Showing 42001 words to 45000 words out of 78516 words

Chapter 15 - FEERYAL Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheeda S Director.doc

Daddy ya dubi FEERYAL dake tsaye jikin ta yagama sanyi hawaye ya cika gold eyes d'inta sai walki suke kiris ya rage su zubo.
ya ce
"Zo muje."
ya yi gaba ta tabiyo bayan sa.

Babban parking lot suka je, ya bud'e kofar d'aya daga cikin motocin da suke jere a gurin,
ya dube ta tare da fad'in
"Shiga mutafi kar kiyi latti."
a hankali cikin sanyin jiki ta shiga motar ta zauna.
tana zama ya maida marfin ya rufe ya zaga gefen direba ya shiga yaja motar da gudu security suka bud'e masa get yayi waje.


Hajiya ko tana shiga sashin Daddy ta taras da kofar da zai sadata da ainahin cikin side d'in nasa a kulle.
ta juya ta fito tana sauke buhun masifa
"Duk in da kaje ma zaka dawo, wlh ko ni ko Fatima yau a gidan nan."

Da mamaki ta tsaya tana kallon in da ta bar FEERYAL wayam babu kowa.
sashin Aunty ta nufa tana zuba uban bala'i.
Aunty na ganin ta ta mike tsaye da sauri tana fad'in
"Barka da shigowa Hajiya ina kwana antashi lafiya."
"Rike gaisuwar ki babu ruwanki da na tashi lafiya ko ban tashi lafiya ba,
ni Fatima zaki ha'inta, ki aje min mugun gamasheka a gida tana cud'anya da jiko ki na,
a dire kika sami Abubakar da hakoran sa cur bakin sa,
bayan nagama wahala da shi, yazamo cikakken mutum ya tara dukiya masu yawa,
sai da ya had'a komai da komai kafin ya auro ki, baki san wahalar shi ko na dai-dai da miskala zarratan ba;
ki zab'a ko zaman auren ki ko rayuwa da aljanar da kika tsinto, dan wlh zaman ta a gidan nan yakawo karshe, ko ki fitar da ita a gidan nan kiyi zaman auren ki ko kuma ku tafi tare,
zan nuna miki ni na haifi Abubakar yau."
Hajiya ta juya fuuu tana cigaba da zuba bala'i kamar zatayi aron baki..

Sharaf Aunty ta zube kan kujera tana furta
"Allahumma'ajirnifimusibati."


Dama Hajiya yaya da masifa bare a bin nima ya samu.
sai da Dad da Abbieh suka taru sukayi ta bata hakuri.

Ajeemal kuwa bai bar school d'in su FEERYAL ba sai da aka taso su,
kasan cewar exams suke awa biyu sukayi a aji.
ya d'auko ta ya dawo da ita gida.

Aunty na ganin ta ta rungume ta,
FEERYAL ta saki kuka tana fad'in
"Ammie bakuwa mai duka zata dukine ni dai tsoro nake ji."
"Bazata duke ki ba kinji yi shiru muje ki cire uniform."
da kyar Aunty ta lallab'a ta suka shige d'aki.

Ajeemal kuwa na sauke FEERYAL side d'in Hajiya ya shige.
Hajiya na ganin sa ko zama bata bari ya yi ba.
ta ce
"Kai Ajimi uban naku har yanzu bai dawo?."
"Ke fa Hajiya kin fiye mita da yawa wlh, mutum yana marmarin ki dawo amma daga dawowar ki jiya-jiya kin addabi mutane da masifa,
wai waya ce miki yarimyar can aljana ce kam,
dan kawai tana da kyau da yawa sai ace ita aljana ce,
dan Allah ki kyale ta tayi zaman ta yarinyar nan is so silent babu ruwan ta da shiga rigima irin na yara,
inda mayya ce ko aljana da bata cinye mu tuntuni ba, ko ta shiga jikin namu kamar yadda kike fad'a,
haba dan Allah Hajiya ki bari Daddy ya sami ladar rike ta mana dan Allah,
yanzu idan kika kore ta ina zata je,
bata da iyayen da suka wuce Daddy da Aunty,
tun da bata san kowa nata ba,
dole mune dangin nata."
"Rufamin baki sokon banza, tun da kake ka tab'a ganin mutum kyakkyawa irin ta, ko a kasashen turawan nan d'ai-d'ai ku ne masu kalar ta;
'yar da aka tsinta cikin ruwa, me yakai jariri cikin ruwa in ba d'iyar mutanen cikin ruwan ba,
aljanun ruwa kyawawa ne tun zamanin iyaye da kakanni ake fad'ar irin kyan su,
me ka sani rufa min baki dall,
tashi maza ka je ka kira min uban ka."

Kafad'a ya d'aga ya mike yana fad'in
"Sai dai in zaki bishi in da yaje dan Daddy baya kasar nan ma."
ya yi waje a bin sa ya barta nan tana ta bombomi,
har sai da ta tashi Hajiya Bishira a bacci.
Hajiya Bishira ta fito tana tambayar ta meke faruwa
cikin masifa Hajiya take fad'in
"Maza kira min Abubakar a waya, duk in da yake ya dawo yazo ya fita da aljanar can, ko nasa direba ya d'auke ta ya fidda ita yaje can ya yasheta."
"Yi hakuri Hajiya adai bari ya dawo tukun."
"Bazan bari ba yanzun nan nake so na nunawa Fatima na isa da Abubakar, ba ita kad'ai ta isa ta rika juyashi yadda take so ba."

Hajiya Bishira ta girgiza kai ta d'aga waya ta kira lambar Daddy,
sai da kiran yakusa yankewa kafin ya d'aga.
daga cikin wayar Daddy ya ce
"Bishira yanzun nan na sauka a jirgi ina airport bari na isa masauki tukun."
"To Yaya dama Hajiya ce ta ce na kira ka."
daga in da Hajiya ke tsaye tana juyo sa kasancewar a handsfree ta saka kiran.
Hajiya ta bud'e murya tana fad'en
"In na isa da kai yanzu-yanzun nan kadawo ka d'auki aljanar da ka aje ka fita da ita a gidan nan,
ko nasa direba yaje ya yasheta cikin kwalbati tabi ruwa ta koma gurin dangin ta."

Da sauri Daddy ya ce
"Kiyi hakuri Hajiya kar ki sa wani ya fidda ita idan na dawo zan d'auketa na maida ita in da muka d'auko ta."

"Na dai gaya maka in ba so kake ka had'u da mummunar b'acin raina ba."

Hajiya Bishira ta kashe wayar tana cewa
"Kibari ya dawo dan Allah Hajiya."

"Yoo in bai dawo kan lokaci bama ni nasan yadda zanyi ai, sai dai ya dawo ya samu na kaita cikin ruwa gun dan gin ta,
ke Kulu zumo min nama mai d'an ruwa-ruwa da kashi mai laushi."
Hajiya ta fad'a tana duban Kulu........!







Mommyn Twinc ce


??/\??/\ *FEERYAL* ??/\??/\


*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*


( _Book 1_)


*~Free page~*



*_Littafin na kud'i ne 500 account no 3170524141 Rashida Salihu first bank ka-ki tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_*

*____________________________________*

*???[???VAINUWA ???VRITER'SA??]Fq??*
*???VSSOCIATION??B惙?_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*???a???_

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*





??T???13






Hajiya na hakimce a kan kujera tana warb'ar ferfesun naman ragon da Kulu ta zubo mata.
Umma Karima ta shigo,
dan labari ya kai mata Hajiya ta ta da bori sai Feeryal tabar gidan.
shine tazo karawa wuta fetur.
karaso cikin parlour'n ta zauna kan kujera tana fad'in
"Ina kwana Hajiya."
Hajiya data kai loman nama baki ta amsa da kai, sai da ta gama taune naman ta had'iye, tabi Umma Karima da kallo.
Umma Karima ta dad'a sake jiki tana marairaice fuska irin yadda marasa lafiya sukeyi.
"Ke karimatu lafiyar ki kuwa, yanaga duk jikin ki ya sake haka?."

Baki ta karkata cikin iya makirci ta ce
"Ina kuwa lafiya Hajiya muna tare da annoba cikin gida,
wlh Hajiya kullum na kwanta bacci da wahalallen mugun ciwo nake tashi,
kullum da kalar razanennen mafarkin da nake akan yarinyar can Feeryal,
yaukam ma abin ya yi muni babu ko da d'in fad'a,
wlh hajiya jikina ya yi mugun sanyi da lamarin."
Hajiya ta waro ido ta ce
"Ai ni tun da ganin yarinyar nan nasan ba karamar gaggaruma bace, wani abu kika gani tana yi ko?.
Umma Karima ta karkata baki
cikin kwarewa a tsalon makirci ta ce
"Wlh Hajiya abun ya munana, har bana son fad'a,
ke nagani cikin mafarki da ita tana binki kina gudu sai da ta turaki cikin wani katon rami kafin ta juyo kai na,
dama jiya sai da Nabila ta ce min ta ganta cikin mafarki tana binta da wuka zata yanka ta,
wlh yarinyar nan barazana ce ga rayuwar mu,
nakasa sukuni ne gara kawai nazo na sanar miki kisan irin zaman da zakiyi da ita."

Hajiya ta gwalalo ido ta buga kirji
"Da wa zan san irin zaman da zanyi da ita,
ai ni da ita hayatan-hayatan, basai ta kuma kwana cikin gidan nan ba kafin ta sami damar bin kurwan mutane cikin dare,
a yau d'in nan zata bar gidan nan bata kuma kwana."
"Ato gara dai dan wannan babbar annoba ce, idan tafi haka a gidan nan ba'a san iya barnar da zatayi ba,
Hajiya
ga wannan hayaki ne na ruko miki,
in zaki kwanta sai kiyi, nima jiya ne nasa aka kawo min, na mance banyi ba na kwanta ai kuwa nasha wuya cikin bacci,
bana kuma kwanci batare da nayi duk da yaran ba."

Hajiya ta amsa tana cewa
"Ai ko nagode zan ajiye maganin wata rana zaiyi amfani,
amma yau kam bata kuma kwanan gidan nan,
bare ma tazo min cikin bacci."

Sai da Umma Karima ta tabbatar da munafurcin ta ya ginu kafin ta tattara ta koma sashin ta.


Hajiya tayi ta zuba ido ganin dawowar Daddy amma shiru har dare.
ta d'agawa Hajiya Bishira hankali sai ta kira mata shi, aka kuwa yi rashin sa'a wayarshi a kashe.
zo kaga masifa gurin hajiya.
tana fa d'in
"Wlh yau sai ta bar gidan nan a daren nan."
Hajiyq Bishira ta ce
"Hajiya bakya jin tsiro idan kuma aljanar ce da gaske ranta ya b'aci tayi miki wani abin fa."
"Ashsha ke kike tsoron aljani, ai idan kika nuna kina jin tsoron su shine ma suke samin garab'asar yi miki tsiya, ai ba'a nuna a na jin tsoron su,
tun kana yara kake gwagwarmaya da su, ni da natab'a kawance ma da aljana tun muna yara,
ai dana gano ta
nayi mata dukan tsiya sai da ta b'ace."
Hajiya Bishira ta girgiza kai.

Hajiya kota d'auki kafa tayi sashin Aunty dan taci alwashin yau fa Feeryal bazata kwana gidan nan ba.
tarika bubbuga jikin get d'in sashin Aunty,
mai ganin get d'in ya bud'e.
jiyo muryar Hajiya ce.
ta shige ciki da sauri ta isa jikin kofar parlour tarika bubbugawa.
Aunty ta taso ta bud'e, ga nin Hajiya ce tashiga yi mata sannu.
ko amsata batayi ba ta bangaje ta tayi cikin parlour'n
"Ina kike tsintacciyar mage fito nan tun da ba gidan ubanki bane, zo ki koma in da kika fito."

Aunty ta durkusa gaban Hajiya ta had'a hannaye biyu tashiga magiya da rokon ta
"Dan girman Allah Hajiya kiyi hakuri, idan ta fita a daren nan ina zata je,
bata san kowa ba sai mu, kiyi hakuri dan Allah Hajiya gari ya waye."
"Bafa zan bari takara ko da kwana d'aya ne a gidan nan ba, bari ma ki gani naje na taso direba yazo ya d'au keta ya fita da ita, can takataci tsiyar ta a can."

ta juya ta yi waje fuuu.
tana fita Aunty ta d'aga waya ta danna lambar Daddy wan da ita kad'ai take da shi a gidan,
idan duk ya kashe sauran wayoyin sa baya tab'a kashe waya mai d'auke da wannan layin, da yanzu take kira.

Feeryal da har tafara bacci tajiyo hayani, ta mike ta fito.
tsayuwa tayi tana kallon Aunty dake tsaye cikin parlour tana hawaye.
da gudu ta karaso inda take ta rungume ta itama ta saki kuka
tana fad'in
"Ammie bakuwa mai duka ne tazo ai naji maganar ta, Ammie tare zamu tafi ni dai bazan tafi na barki ba."

Bubbuga bayanta ta shiga yi tana fad'in
"Yi hakuri yi shiru Feeryal, babu in da zaki je,
kafata kafar ki duk in da zaki shiga ina gun, sai dai mu bar gidan tare tun da ba gidan aljanna ba ce."

"Kada b'acin rai yasa ki fad'in haka,
shin kin mance anan gidan zaki nimi aljannar taki iye Fad'imatu."
maganar Daddy daga cikin wayar dake rike a hannunta wacce ta ma mance da ta kirasa har yama d'aga yana sauraron su,
yayin da yake jin zafi mai gauraye da d'aci a duk fitar sautin kukan su.
Daddy yaci gaba da fad'in
"Hajiya ce ko? kuyi hakuri uwace a gare mu babu yadda muka iya da ita, yazama wajibi muyi mata biyayya amatsayin ta na uwa,
Fad'imatu lallai yau nasan an kure ki har bango, tun da naji fitar kalmar nan daga bakin ki,
kiyi hakuri har na dawo zan yi wa tufkar hanci."

Yana kaiwa nan ya katse kiran.

Ya kunna d'aya daga cikin wayoyinsa.

Lambar Hajiya Bishira ya kira, ya ce ta bawa Hajiya wayar, yakira wayarta bata d'aga ba.
Hajiya Bishira ta shaida masa Hajiya ta fita, taje side d'in Aunty, ya ce
tayi sauri ta kai mata wayar.

Hajiya Bishira na fita can ta hango Hajiya kofar d'akin direbobin gidan, tana bokarin buga musu kofa.

Murya ta d'aga ta dakatar da ita daga bugun kofar nasu.
da sauri ta karaso ta mika mata wayar tana fad'in
"Gashi Yaya na magana."
ta karb'i wayar ta kai kunne tana ce wa
"Ka gama abin da kaje yi tsaf abin ka, bama sai ka dawo ba, yanzu nazo d'aga direba ne ya fita da ita."
"Hajiya kiyi hakuri na dawo tukun ni da kai na zan fita da ita nayi miki alkawari."

Da kyar Daddy ya shawo kan Hajiya akan idan ya dawo zai d'auki Feeryal d'in ya mai da ita in da suka d'auko ta.

Washegari kuwa da zasu tafi makaranta, Hajiya ta fito ta tsare ta ce Feeryal bata isa ta shiga moto d'aya da jikonkin ta ba.
Feeryal ta d'an kalleta a tsorace dan ba karamin tsoron matar take ji ba,
tun da aka ce mata tana duka, Feeryal kuwa ba karamin tsoron duka ta ke ba.

Hajiya ta buga mata wani uban tsawa
"Daina kallo na da wad'annan idanun naki masu kama da na mayu, da jan fuska kamar nunannen gwanda,
anya wannan yarinyar, ta ya za'ayi a ce mutum ce ma, habawa wannan irin kyau haka hankali bazai d'auka ba, wasayyahuuu ya tsaya a kanki li'eeelafi aniya bi aniya, nafi karfin ki da jikoki na."

Feeryal tayi kasa da kai tana kyafkyafta ido zatayi kuka.
ta zuba mata rankwashi a kai
"Munafuka wuce ki bar nan kar ki shafa mana annoba."
ba zato taji saukar rankwashi a ka.
a birkice ta saka hannu tana yamutsa kan, nan da nan idanun ta suka shiga tsiyayar da kwalla.

Hajiya ta kad'a keyar jikokin ta suka shiga mota direba ya ja su suka tafi.
ta juya tana bin Feeryal da harara
"Ai ke da shiga motar nan sai dai ki ganshi da ido mayya mai zubin aljanu, sai ki taka a kafa kije makarantar."
ta wuce ta barta nan tsaye.
tazo daf zata shige side d'in ta kafarta ya hard'e.
ki kake shirimm ta zube kasa kan gwuiwowinta.

Kururuwa mai had'e da salati Hajiya ta sake, tana fad'in
"Wayyo jama'a kuzo kafata, shike nan kafar ta b'alle
yafita, jama'a kuzo jama'a kuzo!."

Feeryal tayi saurin kai hannu ta toshe bakinta da dariya ke son kwace mata, ga kuma tsiraren hawaye a kan kyakkyawar fuskanta.
tana kallon inda Hajiya ke zube, sai kuma ta girgiza kanta.
da alama dai magana take da kai.

A guje security suka taho, Ajeemal Shamsuddin Zaraddin Faisal da suka fito zasu tafi school, suka karaso a guje.
kowa na tambayar yaya me ya faru lafiya?.

Hajiya takuma wage baki tana fad'in
"Ku kirawo mai d'auri na karye wayyo Allah na shike nan nazama gurguwa."

Ciccib'arta sukayi suka shige da ita parlour'n ta.
dan sunga alamun da gaske ko tsayuwa bazata iya ba bare ma tafi.
Dad da Abbieh ne suka shigo hankali tashe.
nan da nan suka kirawo mai d'auri.

Sai a lokacin su Ajeemal suka fito dan in suka dad'a b'ata lokaci zasu makara.

Har lokacin Feeryal tana tsaye a gurin har suka karaso inda take,
tun kan su iso Zaraddin yakafe ta da ido, sai da ya iso daf da ita kafin yawani lumshe ido yaja numfashi kana ya fesar tare da kuma bud'e su a kanta.
murmushi Shamsuddin ya mata yana cewa
"Badai latti kika yi ba Feeryal?."
kai ta girgiza.
Faisal kuwa cewa ya yi
"Shine Miemie bataje ta kira ki ba suka tafi, suka bar ki."
nan ma shiru tayi tana wasa da 'yan yatsunta.

Ajeemal kuwa da ke da tabbacin Hajiya ce zata iya hanata tafiya kamar jiya ya ce
"Zo muje mu sauke ki sai mu wuce."

Suka karasa parking lot, Zaraddin ya yi saurin bud'e gidan baya ya shiga yana fad'in
"Shigo nan ki zauna."
"A'a dawo gaba ku ku zauna a baya."
Ajeemal ya fad'a yana bud'e mata gaban motar, fuska a d'aure, dan tun d'azu ya lura da yanayin sa tun da ya ganta.
tana zama ya rufe ya zaga ya shiga mazaunin direba suma suka shiga yaja motar suka bar gidan.

Sai da suka sauke ta a school d'in su sannan suma suka wuce nasu school d'in.

A gida kuwa maid'auri yazo ya duba kafar Hajiya,
ya ga gwuiwar ta ce ta goce, da kyar aka mayar aka shafa mata magani, Hajiya tayi shame-shame tana sallallami.
mutan gida sai shigowa suke ana gaidata.
dangi na kusa ma tuni sunzazzo.


Satin Hajiya guda ke nan tana zaune tana jinyar kafa,
har kuma yanzu Daddy bai dawo ba yana can kasar China,yana gudanar da wasu harkokin sa.
sai dai kullum suna video call yana ganin yanayin jikin nata.
duk da cuwon dake jikin Hajiya baisa ta saduda ba,
tana daga zaune tana bada umurni da oda.
haka ta kekashe kasa ta hana a rika d'aukar Feeryal a motar kaisu school, takuma sa dole Daddy ya canza musu wata mota yana can kasar bai dawo ba,
a cewar ta wai akwai abu a ciki tun da Feeryal ta shiga.

Ajeemal ne ke kai ta school a motar sa, wani lokacin ya jirata har su tashi idan bashi da abin da zaiyi, wani lokacin kuma ya ajeta yaje ya dawo ya d'auke ta.
baya tab'a bari Zaraddin ya kaita ko ya d'aukota, ko baya da lokaci, yakan iya kashe damuwar sa wajen kaita da d'auko ta,
sau d'aya yatab'a sa Shamsuddin da Faisal suka tab'a d'aukota, ranar d'in ma yana class ne bai fito ba, dan su yana da d'an tabbacin nutsuwa tare da su.

Aunty na kichin tana aiki Feeryal da ta dawo daga school ta shigo.
ta fad'a jikin ta,
Aunty tayi murmushi ta rungume ta tana fad'in
"Oyoyo 'yanmatan Ammie, an dawo ya school?."
d'an karamin bakin ta ta cuno cikin tsiririyar muryarta mai fita da yanayin shagwab'a ta ce
"Ammie wai ba ke kika haife ni ba?."
hannu takai ta toshe bakin ta,
sannan ta waro ido ta ce
"Inji wa? ni na haife ki Feeryal duk wanda ya fad'a miki yafad'a ne kawai, kar ki yadda ki sawa ranki hakan,
to idan ba ni na gaife ki ba to waya haife ki, ko akwai wata mamarki ce a gidan nan?."
kai ta girzaza tana kallon fuskar Aunty.
kumatun ta taja ta ce
"Ko in kaiki gurin wata ce tazamo mamarki tun da kin gaji da ni."
da sauri ta fad'a jikin ta tana cewa
"O'o Ammie ni dai bazanje ba."
dariya Aunty taji ta dad'a rungume ta tana jin kaunarta cikin zuciyar ta.
baki ta kuma cunowa ta ce
"Basu Ameerah bace suke fad'a, wai ke ba ce mamata ba ce kuma Daddy ma ba babana bane, wai ni mayyar aljana ce."
da sauri Aunty ta ce
"Karya suke ni ce nan mamarki Daddy kuma baban ki, kar ki sake biye musu,
oya je ki cire uniform kiyi wanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login