Showing 1 words to 3000 words out of 108226 words

Chapter 1 - ZANYI BIYAYYA Complete Book Hausa Novels FENERH.pdf

FENERH   

03 Oct 2025

12519

ZANYI BIYAYYA COMPLETE




*By FENERH*


*Alhmdulillah masoya na Asali am back nadawo muku da labarin da zai kayatar daku, bazan
iya kwatan tamuku mai ya Kunsa ba sai kun biyoni zakuji da kanku, masoya na godiya mara
adadi naga kauna a last littafina naga masoya masu kaunar cigaba na Allah ya Kara budi da
kauna inyita sambado muku labarai kuna ruwan na data😅, kamar yadda na yi wancan wannan
ma hakane masoya is not for free gsky haryanzu bansamu kudin zuwa hajji ba, ina rokon Allah
ubangijin kowa da komai, yanda nafara wannan rubutun lafiya Allah ya bani ikon kammala shi
lafiya, Hmmm Alhmdulillah masoya masu son karuwata gasky ba Abinda zance muku sai
godiya da fatan Rabbi ya bar kauna, tunban furta littafin na kudi bane wasu har Sunfara biya
wasu kuwa suna jira infara posting su biya, Allahu yasaka muku da Aljannah ya biya dukkan
bukatunku na Alkhairi, one love Real fans*

*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*

1⃣&2⃣

Wani tsoho ne a tsugune ya zubawa wasu Y'an mata guda biyu idanu, dayar zatayi kimanin
shekara Ashirin da biyu, sai kuma karamar mai kimanin shekara sha bakwai, gefe daya kuma
wani matashi ne wanda kana gani shine Babba a cikin su ga mahaifiyar su na sharar kwalla da
gefen zanin ta, "Hajara yanzu bazaki iya yiwa mahaifinki BIYAYYA ba a rayuwar nan duk da bamuda Arziki
amma, yana iya bakin kokarin shi ganin ya kyautata wa rayuwar ku, ya muku duk Abinda uba
nagari zaiyi wa ya'yan shi domin ganin rayuwar su ta inganta,


Cikeda rashin kunya da kuma nuna tsantsar rashin tsoro tace " yanzu don girman Allah a rasa
wadda za a Aurawa naka sasshe sai ni, saboda uban shi yagan mu talakawa, sai kuma ya
lallaba ka kawai ka bashi yarka, wallahi bazan Aure shiba, cikin taushin murya da kwantar da
kai yace "haba Ummi yanzu ke bazaki iya taimako na ba ki fitarda ni kunya? Kinsani duk wani
cigaban ku da nawa sanadin bawan Allah nan ne ya mun komai a duniya batareda mun hada
Alaka ta jini ba, tundaga kan ilimin ku gashi yanzu yayan ku na bautar kasa ke kina 200 level
kanwar ki na final year a secondary wallahi Ummi idan ban sharewa bawan Allah nan hawaye
ba na zama butulu,

"Wallahi baba tunda Allah ya nufe mu da karatun zamuyi koda taimakon shi ko babu zamuyi,

nidai bazan Aure shiba, ka bashi hakuri ya nema wani gidan,

Karamar ce dake kallon Y'ar uwar tata na kelaya rashin mutunci tace "kai yaya Hajara yanzu
kina kallon su baba na miki kuka saboda ki rufa musu Asiri fir Amma shedan na miki hudubar
tsiya ko,
Hannu ta daga zata masgeta, yayan su namiji dake a fusace yace "wallahi daina ganin baba
yace kar in tabaki, Amma kina tabata Saina nakasa ki kema, ba kina kiran wani naka sasshe
ba, HAJARA kibi A hankali duniya ce kina ya' mace Y'ar talaka Amma ego dinki yafi karfin ki a
rayuwa, "Wallahi kitabamin ya' kigani yayanku zanba umarni ya lallasa min ke, Malam kaga Y'ar son
taka ko kaga diyar da kasha duk wata wahalar rayuwa saboda ita ko?
Tsohon da kana gani kasan rayuwar shi bai dauki komai da zafi ba yace "RAHAMA, ki tayani
lallaba Y'ar uwar ki kinji kuje ciki Allah ya ma Rayuwar ku Albarka kinji,


Fuuuu HAJARA ta mike ta wuce d'an karamin dakin su dake tsakiyar gidan,
Kanwar ta ce ta kalli baban su" baba kayi hakuri zata Amince insha Allahu, zan tayaka rokonta,
"To RAHAMA, Allah ya Albarkace ku kinji, Ameen ta Amsa ta wuce cikin dakin itama,
Kafin ya juya cikin natsuwa ya kalli D'anshi namiji da yayi shiru kana ganin shi kasan a zuciye
yake,
"Gadanga kusar yaki, kayi hakuri kaji da halin Y'ar uwar ku, ka zama uba kazamo namiji ako
da yaushe da zai tsaya akan Y'an Uwan shi, kaine Babba kaine gatansu,
Ko bana raye kaine zaka zamo jigo a rayuwar gidan nan, don haka tashi kaje Allah ya maka
Albarka kaji,

Wasu irin hawayen tausayin mahaifin shi ne ya lullube shi, ganin yanda yake fama dasu tsawon
rayuwar su ya tsaya musu akan komai da wahalar neman shi har zuwa yau, ji yake dama shi
mace ne da yau ya rufawa Mahaifin su Asiri ya Auri zabin shi, mikewa kawai yayi yabar gidan,
Bai iya kara cewa komai ba, Amma Addu'a yake Allah ya sa baban ya fita sai ya lallasa ta a
gidan ko ya rage takaici,


Mikewa inna ma tayi zata wuce, yace " zauna matar Aljannah uwargidana ta gari, komawa tayi
ta zauna domin bata iya yimai gardama ko kadan,
Share sauran kwallar tayi "malam sanyin ka yayi yawa,
Dariya yayi kamar bakomai a ranshi yace " so kike inrika daukar zafi a cikin rayuwar da bamai
dorewa bace larai, ki taya ya'yan ki da Addu'a ko mutuncin su kawai da suke tsarewa wani Abu
ne bakya ganin tsananin mu zai iya janyo fadawar ta cikin hadari? Banason ta yi tunanin zanyi
mata Auren dole, larai so nake ta yarda, yanda hankalina zai kwanta ko bayan Auren, Amma in
mun tilasta ta
Anyi wane riba zamu samu yaron da baida lafiya tun tashin shi,

"Malam tuntuni nakejin kana maganar rashin lafiyar shi, wai Meke damun shi ne? Larai Addinin

mu yayi hani ga tsananin bincike, kada musulmi ya tsawaita bincike, Allah yagani tun yaron na
karami mahaifin shi yafada min yasamu nak'asu suka fitar dashi kasar waje, bankuma taba
binciken komai akai ba, yasha fadamin har yanzu yaron bawai ya samu lafiya bane, kuma kanin
shi ma yayi Aure tuntuni harda yara biyu shine dai ya rage saboda lalurar dake damun shi,
Rokona yayi a karon farko, yace min "malam bala ina neman Alfarmar ka bani Y'ar ka Babba
domin nasan ta mallaki hankalin ta zata iya rayuwa da shi, bazan iya watsa mai kasa a idoba
tsawon shekaru yana min hidima bai taba gajiyawa ba sai yanzu kawai rana daya ya roki Abu
guda daya kacal a wurina in kasa yimai, bazan iya ba larai, "Gaskiya Alhaji Shu'ibu mutum ne mai karamci da mutunci ya fi karfin komai kam a wurinka,
"Kingani don haka ki tayani lallaba Y'ar ki larai, yafada cikin barkwanci, " zan yi iya bakin kokari
na insha Allahu malam,





A can cikin dakin kuwa RAHAMA ce ta dauki Quranin ta ta zauna gefen Y'ar uwar ta kan y'ar
madai daiciyar katifar su dake kasan dakin, cikin kwantar da murya tace " yaya HAJARA don
soyayyar ki da manzon tsira kiyi BIYAYYA, zaburowa tayi, a fusace, "wallahi kar inkuma jin
muryar ki a dakin nan da sunan waike kina min zancen Auren da bazan taba yarda da shiba,
zan naka d'a miki na jaki wallahi, "shegiya mai kirar takand'a ke kije ki Aure shi mana,
"Haba yaya ai bazai yuwu ace kina gida ni inyi Aure ba,
Shekara nawa ke tsakanin mu? Kusan Biyar fa, kuma kinsani kece kikafi cancantar Auren
yanzu you are not getting younger everyday,
Jifarta tayi da wani robar cream ta kauce tareda kara rungumar Qur'an nin ta da kyau, tace "
uwarki ce ta ke tsufa baniba shegiya Y'ar iya yi iyami masu kunu da ruwan sanyi,



" keni yanzu da ajina da ilimi na inkare a Auren naka sasshe Wallahi ni ko ubanshi dakeda kudin
bazan Aureshi ba, d'an kudin su da bai wuce cikin cokali ba, wane Arziki gare su wa yasan da
su a duk fadin garin nan ma,
Ke baby mijin HAJARA na nan zuwa zanba kowa mamaki mijina sai an share titin layin nan
motar shi zata shigo,
Kallon kanki ya tabu kawai RAHAMA ke mata, ganin yayar tata ta zauce kar itama ta biye mata
su zama daya yasa ta bude Qur anin ta fara tilawa cikin natsuwa,


WAYE MALAM BALA?

D'an Asalin garin jega ne dake jahar kebbi, neman kudi ya shigo dashi cikin babban birnin na
sokoto, ta sanadiyar sana'ar Albasa, tun yana saurayi har ya samu jari yayi Aure da wahalar

neman shi domin Almajirine tun yana karami iyayen shi suka kawo shi karatu wurin malamin shi,
sai kuma Allah ya dauki ransu, malamin ya rikeshi tareda bashi kulawa har ya koyamai yanda
zaiyi sana'a tun yana saro Albasa a cikin garin Alero yana siyar aa jega har ya fara zuwa
sokoto da sana'ar ta mike, Sanadiyar shigar shi sokoto ya bashi damar koyan karatun Boko kadan bamai zurfi ba domin ya
lura komai na rayuwa saida ilimin nasara kake samun cigaba, koda kanada na Addini, a harkar
kasuwanci kana bukatar na zamani,


Yayi Aure da uwar ya'yan shi larai da ta kasance Y'ar uban rikon shi wato malamin shi, a
lokacin ya dawo da zama cikin garin na sokoto, ya kama gidan haya a cikin Unguwar mabera
gidane na kasa madaidaici,
Suna tafiyarda rayuwar su cikin sauki kasancewar itama larai macece mai biyayya da hakuri,
har lokacin da ta haifi d'an su na farko Aliyu, rayuwa ta fara musu zafi lokacin da ta kuma
haihuwar Y'ar su ta biyu, domin rayuwar HAJARA daban ce tun tana karama komai ta gani sai
ta damu baban ta tanaso, haka yake fafutuka ya nemo mata, domin Allah ya dora mai kaunar
HAJARA wadda yasakawa sunan mahaifiyar shi,

Lokacin da ta isa shiga school kuwa tana shekara shida aka fara kokarin sakata makarantar
gwamnati kamar yanda d'an uwanta ke zuwa, Amma fur taki tace wata makarantar kudi dake
Unguwar su ita take so wanda a lokacin gaba daya sai ya Tara cinikin wata biyu na Albasar shi
zai hada kudin makarantar, kuma ga hidimar gida gata sutura,
Dole ya fara fafutukar neman canjin sana'a domin cikawa Y'ar shi burinta,
Amma Abu ya gagara, ranar yana zaune a bakin titin da yake kasa Albasar shi , wata katuwar
crv ta faka,
Ya tashi da Sauri ya nufi motar don ya saba da mutumin yana mai ciniki sosai don sai yasai
kwando ma wata rana, mutumin kuma yana mai kyauta,


Fitowa mutumin yayi cikin shigar Alfarma irin ta wa inda suka jik'a da naira ya gyara madubin
idanun shi ya mikawa malam bala hannu ba kyama, cikin ladabi ya rusuna sukayi musabaha,
tareda tanbayar shi yau kwando za akawo ko rabi?
"Muje inuwarka muyi magana malam bala taimako nake nema Allah yasa ka Amince,
"Bismillah Alhaji, ya bashi bencin da yake zama, ya ko zauna, tareda fuskantar shi,

"Dama Alfarmar itace, ina son ka Ajiye wannan sana'ar kazo muyi aiki tare idan Badamuwa ka
zamo driver na akoda yaushe, zan rika biyanka Albashi mai tsoka,shiru malam bala yayi, Alhaji
shuaibu yace" nawa ne ribar Albasar ka a kullum?
Shiru yayi nadan lokaci yana nazari kafin yace a kullum ina iya samun ribar dubu biyu, idan na
siyarda ta dubu goma inkuma kasuwar tayi kasa bai wuce ma insamu Dari Biyar a rana wata
rana har Dari biyu,
Kaga in za ayi cefane ma wata rana sai mun shiga cikin uwar kudin ma,

"Toh karka damu, yanzu dai zan hadaka da wani yaro na ya koya maka mota nan da sati biyu in
kana da kai zaka kware da Y'ar dar Allah, ya ciro katin address din shi ya bashi yace ya same
shi a gidan shi dake tamaje quarters,
Yayi godiya sosai, domin yana matukar bukatar canjin sana'ar domin wata rana ma Albasar
tafka hasara yake musamman lokacin zafi taita rubewa,
Suka rabu A ranar da tsantsar farin ciki ya koma gidan shi, ya fadawa inna larai,
Tace "malam zaka iya kuwa? "Insha Allahu larai ki tayani Addu'a kinga HAJARA nakeso insaka
ta makarantar da takeso HAJARA ta nason hutu larai ina son ta huta,
Murmushi tayi tareda kallon Y'ar karamar yarta RAHAMA dake wasan ta a lokacin, bata wuce
shekara daya ba, tace to "ya' tafa? "Dukan su in Allah ya Y'ar da zasuji dadi, to Allah ya bamu
Alkhairi malam Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a, ya Amsa da Ameen,


Alhmdulillah cikin watanni kadan rayuwar su ta canja domin
Domin Alhaji shuaibu mutum ne mai dattako da sanin darajar d'an Adam bayan Albashi harda
hidimar kayan Abinci yi musu yakeyi,,
Don haka har Account malam bala ya bude yana adana kudin shi, domin siyan gidan kanshi,
ana haka mai gidan da suke ciki yanemi su tashi zai siyar da gidan, Hankalin malam bala ya
tashi domin ko rabin kudin gidan baida da ya siya don haka, dole yafara neman gidan haya
domin tashi su bashi gidan ya siyar, Ranar yaje wurin aikin shi yake neman izinin Alhaji shuaibu domin komawa gida da wuri ya
nemi haya domin notice din da aka bashi ya kusa cika,
Anan Alhaji shuaibu ya nemi yafada mai waye mai gidan?

Ya fadamai yace ko yanada number shi ya Bashi, yace eh ya ciro Y'ar karamar Nokia dinshi ya
duba ya bashi, atake ya kirashi yace mai Alhaji shuaibu ne mai dala yabo ai kuwa cikin
tsananin girmamawa ya gaida shi, ya tanbaye shi ina yake yana son ganin shi, cikin rawar jiki
yace Alhaji lafiya? "No akan gidan kane da kakeson ka siyar na mabera so ina son siya, Cikin rawar jiki yace ansiyar maka Alhaji duk da wani ya taya Amma kai nasiyar maka, domin
duk garin sokoto yasan waye Alhaji shuaibu Mai dala yabo, domin ya shahara ta fagen daukaka
da taimakon Al Umma,


A ranar ya biya kudin gidan tareda mallakawa malam bala takardum yace mishi nashine halak
malak, kuka malam bala yayi sosai saboda jin dadin yadda Allah ya kawo Alhaji shuaibu cikin
rayuwar su, gaba daya rayuwar iyalin shi ta inganta sutura Abinci Abin batarwa, ga inna larai
ma tana sana'oin ta a Unguwar ya gyare gidan tsab ya zama na zamani da ajiyar da yakeyi, gini
ne mai tsakar gida dakuna guda hudu ne a tsakar gidan ciki daya daya, sai kitchen da bayan
gida sai kuma bandaki na bayan gida dana wanka,
Tsakar gidan fes yake ya lailayu da suminti wanda suke wanke shi kaida kai kasan cewar inna
larai mace mai tsafta,
Ba Abinda zasuce sai hamdala,

HAJARA na makarantar da takeso, har lokacin da RAHAMA ma ta isa itama aka jefata,
rayuwar su sai hamdala, Aliyu har ya kammala secondary ya shiga d'an fodio university sokoto,
Shekaru na tafiya cikin fik'irar ubangiji da kuma Y'ar dar shi, har Hajara ta shiga itama d'an
fodio wanda da taimakon Alhaji shuaibu duk karatun su ke tafiya ba tangarda don kowa yasan
karatun jami'a ba Abu ne mai sauki ba,
While RAHAMA na Ajin karshe a secondary,

HAJARA yarinya ce mai mugun girman kai da rashin kunya ga sangarta sam bata taba Ajiye
kanta kusa ba don komai tagani duniya sai tasa malam bala ya siyeshi, shikuwa Allah ya dora
mai sonta fiyeda Y'an Uwan ta yace MAMAN shi ce ita gata da sunan mahaifiyar shi gata suna
kama, domin fara ce tas irin farin fulanin Asali tanada jikinta mulmule kamar mai rayuwa cikin
kankara,
Kyakkyawar gaske ce tanada kyau a fuskar ta da laushin fata saidai batada cikar halittar ya
mace ta gefen sura kirjin tama saitaga dama takesa musu brah a gida inzata fitane dai take
Amfani da mai soso domin karawa halittar ta Armashi, sumar kanta kuwa batada tsawo sosai
saidai inka kalleta zakayi tunanin tanada shi saboda yanda suma ke kwance saman goshinta, Tana rikita Maza gida da school domin HAJARA akwai daukar wanka da gayu,
Akwai wulakanci domin har yau taki tsaida kwakkwaran saurayi saboda dogon buri a rayuwar ta
don ita bama ta hango kanta a gidan gwamna tafi hangota a president Villa, tana ikirarin ita fa
matar manya ce, inna tayi tayi ta rage mugun hali taki,
While RAHAMA kuwa she is very cool girl bata cika magana ba gata chocolate color ce ita mai
haske ba mai duhu ba irin color din nan mai wuyar samu, kallo daya idan kayi mata idan tana
tareda HAJARA zakace she is ugly but wanda duk yasan ainihin sirrin kyau yasan tafi HAJARA
sinadaran kyau, eye lashes dinta is natural gira lips everything about her is unique she is very
cam girl and simple,
Fagen jiki kuwa she is slim but akwai body figure ainihin coca cola shape akwai k,asa dai dai
jikinta haka kirjinta a full da har suna damunta kuma irin masu bajewar nan ne saman kirji,
that's why she is always in hijab to hide her body,

A fagen aikin gidan ma itace kan gaba duk aikin gidan shara girki wanke wanke har wankin
kayan su da na HAJARA gata bata taba damuwa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login