Showing 27001 words to 29888 words out of 29888 words

Chapter 10 - Wani Al'amarin Compelet Hausa Novels By Real Shamtr.pdf

03 Oct 2025

619

yana kallon sama.Bayan daya gama wayan mik'ewa yayi ya shiga musu packing kayansu
a gefe sannan ya wuce toilet dan d'aura alwala saboda gabatowar sallar Maghreb,har ya fito
YAZEED na nan a yadda yake kamar mai bacci,a kusa da shi ya d'an tsaya yana sauke hannun
white long sleeve dake jikinsa yana magana
"Broah.! Wake up..! Lokaci fa yayi."
Bud'e ido yayi a hankali ya d'an kallesa kafin ya yunk'ura ya mik'e,a hankali shima YASEER d'in
ya zauna yana jiran ya idar su wuce masjeed,har ya fito ya riske shi a inda ya barshi daga nan
suka fice suka nufi masallaci,sai after isha'a sannan suka shigo cikin gidan,sai a nan yarima ya
samu daman yin magana da YASEER d'in yana shaida masa zai je yaga Umma'nsa,jinjina kai
YASEER yayi sannan ya ce
"Muje idan mun fito sai mu k'arasa gurin Ummi,coz ina tsoron fad'an Ummi idan ta kamanin ni
d'aya.."
Tare suka jera amma babu wani hira a tsakaninsu,har suka shiga suka fito daga nan suka nufi
apartment d'in Ummi'n,tun daga shigarsu Ummi ke binsu da kallon tuhuma,a haka suka gaidata
kana suka zauna shiru,kallonsu tayi su duka biyun taga kowanne fuska a cunkushe,had'e fuska
tayi itanma sannan ta kalli YASEER "Dama abunda ya kawo ku kenan kuzo kumin shiru..?? Ina bayanin da kace zaka sanarmin..??"
Shiru yayi yana sauke kai k'asa hakan da ta gani yasa ta sake yin magana
"Kai nake sauraro ko kuma ka tashi ka bani guri tunda ba abunda na kiraka kamin ba kenan ka
sani.."
Bai iya d'agowa ya kalleta ba,sai magana daya fara cikin sanyin jiki ya fara mata bayanin duk
abunda ya faru a Abuja,har kawo kan resigned da suka yi.Shiru tayi cike da jimami da kuma
takaicin abunda ya farun,idanunta akan Yarima tana binsa da kallon tausayawa,a hankali ta
girgiza kai tana mai jin wani irin yanayi yana tsirga mata na tsantsar b'acin rai,amma duk da
haka bata fasa mgna ba,nasiha sosai tayi musu mai shiga jiki wacce duka ta karkata ne akan
hak'uri da K'addara mai kyau ko kishiyar hakan,sannan suka mata sallama suka fice,bayan
fitarsu a apartment d'in sallama suka yi da juna dan yadda suka ga dare ya soma nisa,daga nan
YASEER ya nufi apartment d'insa shima Yariman ya nufi ainihin apartment d'insu.
Washe gari kam tun da safe maimartaba yasa aka kira masa su lokacin yana apartment d'in
Umma Fulani coz lokacin fitarsa fada baiyi ba,ba tare da b'ata lokaci ba suka nufi apartment d'in
dan amsa kiransa,suna shiga maimartaba ya nuna musu gurin zama cike da nuna musu
alamun su zauna,kawunansu a k'asa suka zauna zuciyoyinsu cike da fargabar abunda zai biyo
baya dan sun san kiran bana lafiya bane,nan suka fara shan ruwan tamvaya daga
maimartaba,inda a karon farko ya fara jifansa YASEER da tambaya
"YASEER..! Shin wane dalili ne yasa kuka ajiye aikin ku..?"
Duk da yasan amsar da zai bayar a lokacin sai da yaji shakkar fad'an,Umma'n YAZEED tana
zaune itama a gefe tana sauraren abunda zai faru dan tunda aka yi waya masarauta aka sanar
da maimartaba abunda ya faru ya shaida mata,wannan dalilin yasa ta bashi shawaran a kirasu

a tambayesu dalilin aikata hakan,b'angaren da YAZEED yake maimartaba ya kalla yana had'e
fuska dan baya son ya nuna musu wani alama da zaisa su k'i fad'ar gaskiya,babu zato Yarima
yaji muryar mahaifinsa yana musu fad'a akan abunda ya faru,har ya gama babu wanda yayi
koda tari,sai a sannan YASEER ya d'an gyara zama ya shiga yiwa maimartaba bayanin duk
abunda ya faru,duk da maganar ta tab'a musu zuciya gaba d'aya'nsu,hakan bai sa ya nuna
musu ba ko a fuska,daga haka ya sake musu nasiha ya kuma nuna musu kuskuren da suka
aikata game da aikinsu sannan ya sallame su suka fice.
Bayan fitarsu a apartment d'in ya rage sai Umma Fulani da maimartaba kad'ai,a nan suka fara
tattaunawa akan matalolin da ake yawan samu akan Yariman wanda a kullum idan aka samu
irin wannan damuwar ko wata magana ta fita dangane da shi d'in take sawa yaji matuk'ar bak'in
ciki da damuwa,sun jima suna tattaunawa kafin suka gangara kan maganar auren Yariman da
Zahra da ake kan samun matsala a yanzun,wanda a k'arshe basu bar maganar ba har sai da
suka yanke shawaran jiran ganin abunda zai faru ta b'angaren Ambassador Abdulmalik.
Kwanaki sun ci gaba da tafiya,ba tare da wani sakamako ko magana daga b'angaren
Ambassador Abdulmalik d'in babkamar yadda maimartaba yayi tsammani,wannan tasa kan dole
maimartaba ya taushi zuciyarsa had'e da yanke shawaran tura d'an aike don samo masa
gamsashen bayani game da inda matsalar ta kwana duk da ya fahimci Ambassador d'in ba
babban mutum bane,wanda shi da kansa sai yanzun ne yake ganin gara ma da aka samu
wannan matsalar har tayi sanadiyyar yankewar alak'ar dake tsakaninsu,ko da sak'on
maimartaba ya riski Ambassador Abdulmalik ba tare da b'ata lokaci ba ya shaidawa d'an sak'on
masarauta nasa sak'on na janye batun aure tsakanin yarima da Zahra,haka d'an aiken ya juyo
da mummunan labarin da ambassador d'in ya shaida masa na rashin yiwuwar auren tare da
soke alak'ar su da masarauta.Lokacin da sak'on ya riski ahalin masarauta ga wasu daga cikinsu
sam basu ji dad'in wannan abun daya faru ba,sai dai babu yadda za suyi nan suka fawwala
lamarin zuwa ga Ubangiji,tare da neman sauk'i daga gurinsa.
Haka rayuwa taci gaba da gangarawa yayin da a kowanne bigire al'amura da dama suke kan
faruwa,wanda mafi yawa daga ciki suka ta'allak'a akan neman aure ga Yarima YAZEED da
akayi tayi amma duka babu nasara.
^^^^^
A b'angaren Adda da ladidi kuwa kusan zamu iya cewa rayuwarsu ta koma gefe guda wanda
tun bayan auren Yariman da suka d'aukewa masarauta k'afa,ko da zuwansa ya kama su basa
lek'awa,idan kuwa har ka gansu sun zo tofa sai dai ko munafurcinsu ya kawo su,haka a ko
wane lokaci zaka iske su basu da buri ko fatan daya wuce ace sunga wani abu na rashin jin
dad'i ya samu wani daga cikin ahalin,tofa a nan ne zaka ga farin cikinsu da murnar su ta
bayyana.
Ita kuwa Aisha a nata gefen tuni ta fara samawa kanta lafiya sai dai har kullum itama kan
neman mafita take amma ta rasa inda ya kamata ace ta nufa wanda zai zame mata wani jigo da
zata kama ya zame mata madogara a rayuwarta.
Kamar ko wane lokaci yauma tana zaune a bedroom d'inta tana sana'ar tata na mugun tunanin
daya zame mata jiki,haka nan ta fara jin fad'uwar gaba na damunta,can kuma kamar wacce aka
tsikara ta mik'e ta zari veil d'inta ta fito fuskarta kamar ta macen dake takaba,babu wanda ta
kula tsakanin Adda ko Ladidi duk da ta gabansu ta wuce tayi ficewarta a gidan ba tare data
tsaya ko bi takan d'aukan mota ba ta kama hanyar fita a line d'in nasu,a bakin hanya ta tsaya

tana duba abun hawa,tricycle ta tsare ta kwatanta masa inda zai ajiyeta daga nan suka d'auko
hanya,dai² kan titi ta sauka bayan ta sallame shi taci gaba da takawa da k'afarta zuwa cikin
royal palace d'in,sai dai maimakon ace ta nufi hanyan cikin gida kamar yadda ta saba,sai ta
d'auke hanya bayan ta wuce k'ofa zuwa wajen line d'in gidajen bayin,sannu a hankali take tafiya
zuciyarta cike da fargabar abunda zai faru har ta k'araso k'ofar gidan,a dai² k'ofar gidan ta tsaya
shiru har zuwa wani lokaci,ta d'auki lokaci a tsaye a gurin tana tunanin gidan ne ko kuwa..??
Kafin ta motsa,ko data gama tabbatarwa kanta gidan ne nan ta tasamma k'ofar shiga ainihin
gidan gadan² zuciyarta na daka.
Bayan fitar Aisha a gidan kuwa da yayi saura daga ladidi sai Adda,nan suka sake bud'e sabon
shafin hira kan al'amuran da suka shafi masarauta,sun kwashe tsawon lokaci suna maganar
kafin Adda ta yunk'ura ta mik'e tana cewa
"Kashh! Kinga nayi ragon azanci na manta ban tambayi yarinyar nan inda zata ba,dan ni kam
cikin kwanakin nan sam na gaza yarda da zaman shiru da take yawan yi,gaba d'aya cikin y'an
wad'annan kwanakin ta daina walwala,itace kulle kanta a d'aki,fita park duk da nasan d'abi'ar
tane to amma ba kamar yanzun ba,haka wani lokacin kuma zata tusa mu a gaba tana
kallo..shin kin kula da wannan canjin kuwa..??"
Shiru Ladidin tayi tana d'an jinjina kai alamun itama d'in ta gano hakan
"Anya kuwa bakya ganin an samu wata matsala ne da har hakan yake faruwa..??"
Adda'n ta sake yin maganar cikin yanayin jimantawa
"To Adda ni mene zance ne akan wannan maganar,na sha fad'a miki babu abunda ya farufa
kawai ki kwantar da hankalinki,ni nasan ba abunda kike tunani bane..Yanzun kam ko da ma ace
abunda kike zargin ne ai na fad'a miki abunda za muyi,daga zara'n mun b'atar da ita shi
kenanfa babu wanda zai zargemu ko ya kawo tunanin mune muka aikata wani abu akanta.." Cikin gamsuwa Adda'n ta girgiza mata kai
"Tabbas wannan shawaran naki yayi,amma bari kiga yanzun'ma ni masarauta nake son zuwa
dan na jiyo wani labari ina son ko da ace bamu yi nasara a baya ba a yanzun muyi nasaran
shiga tsakaninsu ta inda zamu samu burin da muka d'auki tsawon shekaru muna dako ya cika.."
Thumbs up ladidi tama Adda cikin kurantawa had'e da kambamawa ta fara hura mata kai,ai
kuwa take Adda ta fara jin kanta yana k'ara girma kai kace dutsen Dala ne,wanda daga haka ne
ita Adda'n tayi mata bankwana ta fice a cikin gidan tana kama hanyar masarauta.
^^^^^
'Dan k'aramin meeting maimartaba ya kira wanda duka² bayan Hajiya sai shi kansa,Umma
Fulani,Abba GALADIMA sai kuma Ummi'n YASEER,kasancewar meeting d'in na sirri yasa basa
so ace adadinsu ya wuce hakan,maimartaba ne ya fara magana yayin da duka suka yi shiru
suna sauraren dalilin daya tara su a gurin,maganar cike da zallan mulke yake cewa "Kamar yadda kuka sani wannan taron namu bawai taro ne da yake kama da sauran zaman da
muka yi a baya ba,nasan dai duka ko ban fad'a ba wasu cikinmu zasu iya fahimtar dalilin
faruwar hakan...Alal hak'ik'a wannan zaman da muka yi a nan a kuma wannan lokacin ina son
shaida muku ba akan komai muka yi shi ba,face akan yawan matsalolin da muke fuskata a
wannan gidan..Wanda mu kanmu idan muka tsaya muka yi duba babu lallai ace munyi saurin
gano dalili ko mak'asudin da yasa hakan ke yawan faruwa,sai dai bisa mizanin hankali idan
muka yi duba da abubuwan dake kan faruwa a yanzun dama wad'anda suka faru a baya
wannan abubuwan suna b'ullowa ne daga wasu mutane wanda mu kanmu bamu san ko su

waye ba,haka suna faruwa ne ba don komai ba sai don ana so aga bayan wannan gida
namu,amma koma su waye idan har sunfi k'arfin saninmu basu wuce da sanin ubangiji ba,kuma
mu gareshi kuma mik'a dukkan wasu lamuranmu,haka kuma a kullum gurinsa ne kad'ai muke
kai kukan mu tare da neman mafita a gareshi..mun sani wayo,dabara ko K'arfin mu duka ciki bai
isa ya bamu abunda muke nema ba..da wannan ne muke fatan Ubangiji yaci gaba da karemu
daga sharrin masu sharri."
"Ameen" duka suka amsa dan kowa yana da damuwa musamman akan lamarin gidan da lokaci
bayan lokaci sai an samu wani abu ya faru,y'an maganganu aka d'anyi na d'an wani lokaci kafin
Abba GALADIMA da tun zaman bai ce komai ba yayi gyaran murya ya fara magana shima
"Tabbas wannan AL'AMARI akwai rud'ani a cikinsa,haka nan akwai abun dubawa akansa,sai
dai mu a gurinmu babu wani da zamu d'aga muce muna zargin da sa hannunsa a cikin
matsalar,sai dai addu'ar dai ita zamu ci gaba da yi,,haka nan ina rok'on alfarmar musamman
akan matsalar yarona da mu sake jajircewa muna nema masa kariya daga mak'iya..!" Duka sun fahimci akan wanda yake maganar koda baiyi specifying ba,dan haka duk suka sake
nutsuwa suna sauraren jawabin
"Sannan maganata ta gaba,itama dai kan matsalar yarona ne,saboda haka idan na fad'i wata
magana ba dai² ba ina fatan duk zakamin uzuri,dalili kuwa shi d'an adam ajizi ne.."
Na'am suka yi da jawabin nasa,ba tare daya saurara ba ya sake nausawa cikin bayanin abunda
ke ransa
"A dai² wannan lokacin, ina so nayi amfani da wata y'ar dama da naga Ubangiji (S.W.T) ya
bani,wanda a nawa hasashen da kuma tunanin nake ganin a yanzun tunda har Allah yasa kowa
yana jin bazai iya amincewa ya bamu aure a gidansa ba,kan wani dalilinsu da har yau an kasa
samun wanda zai same mu ya mana bayanin kai tsaye,nake ganin mai zai hana mu baza mu
taru mu rufawa kanmu asiri ba..."
Hajiya da itama dukkansu babu wanda ya tofa albarkar bakinsa tun zaman,idan aka d'auke
maimartaba daya fara magana sai ko yanzun da Abba GALADIMA yake kan yin nasa
jawabin,take ta yunk'ura tana tambayar Abba GALADIMA'N
"Wane irin rufin asiri ne kake magana Aliyu..??"
Jinjina kai yayi sannan ya kalli maimartaba da cewa
"Tun daga lokacin da aka fara samun matsala game da maganar auren yaron nan nayi ta
hasashen anya bazamu hak'ura da neman auren Yarinyar kowa ba,tunda har Allah (S.W.T) ya
azurtamu da yaran nan ko da dai ba wai masu yawa bane Alhamdulillahil.!,tunda har muna da
su naga dacewar nace mai zaisa mu baza mu tsakanin yaran namu ba tunda har muna da
yadda za muyi mu nemawa kanmu maganin damuwar mu,amma yaya kuke gani..?? Ni wannan
itace shawara ta,na tabbata dai Abir k'anwa ce a gurinsa babu yadda za'ayi idan har wani a
waje ya guje shi saboda ciwon dake jikinsa ko wani aibu itama ta gujewa hakan,na tabbata bata
da yadda za tayi dole ne ta zauna dashi ko da kuwa ace zai k'are rayuwarsa a haka haka nan
shima kansa,shin yaya kuke ganin shawarata..??"
Yayi maganar yana kallonsu duka,tabbas maganarsa tana kan hanya,amma taya zasu fara
amincewa har ayi wannan AL'AMARI'N bayan sun san cewa Abir k'aramar yarinya ce da duka
har yanzun ko sanin kanta bata gama yi ba,idan har suka ce zasu yi haka tofa sun tabbata zasu
cutar da rayuwarta ne,idan kuma har sun ce baza su yi hakan ba to yaya za suyi kenan..?? Wannan shine tambayar da kowa yake yiwa kansa a gurin idan aka d'auke Fulani da tayi nisa

cikin dogon zangon tunani,nan kowa ya shiga kawo nasa ra'ayin akan maganar,Hajiya kam
tunda suka fara maganar tayi shiru tak'i cewa komai,zuwa wani lokaci ta sauke wani nauyayyar
ajiyar zuciya sannan ta kallesu dai² lokacin da ta fara magana
"Gaskiya ne duka shawaran ku abun a duba ne,sai dai wani hanzari ba gudu ba,kamar yadda
kuka sani Abir yarinya ce k'arama,mutumin da bai gama mallakar hankalinsa ba,ina ganin bai
kamaci ace an zartar da irin wannan hukuncin akansa ba duk da kunsan hakan ba haramun
bane a addini,bayan haka shi akankansa YAZEEDU idan har baku manta ba game da matsalar
dake tare da shi a wancan lokacin kun san irin sharad'in da yake kai na daga magani,shin mai
zai hana muyi wani abu kafin muyi tunanin damk'a Abir a hannunsa.??"
Kallon sune ya koma kan Hajiya harma da hankulansu dan maganarta sosai ta ratsa su
duka,nan ita kuwa Hajiya'n taci gaba da magana
"Ni anawa ra'ayin ina ganin ya kamata mu d'an jinkirta da maganar Abir daga nan zuwa ta d'an
k'ara wayo,kafin lokacin sai muyi amfani da wannan damar muyi k'ok'arin dubawa koda a cikin
bayinmu ne mu nema masa wata k'wark'wara,wanda ta hakama kad'ai ina ganin zamu iya
fahimtar samuwar lafiyarsa..Shin me kuke tunani akan wannan maganar..??" Nan shawara ta koma kan maganar Hajiya'n dan suna ganin maganar tata abar ace sun duba
ce,amma cikin bayin su kansu duk da a k'asansu suke,umarninsu suke bi shin waye zai yarda
ya d'auki y'arsa ya badata har hakan ta faru akanta..?? Anya akwai adalci a cikin wannan
maganar..?? "Tabbas..! Wannan shawara ne da yayi ma'ana,amma kafin nan wace baiwa ce kuke ganin ta
cancanta a zab'a game da wannan AL'AMARI'N.??"
Fulani ta tambaya,murmushi hajiya tayi sannan ta furta
"Mutum d'aya ce nake tunani a wannan bigire,wacce nasan ko me muka ce za muyi akanta
iyayenta ba zasu tab'a k'in amincewa da duk wani hukuncinmu akansu ba.."
Jinjina kai maimartaba yayi cikin gamsuwa da maganar Hajiya'n nasu,a hankali Ummi ta kalli
Umma Fulani bakinta d'auke da tambaya
"Su waye su wad'annan d'in ni kam na gaza fahimta..??"
*"GIDAN SARKIN KASUWA.......!"*
A hankali tayi squeezing fuskarta tana son tunano ainihin gidan da ake magana akai,ido ta fitar
waje cike da fargaba tana fad'in
"Shin wannan hukuncin akan *JEEDDAH* ake magana zai tsaya..?? kuyi min bayani na kasa
ganewa,kamar yadda na sani gidan tsarkin kasuwa bashi da wata yarinya bayan ta,itan ce ake
nufi ko kuwa wata daban aka samo,shin sarautar tsarkin kasuwa tana nan a gidan dana jima da
sani ne ko an canja..??" "Babu wani chanji da aka samu,gidan da Sarautar take har yanzun tana nan a gidan kamar
yadda kika riga kika fad'a,wannan maganar duka akan yarinyarsa muke yinta.."
Hawaye ne suka fara zirarowa daga idanun Ummi'n YASEER a lokacin da taji tabbacin Sarautar
tana nan a gidan data sani,kuma duk maganar kamar yadda taji ba kowa ake nufin za'a bawa
Yariman a matsayin sad'aka ba face *JEEDDAH,* gaba d'aya idanunsu ne ya koma kan Ummi
cike da mamakin kukan da take a lokacin,wanda nima ganin hakan da nayi ya sanya ni shiga
matuk'ar rud'ani game da wannan AL'AMARI'N da yake kan faruwa.........
*Shin wai fan's mene ne hawayen Ummi ke nufi..? Nikam na gaza fahimtar abunda yake shirin
faruwa fa..*

#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login