Showing 6001 words to 9000 words out of 29888 words

Chapter 3 - Wani Al'amarin Compelet Hausa Novels By Real Shamtr.pdf

03 Oct 2025

620

dariya tana tafa hannu da cewa
"A gaida na gaba.."
Bata ko juyo ba bare Sajida tasa ran zata kulata ta fice cikin fushi,duk da Hajiya tasan da
zuwanta a dai² wannan lokacin kam sam bata san da abunda ya faru ba,dan haka Aisha tana
fitowa babu ta kan wanda ta sake bi a gidan ta kama hanyar barin ROYAL PALACE d'in,sanda
ta isa gurin da tayi parking tana cikin matsanancin b'aci rai dan haka ko da tayi reverse a 360 ta
bar gidan ta kama hanyar gida,gudu kawai take shek'awa a kan kwalta,tana zuwa gida bata iya
tsayawa an bud'e get ba,tayi parking nan a waje ta k'arasa da k'afa zuwa cikin hararar gidan
tana shiga ta cillawa malam isuhu mai gadinsu key tayi cikin gida.
Shigowarta duk da bata cikin nutsuwarta nan ta iske k'arshen zancen na Ladidi kasancewar
cikin d'an d'aga murya take magana
"Haba Adda..! Yanzun ta yaya ne kam za'ayi ace Aisha ta gano ko su waye iyayenta..?? Ko
dama ace ta sani babufa abunda zata yi akai ki kwantar da hankalinki..Ko da zata gane ma
lokaci ya k'ure mata dan a dai² lokacin data gano hakan za muyi k'ok'arin b'atar da ita a
duniyar,shi kenan bata had'u dasu ba bare ta sansu.."
"Ba haka bane Ladidi..Sanin kanki ne daga lokacin da akace Yarinyar nan ta gane cewa daga
Royal palace take kuma can ne asalinta zamu shiga uku,duk da dai bawai hakan na nufin zata
yi saurin gano iyayen nata cikin sauk'i ba ki fahimci abunda nake nufi.."

"Shi kenan Adda amma ni dai gaskiya kima dena taso da wannan maganar dan bana son wata
rana maganar nan ta fasu har ta kai ga Aisha ta jimu muna yinta,dan bana fatan ta koma
hannun iyayenta.."
Saurin ja da baya tayi ta b'uya abayan k'aton flower base tana rufe bakinta da duka tafukan
hannayenta dan yadda maganar ya girgizata,cike da tashin hankali ta sake kasa kunne tana
sauraren taji me zasu kuma cewa,dai² nan malam isuhu yaja get da rufe shi wanda hakan yayi
sanadiyyar yi mata shamaki da maganar da su Adda keyi,suma kuwa suna jin haka suka
tabbatar da Aisha'n na daf da shigowa ciki,sai kawai suka rufe hiran,koda Aisha taji haka ai da
sauri ta koma da baya danma kada su Ladidin su zargi ko taji wani abu daga hiran nasu shi
yasa ta gwammace ta koma ta amshi keys d'in daga hannun Malam isuhu.

^^^^^
Kamar wanda aka tilastawa fitowa haka koda ya gama shirin kwanciya ya fito,dai² zai wuce
zuwa kitchen ya hangi table a shirye da kayan alatu a samansa,kallon gurin yayi ya d'auke kai
da nufin yayi abunda ya fito da shi kawai,har yaci gaba da tafiya kuma sai ya sake kai idonsa a
gurin,nazarin gurin yake da dukkan alamun yadda aka tsara gurin ba'a tab'a komai ba har
yanzun "kenan hakan yana nufin itama bata ci abincin ba har zuwa yanzun ko me hakan yake
nufi..?" Ya tambayi kansa,bai samu amsa ba dan haka kawai sai ya fasa wucewa kamar yadda
yayi niyya ya juyo da baya,hanyar bedroom d'inta yabi da niyyan tambayar ta dalili aikata hakan
da tayi,nan ya tsinci kansa da sake tambayar kansa
"Yanzun idan naje nace mata mene ya kawo ni..? Idan tayi zagin wani abu ya kawo ni fa..?
Girmana ya gama zubewa kenan..??"

Shiru yayi yana tunani,a hankali ya yamutsa fuska yana tura hannu a cikin curly hair d'insa,a fili
ya sake yin magana
"No YAZEED ba girmanka bane,idan kace zaka fara kula al'amuranta zata yi tunanin ko ka
fara sonta ne..Kawai ka share dan bata ci abinci ba mene zaka damu kanka,cikinta ne idan taga
dama taci.."
A fiki ya saki tsaki sannan ya wuce zuwa bedroom d'insa ba tare da yayi abunda ya fito da shi
ba.

^^^^^
A b'angaren YASEER kuwa tunda Yarima YAZEED ya sanar da shi ya dawo yake ta son su
had'u dan akwai abubuwa a dama da yake so su tattauna wanda kuma duka ya ta'allak'a ne
akan matsalarsa,sai dai har wajen 10:00pm basu had'u ba,wannan yasa ya bari zuwa gobe idan
sun had'u. Washe gari da safe kuwa kamar yadda yayi timing sanda suka had'u da shi a fada,bayan an
tashi a zaman Yarima ya fara fitowa sai YASEER,nan ya tadda shi a waje yana jiran
fitowarsa,hannu suka bawa juna suna exchange na murmushi da greetings,sannan YASEER ya
d'an kalli hanya,ganin babu mutane sosai sai ya kalli Yarima yana cewa "Broah.! When zamu zauna muyi maganar ne..??"
Kallon rashin fahimta yayi masa kafin ya tambayeshi
"Wane magana kake nufi ne..??"
Had'e fuska YASEER yayi cikin jin haushin abunda Yariman ya fad'a ya ce
"I don't know.."
Yadda yayi maganar yasa Yarima sakin fuska yana murmushi,cikin sigar maganar da babu
lallai mutum ya fahimci da wane yanayi yayi ya ce
"Kai matsalar ka kenan,sai ka d'auko magana idan an nuna ba'a gane ba,ba zaka yiwa mutane
bayani ba,idan na sani zan nuna maka ban sani bane..??"
Kallonsa YASEER yayi ya jinjina kai sannan yace
"Shall u says u have forget about ur conditions..??"
Tak'aitaccen murmushi kawai yayi ba yare da yayi maganna ba,ganin hakka yasa YASEER jin
haushi har ta kaiga yayi magana da cewa
"Yayi maka kyau..!"
Daga haka bai sake cewa komai ba ya rabu da shi,haka suka ci gaba da tafiya har sanda suka
zo inda zasu rabu kowa zaiyi apartment d'insa,anan ne Yarima yake cewa da YASEER
"Broah! Baka ji ba.."
Waiwayowa yayi ya kalleshi yana d'age gira d'aya sama ba tare da yayi magana ba,kallonsa
kawai Yarima yayi sannan ya furta
"Maganar da muka yi da kai jiya nake nufi.."

"Eheen..! Ina sauraronka sai aka yi yaya..??"
Wani kallo Yarima ya jefe shi da shi kafin yace
"A nan kake so muyi maganar..Da zaka cemin kana jina..??"
Dariyar rainin wayo YASEER yayi sannan ya ce masa
"Oohh! Ashe babu dad'i..?? Ni d'azun da nayi maka magana ina nunawa kayima kamar ba da

kai nake ba,shi ne daga yin d'an wannan maganar kai saboda kafi kowa har kayi fushi.."
Jin abunda YASEER ya fad'a ne yasa Yarima sakin fuska kana ya wuce ba tare da yayi
magana ba zuwa ainihin apartment d'insu,girgiza kai kawai YASEER yayi sannan ya biyo shi a
baya,ko da shigarsa a zaune ya iske Yarima da alama kuma shi d'in yake jiran ya k'araso,sanda
ya shigo shima neman guri yayi ya zauna sannan duka suka yi shiru na wucin gadi kafin
YASEER d'in ya kalli YAZEED yana sakin bayyananniyar ajiyar zuciya yana cewa
"Broah.! Ta ina kake ganin zamu b'ullowa wannan matsalan..?"
Shiru Yarima YAZEED yayi kafin ya girgiza masa kai alamun bai sani ba fuskarsa kuma d'auke
da damuwa
"Kana matsayin Doctor kace baka san ya zaka b'ullowa wannan case d'in ba..?? Haba Man
kada ka sani jin kunya mana,kai da kake da maganin matsalar wasu ai bai kamata kace baka
da naka maganin naka matsalan ba.."

"Yeahhh! I know,,buh kada ka manta ni ba Urologist bane ko Nephrology coz ba side d'ina
bane.."
Jinjina kai YASEER yayi sannan ya d'an yi murmushi
"To kaga yanzun ai ka fito da abunda nake son yi maka magana akai,first of it kamata yayi mu
fara tuntub'ar urologist sai mu san abunda ya kamata muyi..Ina ganin wannan hanyan kad'ai ya
kamata mu fara bi.."
Jinjina kai Yarima yayi cike da gamsuwa akan abunda ya kamata yayin kamar yadda ya samu
shawara daga bakin YASEER,sun jima suna tattaunawa akan matsaloli da dama sannan suka
fice daga apartment d'in.

Bayan kwana biyu da yin maganar tasu,Yarima ya dage gurin contacting likitoci da dama akan
matsalan nasa,alhamdulillah hakkan da yayi sosai ya taimaka masa wajen samun mafita ta
hanyar shawarwarin da yake yawan samu daga garesu akan matsalan nasa,bayan wasu y'an
kwanaki kuma ko da suka koma bakin aiki,sannan ne yayi k'ok'arin had'uwa da urologist a garin
abuja,amma abunda ya matuk'ar basu mamakin shi ne yadda duk wani bincike da aka gudanar
a kansa yake nuna komai lafiya,wannan dalilin yasa ya sake tuntub'ar YASEER akan hanyan
kuma daya kamata su sake bi.......





#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.



*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉

[7:31AM, 6/16/2019] Itz Ibraheem: 💠💠💠💠💠
*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*



 *WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*

مسب الله نمحرلا رلا .ميح
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Thanks 4 d luv n care Cweet mom Maryam (Meerahgee) am really appreciate..*

*MAMAN NOORUL HUDA ban manta dake ba,gaisuwarki ta mussaman had'e da jinjina ban
girma,fatan rabb ya k'aro basira,d'aukaka+hak'uri da jama'a..*
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 4.*
^^^^^^^^
Shigowar Aisha cikin parlour'n yasa su Adda yin shiru kamar ruwa ya cinyesu sai raba idanu
da suke cike da tsarguwa,duk da suna da tabbaci kan Aisha bata ji komai ba,fuskarta d'auke da
yanayi biyu ta shigo wannan dalilin yasa su kasa tantance ainihin damuwar ta,ladidi kam tunda
Aisha ta shigo take binta da kallo tana nazarin ta,a hankali itama ta d'an kallesu fuska babu
wadatacciyar walwala
"Adda barkanku da hutawa.."
Abunda kawai ta iya fad'a kenan cikin wata irin murya ta wuce zuwa wajen da center table yake
ta ajiye keys d'in hannunta kana ta wuce zuwa hanyan bedroom d'inta
"Aishatu daga ina kike ne..??"
Adda tayi tambayar tana binta da kallo,a hankali ta waiwayo tana kallon Adda da rinannun
idanunta
"Adda naje shopping nefa,kuma na bar sak'o a fad'a miki idan kin fito.."
Jinjina kai Adda tayi kafin ta sake k'are mata kallo

"Me yake damunki Aisha..??"
Kai ta girgiza alamun babu komai,nan kuwa Adda ta fara shan jinin jikinta
"Zo nan ki fad'a min abunda ke damunki,dan wad'annan idanun naki sun gama bayyanamin
kina da damuwa.."
Zama tayi a jikin Adda kana ta zame ta kwanta idanunta na ciccikowa da hawaye
"Ni Adda fa kaina ne kemin ciwo kawai.."

"A'a Aisha ban yarda da wannan ba,dole ne akwai wani abu daya b'ata miki rai,ciwon kai
kawai ba zaisa idanun ki dama ke kanki ku koma haka ba..Gayamin damuwar ki kinji y'ar
lelena.."
Tayi furucin tana d'an murmushin da ita kad'ai tasan ma'anar sa
"Ni...ni..nifa na ce miki babu komai kawai ciwon kan ne nake jin na yau kamar ban tab'a irin
saba,kuma ma ko a shopping mall dana je ne kawai wani guy ya b'ata min rai,shi nefa na dawo
ban sayo komai ba.."

"Kayya dai ni nasan ruwa baya tab'a tsami haka nan banza,ga inda maganar take nan,da nace
an miki wani abu kina cemin a'a yanzun kuwa ai naji gaskiyar zance,to amma tunda kika fita
wajen 12:00pm ina kika tsaya ba ki dawo gida ba har wannan lokacin.."
Tun kafin Adda ta kai aya ai tuni dabara ta fad'o mata
"Adda nifa park na wuce ko zan samu damuwana ya ragu,amma aikin banza yadda naje haka
na dawo duk ya haddasa min yini da b'acin rai.."
Kallon Ladidi Adda tayi tana kashe mata ido had'e da yin murmushi
"To yanzun maza je kiyi wanka sai ki kwanta ki huta idan kin samu bacci ciwon kan zai
sauka,na tabbata lokacin da kika tashi zaki tashi normal.."
Tura baki tayi gaba sannan ta mik'e tana jan d'an siririn Vail d'in data yasar nan a k'asa tayi
hanyan staircase tana tafiya kamar bata so,da ido su Adda suka rakata su duka biyun,tana
kaiwa ga b'acewa ganinsu kuwa nan Ladidi ta juyo ga Adda tana sauke nauyayyun ajiyan
zuciya "Haba Adda ni dai nasan dama babu yadda za'ayi ace taji abunda muka ce,tunda tun kafin ta
shigo muka bar maganar.."

"Ke bazaki gane ba,kamar yadda hausawa ke cewa 'magana zarar bunu' wannan karin
maganar tasu haka yake,muka sani ko iska ya d'iba ya kawai mata,abunda duk baka tab'a
tsammanin wanda kayi dominsa zai jiba shi yafi sauk'i a gurinsa ya sani,amma tunda Allah yaso
bata jiba shi kenan,dama shi yasa nayi ta tambayarta ai ko ta jin,sai kuma muka yi sa'a bata ma
san munyi ba,dan ni dai yanayin fuskarta shi ya bani tsoro sanda ta shigo.."
Wata dariya Ladidi tayiwa Adda dan yadda duk ta shiga reserve kamar ance mata a gaban
Aisha'n suka yi zancen.Ita kuwa Aisha dai² lokacin data shiga bedroom d'inta kulle k'ofar tayi da
key,a hankali hawayen dake mak'ale a idanunta suka samu damar fara sauka saman
fuskarta,saurin toshe bakinta tayi da hannunta d'aya tayi hanyar toilet da gudu,sanda ta
tabbatar ta shiga ta kulle k'ofar had'e da kunna tap ta k'uresa yana sauka k'asa ta saki wani
marayan kuka mai cike da ban tausayi,ta d'auki tsawon lokaci tana rera kuka a nan cikin toilet
kafin ta fito sai ajiyan zuciyar da take ta saki babu k'ak'k'autawa,saman bed ta haye kasancewar

tana fashin sallah lokacin,duk da sallar ma ba damunsu tayi su yita akan lokaci ba,dan wani
lokacin ma idan ta wuce tofa baza ayi ta ranar ba,daga nan kuwa bacci mai cike da wahala ya
d'auke ta..

^^^^^
Sam cikin wad'annan kwanakin Yarima baya wani samun lokacin zama bare Sajida tasa ran
ganinsa ko samun wata kulawa daga gareshi,idan yana garinma a wasu lokutan zaka samu sun
fice ne tare da YASEER,kuma duk wannan zirga² da suke yi ba kan komai suke ba sai na
neman magani da neman mafitan matsalan data ke tattare da Yarima,a mafi yawan lokuta kuwa
idan sun fita baya samun dawowa gida da wuri sai dare,wani lokacin kuma yana cikin gidan
suna tare da YASEER a apartment d'insu na da,dan wani lokacin ma a nan YASEER yake tafiya
ya barshi,ba shi zai fita ba sai ya tabbatar sahun k'afafu ya d'auke sannan ne zai fito ya wuce
nasa apartment d'in.
Wannan weekend d'inma koda suka dawo garin basu zauna ba,tafe suke a mota yayin da
Yarima YAZEED yake driving,shiru motan ya d'auka babu mai magana a cikinsu,har YASEER
ya juyo zaiyi masa magana kunnensa ya kwaso masa tallan irin masu maganin gargajiya d'in
nan,ai take yayi shiru ya fasa maganar,kana ya juya yana kallon side d'in da mai maganin
yake,tsaf tallan ya d'ebi hankalinsu duka musamman ma YASEER dan kisan zan iya cewa yafi
damuwa da ciwon Yariman akan shi da ciwon ke tattare da shi har abun yaso rud'ar
YASEER,cike da mamaki YASEER ya kalli Yariman yana shirin yin magana Yariman ya riga shi
"Broah..! Anya kuwa gaskiya ne wannan duka abun daya lissafo.??"

"I don't know.. Buh ina tunanin magani ai sai mutum yayi trying kafin ya gane gaskiyar
ingancinsa.."

"No broah i don't mean ur words..Na tambaya ne nima,ba wai zan yi anfani da shiba,amma kai
yanzun kana nufin tunda har yanzun ba'a san mene actual matsalan ba sai nayi trying irin
wannan traditional remedy's d'in..??"

"K'waraifa..! Nima ina tunanin haka yanzun kam."
Cikin k'araji Yarima ya buga masa wata tsawa
"Haba..! Man nine zanyi taking irin wannan traditional things d'in..?? Ni wai kake nufi..??"
Kallonsa kawai YASEER yake yana matse dariyar dake son taho masa saboda yadda yaga
Yarima ya fututtuke fuska,kai yake girgizawa yana kallonsa had'e da fad'in
"Never...!"
Kallonsa YASEER yayi yana had'e fuska
"Shi kenan to tunda baka so,ai sai kayi ta zama with ur syndromes,a hakan nan kuwa da kake
wollahi babu yarinyar da zata juri zama da kai duk kusancinku ko dangantakar ku,gara ma tun
kafin su Hajiya su fahimci wani abu kayi k'ok'arin amfani da different medications,if not kuma
nayi alk'awari ni da kaina zan je na sanar da Hajiya har ma da su Ummah Fulani,dan wollahi
kaji na rantse ko dai kayi abunda ya kamata ko kuma zan sa a tara maka family aka.."
Wani uban juyowa yayi ya kalli YASEER
"Are u insane...??"

Harara YASEER ya jefe shi da ita
"Aaa! Ka manta am from asylum.."
Tsaki Yarima yaja sannan ya d'auke kai had'e da yin shiru daga magana da YASEER dan ya
fahimci idan yaci gaba da magana da shi yau kam ba zai barshi ya sha ruwa cikin nutsuwa
ba,yadda yayi shiru ya d'auke wuta yasa YASEER

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login