Showing 15001 words to 18000 words out of 29888 words

Chapter 6 - Wani Al'amarin Compelet Hausa Novels By Real Shamtr.pdf

03 Oct 2025

1211

ta
sake jin abun wani iri sai dai kawai tayi shiru bata ce komai ba yaci gaba da sauraro tana jiran

taji abunda bai mata ba,Abba GALADIMA ne ya sake kallonsu kafin yaci gaba da magana
"Alhamdulillahil.! Da Allah yasa haka ta faru kuma a gaban kowa,duk da kasancewar mu mun
fito ne ta tsatso d'aya,sai dai wannan ba shi ne dalilin da zaisa mu yanke hukunci kai tsaye ba
tare da munyi shawaran da junan muba,alal hak'ik'a duk da ni an d'ora mun wannan nauyi
wanda ya zama wajibi akaina na sauke,ba shi ne hujjar da zata sa nayi abu kai tsaye ba,sai dai
duk da haka bazan ce komai ba yanzun har sai mun tuntub'i yaran nan kunji ta bakinsu gudun
kada mu tauye su mu shiga hak'ik'insu,a bisa haka nake ganin dacewar mu tambayesu idan har
suna ganin zasu iya yiwa junansu adalci kuma zasu iya jinkirin shekara guda zuwa muga yadda
hukuncin Ubangiji da abunda ya k'addara zai kasance..Ko kuwa me kuke gani..??"
Yayi tambayar yana kallon duka mutanen wajen kama daga kan Hajiya,Maimartaba,Umma
Fulani,Abba Matawalle,Hajiya Suwaiba,Ummi'n YASEER,har zuwa kan sauran yaran dake
zaune a gurin su da abun kW faruwa akansu,tun kafinma ya kaiga tambayar su Yarima ai tuni
Hajiya Suwaiba tayi tsallen albarka da cewa "Ai GALADIMA ina ganin ba sai anyi haka ba,abunda kawai yafi cancanta kuma yafi kamata
ayi shi ne a raba wannan auren ni dai a nawa ra'ayin hakan nake ganin zaifi..!"
Bata k'arasa ba Abba Matawalle ya datseta
"Haba Suwaiba shin abunda ya kamata ya fito daga bakinki kenan..Idan kuma ace yaran nan
sun k'udurce basa son a rabasu kiyi yaya kenan..??"
Hura hanci ta shiga yi kafin ta bashi amsa
"Haba Abban Sajida shi kenan kai dan Allah komai ba zaka iya tsayawa kayi ba sai dai ka bada
wakilci,nifa gaskiya bana son irin wannan rayuwar,yanzun dan Allah banda kai ta ina zaka sowa
yarinyar nan zama da mutumin da babu abunda zai iya amfanawa rayuwarta..?? Ai ni wollahi
nama ga k'ok'arin ta data iya hak'uri da juriyar watanni biyar,Allah ya sani babu yadda za'ayi
rayuwa ta yiwu kuma tayi kyau tsakanin mutum mai lafiya da kuma *GUNKI........."*


*Bola'i...! Wai shin fan's dawa Hajiya Suwaiba take ne...? Waye ta kira da GUNKI..??* 😱😱😱


*Sai kunyi hak'uri dani,har yanzun muna cikin wani yanayi ne na rashin wutar NEPA,amma in
sha Allah komai ya zo k'arshe dan a ko wane irin yanayi zaku ga na dawo kamar da,nd sai
kunyi hak'uri da turancin nawa coz na y'an koyo ne...*🙈🙈


#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.



*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.* 😉
[9:42PM, 6/21/2019] Hajjaju: 💠💠💠💠💠

*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*



 *WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*

مسب الله نمحرلا رلا .ميح
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*HAPPY BIRTHDAY IN ADVANCE.*
_On this birthday i wish that u have a young life by living honestly,eating slowly and learning to
lie about ur age.😜Happy Birthday in advance sisters.!��_
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 8.*
^^^^^^^^
Kalmar data fito a bakin Hajiya Suwaiba ba k'aramin bawa ilahirin mutanen parlour'n mamaki
tayi ba musamman ma Umma Fulani who feels Hajiya Suwaiba's words like descent of fluid
steel,yau wai ita ce har ake jifan d'an cikinta da irin wannan kakkausar maganar kuma tayi shiru
ta kasa cewa komai duk da yadda taji maganar a ranta,sai dai ko kafin ta kaiga gama wannan
tunanin har tayi magana tuni Ummi ta amsa maganar
"Hajiya Suwaiba waye kike kira da *GUNKI..??*

"Yo akwai wanda sunan yafi dacewa da shi ne sama da wanda aka had'a yarinyata da shi..??
Fisabilillah! Ai kunsan bashi da cikakkiyar lafiya amma kuka gagara sanar damu gaskiya
saboda tsabar cuta,kuma a rasa wadda za'a had'a da shi sai yarinyata,duk iya irin wannan abun
kuma bai isa ba sai azo a nemi k'arawa da makircin ta jirashi har na tsawon shekara guda..??" Tsawa Hajiya tayi mata saboda yadda taga zuba mata idon da suka yi ya kasa sawa tayi
shiru,irin kwarjinin dake tattare da ita shi yasa ta yin shirun da bata yi niyya ba,ran Hajiya a
lokacin idan akace yayi dubu wajen b'aci tofa tabbas babu musu,ga Abba Matawalle kuwa a
dai² wannan lokacin kunya ce tayi masa wani irin sauka duka ta lullub'e shi saboda irin

maganganun da Hajiya Suwaiba ta furta ji yake kamar ya tsaga k'asa ya shige dan yadda yake
jin kunya da nauyin wad'annan bayin Allah,kaf babu wanda baiji daban ba a gaba d'aya
kalamanta sai dai babu wanda yayi mata magana,nan take Maimartaba dake zaune tun farko
baiyi magana ba ya kalli Yarima kana ya juya ya kalli Sajida maganarsa cike da mulki ya ce "Sajida shin kina ganin zaki iya zama da d'an uwanki duk da wannan larurar da aka tabbatar
yana tare da shi..??"
Duk da bata d'ago ba bare ta kalli maimartaba sai da taji shakkar amsawa dan yadda nuryarsa
kad'ai ta cika ido da zuciyar ta da kwarjini,kusan sau uku yana maimaita tambayar amma ko
guda d'aya ta kasa amsawa sai kai da take sake sunkuyarwa a duk lokacin da yayi
maganar,duk abunda ke wakana akan idon Abba Matawalle ne dan yana ankare da yadda
Hajiya Suwaiba wacce tun d'azun take girgizawa Sajida kai tana kuma warning d'inta da ido
akan kada ta kuskure ta amsa abunda ake tambayarta,wannan dalilin yasa Matawallen jin wani
irin takaici da haushin abunda Hajiya Suwaibar keyi sai dai ya zuba mata ido ne yaga ko zata yi
hankali ta kuma yi masa kara,b'angaren Yarima Maimartaba ya dawo da tambayarsa inda yake
cewa
"YAZEED..! Shin har yanzun kana son matarka,zaka iya ci gaba da zama da ita..Ko kuwa kana
da wani uzurin..??"
Shi kansa kasa magana yayi dan yadda yake jin nauyin mahaifansa da nauyin abunda yake
k'unshe a k'asan zuciyar sa,saima sake sunkuyar da kai da yayi tamkar mai d'aukan
darasi,tab'a shi YASEER yayi yana masa alamar ya amsa amma ina gogan yayi kirim babu
amsa (kamar dai sunan da hajiya Suwaiba ta rad'a masa..face smile:-),a hankali Abba
Matawalle ya sauke ajiyar zuciya sai dai ko kafin ya k'arasa sauke numfashinsa tuni muryan
Hajiya Suwaiba tayi masa kutse cikin lamarinsa
"Gaskiya harga nifa ina da abun cewa,tsakani da Allah idan har ba'a bani dama an fita
hak'k'ina na uwa mahaifiya ba anyi ba dai² ba..!"
Kallonta kawai yayi yana girgiza kai cike da takaici ba tare da yayi magana ba,dan yadda
takaicinta ya sa shi neman abun fad'a ya rasa,maganarta babu wanda bata bawa mamaki ba
sai dai kowa ya adana hakan a ransa,ga maimartaba kuwa duk da yaji rashin dad'in kalamanta
hakan bai hana shi yin magana ba "Hajiya Suwaiba shin kina da wani abun fad'a ne..??"
Tun kafinma ya k'arasa har ta karb'a masa
"K'warai kuwa ni nake da abubuwan fad'a tunda naga kowa ya rasa.."
Daman magana ya bata inda take ba tare da tsoron Allah ba ko kunyar wad'annan nayi nasa
ta fara fayyace duk abunda ke k'unshe a ranta
"Yanzun Fisabilillah! Tun farko da aka san yaron nan yana da larura ai bai kamata ma taso da
batun za'a had'a auren nan ba,sai a bari idan ya samu lafiya duk ma abunda za'ayi ayi kufa
duba zancen nan,amma saboda Allah sai bayan komai ya cab'e sannan ayi batun zama
tsakanin wacce take lafiyayya da majinyaci..?? A gaskiya idan har a son raina ne kuma ana
neman mafita nikam gara a raba auren nan shi yafi komai zama masalaha a garemu,in yaso a
nema masa magani ko kuwa wannan fa itace magana ta domin Allah.."

"Shin abunda za ki iya cewa kenan..??"
Abba GALADIMA ya tambaya

"K'warai kam wannan itace magana ta,kuma nasan ko ita yarinyar nan shirun da tayi ba yana
nufin zata iya zama da mutumin da bazai iya morarawa rayuwarta wani abu bane..!"
Babu wanda ya iya yin sharhi akan maganarta sai Abba Matawalle da ya kalleta ya zabga maa
harara cike da haushinta yace
"GALADIMA nifa ina ganin tun farko munyi kuskure.."
Kallonsa duka parlour'n suka yi jin wannan furucin da yayi wanda yasa wasu da dama a ciki har
sun fara zaton ko dai shima d'in yabi bayan maganar Hajiya Suwaiba,fuskar Abba GALADIMA
da mamaki ya kalleshi yana tambaya
"Kuskure wane iri kenan Matawalle..??"
Ajiyar zuciya yayi yana d'auke kansa daga kallon Hajiya Suwaiba da yakewa warning da ido
akan kada ya sake jin bakinta a zancen da ake
"Yo nace munyi kuskure mana,ai duk abunda za'a sa mata aciki lallaine akwai kuskure
acikinsa,shi yasa tun farko da nasan irin wannan maganar za ayi dana bada shawaran muyita a
tsakaninmu idan yaso su d'in a sanar da su daga baya.."

"A'a Matawalle gara dai da akayi hakan kaga kowa an fita hak'k'insa ai yafi,ba wai ace mun
yanke hukunci tsakaninmu ba.."

"A to.! Ai kai da yake kasan gaskiya kaji abunda ka fad'a,gara abawa kowa hak'k'insa shi ne
batu.."
Cike da hasala Abba Matawalle ya kalli sashen da matarsa take
"Hajiya Suwaiba wollahi kada ki kuskura na sake jin bakinki akan maganar nan,shin babu wani
mai baki ne anan sai ke kad'ai..?? Kowa yayi shiru yana jiran yaji me za'a zartar amma ke tun
d'azun kin hana mu neman mafitan da duka ita ta had'a mu anan,wannan wace irin rayuwa ce
ne haka..??"
"Nifa ba wani abu yasa nayi maganar nan ba face akan y'ancin yarinyata tsakani da Allah ni
kam nafi son a raba auren nan,kuma itama kanta nasan zata fi son hakan saboda dama ce zata
samu da zata sa ta auri wanda take so.."
Cikin mamakin kalamanta uasa Hajiya ta kalleta tana maimaita abunda ta fad'a
"Ta auri wanda take so..?? Shin dama Sajida tana da wani saurayin ne amma baku fad'a ba
aka aurar da ita ga YAZEEDU..??"
Shiru parlour'n ya d'auka ba tare da an samu mai bawa Hajiya amsa ba,ranta a b'ace taci gaba
da magana
"Shi kenan yanzun naji duk abunda kuka tattauna kuma in sha Allah ba za muyi abunda zai zo
ya lalata zumuncin mu ba,zamu bada dama don a fita hak'k'in kowa kada daga baya azo ana
k'ananun maganganu."
Sajida ta kalla kafin taja numfashi da cewa
"Sajida nasan kinji duk abunda ake magana akai ko..?? To ina so ki tabbatar mana shin zaki
iya hak'uri ki zauna da YAZEEDU har zuwa nan da shekara d'ayan ko kuwa..??"
Sunkuyar da kai tayi ta kasa amsawa
"Ke sakarya ki d'aga kai kiyi magana kada ki cuci kanki.."
Hajiya Suwaiba tayi furucin cike da masifa

"A'a..!"
Wannan kalmar data fito a bakin Sajida ba k'aramin jefa su ta sake yi a commotions ba
musamman ma Abba Matawalle,sake kallonta Hajiya tayi da kyau kafin ta ce
"Me kike nufi da A'a..Ina so kiyi magana yadda kowa zai fahimci abunda kike nufi."

"A'a Hajiya..Na hak'ura da auren..!"

"Kina nufin kema kinfi son a raba auren naku..??"
Hajiya ta tambayeta,da kai ta amsa mata alamun hakan ne,jinjina kai kawai Hajiyar tayi cike da
mamaki da kuma takaici,ba ita kad'ai ba hatta da su Abba GALADIMA,Abba Matawalle
mahaifinta,dama su Ummi babu wanda baiji mamaki ba,a b'angaren Yarima hamdala yayi ga
Allah (S.W.T) dan dama haka yake so,haka nan zamu iya cewa yama fi Hajiya Suwaiba farin
ciki da maganar ta zo a haka,kunya a gurin Abba Matawalle kuwa a lokacin data tabbatar musu
tafi so a raba auren ko wata macen albarka,sun d'auki lokaci mai tsayi ana ta muhawara akan
maganar raba auren kafin Hajiya tasa aka kawo abun takarda da alk'alami nan take taa umarci
Yarima daya rubuta takardar kuma ta hire shi da kada yayi abunda ya sab'awa addini,saki d'aya
tak ya rubuta kana ya mik'awa YASEER ya karantawa iyayen kafin aka mik'a musu,Hajiya
Suwaiba ta karb'a tana mai jin farin ciki duk da dai ba haka ta so ba,haka nan a saman fuskarta
ma sai data kasa b'oye haan,daga haka taron ya tashi Abba Matawalle sai hak'uri yake ta
bayarwa,babu wanda yaji haushin sa duka ciki saboda ba k'aramin namijin k'ok'ari ba na ganin
cewa an samu masalaha,kuma tabbas ba don Hajiya Suwaiba na nan ba wacce itace ta assasa
hura wutar har ya kasance a k'arshe sai da aka rabu da babu abunda zai hana bai yiwa Sajida
umarnin taci gaba da zama a gidan ba a kuma matsayin matar Yariman,daga haka kowa yayi
nasa gidan sai dai duk da haka rayuka basu yi dad'i ba..


A b'angaren Abba Matawalle kuwa lokacin da ya isa gida kasancewar ba tare suka koma
dasu Sajida ba,nan ya iske su a parlor Hajiya Suwaiba sai hud'uba take sake yi mata suna ta
shewa abunsa,shigowarsa ce tasa su kintsuwa nan ya nemi guri ya zauna yana binsu da kallon
mamaki dan dukansu ba k'aramin kunyata shi suka yiba a yau,ya d'auki lokaci yana kallonsu
kafin yayi magana
"Sajida a yau nayi bak'in cikin kasancewar ki y'ar dana haifa a dalilin k'in yimin biyayya da kika
yi,wannan ya gwadawa duniya cewa kinfi k'arfi na,ban kuma isa na baki umarni ki biba sai
abunda uwarki tasa ki shi za kiyi,sai dai abunda nake son shaida muku yanzun shi ne tunda har
ni kuka kunyata a idon y'an uwana ku sani,dama wannan gidan nawa ne ko..?? Kuma babu da
wanda muka had'a kud'i wajen ginawa,to abunda nake so da ke shi ne ki bud'e kunnenki sosai
ki sauraren ni,a yau kin biyewa mahaifiyarki kin kashe auren ki ba,kinga wannan gidan da kike
ciki..?? Ina so maza kafin fushi na ya sauka akanku,ki gaggauta fitar da miji daga zaran kin
gama idda saboda ni bazan zauna da d'an da bazai min biyayya ba.."
Kanta a k'asa saboda yadda take jin kalaman mahaifin nata wanda ko a mafarki bata tab'a
tunanin hakan zai faru tsakaninsu ba,wai yau itace da mahaifinta yake fad'a mata gidansa bana
zamanta bane.Lallai kam sai yanzun ne take jin tayi kuskuren da zaiyi wuya ta iya

gyarawa,haka nan sai yanzun ne take ganin aibun abunda tayiwa mahaifinta mai tsananin
k'aunarta,shin wannan shi ne sakayyar irin soyayyar daya nuna mata..?? Da wannan ne ya
kamata ace ta biya shi ladan nauyi da d'awainiyar da yayi da ita tun daga haihuwa..??
Wannan tunanin shi ne yasa taji a duniyarta tayi asarar wani abu mai girma wanda zai yi mata
wahala ace ta dawo da shi.
Abba Matawalle kuwa koda ya gama fad'an ya tashi ya bar musu gurin dan dukansu yana
fushi ne da su shi yasa ma baya son a yanzun ya zauna guri d'aya da su duka saboda yadda
yake jin haushinsu.

Bayan tashin sa a gurin hajiya Suwaiba ta kalli Sajida taga ta kife kai a tsakanin laps d'in ta
tana sheshshek'ar kuka,sai ta dafa ta tana sake ingizata da kalamai marasa ma'ana nan ba tare
da y'ar ta kulata ba ta mik'e da gudu ta bar wajen tana rusa kuka,da ido ta bita tana tab'e baki
dan tasan za tayi kuma ta bari Harma ta dawo kan turbar data d'ora ta.(ni kuwa dai na ce da
Sajida matuk'ar kuka ne yanzun ta fara shi,lokacin da zata zubar da hawaye bai zoba tukuna).

A b'angaren Yarima kuwa lokacin da suka tashi a meeting d'in koda ya fito babu wata
damuwa a tattare da shi dan haka duk wani jaje da ban baki da su Hajiya keyi masa shi jinsu
kawai yake coz abun bai b'ata masa rai ba haka nan bai d'aga masa hankali ba,hasalima da
zasu bincika zuciyar sa a lokacin to da babu abunda zasu tsinto face zallar farin ciki mara
misaltuwa.
Tun daga ranar da wannan al'amarin ya faru ta gefen Yarima bai sake bi ta kan wani maganar
aure ko mata ba,hasalima aikinsa ya sake rik'ewa da gaskiya,wanda ko a weekend ma a
magiya yawancin lokaci sai ya zama ba ko wane weekend yake dawowa gida ba,dan wani
lokacin ma sai ya shafe a k'alla sati uku bai zoba sai dai ko suyi waya,haka rayuwar ta ci gaba
da gangarawa cike da nasarori,wanda abubuwa da dama suka faru a cikinta wasu masu dad'i
wasu kuma akasin haka..............

*ONE YEAR LEAP...*



*Aradun Allah zanyi muku tijara,dan yanzun sam babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login