Showing 12001 words to 15000 words out of 29888 words
Chapter 5 - Wani Al'amarin Compelet Hausa Novels By Real Shamtr.pdf
shiga taradaddi da tunanin kan irin maganar da zata iya fitowa a bakin
Yariman, ilaihi kuwa dai² lokacin da yake cikin wannan halin suna cikin tafiya Yarima ya kalli
fuskar d'an uwan nasa kafin ya ce.............
*Afuwaan fan's wollah yau nayi niyyan yin typing sosai sai dai bana jin dad'i sosai,kuyi hak'uri
da wannan.*
#Follow
#Vote
#Comment. Then
#Share.
*®ɛąl Ê‚mąʂɧɛr.*í ½í¸‰[10:05PM, 6/20/2019] Itz Ibraheem: í ½í² í ½í² í ½í² í ½í² í ½í²
*AWESOME WRITER'S ASSO..í ¼í¿®*
~_{Palace of excitation & pleasant writer's}._~
*©® 2019..*
 *WANI AL'AMARIN..!*í ½í²¥
*(Book 2)*
í ½í²£í ½í²£
í ½í²¥
*иα*
*♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡*
*Wattpad&Instagram*
*@Jeeddahmu898*
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:*https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
*_____________________*
*LOYAL TO MY FAMILY.♥*
مسب الله Ù†Ù…ØØ±Ù„ا رلا .ميØ
^^^^^^^^^^^^^^^^^
*Masoyana a duk inda kuke ina yi muku fatan alkhairi na fili dana b'oye,a kullum abu d'aya na
sani kuma shi nake maimaitawa #Ina matuk'ar k'aunar ku har cikin raina..*
*Oum Feedy (Hajiya Maryam),Queen Acid,Bushrah,Fatima M.D,Fateema (red rose) ina
gaisuwa,taki dabance da saura na gaisheku kyauta.*
___________________
*BOOK 2. í ½í³“*
*Pg 7.*
^^^^^^^^
Kallon kallo aka fara tsakanin Yarima da YASEER dan sam basu yi tunanin jin haka ba,amma
kuma to ya suka iya..? Sun sani cewa matuk'ar suna son suga sauk'i cikin lamarin dole ne sai
sun karb'i maganin,a hankali Yarima ya d'aga ido yayiwa YASEER alama daya tambayi Malam
Adamu,jinjina kai yayi sannan ya juyar da kallonsa ga malam Adamu yana cewa "Baba to amma idan ya kasance wanda yake da irin wannan larurar yana da aure kuma fa..?"
Murmushi malam Adamu yayi sannan ya ce
"Ai shi ya sama tun da farko na sanar da ku k'a'idar maganin dan haka baya tab'a faruwa,sai
dai ko mutum yayi hak'uri da batun aure zuwa sanda wa'adin da aka d'iban masa zai
cika..Saboda doka ce irin ta maganin kuma in dan mutum yana son samun lafiya ne tofa sai ya
jure.." Godiya suka yiwa malam Adamu sannan suka karb'i maganin bayan sun cika shi da alkhairi
suka kamo hanyar gida,tafe suke amma kowa da abunda yake tunani game da
maganin,YASEER ne ya fara yin magana
"Broah..! It's necessarily for us mu sanar da wani cikin iyayen mu game da wannan case d'in
naka,kaga bazai yiwu ace kana tare da irin wannan problem din kuma ace kana tare da yarinyar
mutane ba,tabbas ba kowa ne zai iya hak'uri da zaman jira har na tsawon shekara ba,due to
this problem da kuma lokacin da za'a d'auka kafin a samu haske ina ganin kawai mu sanar dasu
duk decision d'in da zasu yanke ma to sai mu jira muji daga gare su.."
Shi kam Yarima shiru yayi ya kasa magana,buh a zuciyar sa tunanin ta yadda zai iya fuskantar
wani cikin iyayensa ya sanar dasu wannan al'amarin yake,babban damuwar kuma shi ne rashin
tabbas d'in decision d'in da za'a d'auka akan matsalan ba,shin idan ya fad'a za'a raba auren
nasa da sajida ne ko kuwa za'a ce yaci gaba da zama da ita har zuwa lokacin da zai samu
lafiya..?? Anya kuwa ma zasu amince su yarda yana tare da wata matsalar ko kuwa zasu
k'aryata..?? Shi kam da za'a bi ta son ransa ko a bashi zab'i tabbas da zai rok'i alfarmar a raba
auren nan dan shi har yanzun baya jin wani alamu na shak'uwa ko so a tattare da shi game da
yarinyar..To amma ya zai yine tunda itan itace ZAB'IN IYAYENSA..?
Irin tunanukan da yayi ta yi kenan har sanda suka shigo harabar Royal palace ba tare daya
sani ba,dan tun da suka d'auko hanya abun yake ta ci masa rai yana wannan mugun tunanin
har bai san sun k'araso gida ba sai jin tsayuwar motan yayi,yana d'agowa da niyyan duba dalilin
tsayuwarsu ya gan har sun iso cikin gidan,ajiyar zuciya ya saki lokacin da yake k'ok'arin fita
daga motan YASEER ya dakatar da shi ta hanyar rik'o hannunsa,a hankali ya waiwayo yana
kallonsa da damuwa a fuskarsa
"Wait mana,nayi magana tun d'azun da kai amma naji baka ce dani komai ba,anya kana ganin
yin shiru akan matsalar nan mafita ne a gurin mu..?? Ya kamata fa duk abunda za ayi ace iyaye
sun sani,gudun kada wani abu ya faru nan gaba,amma ban san kai ya kake gani ba.."
Ya fad'a yana kallonsa
"Ni kaina ban san ya za'ayi ba,buh ka bani lokaci nayi tunanin abunda ya dace.."
"Shi kenan kamar yadda ka fad'a d'in amma fa ka sani wannan ba abune da za'a ce mun b'ata
lokaci akansa ba,ya kamata muyi tunanin mafita da wuri kada kuma sai abun ya kwab'e mu
rasa mafitan.."
"In sha Allah babu abunda zai faru makamancin haka.."
Sun d'an d'auki lokaci a cikin motan suna magana kafin su fito su kama hanyan cikin
gida,suna tafe bayin dake kewaye da gidan suna mik'o gaisuwa ta ko wane fuska,a garesu kam
hannu kawai suke iya yi musu alama da shi amma ko wanne jin bakinsa yake ya masa nauyin
da bazai iya magana ba da haka har suka shige.
Wasa² sai da aka d'auki a k'alla sati kusan uku ba tare da yarima ya iya nemo mafitan da yake
tunanin yana da ita ba,wanda a iya tsayin wannan lokacin ma iya cewa da aurensu kad'ai an
kwashi a k'alla wajen watanni biyar,yau kam abun ya ishi YASEER dan yana ganin zubawa
yarima ido sam ba mafita bane a gurinsa tunda yin shirun nasa ma sam yak'i yin amfani,dan
haka a yau kam ya k'udurce samunsa suyi duk ma wacce za suyi,a parlour'n Ummi'nsa ya iske
shi suna hira dan haka yana shigowa koda suka had'a ido nan take ya aika masa da sak'on
tuhuma,ga yarima YAZEED kuwa nunawa yayi kamar bai gane me yayi ba nan ya share
shi,girgiza kai YASEER yayi kafin ya samu guri ya zauna yana gaida Ummi'n nasa,cikin kulawa
ta amsa masa har tana tambayarsa iyali,sauke kansa k'asa yayi alamun jin nauyinta,zuwa wani
lokaci kuma ya d'ago ya d'an kalleta,cikin wani rough sounding ya furta
"Ummi gurinki na zo nd i want to talk to u.."
D'an kallonsa tayi itama tana mamakin maganarsa,in a serious tone ta furta
"Wane irin magana ne wannan YASEER kake son fad'a haka..?? Shin maganar tana buk'atan
sirri ne..??"
"Ehh Ummi.."
Ya bata amsa yana sake yin k'asa da kansa
"To ina saurarenka.. Allah yasa muji alkhairi.."
Ga Yarima kuwa koda yaji YASEER ya furta yana son yin magana da Ummi,nd da dukkan
alamu maganar sirri ne tsakaninku,dan yana jin tambayar da tayi kuma YASEER d'in ya
tabbatar mata sirri ne,baiyi k'asa a gwuiwa ba sai yayi haramar tashi with intention of forsaken
them alone.."
Cikin wani yanayi na rashin son magana ya mik'e yana cewa da Ummi'n
"Ummi am leaving,maybe i will be back.."
Kallonsa tayi lokacin har ya juya baya,ko kafin tayi magana tuni YASEER ya rigata ta hanyar
cewa
"Wait Man,,,u have to stay..!"
Wani burki yaci a inda yake ba tare daya juyo ba take zuciyar sa ta fara tunasar da shi wani
abu daga cikin zancen YASEER d'in,in seconds yayi turning back to where he arose,duka jijiyon
jikinsa a lokacin banda amsawa babu abunda suke yi dan yadda yake afirgicen nan yasan ba
wani abu YASEER d'in zai fad'a ba face game da case d'insa da tuni ya kamata ace sun samu
matsaya amma ya tsaya shiririta,dai² ya d'ago idanunsa suka had'a ido da YASEER d'in yana
jifansa da wani irin kallo,yadda ya ganshi ya tamke fuska yasa shi sake shan jinin jikinsa
"Have u decide to inform someone..Or else..??"
Wani wawan kallo ya jefe shi da shi mai cike da warning na kar ya sake ya furta abunda ke
bakinsa,kallon baka isaba yayi masa shima,sannan ya maida kallonsa ga Ummi data zuba
musu ido tana kallonsu
"Kunga ba zaku sani gaba kuna muhawara ba,if baku shirya sanar dani maganar ba maza ku
b'ace min da gani.."
"No Ummi,, ba muhawara muke yiba,I was confused ne buh now i will tell u.."
"Akan mene kake confusion..?? Maganar ba shida muhimmanci ne kake fad'a min haka..??"
"No Ummi zanfa sanar miki,nd maganar da zan fad'a na tabbatar tafi duk yadda zan fasalta
miki.."
Shiru tayi tana saurarensa,nan kuwa ba tare daya bi takan Yarima YAZEED ba duk yadda
yake jifanta da mugun kallon yana masa alamun kar ya fad'a ya shareshi ya shiga zayyana
mata komai,sai daya zayyanewa Ummi duk abunda ya sani hatta da had'uwar da suka yi da
'Dan DAMFARAR nan da kuma halin da ake ciki yanzun har zuwa kan maganin da Malam
Adamu ya basu da duk sharad'in daya gindaya musu,shiru tayi ita kanta Ummi'n dan yadda
maganar tasa ta shiga commotion,totally she's speechless sai kallonsu duka da take yi,ta d'auki
tsawon mintuna a haka kafin tayi yak'i da bakinta gurin samun y'an wasu words da suma bana
jin zasu wuce a lissafa
"Why da kuka san da wannan problem d'in za kuyi shiru..?? Me yasa tun farko kuka kasa fad'a
a nemi magani..? Sai yanzun ne kuke tunanin samun mafita bayan lokaci ya k'ure..??"
Fuskokinsu duka da wani irin expressions suka duk'ar da kai k'asa,ita kuwa Ummi nan tayita
musu fad'an k'in fad'a da sukayi da wuri
"Yanzun ya kuke so ayi tunda kun koma iyayen mu mun zama y'ay'an ku..??"
Saurin kallonta sukayi fuskokinsu na komawa na tausayi
"Ummi bafa haka bane..!"
"Kamar yaya ba haka bane..?? Idan har ba kun maida mu wad'anda basu da amfani ba,taya
bazan ce kun koma iyayen mu ba..??"
Hak'uri sukaita bata bama kamar shi YAZEED da laifin sa yafi na kowa dan shi ne babban mai
laifin,amma ita kuma laifin YASEER take hanga
"Shi kenan zan hak'ura amma kafin nan sai kun tabbatar kunyi magana da iyayen ku maza
dan asan abun yi,duk abunda suka yanke shi kenan.."
"Ummi me yasa sai sun sani..??"
Kallon baku da wayo tayi musu kafin tayi magana
"Ni yanzun dan kunzo kun sanarmin shi kenan kuna tunanin zanyi shiru ne..?? Ko kuwa kuna
son ku d'aure ni,shi kenan duk ranar da maganar ta fita sai ace Ummi ta sani ko..?? Ni kam ban
zama sakarai irinku ba dan haka maza tun muna shaidar juna ku samu kuyi magana da iyayen
ku idan ba haka ba,don't even involve me in ur case.." Tana maganar tana had'e fuskarta alamun babu wasa,rasa yadda za suyi da Ummi akan tayi
hak'uri suka yi dan a k'arshe ma cewa tayi su fice mata daga gurin,jiki babu k'wari duka suka
mik'e suka fita.
Bayan fitarsu a apartment d'in Ummi rasa yadda za suyi suka yi dan sam basu tab'a tunanin
haka daga Ummi'n ba,kallon Yarima YASEER yayi yana had'e fuska,shi kam gareshi babu laifin
wanda yake gani face Yarima dam duk wani abu mai muhimmanci shi bashi yake d'auka mai
muhimmancin ba,yanzun abunda yake damun kama ace baza ka iya maida kai akansa ba,,,shi
kuwa ga yarima kallon YASEER kawai ya d'an tsaya dan yasan laifi kam nasa ne duk abunda
zai faru yasan shine ya janyo hakan,tun farko daya d'auki shawaran da YASEER d'in ya bashi
ya tabbata da hakan bai faru ba,to yanzun ga abunda ya faru nan gayya zai gyara wannan
kuskuren..?? A hankali ya d'ago ya kalli YASEER kafin yayi magana
"Broah..! What should i do..??
"Ai bai kamata ka tambayeni ba,tun farko me nace maka..?? Nd what do u do..?? Ai sai dana
fad'a maka abun nan baya buk'atan b'ata lokaci,amma da yake ka maida ni wani sauna a duk
lokacin da nake nuna maka muhimmancin abu sai ka dunga gocewa,yanzun ai ga irinta
naan,kaga yanzun kuma sai ka san yadda za kayi ka tunkari su Abba da wannan jawabin
naka.."
Saurin kallonsa Yariman yayi yana cewa
"Haba Man! Me kake cewa ne..?? Ni ne zan tunkara su Abba da wannan maganar..??"
"To idan baka fad'a ba da waye zai fad'a..?? Ni kake so na je na fad'a..?? Saboda gani sarkin
marasa kunya ko..??"
Duk yadda yarima yake tunanin abun sai daya so wuce kansa,dan yadda shima YASEER a
lokacin ya birkice masa sai masifa yake zazzaga masa,tun yana lallashinsa har abun ya soma
fusata shi shima d'in dan yaga abun nasa bana k'are bane,nan kuwa ya juye shima ya shiga
zazzaga masa fad'a dama lallab'awar kawai yana dannewa ne bawai dan ya nutsuba (kunsan
ance mai hali...!!),shiru YASEER yayi masa daga k'arshe dan yadda yaga mutumin nasa ya
birkice masa,ai kuwa nan ya furta "Allah ya kyauta" kana ya wuce ya rabu da shi,wasa² sai da
suka d'auki kwanaki ba tare da wata maganar arziki ta kuma had'a suba,dan yadda kowa yayi
fushi da kowa,idan har ba gaisuwa ba tofa babu abunda yake had'a su,shima da sun gaisa d'in
kowanne zaiyi k'ok'arin barin wajen,wannan sabuwar al'ada da suka b'ullowa junansu da ita ba
k'aramin wahalar da juna suke ba,dan kowa ba son wannan wasan shirun yake ba,kawai dai
sun d'auki hakan ne a matsayin makamin da zaisa kowa ya fahimci muhimmancin d'aya a gurin
d'ayan,amma a bad'ini kawai suna azabtar da kawunansu ne (Shak'uwa kenan).
Tashin sa kenan daga bacci a dalilin ring d'in da wayansa keyi,sai da yayi juyi zuwa gefensa
na dama sannan ya mik'a hannu ya janyo wayan,ba tare daya duba mai kiran nasa ba yayi
answering kiran yana sata a hands free,muryar YASEER ne ya daki kunnensa cikin wani husky
voice ya furta "Zaka iya zuwa parlour'n Hajiya su Abba na son ganinka yanzun..!"
Sanda yaji sak'on sai da yaji bugun zuciyarsa ya tsananta dan sam baisan mene zaije ya tarar
ba a can d'in,amma dai all he knows bazai wuce kan matsalar sa ba.Amsa masa yayi da yana
tafe,inda nan take ya dire daga saman royal bed d'insan ya shiga shiri,a gaggauce ya gama
shiryawa sannan ya fice yana nufar apartment d'in Hajiya,lokacin daya shigo parlour'n tan sai da
numfashin sa ya tafi lesser strike dan yadda ya tarar da ahalin gidan gaba d'aya a zaune kamar
masu juran wani muhimmin abu,aifa nan bugun zuciyarsa ya sake ninkuwa sama da sanda aka
sanar da shi sak'on kiran da ake masa,duka su Abba suna zaune a parlour'n,a hankali ya juya
idanunsa zuwa kan Maimartaba yaga ya had'e fuska kamar bai tab'a dariya ba,sannu a hankali
yaci gaba da bin mutanen parlour'n da kallo har zuwa sanda idanunsa suka sauka kan Sajida
dake kusa da k'afar Hajiya Suwaiba mahaifiyarta,wani irin gumi ne ya fara keto masa duk da irin
sanyin dake cikin parlour'n kuma da kasancewar lokacin rana bata riga da tayi ba,Abba
GALADIMA ne ya kalleshi kafin yayi magana
"YAZEED ka samu guri mana ka zauna..!"
A hankali ya fara d'aga k'afar sa duk da yadda a lokacin yake jin duka vein d'in jikinsa suna gaf
da tsayawa a aiki,har dai ya samu damar zaman a kusa da YASEER,cikin hikima da dabara
Abba GALADIMA yayi gyaran murya sannan ya fara da tambayar YASEER matsalar da ake
ciki,nan YASEER ya shiga zayyana komai ba tare da shakka ko ya b'oye wani abuba,kan
Yarima Abba ya juya da kallonsa harma da tambayoyinsa inda nan take kuwa ya tabbatar masa
da abunda YASEER ya fad'a,kaf a cikin iyayen babu wanda bai shiga commotions ba
musamman ma Umma Fulani dan ita sam bata san da wannan matsalan ba sai yanzun kuma
sam ko da wasa bai tab'a sanar da ita ba,ita kuwa Ummi da dama ta riga ta san maganar babu
wani abu data ji,shiru duka parlour'n ya d'auka na wucin gadi,kafin aka koma batun yadda za'a
b'ullowa lamarin batun malam Adamu mai magani,a nan nefa kowa yayi tsit ana jiran aji
hukuncin da za'a yanke,tashin farko Abba GALADIMA bai tsaya shawara da matan ba dan
yasan zasu iya kawo masa cikas a zancen ya juya ga Abba Matawalle
"Matawalle..Shin yaya kake gani zamu zartar da wannan hukuncin..??"
Murmushi yayi masa cikin hikima ya ce
"Ai GALADIMA ina ganin zaka fini sanin hukuncin daya dace a zartar dalili kuwa duka yaran
nan naka ne..Saboda haka wannan hukuncine da ko ina nan ko bana nan zaka iya zartarwa
kuma ya zauna ba sai lallai ina nan ba tunda kai ne gaba dani.."
Sosai maimartaba da Abba GALADIMA suka ji dad'in furucin sa Harma da sauran iyayen
mata,sai dai ko dajin haka a b'angaren Hajiya Suwaiba kuwa da duk jawabin da ake jinsa kad'ai
take tana jiran taji hukuncin da za'a zartar,sai kuma taji mijin nata ya fad'i hakan,ai kuwa nan