Showing 21001 words to 24000 words out of 29888 words

Chapter 8 - Wani Al'amarin Compelet Hausa Novels By Real Shamtr.pdf

03 Oct 2025

617

*LOYAL TO MY FAMILY.♥*

مسب الله نمحرلا رلا .ميح
^^^^^^^^^^^^^^^^^
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 10.*
^^^^^^^^
*#Wife searchable.*

Hiran da suke akan neman matar da ya kamata a aurawa Yariman suka ci gaba da
tattaunawa,shi dai bai ce da su komai ba hasalima sai komawa da yayi ya kwanta a jikin
manyan tuntum dake baje a parlour'n yana clicking wayansa data d'auke masa hankali,duk
maganar da suke ya kasance tsakanin Ummi ne kad'ai da YASEER,can YASEER ya d'an tab'a
shi yana cewa
"Broah..! Can't u say something..??"
Gira d'aya ya d'age masa alamun tambaya akan abunda zai yi magana
"Ohh! U don't even know what to say..??"
Da ka ya masa alamar haka d'in ne ba tare daya san me yake cewa ba,ganin hankalinsa baya
tare da su yasa YASEER d'in fizge wayar dake hannunsa,saurin d'agowa yayi ya kalleshi yana
had'e girar sama dana k'asa
"Why always kake so ka dungamin irin haka ne..??"

"I don't even know.!"
Ya d'age shoulder sama yana sakar masa d'an k'aramin smirk,tsaki ya saki kafin ya mik'a
masa hannu alamun ya bashi abunsa
"I can't do this,unless u were free ur mind.."
Harara ya zabga masa cikin takaici ya ce
"Bazan ce ba d'in,it's necessarily sai nayi magana..??"
Duk wannan abun da Yariman yake ko d'aya baisa YASEER jin babu dad'i ba sai ma shi d'in
daya maida abun kamar tsokana
"Ai kuwa yau bazan bada ba har saika yi magana.."
Ummi ya juya ya kalla yana marairaicewa
"Please Ummi say something..!"

"Waye zai shiga tsakaninku..?? Haka kawai ina zaune yanzun kusa ni jin kunya..Tsakaninku ne
maza karb'i a hannunsa ai ba k'arfin ka yafi ba.."
Shima d'in koda jin abunda Ummi ta fad'a sai tasa shi sakin siririn murmushi kafin ya juya ga
YASEER yana fad'in
"Heey Man..are u ready to confer or not..??"

"Am not..!"
YASEER d'in ya fad'a,mik'ewa yayi ya nufi inda yake tun kafin ya k'araso tuni YASEER ya ajiye
masa ita a k'asa,k'wafa yayi kafin ya d'auka yana cewa
"Coward men..! Daka bari ai na iso kaga abunda zanyi maka.."
Dariya duka suka fashe har Ummi data zuba musu ido tana murmushin drama d'in nasu,sai
daya koma ya zauna sannan Ummi ta kalleshi tana fad'in
"YAZEED son..when zaka nemo matar ne.?? Naga kai hankalinka sam baya tare damu.."
D'an kallonta yayi ta gefe ya had'iye yahu kafin ya iya bata amsa
"Soon Ummi in sha Allah.."

"To Allah yasa kada a tsaya shiririta kamar wancan lokacin.."

Saurin cafe maganar YASEER yayi
"Ai wollahi kuwa Ummi kamar kinsan abunda zai faru kenan,yo mutumin da baya tsayawa da
y'an mata wace ce zata yi sha'awar ganinsa kusa da ita,wasufa y'an matan har nunawa suke
suna ra'ayi amma mutum kamar Gunki shi ko damuwa da lamarin baiyi.."
Kallonsa duka suka yi lokaci guda kuma suka yi murmushi tsakanin Ummi da Yariman
"Hey! Man it's not a case of urs..u have to cover up ur lips.."

"Bazan yiba d'in,kin jishi ko Ummi sai an fara magana yace babu ruwana a ciki,idan har babu
ruwana a ciki me zai hana kayi zuciya ka duba mai sonka ko da cikin wanda suke maka tallar
kansu ne..??"

"Yeah! YAZEED son u have to fixed up someone da zata kula mana da kai,kada ka duba
maganar d'an uwanka,but ya kamata ace ka tsaya kayi tunani kaji kaga wulak'anci babu dad'i
koba haka ba..??"
Shiru yayi cikin ransa yana gasgata maganar Ummi'n,a hankali kuma ya d'an d'ago kansa ya
kalleta ya furta
"Ok Ummi.. I will try my best.!"
Murmushi tayi masa itama na jin dad'i,saboda ganin a ko wane lokaci yakan yi k'ok'arin yabi
shawararta
"May almighty Allah pinpoint us uprightness..!"

"Ameen" suka amsa duka,kallon gefen YASEER Yarima yayi cikin zolaya ya ce
"Man..! Ashe u are slower sometimes.."
Hararar sa YASEER yayi kafin yace
"Ka manta am from asylum.."
Dariya duka suka sa,haka suka ci gaba da hira a nan apartment d'in Ummi,basu sukabaje ba
sai dare sannan kowa ya nufi nasa apartment d'in.

Jeeddah kuwa ko data gama aikinta bayan ta gyara ko ina ta maida komai muhallinsa sai ta
sulale ta k'ofar baya,tayi ficewarta dan yadda take jin suna hira bata so ace ta biyo ta nan,bare
kuma har ya zama tayi calling attention nasu zuwa gareta,ranar kam bata ko samu damar yiwa
Ummi sallama ba,sai sak'on data bawa ABEELA akan ta sanar da Ummi'n ta wuce sai da
safe.Kasancewar yanzun duk wani aiki na apartment d'in Ummi an d'auke mata illa iyaka girki
kad'ai da take yima Ummi'n,shima dan tak'i yarda da kowa yayi mata ne,duk da adadin
hadimanta amma tak'i amincewa a kawo mata wata sai jeeddan ke yi.
Da zuwanta gida ta iske babu kowa dan haka kai tsaye ta wuce d'aki ta rage kayan jikinta
sannan ta fito tsakar gida tana y'an aikace² da baza'a rasaba,sai a sannan ta tuna da abunda ya
faru d'azun a kitchen,haka nan ta d'an saki murmushi,ta jima tana tuna abun tana murmusawa
da alama abun yana matuk'ar bata nishad'i, har ta gama y'an share² babu wanda ya shigo
gidan,
dan haka ko data kammala itama alwalar Maghreb ta d'aura sannan ta wuce zuwa d'aki abunta.

A gefen Yarima kuwa tunda Ummi tayi masa maganar ya kamata ya duba wata mai sonsa ko

da cikin y'an matan da YASEER yake magana ne,tun a sannan sai hankalinsa ya kasu shima
akan ya duba d'in,babban burinsa a lokacin kuwa bai wuce ace yayi abunda Ummi'n nasu ta
sashi ba,a dai² wannan lokacin shima d'in da kansa bayan waccan maganar da suka yin sai ya
dunga jin bashi da buk'atan daya wuce yayi auren,sai dai kuma abu d'aya ke dakatar da shi a
duk lokacin da tunanin hakan yazo masa,shi ne rashin tsayayya wacce ya kamata ace ya nufa
da irin wannan maganar tunda shi d'in ba ma'abocin kule² bane bare yace ga wata wacce suka
fi shiri tunda ko wacce share ta yake.
Yau kam tunda ya dawo daga office ya zauna a parlor yana clicking waya,kamar daga sama
new number tayi masa magana,har ya wuce sai kuma zuciyar sa tasa shi dawowa baya,cikin
basarwa ya shiga amsa maganar,zuwa sanda ya gama fahimtar da mace yake magana,abun
mamaki a d'an wannan maganar da ya d'an tsaya suka yi haka nan sai ya fara jinsa kamar wani
cikakken mutum,yana zaune sai ya d'an saki murmushi,wisely suke hira tun baya sakewa sosai
yayi magana har kuma ya zama ya d'an fara bada had'in kai,wasa² tun abun bai soma shigar sa
ba,sai gashi yau da gobe tasa ya fara sakewa da Yarinyar,wacce tuni ta shaida masa sunanta
Zahra,da kasancewarta y'a ga ambassador Abdulmalik,jakadan nigeria a k'asar
london,kasancewar through internet ne suka had'u sai had'uwar tasu tazo musu a
bazata,kwanaki sunci gaba da gangarawa,wanda izuwa wannan lokaci da aka d'auka tuni
shak'uwa ta fara shiga tsakanin Yarima da Zahra duka kuma ba tare da sun tab'a ganin juna
ba,cikin haka ne wata rana suna hira kamar yadda abun ya zame musu sabo,a nan ne Zahra
take tambayar Yarima when zai zo gidansu..??
Tambayar da fari taso bashi dariya amma sai yaga itan da gaske take,dan haka sai ya maida
abun serious shima suka ci gaba da hiran har ta kaiga ya sanar mata sanda zai je gareta,amma
dai ta fara tura masa address nata,da murnarta ta tura masa details d'in komai,after sai suka ci
gaba da hira kamar ko wane lokaci har zuwa sanda suka yi sallama. Kwanaki biyu tsakani kasancewar itama suna zaune ne a garin Abuja'n,suna waya da Yarima
yake sanar mata da zuwansa a washe gari daya kasance Friday saboda yana son wucewa
Kano shi yasa ya yanke shawaran zuwa a washe garin.
Hakan ce ta kasance a washe garin kamar yadda ya fad'a mata,bayan sun kammala duk
abunda za suyi suka d'auki hanyan zuwa gidan su Zahra'n shi da YASEER, sanda suka isa
sunji mamaki sosai dan ganin yadda suka riski line d'in da securities duk da yasan wace Zahra
Abdulmalik,tun daga farko har k'arshen line d'in ta ko ina securities ne,duk wanda zai shiga ko
ya fita a harabar line d'in sai ya sha tsanani gurin bincike,suna zuwa sukam basu wani b'ata
lokaci ba kasancewar sun fad'i gidan da suka zo haka an san da zuwansu,dan haka ba'a b'ata
musu lokaci ba aka basu hanya suka wuce kai tsaye,wannan abu daya faru ba k'aramin
mamaki ya basu ba har sanda suka isa zuwa mansion d'in wanda idan har ana batun had'uwa
da tsaruwa to wannan gidan ya wuce duk yadda za'a kwatanta shi kuma ba wai iya kad'ai a
garin Abuja ba hatta da sauran garuruwan 9ja sai an bincika kafin a samo kwatankwacin
sa,guest sitting room aka kaisu wanda ko iya shi kad'ai mutum ya kalla zaisan naira na kokawa
a wannan gida,babu jimawa tsakanin zuwansu sai ga itama Zahra'n ta shigo cikin ado sai
murmushi take dokawa,barka da zuwa ta musu sannan suka gaisa fuskarta a sake,basu wani
jima ba sosai kasancewar dama a hanya suke,nan suka barta akan idan sun dawo zai yi mata
zuwa na musamman,daga haka suka yi sallama da ita suka wuce,itama ta koma gida sai farin
ciki take musamman na irin wannan tsintar dami a akala.

Lokaci yaci gaba da tafiya,cikin haka shak'uwa mai tsanani ta sake shiga tsakanin Yarima da
Zahra wanda har ya wuce a kwatanta,sai dai shi a gefen Yarima duk wannan shak'uwar da suka
yi da ita duka yana d'aukan tane a matsayin ba komai ba,ko da YASEER ya masa maganar
yana sonta ne nan yayi ta masa musu akan hakan,wai shi dai kawai friendship ne
tsakaninsu,lokacin daya fad'a dariya kawai YASEER yayi ya rabu da shi dan yasan ko kwana
zaiyi yana masa bayani bazai tab'a yarda da shi ba.
Sai dai wani abun mamaki bayan y'an kwanaki tsakanin maganar tasu sai ga yarima yazo
masa da maganar da tasa shi darwa sosai,yana zaune Yariman ya zo ya zaune kusa da shi,a
hankali ya d'an kalleshi cikin wani yanayi kafin ya furta
"Broah..! Ina tunanin yin aure kwana kusa..!"
Saurin kallonsa YASEER yayi yana sake bud'e idanunsa,kamar wanda bai fahimci abunda ya
fad'a ba yace
"Kace mene..??"
Ba tare daya kalleshi ba yace
"Abunda kunnenka suka ji maka..!"
Dariya YASEER yayi ta masa kafin ya tsagaita yana tambayarsa
"Wace mai sa'ar ce haka..Allah yayi da rabonta..??"

Kallonsa ya d'anyi dan yasan maganarsa akwai wani abu da take nufi,bawai iya tambayar
bane kad'ai,ganin bai ce wani abu kuma sai yasa shima ya share ya kuma bashi amsa
"Zahra ne.!"

Jinjina kai yayi bayan yaji amsar tasa,sannan yaci gaba da magana
"Eheen! Allah ya taimaka to.."
Bai iya cewa komai ba dan yadda ya fahimci hankalin YASEER yayi wani gurin daban,ko da
ganin YASEER d'in baice masa komai ba sai shima d'in ya kyale shi bai sake masa maganar
ba,sai dai ya yankema ransa zai kira Ummi suyi maganar kawai,hakan kuwa akayi da dare after
sallar isha'a ya kira Ummi ya zayyana mata komai tun daga had'uwar sa da Zahra'n har kawo
yanzun bai bari ya fad'a mata wani abu da babu shiba,addu'o'i na fatan sanyawar alkhairi ta
bishi da su sannan ta shaida masa in sha Allah da idan Abba ya shigo zata sanar masa dan ayi
komai cikin lokaci kad'an ba sai anzo ana ta jan rai ba.

A gefen Zahra ma haka abun ya kasance dan tuni ita kam Yarima yayi mata kawai dai tana ta
addu'a ne da fatan ya kasance nata har abada,kuma da yake itan ta kasance y'ar boko mai
masifar wayo sai bata fito fili ta nuna masa ba,kamar yadda ya sanar da ita ta fad'awa iyayenta
maganar zuwan magabatansa dan neman aurenta,yasa bata yi k'asa a guiwa ba ta shaida
musu,ai kuwa nan ambassador Abdulmalik ya shiga shirin tarbar bak'in nasa kamar yadda suka
yi zasu iso a cikin satin.

Maganar nemawa Yarima auren Zahra tuni ya kankama a cikin k'aramin lokaci,wanda kan
kace kobo tuni har maganar ta gama karad'e Royal Family,masu murna nayi haka ma masu
bakin ciki duka tuni suka fara bayyana kansu.Kamar yadda aka al'k'awartawa ambassador

Abdulmalik cikin satin tawagar su Abba GALADIMA ta d'auki hanyar birnin tarayya,kasancewar
a private jet na masarauta suka tafi,wanda a wanna tafiya bawai iya kad'ai Abba GALADIMA
bane,tafiyar ta k'unshi wasu daga cikin manya na masarauta ciki kuwa har da Abba
Matawalle,wanda shima cewa yayi baza'a barshi a baya ba,wanda yace tunda y'arsa tak'i
wannan ba shi ne abunda zaisa shi kuma ya nuna jin haushi akan neman auren na Yariman
ba,a cewar sa duk abunda ya faru ita ta jawowa kanta.Haka suka je Abuja suka kuma dawo
cike da farin cikin yadda al'amarin ya kasance cike da mutunta juna,bayan dawowarsu babu
b'ata lolaci Abba GALADIMA ya sanarwa Maimartaba yadda komai ya wakana,inda Abba
GALADIMA'N ya shaidawa maimartaba batun tsayar da ranar auren nan da sati uku masu
zuwa.

A can gefen Zahra kuwa a dai² wannan lokaci da duka ahalinta ke cikin tsananin farin ciki,ita
kuma a sannan ne wani abun tashin hankali ya kunno mata cikin lamuranta a wayewar garin
data fara tabbatarwa ranta ita da Yarima abun daya rage musu su mallaki juna bashi da yawa.
Fitowarta a wanka kenan daga ita sai towel iya cinyanta ta tsaya gaban mirror don shiryawa
saboda Yarima ya shaida mata zai zo,bata kaiga zama ba k'arar shigowar sak'o ya katse mata
abunda take,cike da son dubawa ta d'ago wayar tana murmushi duka a tunaninta sak'on ya fito
ne daga gurin Yariman...............



#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.



*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*😉

*®ɛąl ʂmąʂɧɛr.*
💠💠💠💠💠
*©® 2019..*



 *WANI AL'AMARIN..!*💥
*(Book 2)*
💣💣
💥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*

*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*

مسب الله نمحرلا رلا .ميح
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Zuwa ga masu k'orafin bana son amsa musu idan sunyi comments,babban abunda nake son
ku fahimta shi ne,a duk lokacin da kuka ga kunyi sharhi marubuci bai yi magana ba,uzuri ne
farkon abunda ya kamata kuyi mana coz ba kowa ne lokaci ne muke samu mu bibiyi sak'onnin
kuba,amma nasan iya k'ok'ari muna yi na ganin mun duba d'in har ma muyi sharhi idan lokaci
ya samu,sai dai muna fatan zaku sake yi mana uzuri,sannan ina mai k'ara baku hak'uri ga duk
wanda bamu samu mun amsa masa ba,a bunne da yawa shi yasa wani lokacin ake samun irin
wannan matsalar,ku sani a ko wane lokaci muna tare daku ko da kuwa ace bama cikin group
d'in da ake posting novels d'inmu..In sha Allah wad'anda muke tare zamu yi k'ok'arin ganin mun
amsa muku a duk lokacin da dama ta samu.Wannan sak'o me daga duka marubuta ba wai iya
*Real smasher* ba,muna godiya sosai da nuna mana soyayya da kuke,#Ina mugun ji da ku.*
___________________
*BOOK 2. 📓*
*Pg 11.*
^^^^^^^^
*#Distressing of marriage spoken.*

Wani mummunan fad'uwa gaban Zahra yayi a lokacin data ci karo da sak'on,wanda kallonsa
kad'ai ya haifar mata wani irin fargaba,tun kafin ta kaiga karantawa tuni har jikinta ya fara
rawa,stool d'in dake gabanta taja ta zauna sannan ta shiga k'ok'arin bin harufan da sak'on ya
k'unsa d'aya bayan d'aya ba tare da tana cikin wadatacciyar nutsuwar da zata sa ta fahimci
abunda sak'on ya k'unsa kai tsaye.Babu ko sallama a gaba d'aya sak'on wannan ya sake
tabbatar mata sak'on ba daga Yariman yake ba kamar yadda ta zata a farko,ga abunda sak'on
ya k'unsa
_"Zahra Abdulmalik..! Babbar y'a ga jakadan k'asa mai wakiltar Nigeria,wacce al'ummah da
yawa suka fi sani da *ZAHRAMALEEK*, tabbas mun san zaki ji mamakin ganin wannan sak'on
a dai² irin wannan lokaci da baki zata ba,kamar yadda muka san zai yi wahala a gareki ki yarda
da abunda zamu sanar dake,safari dai muna so ne ki nutsu,sannan kiyiwa kanki adalci,kada ki
bari soyayya ta rufe miki ido har ta kai ga kin aikata abunda nan gaba zai zame miki abun
tir,Allah wadai da gori a idon duniya..Ke d'in mace ce wacce muka san tana ji da ilimi,wayewa
had'e da gogewa irin ta mutanen da suka rayu a k'asashen duniya kuma suka yi gogayya da
manyan turawa,sai dai wannan wata y'ar dama ce ta sameki da ya kamata ace kinyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login