Showing 18001 words to 21000 words out of 29888 words

Chapter 7 - Wani Al'amarin Compelet Hausa Novels By Real Shamtr.pdf

03 Oct 2025

618

comment's d'in da suke gamsheni,so
zanja gefe na k'ame dama dagiya ce kawai nake tunda kunsan matsalar da muka samu,kunga
daga yau saina koma posting duk sanda na bushi iska,tunda kuma kun koma gefen sai aikin na
turo amma babu comment's,masu yin comment's duka basu wuce na lissafa da yatsun
hannuna..Allah ya sani kamar yadda kuke son farin ciki kowa ma yana so,mu fa da comment's
d'in ku kawai muke samun farin cikin,yanzun idan babu comment's Fisabilillah ku fad'a min yaya
kuke tunanin tsarin labarin zai kasance...???*



#Follow
#Vote

#Comment. Then
#Share.



*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
[8:18AM, 6/23/2019] Itz Ibraheem: 💠💠💠💠💠
*©® 2019..*



 *WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*

مسب الله نمحرلا رلا .ميح
^^^^^^^^^^^^^^^^^
���
_My love for u knows no bounds,my respect for u is equally immense.U are my ultimate
emotional support and my sweetest love.Every memory from the gone years,makes me glad
that u are my sisters.And i wish both of u a very warm & happy Birthday.I love u my sisters.!_
�🍿🥂 *Happy belated birthday (NI'IMATULLAH & RAHMATULLAH).*🥂🍿�
���
___________________
_It's all for u alone *🌷FENERH🌷* of Golden pen writer's asso,d writer of *🌷KUSKURE
NA🌷,* i have heard that friends do a lot in life.But,now i saw for myself,i can't thank u enough
for the pain u took for me,i appreciate the time nd efforts.So,glad that i have a loving friend like
u.Truly thank u.!_ ___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 9.*
^^^^^^^^
*ONE YEAR LEAP...*
Kimanin shekara guda kenan da faruwar *AL'AMARI'N* wanda izuwa wannan lokaci abubuwa

da dama sun faru,wasu masu dad'i wasu kuma kishiyar hakan,a bayan rabuwar auren YARIMA
YAZEED da Sajida kuwa,wanda kafin rabuwar tasu sai da aka kai ruwa rana tsakanin iyayen na
Sajida,haka bayan wannan kuma sai labarin rashin lafiyar Yariman da shima tuni ya baza ko ina
a cikin k'waryar birnin,naji mamaki akan ta inda labarin ya bazu haka wanda ba iya ni kad'ai
ba,hatta da cikin gidan Sarautar su kansu sai da abun ya so girgiza su,dalilin da yasa duk suke
mamaki da faruwar hakan kuwa sun sani ko a lokacin da cikin gidan suka san cewa Yariman
yana fama da larurar su kansu a tsakaninsu ba kowa ne ya sani ba,amma yanzun ace hatta da
mutanen gari sun san da matsalar,dole ne wannan yasa su shiga tsananin mamaki.

A b'angaren Yarima kuwa koda yaga zuwa lokacin shekara guda har ya zagayo da karb'ar
maganin da suka yi,nan ya fara tunanin ta inda zai fara tunkarar gurin malam Adamu dan sanin
ainihin inda matsayar su take,da yammacin ranar bayan ya kammala shirinsa ya fito cikin shigar
gargajiya ta manyan kaya wanda suka sake fitar da cikar kamalarsa da girmansa cikin wani
farin yadi haka hulan dake sanye kansa wacce akewa lak'abi da minister itama farar ce
kar,atak'aice dai tun daga sama har k'asa shigar da yayi kenan na farin color,da fitowarsa
apartment d'insu YASEER ya fara nufa yana zuwa yayi knocking door d'in,dai² an bud'e k'ofar
ya juya yana kallon wanda ke gurin a tunanin sa ko cikin hadiman dake kula da side d'in ne,da
YASEER suka yi arba nan take ya juya ba tare da yayi magana ba cike da k'asaita, girgiza kai
YASEER d'in yayi sannan ya biyo bayansa cikin d'an d'aga k'afa,a mota suka had'u ba tare da
wani cikinsu yayi magana ba yayi warming motan sannan suka d'auki hanyar sharad'a,dai² inda
suka tsaya wancan lokacin wannan karonma a nan yayi parking duk da y'an canje² da aka
samu wanda ba za'a rasa ba,kafin suka ci gaba da takawa da k'afa har suka iso k'ofar gidan
wanda yake d'auke da katuwar bishiyar ced'iya da d'an madaidaicin masallaci sai d'akin da yake
ganin masu larura dake nan jikin gidan nasa yana kallon k'ofar masallacin,a lokacin kasancewar
yamma,bai hana mutane taruwa ba dan haka ba tare da wani ya fahimci wani abu a tare da su
ba,suka nemi wani benche suka zauna suna jiran mutane su d'an ragu a gurin,suna nan zaune
har zuwa lokacin da mutanen da suka tarar suka yi sauk'i sannan suka matsa dai² bakin k'ofar
tasa suka yi masa sallama,cikin sakin fuska ya amsa musu kafin yayi musu izinin shigowa yana
gyara musu shimfid'ar dake baje a cikin gurin yana sake musu marhaban dan izuwa wannan
lokacin tuni datijjon ya shaida su,saboda lokaci zuwa lokaci sukan je su gaishe shi tare da yi
masa alkhairi,bayan sun gaisa kamar ko wane lokaci da suka saba sai duk suka yi shiru na d'an
lokaci kafin YASEER ya kalli malam Adamu da cewa
"Baba yau dai gamu mun sake dawowa kamar wancan lokacin na farko da muka fara zuwa
gareka,cikin hukuncin Ubangiji kamar yadda kayi mana bayani a wancan karon Allah ya ara
mana rai da lafiyar dawowa kamar yadda a yau muka kawo shekara guda dai².."
Jinjina kai malam Adamu yayi cike da gasgata maganar YASEER yana cewa
"Haka fa akayi,yau shekara guda cif da kuka zo,Ubangiji mai iko da hikima kamar yau ne kam
gashi cikin k'udirar Ubangiji har lokacin ya kuma zagayowa..To Ubangiji ya bamu ikon cikawa da
imani.."
"Ameen" suka amsa masa,cikin hikima ya d'an juya ya kallesu su duka biyun kafin yayi
magana
"To samari yanzun yaya muke ciki..??"
Ya kalli Yarima da kansa ke k'asa yana sake cewa

"Ina fatan akwai matar dai ko..??"
Cikin rashin fahimtar maganarsa YASEER yace
"Baba ai tun wancan lokacin ka shaida mana ba zaiyi aure ba har sai mun shekara da karb'ar
magani..!"

"K'warai haka muka yi..Kuma maganar da nake yi nima a yanzun ba wai ina nufin wani abu
bane,abunda nake magana akai shine shin akwai matar da zai aura kwana kusa ne ko kuwa..??
Saboda ta haka ne kad'ai zamu iya mu fahimci inda muka nufa gaba d'aya ni da ku..ko ba haka
ba..??" Jinjina kai YASEER yayi cike da gamsuwa da maganar dattijon yana cewa
"Haka ne baba.."

"Yawwa..! To Malam YAZEEDU ina fatan kaji batuna kuma a shirye kake a ko wane irin lokaci
zaka iya zuwa min da labarin auren ko..??"
Tunda suka zo bayan gaisuwa da suka yi da malam Adamu ya sauke kai k'asa sai yanzun ya
d'ago kansa fuskarsa d'auke da murmushi ya jinjina kai sannan yace
"In sha Allah Baba..!"

"To Ubangiji yayi mana kyakykyawan jagoranci."
Nan ma da "ameen" suka amsa kana d'akin ya d'auki shiru na y'an wasu mintuna,y'an wasu
magunguna ya sake had'a masa ya bashi sannan yayi masa bayanin yadda zai yi amfani da
su,bayan sun kuma tsaida magana akan bayan auren Yariman zasu sake komawa gurinsa dan
yasan yadda ci gaban al'amarin yake,godiya suka masa sannan suka masa alkhairi suka sake
d'aukan hanyan komawa gida.

Mintuna goma sha biyar ya kawo su gida kasancewar sun d'an samu tsaiko a dalilin traffic da
suka mak'ale har na wasu y'an mintuna,sanda suka dawo direct apartment d'in Ummi suka nufa
dan dama itace abokiyar shawararsu a kaf gidan,duk da a wasu lokutan sukan je gurin
Umma'nsa sai dai itan ba ko wace irin magana yake sakewa suyi da itaba,haka nan irin wannan
maganar tun daga sanda al'amarin ya faru ko sau d'aya bai tab'a tsayawa sun tattauna akan
matsalar ba,sai dai ko ayi da Ummi ta kuma ta sanar mata,yanzunma suna shigowa da
ABEELA da Abir suka fara tozali,cikin girmamawa suka gaida su kafin suka samu guri suka
zauna suna tambayar Ummi saboda basu ganta ba.Abir ce ta basu amsa da cewar tana cikin
turakar Abba,shiru suka yi na d'an wani lokaci kafin ABEELA ta mik'e ta nufi hanyan kitchen d'in
Ummi kasancewar su kad'ai ne sai ko su Yarima da suka shigo yanzun,kuma suma d'in da suka
shigo ba wani hira suke yi ba,tana shiga kitchen d'in ta hangeta ta juya ma k'ofa baga shigowa
baya sai aikinta take babu wani mai taimaka mata ko da hira ne,murmushi ta d'an yi cike da son
ta d'an tsokaneta,cikin sand'a ta isa kusa da ita,a hankali ta d'an yi d'age saboda ta d'an fita
tsayi ta mik'a hannunta saman kanta had'e da yaye nik'ab d'in data rufe fuskarta da shi,cikin
razani jeeddah dake kan had'a farfesun jin an yaye mata nik'ab nd she knows there is no one
near to her,yasa ta fasa wani k'ara mai firgitarwa tana runtse ido gami da dafe k'irjinta dake
bugawa da sauri,dai² nan dariyar ABEELA tasa ta bud'e ido a hankali kamar wacce aka ce idan
ta bud'e su one time zata ga wani gagarumin abu,a d'an tsorace ta sauke idonta akan

Abeela'n,hararar wasa ABEELA tayi mata ta ce
"Kai..! gaskiya kin cika tsoro wollahi,ni da nazo na taimaka miki dan yadda ake zafi amma na
ganki da nik'ab kuma ki rasa inda zaki sa sai a kitchen,sai kawai ki wani tsorata.."
Ajiyar zuciya ta sake saki mai nauyi sannan ta juya ta ajiye utensil d'in hannunta tana cewa
"Haba ai dole ne naji tsoro dan ban san da zuwanki ba..nd nasan babu wani a kusa dani.."

Dai² nan YASEER ya k'araso gurin yana kiran sunan ABEELA coz bai san da wani a gurin
ba,duka tunaninsa ya tafi akan wani abu ya sameta ne,sai daya iso cikin kitchen d'in sannan ya
ga jeeddah tsaye suna magana da Abeela'n,ajiyar zuciya shima ya saki dai² yana sake
k'arasowa kusa da ita,da murmushi a fuskar jeeddah harma ita kanta Abeela'n suka kalle shi
tana amsa kiran daya mata na k'arshe
"Chocolatey..! Gani fa kana kira na.."
Hannunta ya rik'o yana sake janta zuwa jikinsa yana kallonta cike da so kafin ya furta wani abu
tuni jeeddah ta juya musu baya dan yadda taga Babban yayan nata yana neman rungume
ABEELA a gabanta ba tare da jin kunyarta ba,cikin rad'a yake tambayarta
"What's wrong kuke ihu haka..??"
Ture shi ta fara yi tana masa nuni da jeeddah dake cikin kitchen d'in da ido,murmushi ya sake
yi kafin ya sake rik'o ta yana rad'a mata,ganinta is nothing to him,k'ok'arin k'wace kanta ta ci
gaba da yi tana b'ata fuska,dai² nan sai ga Yarima shima ya kawo kai,a bakin kitchen d'in ya
tsaya ganin halin da suke ciki sai yasa shi yin voice amendments,still ba tare da YASEER ya
saketa ba ya waiwaya baya yana kallon Yarima da yayi kicin² da fuska,harara ya zabga masa
kafin ya janye idonsa akansu yana fad'in
"Ai sai ku fice anan ko sarakan rashin ta ido..!"

Dariya maganarsa tasa YASEER kafin ya bashi amsa
"Idan munk'i fa..??"

"I will try to inform Ummi..So u have to leave..now.!"
Zaro ido YASEER yayi sannan ya saki ABEELA yana cewa
"Me yayi zafi..?? Ko kana so ka had'ani da ita tace dama bani da...."

"Ba sai ka wahalar da kanka ba dan dama ba ita gareku ba.."
Dariya YASEER ya d'an yi cikin zolaya ya furta
"Time would convict u..We would see ur phase.."
Sake d'aure fuska yayi kafin ya wuce ta gefe ya d'auka cup ba tare da yayi magana ba ya
tsiyaya ruwa a ciki,half cup d'in ya sha sannan ya ajiye dai² lokacin da idanunsa suka sauka kan
jeeddah wacce iya bayanta kawai yake iya gani,saurin jutawa yayi zuwa gefen da su YASEER
suke tsaye har lokacin yana tambayarsa da ido akan dama tana gurin tun d'azun..? Da kai ya
amsa masa,jinjina kai kawai yayi ya ajiye cup d'in ya nufi hanyan fita zai bar wajen,har ya iso
dai² inda yake tsaye a tunaninsu ya gama abunda yake a gurin ne,sai dai ko da zuwansa ba
tare da tsayawa tunanin komai ba ya fizgi hannun YASEER suka yi waje,ABEELA kuwa bakinta
kad'ai ta iya toshewa saboda dariyar dake neman k'wace mata na ganin yadda Yayan nata ya
fizgi YASEER suka yi waje ba tare daya shiryawa hakan ba,kusa da jeeddah ta k'arasa dai²

tana cewa
"Lemme help u.."
D'an juyo wa tayi ta kalleta da murmushi a fuskarta
"A'a..kam na gode sosai,gara ki huta kema.."

"Ohh! Nice bakya so na taimaka miki ko..??"
Murmushi ta sake yi kafin tace
"Ko kad'an ba haka bane,kawai dai naga rashin dacewar hakan ne,shi yasa na fad'a.."
Babu yadda ABEELA bata yiba akan ta taimaka mata amma tak'i yarda dan haka sai kawai ta
hak'ura taja gefe saman stool ta zauna tana ta mata hira,wani abun tasa ta dariya wani kuma
sai dai tayi d'an murmushi kawai abunta a haka har ta kammala abunda za tayi suna tare a
kitchen d'in,haka ko sanda zata fito da kayan zuwa dining area tana setting gurin nan ma duk
suna tare sai anan nema Jeeddan ta hak'ura Abeela'n ta taimaka mata.

Su YASEER kuwa lokacin da suka fito a kitchen d'in babu jimawa sai ga Ummi ta fito saboda
lokacin Abba ya fita,nan ta iske su suna y'an hirarrakinsu YASEER d'in sai tsokanar Yarima
yake,zama tayi cike da farin cikin ganin a kowane lokaci kan yaran nasu a had'e,nan suka
maida hankulansu kanta suka shiga gaisheta,cike da farin ciki ta amsa musu,kana ta fara
tambayarsu batun zuwa gurin mai magani coz sun fad'a mata zasu je amma bata san ainihin
takamaiman lokacin da zasun ba,bayanin duk yadda suka yi da malam Adamu a lokacin suka
mata,cikin nuna jin dad'i da bayanin nasa kuwa ta kalli Yarima tana cewa
"Son to ko dai zamu je bikon Sajida ne..??"
Saurin kallonta suka yi su duka har suna had'a baki gurin tambaya
"Ummi wace Sajida kike nufi..??"
D'an murmushi tayi itama na zolaya kafin tace
"Kuna da wata Sajida da kuka sani ne bayan y'ar baffanku Matawalle..??"
Ai kuwa take suka sake furta
"Whaaat..?? Ummi wannan kike nufi..?"
Kallonsu tayi dan yadda suke had'a baki a magana abun har ya bata mamaki
"Wani abu ne dan nace itan..??"
Duka suka girgiza mata kai
"A'a Ummi babu komai,amma dai ai...!"
Sai duk suka yi shiru suna kallon juna dan suma maganar tasu mamaki take basu,murmushi
Ummi tayi kafin tace
"To sarakan had'in kai nima da wasa nake..Taya zanso wani abu ya sake had'a mu da irin
Hajiya Suwaiba imma badan shi Matawallen da yake da alak'a da gidan nanba,ai nasan My son
ya wuce ajin Sajida,ko yarona...?"
Baice komai ba sai murmushi kad'ai da yad'an yi,nan Ummi tasa su gaba bayan d'an wasan
da ta saba jansu sannan tayi musu nasiha akan su nutsu kuma su san rayuwa,kada dan suna
ganin Allah ya d'aukakasu su nemi cin zarafin wani bawa nasa,ta jima tana musu nasihanta mai
ratsa jiki kafin suka koma kan maganar auren Yariman...............

*Wai shin Fan's wace ce kuke ganin a wannan lokacin ta dace da Yarima tunda dai kun san
halin mutumin ba kula y'an mata yake ba..??*

*Amma kuyi alk'alanci tsakanin y'an matan nan biyu wacce tafi dacewa da gidan Yariman..??*

*#Aisha..??* Ko kuma *#Sajida..??*



#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.



*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉
[10:58PM, 6/23/2019] Itz Ibraheem: 💠💠💠💠💠
*©® 2019..*



 *WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login