Showing 24001 words to 27000 words out of 29888 words

Chapter 9 - Wani Al'amarin Compelet Hausa Novels By Real Shamtr.pdf

03 Oct 2025

1212

bincike
akan wannan hamshak'in saurayin naki da kike rawar k'afa akansa,kafin nace komai zan fara ne
da baki shawaran bincikar asalinsa da halayensa,mun san kinsan waye muke nufi a wannan
d'an tak'aitaccen zancen namu,duka ba wani muke magana akansa ba face *YARIMA YAZEED*

babban d'a ga Sarkin Kano ABU YAZEED...Mun so sanar dake wasu muhimman abubawa
dangane da shi,sai dai bama so kiji daga gare mu,amma ga kad'an daga cikin tarihinsa wanda a
ciki ya had'a da zamansa a gidan kaso har na tsawon shekaru biyar,idan har kin d'auki wannan
maganar wasa lallai ne kin tabbata *lusara* haka nan idan kin yarda kin tabbata *mai
wayo*,idan kin aminta da batun/baki aminta ba zaki iya bincikawa da kanki dan ki tabbatar da
gaskiyar wannan maganar...Mun barki lafiya.!"_
Maimaita karanta sak'on take ko zata fuskanci abunda ake nufi,a k'alla saida ta karanta ta
maimaita yafi sau a k'irga kafin ta fara dawowa cikin nutsuwarta,tana daga zaune saman stool
d'in amma jiri take ji yana neman kada ita k'asa,a daddafe ta mik'e a gurin ta isa bakin Italian
bed d'inta ta kwanta dan yadda take jin zuciyarta na wani irin skipping kamar zata faso k'irjinta
ta fito kan tsabar tashin hankalin da take jinta acikinsa,k'aran shigowar wani sak'on a karo na
biyu ne yasa ta d'an mirgina gefe tana kallon wayanta,da kyar ta iya kai hannu ta d'auka dan a
lokacin ji take komaima yayi mata nauyi,a hankali tayi clicking sannan ta fara karantawa
_"Idan har kin aminta da abundabatun da muka fad'a a yanzun,muna so ki fara investigation
daga yanzun,nd kafin kiyi tunanin tunkarar Central Jail ki fara ta kan *REMAND HOME* dake
nan Kano state a Goron dutse,Dala L.G.A,coz zaki fi samun abunda kike buk'ata,na tabbata
daga lokacin da kika san komai zaki fahimci waye asalin *YARIMA YAZEED..! "_* Shiru ta d'auka har bata san lokacin da wayan ya zame a hannunta ya fad'i k'asa ba,nan da
nan saddest tears suka fara chasing akan cheeks d'in ta,ba tare data san dalilin kukan ba,dan
kanta kuma koda ta gaji ta bar kukan,ta jima shiru ita d'aya yayin da zuciyarta ta tafi can wani
nahiya na daban,tana tsaka da mugun tunanin kirana ya shigo wayantaamma tayi biris da shi ta
kasa koda motsawa bare ayi tunanin zata d'auka,haka yayi ta kiranta amma tana ji tak'i koda
d'aukan wayan bare ta duba taga waye yake kirantan.

A can gefen Yarima kuwa,kamar yadda yayi mata alk'awari zai je,tun bayan da ya gama shirin
zuwansa yake ta trying kiranta amma sam tak'i d'auka,ko da ya kira ya maimaita ba'a d'auka ba
sai kawai ya hak'ura da neman line d'in zuciyar sa na wani irin tsinkewa dan yadda fargaba ta
sashi a gaba har ya rasa abunda zaiyi. Tunani ya d'an tafi tin daga time d'in da yake sanar da ita zuwansa har kawo yanzun da yake
tsaye,amma sam ya gaza gano wani abu da zaisa tak'i picking call d'in nasa,"shin mene ne
yake faruwa haka da zai ta kiranta ta kasa d'auka...??" Ya d'auki wasu y'an mintuna yana tunani
amma ko d'aya bai gano wani dalilin da zai kama ba akan ko yayi mata wani abu ne,a hankali
ya koma ya kwanta saman resting chair yana sauke numfashi cikin zuciyarsa yana fata akan
baiyi mata wani abu da zaisa tak'i answering call d'insa ba,yana wannan tunanin bacci mai cike
da fargaba ya d'auke shi a nan dan dama ba wani cikakken bacci ya samu yayi ba da dare coz
bai dawo daga hospital da wuri ba.

^^^^^
A can gefen Aisha ma,ba'a barta a baya ba dan tun daga lokacin da yarima ya gargad'i
Sajida akan baya son ganinta ta shatawa gidan line ba'a sake ganinta ba,haka ko data samu
labarin abunda ya faru na daga rabuwar auren Sajidar da Yariman duk da taji babu dad'i a ranta
na daga faruwar hakan ba,haka tana zargin kanta da aikata mummunan nufin da aka sata duka
a garin neman comma buri sai dai ta san ko giyar wake ta sha bata isa ta fito ta bayyana cewar

ga ainihin abunda ya faru da har ya janyo hakan ba,kullum a yanzun bata da aikin da ya wuce
yini a d'aki idan ta gaji da zaman kad'aici kuma ta d'auka car keys ta fice zuwa park,wani lokacin
idan ta rasa abun yi haka zata yita kuka ko ta samawa zuciyarta ta sassaucin damuwoyinta,tare
da fatan Ubangiji ya bayyana mata wata hanya da zata sadu da wani nata.
Duk irin wannan jin kan da Aisha ta kasance tana da shi a yanzun ta koma wata iri,mutanen
da ada take d'aukan su ba komai ba,yanzun idan ta gansu sai dai ta bisu da ido,wanda sosai
wannan canjin d'abi'un nata suka fara bawa da yawa daga cikin mutane mamaki,amma kowa ya
b'oye abun a ransa yak'i furtawa,ni kuwa dai nace ko me suke tunani da suka k'i fad'an ohoo
musu.

^^^^^
Tun data gama kukan ta mik'e da mataccen jikinta da take jin duk duniya ma tayi mata zafi,ta
shafe a k'alla mintuna sama da 40 tana tunani da kokwanton al'amarin kafin ta amshi tayin da
zuciyarta take mata game da tracing case d'in da aka fad'a matan,sai data gama shiryawa kafin
ta nemi guri ta zauna tayi connecting bluetooth d'inta dana wani amintaccen security'nsu mai
suna Saleem,cikin kasala take magana da zallan harshen nasara
"Hello..! Saleem kana ina...??"
Shi ne abunda ta fara fad'a,banji amsan da ya bata ba,sai dai naji tace
"Ok..Kazo yanzun ina son ganinka..!"
A hankali ta koma ta kwanta da baya tana closing eye's nata,mintuna kad'an akayi nocking
door d'in,ba tare data bud'e ido ba kota damu da duba waye ta furta
"Shigo..!"
K'ofar ya turo bakinsa d'auke da sallama,ya tsaya yana jiran yaji me zata fad'a,still tana daga
kwancen ta furta
"Saleem..!"
Ya amsa mata da girmamawa
"Yes ma'am.."

"Kasan dalilin da yasa na kiraka..??"

"No! Ma'am.."
Jinjina kai tayi duk da yadda take jin kanta kamar zai bar gangar jikinta,a hankali taci gaba da
magana
"Kasan dai yarda ce tasa har yanzun kake nan a matsayin guard namu ko..??"

"Yes! Ma'am..!"
Sai a lokacin ta yunk'ura ta mik'e zaune tana runtse idonta
"Good..! Ina son na saka wani aiki ne,nd ina fatan zaka yi,sannan ya kasance sirri dan bana
son kowa ya sani bayan mu biyun nan.."
Jinjina kai yayi cike da gamsuwa,a hankali ita ta jinjina kai kafin ta kai hannunta kan laptop
dake gefenta ta shiga y'an wasu dube²,kusan mintuna biyar ta d'auka kafin ta d'ago tana fad'in
"Na tura maka da abunda nake buk'ata,nd it's urgent,i need it within a few hour's idan da

hali..!"

"Ok ma'am...as u wish.."
Kud'ad'e ta zage jakarta ta ciro wanda ita kanta bata san ko nawa bane,ta mik'a masa tana
sake fad'in
"Idan da wani abu kuma let me know.!"
Bayan nan ta sallameshi bayan ta gama masa k'arin bayani,nan ya fita ya barta zuciyarta cike
da wani irin panic da yake taso mata.

Bayan fitar guard Saleem daga gurin uwar gijiyar tasa,sai ya shiga k'ok'arin duba abunda ta
tura masa,nan yaci karo da sak'onta,ko daya gama dubawa daga nan airport ya nufa don yin
bucking flight wanda zai kai shi Kano.Sai dai yayi rashin sa'a dan a ranar bai samu jiri ba,sai dai
ya gama komai damar tashi ne babu a ranar,sai ya jira washe gari kasancewar bai riga da yayi
bucking da wuri ba da yake yamma yayi masa a lokacin.

A washe gari kam tun da sassafe ya gama shirin tafiya,misalin k'arfe 7:00am jirginsu ya tashi
sai Kanon dabo,in 3 hours 48 minutes jirginsu yayi arriving,kai tsaye sanda ya fito daga airport
d'in yayi nemi cab daga nan zuwa criss cross hotel dake nassarawa don ya kama lodged na
kwana biyar kamar yadda yake tunanin binciken nasa ba zai haura wannan kwanakin ba,haka
nan baya tunanin zai haura wad'annan kwanakin ba tare daya koma ba,sanda ya huta ya samu
abinci ya kaiwa yayan hanjinsa sannan ya fara tunanin kiran madam d'in nasa,tana d'auka ya
sanar da ita sun sauka lafiya,daga nan kuma suka d'an sake tattaunawa tana sake bashi logic
na yadda ya kamata ya fara binciken,amsawa yayi with reverence sannan suka yi sallama.

^^^^^
Yarima kuwa a nasa gefen tun daga kiran da yayi ta mata tak'i d'auka,bayan ya tashi a bacci
ma haka bai hak'ura ba ya sake trying number nata amma still bata d'auka ba,jikinsa ne ya sake
mutuwa dan yasan haka nan banza bazai tab'a yi mata irin wannan kiran tak'i responding
ba,kuma yasan baza taga miss calls nasa ace har tsawon wad'annan awannin tak'i bin kiran
ba,sai dai ko idan akwai wani abu dake kan faruwa,wannan tunanin ya zo masa a lokacin.
Yini guda haka yayi ta fama da kiranta ba'a d'auka daga k'arshe da ya sake trying sai jin wayar
yayi a kashe,sosai abun ya d'aure masa kai dan bai tab'a tunanin hakan daga gareta ba,washe
gari ma abunda ya faru kenan,ganin hakan ba mafita bane yasa ko daya tashi a aiki ya kasa
wucewa gida,kai tsaye sai ya nufi hanyar gidan su Zahra'n dan jin abunda ke faruwa,sanda ya
iso tun daga get d'in farko na line d'in inda securities suke suka fara shaida masa madam d'in
bata nan kamar yadda ta bada umarnin a sanar da duk wani mai nemanta,abun ya bashi
mamaki sosai har ya fara tambayar kansa "me ke faruwa haka..??" Reverse yayi kawai ya
kama hanyar gida,da zuwansa ya yada zango tun daga parlor,dan daga suit d'insa har lab coat
d'inma a hannu ya shigo da shi yana shigowa kuwa ya ci gaba da k'ok'arin zare tie d'in wuyansa
yana b'alle botiran long sleeve d'in,shigowar YASEER kenan shima bayan y'an mintuna ya tarar
da shi a wannan halin idanunsa a rufe ya dafe forehead d'insa da hannu d'aya,kallo d'aya ya
masa ya fuskanci akwai damuwa sai dai bai tsaya kusa da shiba ya wuce ya barshi a
nan,sanda ya samu nutsuwa ya dawo ya zauna kusa da shi yana tab'a shi,bai d'ago ba haka

bai bud'e idonsa ba ya furta
"Leave me alone..Please!"
Mamaki sosai YASEER yayi da jin maganarsa,nan ya sake tabbatarwa ba lafiya ba,duk da yaji
abunda ya fad'a hakan bai hana shi tambayar saba
"Broah..! What happened..??"
Wani irin huci ya fesar mai d'umi sannan ya bud'e ido a hankali yana kallon YASEER
"Ina cikin matsala broah.."
Ajiyar zuciya YASEER yayi kafin yace
"Duk damuwarka u have to pray,kasan komai mutum yake in har zai dunga addu'ah zaiga
sauk'i ko..??"
Kai ya jinjina masa cikin wani irin yanayi da bai sanma yayi ba.Wasa² sai da suka shafe ak'alla
4 day's a haka ba tare da ya samu wani madogara ba daga ganeta.

^^^^^
Ita kuwa Zahra tun bayan data gama magana da guard Saleem lokacin daya sauka a Kano take
yawan jin fad'uwar gaba mai tsanani,haka ta ci gaba da daurewa tun abun na damunta sosai
har ya zama ta fara yakice shi a ranta.
Tsawon kwanaki uku Saleem ya d'auka a Kano duk akan binciken a ranata hud'u ya juyo zuwa
Abuja cike da nasarar abunda ya kaishi,lokacin daya shigo garin Abuja bai jira zuwa ya huta ba
kai tsaye ta wuce gidan Ambassador Abdulmalik don kai rahoton aikinsa.A dai² lokacin daya iso
itama Zahra shi d'in kawai take jira dan tunda ya sauka daya shaida mata yana nan tafe ta kasa
zaune bare tsaye,cike da zumud'i ta tare shi da muradin ganin abunda tasa shi yayi mata
binciken,can k'asan zuciyar ta kuma tana fatan sakamakon ya kasance sab'anin abunda zuciyar
ta ke hakaito mata,lokacin daya tsaya gabanta yana gaisheta ko takan gaisuwar sa bata biba
dan ita ba shi ne abunda tafi damuwa da shi ba,wani dogon sharhi Guard Saleem ya fara mata
nan ta d'aga masa hannu cikin kasala ta ce
"Ba abunda nake buk'ata kenan daga gareka ba,ina aikin dana saka..??"
Tana mik'a masa hannu,babu yadda ya iya dolensa ne yayi abunda tace,dan haka babu b'ata
lokaci ya shiga clicking wayansa yana duba folder d'in da yayiwa duka documents daya samu
game da abunda ya shafi rayuwar Yariman a REMAND HOME,Harma zuwa zamansa a Central
Jail,lokacin data karb'a harta juya ga laptop d'inta sai kuma ta kalleshi a hankali ta ce "Kaje saina nemeka..!"
Daga haka bata kuma bi ta kansa ba ta juya,nan shima yayi mata godiya sannan ya fice.Ita
kad'ai ya rage d'akin bayan fitar guard Saleem,nan take tayi connecting wayan da computer ta
shiga dubawa,page by page ta fara bi tana dubawa,har ta kai k'arshe wanda duk cikin dauriya
ne take binsu,izuwa lokacin kuwa idanunta har sun gaji da tsiyayar ruwan hawayen da har bata
san adadin kukan da tayi ba,tana zuwa paging k'arshe kawai sai ta kife computer tana sake
rushewa da wani irin saddest cry,sanda ta gama kukanta tsaf sannan ta kuna network d'in
wayan dama shi ta kashe bawai wayan ba,number Yarima ta shiga trying bugu biyu ana uku
yayi answering yana sakin siririyar ajiyar zuciya,tashin farko kalmar daya fito a bakin Zahra shi
ne
"Me yasa zaka munafurce ni..?? Why ain't u told me the truth of ur affairs..? Why do u need to
hide these important issues..?"

Shi dai yarima jin abunda take fad'a ne yasa kalmomin da yake son fad'a mak'alewa a fatar
bakinsa
"Da gaske ne ka tab'a rayuwa a *Jail...??"*
Maganar yazo masa a bazata,had'e da wani mugun tashin hankali daya ziyarce shi wanda
tunda yake a rayuwarsa wannan shi ne karo na biyu da zai iya tunawa daya tab'a jin
kwatankwacin hakan a tare da shi,shirun da yayi bai amsa taba yasa ta fashe da kuka tana
cewa "I will never marry u azzalumi..! Ka cuce ni ka kuma zalunci zuciyata,da sannu zaka ga
sakayyan abunda kamin..!"
Runtse idonsa kawai ya iya yi yana jin yadda maganarta ke shigar sa tamkar kaifin takobi tana
ratsa duk wani gab'a na jikinsa,ko kafin ya kaiga yin wani magana tuni har ta katse kiran tana ci
gaba da fashewa da matsanancin kuka...............


*#Tofa...! Wannan shi ake kira da "tashin hankali.....(gobarar gemu)" 😢😢,wai shin Fan's me
yake shirin faruwa da Yarima ne kuma ma..?? Ni kaina na gaza fuskantar komai...Ku kawo
agaji..😭😭😭*




#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.



*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉

*©® 2019..*
*WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*

مسب الله نمحرلا رلا .ميح
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 13.*
^^^^^^^^
*#His Slave*
Har jirginsu yayi arriving a Kano,babu wanda yasan da zuwansu,dan haka ko da suka sauka
banyi tunanin akwai wanda zaizo tafiya da suba,amma abun mamakin sai naga wasu mutum
biyu sanye da kayan fadawa wanda bayin masarautar kano ke amfani da shi,a wani k'atuwar
range robber mai duhun glasses suna jiran isowarsu,fitowarsu babu jimawa bayin suka nufe su
had'e da amsar luggage's d'in sannan suka bud'e musu k'ofa suka fad'a cikin motan,mintuna 30
suka kawo su royal palace,ba tare da kowa yasan da zuwansu ba suka nufi apartment d'insu,sai
a sannan ne YASEER ya d'an kalli yarima cike da fargabar abunda zai biyo baya yana cewa
"Broah.! Yanzun me zamu fad'awa maimartaba idan ya tambaya dalilin dawowar mu dai² lokacin
da yasan muna kan aiki...??"
Wani kallo Yarima yayi masa mai kama da harara kafin yace
"Say's whatever ur mind personified.."
"Haba broah yanzun kawai saina fad'a masa nayi resigned a aiki,me kake tunanin zai faru..??"
Gaba d'aya ya juyo yana fuskantar sa,cikin magana mai kama da gatsali ya furta
"Are u ready to violate at him..??"
Kai YASEER ya girgiza,nan shima Yariman ya ci gaba da abunda yake yana sake cewa
"If u didn't..Just ka fad'a masa abunda ya faru kawai.."
Jinjina kai yayi kamar wani dole sannan ya zube cikin cuition yana sakin ajiyan zuciya,zaman
kurame suka fara ko da ganin haka yasa YASEER d'aukan waya ya shiga clicking,number
Ummi'nsa ya fara kira kafin ya nemi matarsa,da sallama ta amsa masa after sun gaisa take
tambayarsa "Son ya aikin..??"
Ajiyan zuciya yayi guiwansa cike da sanyi ya ce
"Ummi muna Kano ai yanzun.."
"Kano..?? Yaushe kuka zo d'in.. Nd mene ya kawo ku Kano..??"
Jim yayi yana tunanin yadda zai fad'a mata abunda ya faru,yana a halin shirun yajiyo muryar ta
cikin fad'a tana sake tambayarsa,sai da yayi jarumta sannan ya iya cewa
"We make a decision to resigned..!"
Duk da Ummi bata gurin sanda ya fad'i kalmar sai data fidda ido waje,kalmar Innalillahi wa'inna
ilahiii raji'un kawai take maimaitawa,sai data maimaita yafi sau nawa sannan tace
"What happened..?? Da har ya janyo za kuyi wannan d'anyen aikin ba tare da kun sanar damu
halin da ake ciki ba..?? Anya kuwa yaran nan kuna cikin hankalinku..??"
Shiru yayi har zuwa lokacin data kai aya sannan cikin sanyi yace
"Ummi please na,bafa haka nan muka yi abu da kai ba,it becomes necessary..!"
"Kai ban son shirmen nan naku,idan banda kun raina mutane me zaisa kuyi hakan..?? Shi
kenan idan kunga dama tunda kun baro aikin sai ku zauna gida tunda haka kuka zab'a.."
"Please Ummi zan k'araso yanzun zaki ji dalilin faruwar hakan in sha Allah,bada niyyan muka yi

ba..."
"Allah ya kawo ka lafiya,idan naji abunda bai min ba ai kasan rai zai b'aci.."
Ajiyar zuciya yayi sannan ya furta
"Ummi sai dai na shigo d'in.."
Daga haka suka ajiye wayan,duk abunda yake idanunsa na kan Yarima daya kwanta idanunsa
a rufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login