Showing 1 words to 3000 words out of 29888 words
Chapter 1 - Wani Al'amarin Compelet Hausa Novels By Real Shamtr.pdf
COMPILED BY
Abubakar Saleh Quyraemey Ne Mutumin ku
Admin @Top Hausa Novels
What@PP No: 08138873799
@Facebook Group: Qurami Hausa Novel Group
For more novel u can contact me with low price
[7:18AM, 6/11/2019] Itz Ibraheem: í ½í² í ½í² í ½í² í ½í² í ½í²
*AWESOME WRITER'S ASSO..í ¼í¿®*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
 *WANI AL'AMARIN..!*í ½í²¥
*(Book 2)*
í ½í²£í ½í²£
í ½í²¥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا .ميØ
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Tak'abalalla minna wa-minkum...*
_Happy Eid-el'fid'r to u and ur family may Allah accept our du'a and may he forgive our
sin's,may we live to witness more with sound health and wealth...Ameen_
___________________
*BOOK 2. í ½í³“*
*Pg 1.*
^^^^^^^^
Wani irin mugun juyi yayi wanda ya haddasa masa komawa gefe guda ya kwanta yana
curewa guri d'aya tamkar kayan wankin da suke jiran mawankin da zai fiddasu daga k'angin
daud'ar da suka fad'a,mararsa ya damk'e saboda tsananin ciwon da take masa a daidai
lokacin,wanda cikin k'ank'anin lokaci yasa shi manta a inda yake dama duniyar da yake ciki,a
hankali bakinsa ya soma motsawa cikin rauni ya shiga kiran sunan YASEER,wanda a iya
hasashen da nayi nake da tabbacin tsakaninsa da shi tuni duniyoyinsu suka jima da yiwa juna
bankwana,haka zalika a wannan lokaci kam na tabbata babu ta yadda za ayi ya iya sanin halin
da d'an uwan nasa yake ciki.
Gareta kuwa itama sajidar ba'a barta a baya ba,dan tunda taji yarima ya mirgina gefenta ya
kwanta yana sakin wani irin numfashi ta runtse idanunta cikin wani irin mawuyacin hali itama ta
shiga sauke numfashin wahala,sai dai ko da jin muryar Yariman sanda yake kan kiran YASEER
bata fita sosai,da kuma jin sunan wanda yake kira,tuni hakan yasa tayi hanzarin bud'e kulallun
idanunta da suka mata nauyi ta juya gare shi tana zubasu a kansa,koda tayi arba da halin da
yake ciki,ai take ba tare data tsaya tunani ko jinkiri kan halin da take ciki ba ta matsa inda yake
tana tallafo kansa,cikin kid'imewa take jifansa da tambayoyin da bata san suna fita daga bakin
nata ba
"Yah Prince what's going wrong..?? Are u alright...??"
Duk tambayoyin tana yi masa sune amma ba tare da tana cikin nutsuwarta ba,haka sai
duddubawa take duk dan ta gano inda matsalar take,sai dai da yake ba b'angaren ta bane
hakan yasa ta gagara ganowa.Cikin muryan majinyata yake mata alama da hannu kan ta kira
masa YASEER a waya ta sanar da shi yana nemansa,saurin amsa masa tayi sannan ta ja masa
blanket ta rufeshi kana ta sauka a kan bed d'in,wayansa ta d'auko ta shiga neman line YASEER
amma ina ko labarin zata same shi babu dan tana kira baturiyar nan ta company ta shiga sanar
da ita wayan nasa na a kashe,wani mugun tsaki ta saki mai had'e da furzar da zazzafar iska,ta
gwada kiran lines d'insa yafi a k'irga amma duka babu wanda ta samu,ko da ganin haka sai ta
yanke shawaran fita da kanta zuwa side d'insu YASEER d'in,dan yadda taga yana sake
galabaita wannan ne kad'ai hanyar da take ganin za'a samu sassauci idan har ta samu damar
yin arba da YASEER d'in,wannan tunanin shi ya bata k'warin guiwar daya sata d'auko riganta
doguwa har k'asa ta saka sannan ta zari slippers da hijab d'inta ta fita,tafiya kawai take ita d'aya
ta kama hanyan apartment d'in amma ko k'waro bata had'u da shi ba bare mutum duk kuwa da
yadda gidan yake cike da masu tsaro,a bakin k'ofar apartment d'in ta tsaya ta shiga knocking,ta
d'an d'auki lokaci kafin aka bud'e k'ofar,YASEER ne da kansa ya bud'e k'ofar,ko da ganinta a irin
wannan lokacin take ya fahimci ba lafiya ba,dan haka bai yi jinkiri ba wajen jifanta da tambayar
"Sajida lafiya..?? Na ganki a irin wannan lokacin..?? Me yake faruwa..??"
Hawayen daya ziraro mata tasa bayan hannu ta goge ko kafin ta bashi amsa tuni har yayi
gaba ya barta a nan a tsaye dan ya gama fahimta a kwai damuwa,sanda ta juya kuwa da
niyyan yi masa magana tuni ta hango shi har yayi nisa,a baya ta biyo shi cikin sauri,dan sai
lokacin nema ta fara jin tsoron fitowa da tayi a irin wannan talatainin daren,sauri ta k'ara duk
dan ta tarar da shi amma duk da haka bata iya tarar da shi d'inba,sai data shiga apartment d'in
nasu sannan ta ganshi tsaye a parlor ya goya hannayensa a baya yana safa da marwa
"Yana ina ne.???"
Ya tambaya dan yadda zuciyarsa ta gama bayyana masa matsala tana tattare da d'an uwan
nasa,ba tare data bashi amsa ba ta wuce gaba,nan yayi saurin biyo bayanta zuwa cikin
bedroom d'in,can a saman bed ya hangoshi ya cukuikuye sai numfarfashi yake kamar na
mutumin da yake gargarar mutuwa,saurin nufarsa yayi yana kiran sunansa,Yarima kuwa ko da
ya jiyo muryar mutumin da dama shi yake da buk'atan gani nan ya shiga k'ok'arin bud'e
nauyayyun idanunsa masu cike da tsabar ciwo,sannu YASEER ya fara jera masa kafin ya kalli
sajidar dake rab'e daga gefe guda yana jikanta da tambayar
"Me yake damunsa..??"
Bata iya bashi amsa ba saboda yadda takemin nauyin abunda zata ce ya faru,yadda ta
sunkuyar da kai k'asa ya sashi kallon yarima sannan ya furta
"Kawomin lime da sauri.."
Ya bata umarnin ba tare daya kalleta ba,fita tayi da saurinta har tana yi kamar zata fad'i k'asa
dan saurin da take yi,YASEER ne ya zauna daga gefen Yarima yana kallonsa kafin ya jefo
masa tambayar
"Akwai inda yake maka ciwo ne..??"
Da hannu ya masa nuni ba tare daya iya furtawa ba,yana shirin sake tambayarsa sajida ta
shigo hannunta d'auke da cup mai cike da ruwan lime juice,hannu ya mik'a ya karb'a sannan ya
ajiye ya matsa kusa da Yarima ya d'an d'ago shi,sai daya tabbatar ya shanye duk iya yadda
yake matsar fuska sannan ya rabu dashi,ba'a wani d'auki lokaci mai tsayi ba gumi ya fara yanko
masa,ya jima a wannan halin duk da irin sanyin da d'akin yake d'auke da shi sannan ya iya
zama sosai har yana jingina bayansa ajikin bed d'in yana sauke numfashin wahala,sannu suka
shiga jera masa kafin daga bisani YASEER en bayan ya tabbatar da komai lafiya yayi musu
sallama ya tafi,bayansa tabi da niyyar ta rufe apartment d'in sannan ta dawo lokacin kuwa tana
dawowa ta tarar da d'akin wayam babu Yarima bare dalilin sa,bakin bed ta zauna zuciyarta cike
da tunanin abunda ke faruwa,ta jima zaune tana tunane² sannan ta tashi ta cire hijab d'in data
sa da rigan sannan ta nemi guri ta kwanta,zuciyarta da tunanin dawowar Yariman.
Lokacin da suka fita kuwa a gefen Yarima tsam yayi ya mik'e ya fice a d'akin,direct bai tsaya
ko ina ba sai bedroom d'insa,yana zuwa kuwa ya nufi toilet had'e da sakarwa jikinsa ruwa mai
sanyi,yadda ruwan yake ratsashi haka kasala ke dad'a rufeshi,ji yake a lokacin banda kwanciya
babu abunda yake buk'atan yi,towel ya d'aura yana fitowa kuwa ya nufi closest ya cire wasu
pajamas d'in masu kalar sararin samaniya,bayan daya shirya kuwa nan ya haye saman royal
bed d'insa yayi kwanciyar sa,bai jima da kwanciyar ba kuwa bacci mai nauyin gaske yayi gaba
da shi cike da mafarkai..
^^^^^
Lokacin da Adda tazo k'arshe a labarin da take bawa Aisha dangane da lak'arsu da ROYAL
PALACE kuwa,ko da suka gama tattaunawa sai Adda'n tayi mata sallama akan zata tafi ta
kwanta saboda ganin dare daya soma nisa,ga Aisha kuwa a lokacin ji tayi sam bata so ace
lokacin ya zo a haka ba,dan yadda ta so ace Adda ta labarta mata har asalinta,la'alla ta san
asalinta da inda iyayenta suke,duk da dai ta fara jin k'ishin² d'in inda asalintan ya fito,ma'ana dai
ba iyayenta ne suka bada ita ba kamar yadda ladidi ta fara sanar mata tun a wancan lokacin
daya gabata,ta dai yi mata k'arya ne da hakan ba don komai ba sai don wani k'udiri nata,hak'uri
ta bawa ranta amma ba don taso hakan ba,a son ranta kam taso ace suyi ta zama da Adda har
sai taji k'arshen labarin,sallamar itama tayiwa Adda sannan kowanne a cikinsu ya kama hanyar
bedroom d'in sa.
Lokacin da Aisha ta tabbatar ta shiga d'aki kayan jikinta ta fara ragewa sannan ta nufi
toilet,ruwa ta tara a kwamin wankan sannan ta zuba turaruka masu sanyin dad'i da tasan zasu
taimaka wajen rage mata rad'ad'in da zuciyarta keyi a lokacin a dalilin rashin sanin madafa da
sanin takamaiman inda ya kamata ta fara dosa dan binciken mahaifanta. Kwanciya tayi cikin ruwan yayin da damuwa ke dad'a saukar mata,ta jima a wannan halin
kafin ta iya yin wankan ta fito zuciya da gangar jiki duka babu dad'i.Fitowarta babu jimawa tayi
shirin kwanciya sannan ta haye bed tana lumshe idanunta wanda suke cike da bacci da
gajiya,haka zalika masu d'auke da tsantsar damuwa.
^^^^^
Washe gari tun da sanyin safiya bayan da Yarima ya gama shirinsa,babu wanda ya sanarwa
da tafiyarsa ya fice a gidan,dan tun daya fita sallah bai bari ya dawo ba ya nufi airport,bai tsaya
bin takan emirate flight ba yayi bucking flight mai zuwa abuja a safiyar,wajejen 8:00am jirginsu
ya d'aga sai birnin tarayya,gidan da aka mallaka musu ya nufa,da zuwansa kuwa ya baje a
parlor take wani baccin yayi gaba da shi.Sai daya shafe ak'alla awanni biyu yana baccin gajiya
kafin ya farka,fuskarnan a had'e kamar ba ta sabon ango ba,haka yaci gaba da gudanar da
al'amuransa ba tare da wani damuwa ba ko tunanin neman wani cikin ahalinsa ciki kuwa harda
aminin nasa wato YASEER.
Can kuwa a Kano lokacin da gari ya gama wayewa,Sajida ta fito daga bedroom d'inta ciki
kwalliya,lokacin data nufo cikin parlor da niyyar zama sai akayi knocking,fasawa tayi sannan ta
nufi bakin k'ofa da niyyar ganin ko waye,bud'e k'ofar keda wuya tayi arba da matashiyar sanye
cikin bak'ak'en kaya hatta kuwa da fuskarta,tsayyawa tayi kawai tana nazarinta har na wucewar
wasu sa'o'i kafin cikin isa ta furta
"Daga ina baiwar Allah..??"
Itanma cikin wani yanayi mai kama dana nuna halin ko in kula da halin da mai maganar yake ta
furta
"Sak'o ne na kawo daga gurin Fulani.."
Kallonta sajida ta sake yi sosai kafin ta matsa ta bata hanya tana sake binta da kallon
mamaki,wucewa matashiyar tayi zuwa ciki ta nufi dinning area ta ajiye kayan dake hannunta,sai
data ajiye basket d'in sannan ta kama hanyar fita ba tare da tayi wata maganar ba,har ta kusa
da k'ofar fita sajida ta d'an d'aga muryarta tana fad'in "Ki mik'a min gaisuwa gurin Umma'n kafin mu shigo.."
'Dan waiwayowa tayi ta kalleta ta tsakanin mayafin daya rufe mata fuska kafin ta girgiza mata
kai kawai sannan tasa kai ta fice daga apartment d'in ba tare data sake furta komai ba,fuskar
sajida kuwa da mamakin hali irin da kuma k'arfin hali irin na wannan khadima ta rakata da ido.
A gefen su YASEER kuwa sanda Fulani ta bada umarnin kai musu breakfast kamar yadda tayi
gasu YAZEED,sanda sak'on ya riske su,ko bayan da suka gama break d'in ya d'auki lokaci yana
neman lines d'in Yarima sai dai amsa d'aya ya samu shi ne wayoyin a kashe suke,hak'ura yayi
da kiransa ya kammala shirinsa sannan ya fita da niyyan zuwa ya duba ko lafiya YAZEED d'in
yake zuwa wannan lokacin,tunda ya riga ya san abunda ya faru a daren daya gabata,sanda ya
iso apartment d'in ya iske shi a kulle,da har yayi niyyan juyawa kuma ko me ya tuna ya fasa
sannan yayi nocking,Sajida da tunda hadimar ta shigo ta fita take zaune tana zaman jiran ganin
fitowar Yarima ta mik'e tana nufar k'ofa da niyyan bud'ewa,da YASEER tayi arba,ko da ganin
haka sai ta saki fuska tana bashi hanya ya wuce,cikin girmamawa ta gaishe shi,yana tafiya
yana amsawa har ya k'araso cikin tsakiyar parlour'n,tambayanta Yarima ya soma nan ta shiga
bashi amsa
"Ina tunanin ko yana bacci ne dan ban ga fitowarsa ba har yanzun.."
Ido YASEER ya d'an bud'e yana kallonta kafin ya furta
"Wane irin bacci ne wannan har to 11:00am ace mutum bai tashi ba.."
Yana maganar yana kallon corridor d'in da zai sada shi da bedroom d'in
"Bari na duba na gani ko ya tashi.."
Ta fad'a tana bin hanyar bedroom d'insa,sai dai koda ta shiga bedroom d'in bata tarar da
komai ba face k'amshin perfume d'insa,dan haka ko data tabbatar baya nan sai kawai ta fito jiki
a sanyaye babu laka ta sanarwa da YASEER halin da ake ciki,mamakinsa sosai ya bayyana
dan yadda yake ganin ina ne zai nufa a irin wannan lokacin,wani tunani ne ya fad'o masa nan
take ya jinjina kai sannan ya mata sallama da niyyan fita,zuciyarsa da tunanin ina d'an uwan
nasa ya nufa da wannan safiyar da har ya fice ba tare da wacce suka kwana guri guda ta sani
ba........
*Kuyi hak'uri da wannan masoya,ni kaina ban tab'a tunanin za'a kawo tsawon wannan lokacin
ba tare da kun jini ba,sai dai matsalar da muka samu tasa aka samu wannan jinkirin,amma ku
k'ara hak'uri in sha Allah matsalar ta kusa zuwa k'arshe da izinin mai duka.*
*Don't forgets to follow me on wattpad@jeeddahmu898*
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl Ê‚mąʂɧɛr.í ½í¸‰*
[9:31PM, 6/11/2019] Itz Ibraheem: í ½í² í ½í² í ½í² í ½í² í ½í²
*AWESOME WRITER'S ASSO..í ¼í¿®*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
 *WANI AL'AMARIN..!*í ½í²¥
*(Book 2)*
í ½í²£í ½í²£
í ½í²¥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا .ميØ
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Ban san iya adadin farin cikin daya kamata nayi ba,saboda soyayyarku a gareni ta wuce a
misalta,fatana har kullum baya wuce addu'ar Ubangiji ya barmin ku har k'arshen
numfashi,#Ahabbakumullahul-laziiy ahbabtaniy lahu.*
___________________
*BOOK 2. í ½í³“*
*Pg 2.*
^^^^^^^^
Duk inda YASEER yake tunanin samun Yarima YAZEED ya duba kuma ya bincika amma ko
mai kama da shi bai samu ba,haka duk wanda yake ganin idan ya tambaya game da labarin
Yariman sai daya tambaya amma kowa cewa yake masa bai ganshi ba,hankalinsa bai gama
tashi ba sai daya dangana da gefen Fulani,ko daya je d'inma bai iya fitowa fili ya tambayi
Yariman ba,dan yadda yake jin nauyin yin haka,sanda yayi iya yinsa da dubawa duka dan ya
gano ahi,amma hakan ya faskara,dan ko inuwarsa bai hanga ba bare kuma shi d'in
kansa,ficewa yayi niyyan yi dan yadda yake jin hankalinsa na sake tashi a duk lokacin da yaje
inda yake tunanin samunsa bai ganshinba,har ya dangana da k'ofar fita muryar Fulani ta tarar
da shi inda take jifansa da tambayar
"YASEER ina ka baro d'an uwanka ne..Naga ka shigo kai d'aya.."
Shiru yayi yana sauke b'oyayyiyar ajiyar zuciya kafin ya waiwayo fuskarsa d'auke da
murmushin yak'e
"Amm! Ummah Fulani ai ina tunanin ko ya rugani shigowa ne shi yasa ban tuntub'e shi ba da
zan shigo.."
"A'a'a.! Ai kam bai shigo ba,amma wata k'ila ko wani uzurin ya rik'e shi,ina tunanin ko shi
yasama bai nemekan ba kai d'inma.."
"Ehh! Haka ne Ummah,amma barin duba shi naga ko lafiya.."
Murmushi Fulani tayi irin nasu na manya kafin ta furta
"Lafiya ai ita take b'oye mutum.."
Murmushin shima yayi na k'arfin hali sannan ya mata sallama ya fice zuciyarsa cike da zullumin
inda YAZEED ya shige da wannan safiyar.Yana fitowa apartment d'insu ya koma na da,yana
shiga kuwa yaci gaba da k'ok'arin kiran line d'insa cikin sa'a yana gwadawa a wannan karon
wayan ya shiga,jikin YASEER har rawa