan.
cikin had'a kalomomi take fad'in
"Dan Allah.. ka..kayi hakuri kar..kar ka tafi da ni, ni bana sonka bazan aure ka ba."

A fusace ya fisgota da karfi ya cirota a kirjinsa ya turata kan bed d'in, ya yi saurin binta da allura ya dannan mata, ta saki wani uban kara jikinta na rawa.
zuwa can kuma a hankali tashiga sauke numfashi, a hankali a hankali nan da nan bacci ya tafi da ita.

Tsayuwarsa ya gyara tare da gyara zaman singilet d'in jikin sa da ta tukuikuye shi,
yawani had'e rai yana kumbura had'e da jan tsaki, kamar wacce take ganin sa,
a ransa yake fad'in
"Yar wannan abin wai take maganar aure msstt."
yaja tsaki had'e da yin kwafa,
duk ta gajiyar da shi ta makalkale masa wuya,
kwafa ya yi a fili.
kana nan da nan ya shiga bata taimakon gaggawa, yana yi yana jan gajeren tsaki da kaga yadda yake dai zakasan bawai da son ransa yake taimakon nata ba.
daga bisani ya d'aura mata drip had'e da ruwan allurai masu karfi da inganci.
yana gamawa kuwa ya juya bai kuma waiwayota ba ya yi gaba abinsa.
nurse yashiga kimsa abubuwan da yayi amfani da su.

Yana fita Major Sadam da Inspector Nasir suka mike suna son jin meke faruwa kuma yanzu.
Nasir ya ce
"Ka sami nasarar cito rayuwarta kuwa?."
"Kushiga ku duba."
yafad'a a takaice.
da sauri sukayi cikin room d'in, shiko yasa kai ya fice a asibitin.

Wani numfashi Major Sadam ya sauke ganinta a kwance tana numfashi, sai dai idanunta a fure da alama dai bacci take.
Nasir ya ce
"Alhamdulillah!."
nurse d'in dake ta kimsa gurin ya yi murmushi yana cewa
"Ai tun da Dr A.A Fiya ne ya fara jinyarta da kansa ai insha'allah zata tashi."

Sai a lokacin suka sami sukuni ganin ta farfad'o har ta sami bacci.
wajen karfe 3 da rabi na dare.
nan suka fita a asibitin bayan sun aje jami'an tsaro kewaye da asibitin.

A b'angaren su Hajja Umma kuwa, ranar sunga tashin hankali.
ga tashin hankalin sace FEERYAL ga karar harb'e-harben da ya birkita cikin unguwar kamr za'a tada unguwar da harbi. bayan lafawar tarzoman,
aka turo jami'an tsaro gidan, yadda sukaga rana haka sukaga dare kowa a zaune ya kwana cikin zullumi da fargaba.
duk da Inspector Nasir ya sanar musu sun kwato FEERYAL a hannun 'yan ta'addan nan sai dai a dame suke da son jin halin da take ciki, dan ya sanar musu tana asibiti.
fatan su dai Allah yasa ba harbinta akayi ko wani abun b'arayin sukayi mata ba.
a cikin daren Nasir yasanar musu ta farfad'o.
Abba ya ce zasuje su ganta, ya ce subari
gari ya waye tukun, tana cikin tsaro sosai a asibitin.

A b'angaren Dr A.A Fiya kuwa, yana komawa gidan sa.
ya fad'a bathroom ya yi wanka tare da d'auro al'waka ya zura jallabi, ya haye kan sallaya yasoma gabatar da sallar nafila,
har sai da aka kira sallar asuba kana ya fita zuwa masallaci.
bayan an idar ya gabatar da azkhar sannan ya nufo gida.
yana shiga bedroom d'in sa ya soma had'a kaya, ya janyo wayarsa ya daddannan kana ya kara a kunnensa.
ringing d'aya ana biyu a ka d'aga.
"Zo ka kaini airport 6:30 airplane zai tashi."
yana fad'in haka ya kashe wayar.
Dr Imran yabi wayar da kallo yana nanata kalmar da ya fad'a.
ya maida kiran nasa yana d'agawa Dr Imran ya ce
"A.A wai ina zakaje ne da asuba d'in nan?."
"Kana b'ata min lokaci kafito kazo ka kai ni ko na aje motar a can airport kazo ka d'auko ta."
ya kashe wayar.
da sauri Dr Imran ya mike yafito daga gidan kwanan likitoci, wan da shima d'aya ne daga cikin gidajen sa da suke cikin unguwar. likitoci ma'aikatan asibitin sa ne suke zaune a ciki.

Dr Imran na shiga gidan nasa ya hangosa a parking lot yana saka jakarsa cikin mota.
ya karaso da sauri ya iso gurin.
key'n motar ya jefawa Dr Imran kana yabud'e gaban motar ya shiga ya zauna yana fad'in
"Yi sauri muje time na tafiya."
Dr Imran yashiga mazaunin direba ya juyo yana duban sa.
"A.A wai ina zakaje ne shekaran jiya-jiyan nan fa ka shigo, ko zaka shiga Lagos ne kabari na shirya mu tafi tare mana."
"Germany zan koma kamar nafi samin bacci da hutu acan, na zo dan na huta amma jiya ko rumtsawa ba'a barni nayi ba, akan wata yarinyar da ma ba lallaine tayi raiba,
haka shikaran jiya ina sauka kuka wani barni da patent, ba gara na koma ba kawai."
baki Dr Imran ya bud'e da mamaki yake kallonsa, sannan ya ce
"Kayi hakuri ka bar tafiyar nan, shima can ai duk aikin ne idan ka koma,
ka dai sani patient zaman jiranka suke, suna sanin komawar ka kuwa zasu taho ganin ka, kuma dole ka duba su, kaga ba hutu ke nan can d'inma."
"Dan Allah muje."
yafad'a yana nuna masa hanya
Dr Imran ya girgiza kai ya yi wa motar key mai gadi ya bud'e suka fice a gidan.

A hanya Dr Imran ya yi ta bashi baki ko zai canza shawari ya hakura da tafiyar, amma sai ce wa ya yi, maganar Imran d'in ma karasa masa gajiya take, yabar cika masa kunne.
sanin halinsa yasa Dr Imran yin shiru, har suka isa airport suna isa kuwa baifi da minti 10 ba jirgi ta d'aga.
Dr Imran ya juyo gida.
tun daga kwanar shiga layin ya hango motar sojoji dana police a kofar asibitin su.
har zai wuce gida kafin ya yi shirin fitowa asibitin. sai kuma ya yi kwana ya shige asibitin dan son sanin me ke faruwa.
Major Sadam da Inspector Nasir da shigowarsu kenan yagani tsaye a parlour'n asibitin, suna tambayar nurse's har yanzu likitan bai zoba suma sauran likitocin basu fito?.
suna kokarin basu amsa Dr Imran ya shigo.
suka nuna shi suna cewa ga Dr d'aya ma ya shigo.
inspector Nasir ya dubi Dr Imran ya mika masa hannu suka gaisa kana ya ce
"Muna da patient a ciki jiya muka kawo ta da daddare, patient in Dr A.A Fiya ne, amma kamar bai shigo asibiti har yanzu ba ko?."
Dr Imran ya ce
"Eh bai shigo ba tukun, amma ta fard'o kuwa Jasin?."
ya karasa maganar yana duban nurse Jasin ya nufi ICU Nurse Jasin ya biyo bayansa yana fad'in
"Sir har yanzu tana bacci, akwai allurar bacci cikin drip d'in da ke shiga jikinta."
kai ya jinjina dai-dai san da suke shigewa cikin room d'in.

Har lokacin FEERYAL tana bacci.
tsayuwa suka yi a bakin gadon Dr Imran ya ware ido sosai a kanta yana kallon ta da yadda ruwan yake shiga a hankali sosai.
yana mai mamakin a ina suka samo ta, ko tana cikin masu kawowa Nigeria ziyara ce ciwo ya kamata.
Dr Imran ya dubi Jasin ya ce
"Ina fayel d'in ta d'uko system mu gani?."
nurse Jasin ya ce
"Ba'a bud'e fayel file ba."
kai ya jinjina a kasan ransa ya ke fad'in
"A.A ke nan 'yar da yake sawa mutuwa gata haryanzu tana numfashi, ai tun da ta fad'o hannunka da ikon Allah da sauran shanruwanta."
nan shima ya d'aura nashi aikin kan na Dr A.A Fiya.

Su Abba sun kasa nutsuwa har sai da suka taho asibitin, sai dai har lokacin da suka ison ma bata farkaba.

Tuni 'yan jaridu da gidajen TV dana radio harma da social media suka fara watsa labarai da rahotanni kan faruwal lamarin.
inda suke sanar da nasarar da jami'an tsaro suka samu kan kama 'yan ta'addan da aka jima ake farautarsu.
NTA ta fito da rahoton faruwar lamarin da yadda komai ya kasance.
ta bakin d'an jaridar da yake karanto

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login