Showing 78001 words to 81000 words out of 108226 words
Chapter 27 - ZANYI BIYAYYA Complete Book Hausa Novels FENERH.pdf
yayi "yanzu momy shine sadiq din da kanshi yafito yace ayi mai Aure?
Wata irin kunya ta rufe RAHAMA wai Aure lallai ma yaron nan baida kunya, "yanzu don girman
Allah momy sadiq ne za ayiwa Aure? "Eh nadai fada maka sakone na isar kuyi duk Abinda
kuka ga dama, "yanzu momy koni lokacina ai ku kuka sa nayi Aure bantaba fadar irin haka ba
bare shi "karka hada kanka dashi inbaso kake inyi maka tone tone ba,
"Ayi hakuri zanduba yafada yana daukar juice din da Aka Ajiye mai ya kurba yana tunanin
tabbas shima badon baida lafiya ba lokacin shi kila da ya nemi Auren kila irin halittar shi sadiq
din yakeda,
A natse RAHAMA ta gyara zama " momy yafada miki yasamu mata ne? "Aa yace zai nema ko
a nemo mai Amma wai sweet sixteen fa, tsaki Al Ameen yayi " yanason Aure za abashi
karamar yarinya don yana mugu, inya shirya ya Nemo sai inyi mai,
"Inada shawara momy, RAHAMA tafada, cikda hikima tafara cewa "ni ina ganin da an hadashi
da Y'ar uwar shi duk da shekarun su daya amma hakan kamar yafi tunda ta mallaki hankalin
kanta,
Wani irin washe fuska momy tayi "nadade ina hango wannan hadin to kinsan halin d'an gidan
nawa bayason babbar mace wai sun bude ido kiji min shirme fa,
Al Ameen yace "indai batada miji tsayayye zan yi magana da Alhaji bello mu tsaida zance a
bashi ita a wuce wurin, "toh ku tattauna inkun gama komai sai infada mai
Amma akwai tsiya fa kasan halinka ya dakko harma yafika kafiya sadiq karyazo ya sa Y'ar
mutane a gaba ya wulakanta,
"Zankoci mutuncin shi inya wulakanta min ya wallahi, inji RAHAMA don haka zan bashi mugun
gargadi akan Y'ar nan kafin ma a daura, "toh Adai fara tanbayar ubanta muji sai ka kira su
Husna da Aliyu ku tsara Abinku nidai ina gefe, tafada cikeda farin ciki ranta yagani har ana
zancen Auren jikanta,........ í ½í¶Š
*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: í ¼í¼»í ¼í¼»
*ZANYI BIYAYYA*
í ¼í¼»í ¼í¼»
*By FENERH*
6⃣3⃣&6⃣4⃣
A kwance yake akan wani tafkeken gado yana faman juyi shikadai domin tunjiya yakasa bacci,
hannu yasa yana dafe kasan shi tareda jan numfashi na wuya, ko runtsawa baiyi ba tsabar
wahala a daren jiya, don haka wayar shi ya janyo yana nishi dakyar, bugun farko ta daga, saida
ya gyara murya yace "grandma kinfadawa Dady? Banji me take fada ba yace "gakiya suyi sauri
nidai su min Aure kafin in mutu wallahi nakasa bacci tunjiya marata ciwo takeyi grandma,
yafada yana nishi, "kuma ni banason Y'ar jami'a budurwa nakeso wallahi wadda zanbude da
kaina,
Datse call din yayi jin ya kunna kakar tashi tafara ruwan fada, yace "Allah ya barmin ke
grandma, dakyar ya mike ko iya tsayawa straight baiyi saboda yanda yakejin ciwon marar
tashi,
Wanka yayi tareda shiryawa cikin native wear ya fito yana baza kamshi da Annuri fadin haduwar
wannan gayen ba a magana domin ya gaji kyau ta koina,
Motar shi ya fada ya nufi hanyar gidan su daga quarters din da yake nasu na ma'aikata yana
tafe yana tunanin yanda zai hada ido da momyn shi, don yasan ba wani iya sakewa takeyi a
tareda shiba saboda kunyar ta, tundaga gate masu gadi suka fara miko gaisuwa, hannu yake
daga musu kawai har yayi parking ya sauka, masu aikin gidan ta ko ina suna harkar su, Katon falon ya shiga wanda ya samu momyn shi da dadyn a zaune, gab da juna daga gani hira
suke mai dad'i kamar koda yaushe, rayuwar iyayen nashi na matukar burgeshi, tun tasowsr shi
bai tabaji ko ganin fadan su ba he pray Allah yasa shima yasamu Abokiyar zama mai hakuri irin
momyn shi,
Yanayin Sallama suka d'an gyara zama, ya dukar da kanshi har zuwa gaban su, "good morning
Dady, momy good morning, yafada a jere, "how are you? Baban ya Amsa tareda zuba mai ido
" naji sakon ka wurin momy na, me yasa kakeson damun matar nan ne kai, wato bazaka iya
zuwa kai tsaye kafada min ba ko? good kaje ka shirya mungama magana end month za a
daura maka Aure da meenal,
Wani irin zabura yayi ya kalli dadyn nashi, "Dady wace meenal din? " Amina Y'ar uwar ka,
"please Dady bana sonta she is my mate fa haba, ina ma laifin Aisha ko kanwar ta but meenal
da tare ma muka gama school nidai Dady nama fasa Auren,
"Saboda kafita daraja ko me kake nufi,? Inji momyn nashi, "toh kafita idona in rufe tunda ka iya
bude baki kace Aure to Angama get ready yanda dadyn ku yace haka za ayi, kuma wallahi
zamu hadu dakai inka wulakanta min ya'
Katashi ka wuce, tafada tana mikewa, tabar musu falon, dukar da kanshi yayi domin bayason
fushin momy sam ita bata mai sauki Amma Dady yana lallashin shi domin Allah ya dora mai son
shi sosai,
Lallashin shi yafarayi tareda fada mai yayi BIYAYYA zaiyi farin ciki, Auren biyayya nada riba
Abubakar zakayi farin ciki insha Allahu kaji, ya aikin naku? "Alhmdulillah yafada ciki ciki, Allah
yasani he is not happy at all duk da Auren yakeso shi baya son saura gaskiya budurwa yakeso
shi wannan yarinyar ma baisan ya takeba don bai taba tsayawa ya kalleta na minti biyu ba a
fisge yake ganin ta ya wuce,
Wallahi da yasan ita za ace za abashi da ya hakura da zancen Auren saidai sha'awa ta kashe
shi da dai ya Auri macen da har ta kammala degree,
Shifa yana son Auren under age ka more sadakin ka yanda kakeso Amma ka Auri Y'ar jami'a ai
kai zata more,
Mikewa yayi ya nufi dakin shi dake cikin gidan tareda fadawa mai aiki takawo mai breakfast,
dakin shi ya tafi fadawa yayi kan kujera ya rufe ido yana ya mutsa sumar kanshi, "I don't want
her yafada can kasan makoshi,
Har saida mai aikin ta yi Sallama ta shigo tareda ajiye mai Abincin ta juya, ya gyara zama
ya fara taimakawa kanshi,
Karfe goma na safe ta iso gidan na momy RAHAMA, tun shigowar ta ta hango motar shi wani
irin farin ciki taji ya mugun rufeta, zata ganshi a arha yau bayan ta kwana tunanin shi, bata taba
tunanin ganin shi a gidan ba tasan yafi rayuwa a gidan grandma shiyasa tanason zuwa gidan
duk da zata iya zuwa sau goma bata ganshi ba, Cikin natsuwar ta ta isa cikin gidan tanajin kamar anyaye mata duk wata damuwa da ta kwana
da ita domin jiya sam bata iya runtsawa ba saboda tunanin in har anhada ta Aure da wani to
akwai babbar matsala kuwa a rayuwar ta, domin soyayyar sadiq tayi mata karan tsaye a
zuciyar ta,
Dakin su Aisha ta nufa wanda ta samesu suna maida bacci, ta buga kafaafun su "ku har yanzu
gari bai waye muku ba?
" dakyar suka iya bude idanun su " Aunty meenal yau ba school to bari mu huta kawai ni har na
tashi zan fita naji shigowar dodo gidan mu dole na hakura nadawo inji Fatima ,
"Ai ni ina jin kamshin Arnen turaren shi nace wahayi ya sauka, Amma kunsan ni da son jin
gulma, naji ana zancen wai Aure yakeso kiji d'an rainin wayau shida bai kallon mata, wace
macen cema zata yarda ta Aure shi,
Wani irin faduwar gaba Meenal taji tayi saurin mikewa " ina momy? Tace musu, "inaga takoma
dakinta kije kigani nidai yau ina daki sai ya sadiq yabar gidan nan, tafada tana koma kwanciya,
Fita meenal tayi cikin wani irin tashin hankali "Aure yakeso that' means yanada wadda yakeso
kenan, wani irin tukukin kishi da bakin ciki ya rufe mata zuciya, Wallahi batason taga ko wata
mace ya Kalla bare zancen Aure bazata iya jurewa ba gaskiya zuciyar ta zata buga,
Jin muryar momy yasa ta shiga taitayin ta, " Amina kinzo? "Eh momy ina kwana tafada tana
saita tunanin ta, "lafiya kalau zo muje daga ciki, bin bayan ta tayi har cikin part din ta, a falon ta
suka zauna, "bakya bukatar komai? kije ki nemi Abun motsa baki a kitchen, "na Koshi sai zuwa
Anjima tafada tana dukar dakai,
"Amina kinsan me yasa nakiraki? Girgiza kai tayi, " ok inaso inbaki wani misali ne sannan ke ki
yankewa kanki hukunci da karan kanki idan kinso zaki yi farin ciki nan gaba idan kin bijire zaki yi
kuka da kanki, wanda shine banaso,
Kintaba sanin cewa dadyn su Aisha shine aka fara zabawa Yaya HAJARA ta bijire?
Dago kanta tayi ta kalli RAHAMA a natse take fada mata yanda maman ta ta bijire daga baya
tadawo tana data sani saboda zugar kawa, datakai ta tabaro,
Banyi niyayyar fada miki ba Amma yaya tasa infada miki komai domin karkuyi kuskure irin nata,
Na Auri dadyn su Aisha lokacin batareda inaso ba Amma BIYAYYA da kuma son rufawa iyayen
mu asiri yakawoni wannan matsayin wanda nasan idan kikayi BIYAYYA kema wata rana zaki
fimu farin ciki, don haka yanzu kiyiwa kanki duk hukuncin da kikaga shine dai dai,
Wasu irin hawaye masu zafi suka zubo mata ta share tareda dago kanta ta kalli RAHAMA "
momy I promise you nima zanyi biyayya insha Allahu domin insamu dacewa duniya da lahira
koda yau su baba sunbani miji zan karba bazanso inyi kuskuren da mama tayi ba, koda kuwa
Auren zai zamo Ajalina, tafada tana faahewa da wani irin kuka,
Tuni RAHAMA taji tausayin ta ya rufeta ba Abinda ta tuna sai lokacin da aka ce ta Auri Al
Ameen, Allah kadai yasan irin Abinda ta hadiya ita kadai sai d'an Uwan ta da ya kwantar mata
da hankali,
Allah sarki yaya Aliyu, tafada tana tuna baya, yau gasu sanadin ta, duka suna farin ciki,
rungume Meenal tayi cikeda rarrashi tace "ya isa ko insha Allahu zakiyi farin ciki like me wata
rana,
Daga kai tayi Kawai ta mike tace momy nagode sosai, ta fita tana tunanin da badan komai a
rubuce yake ba datace maman ta tayiwa kanta sosai domin ita kanta tana mugun sha'awar
rayuwar gidan momyn rayuwa ce data ginu a kan tsari na Addini da tsantsar tarbiya ga daula
kuma wadda suma suna lasawa,
Zatayi iya kokarin ta taga ta zare soyayyar sadiq a ranta kodan ta tsira da mutuncin ta domin
tasan bazai taba sontaba, Amma kuma tayaya zata iya cire son da batasan lokacin da ya
shigeta ba,
Dakin kannen nata ta koma ta samu sun tashi yanzu har suna gyara dakin nasu,
Tace "ina brother DJ? Wato kamar yanda nafada yaran RAHAMA su hudu ne a yanzu Sadiq da
kanin shi Auwal sai Aisha da Fatima, wadda itace karamar duk da kusan kansu daya kamar
Y'an biyu saboda bawani tazara a tsakanin su duka ya'yan nata kaida kai ta haifesu,
"Ai yaya Auwal na gidan Auncle Aliyu kinsan harkar su tafi tafiya shida sa an shi abokin burmin
shi, yaya nasir, d'an murmushi tayi kadan tasan bazasu taba rabuwa ba koda yaushe suna
tare bama ka gane ba uwa daya sukeba saboda kamar jini da sukeda, kamar ba kannen taba
saboda maza yanzu suke saurin girma,
Wayar ta taciro ta kira number nasir domin tanaso ya maida ita gida don napep ta biyo, a
kwance suke a dakin nashi suna hira, " wallahi dude da badon yaya Sadiq da ya min karan
tsaye ba ko tsab zan iya fitowa infada wa momy ni inason meenal yarinyar taji kaya malam,
Wani irin mugun kallo Auwal ya watsa mai "amma bakada kunya wallahi inazaka kai ta yayar
kace fa? "To sai me niba namiji bane ai ina fada maka tunda ya sadiq baiyi Aureba muma bamu
isa mufito mufada ba Amma yau dazaiyi Aure wallahi ballo ruwa zanyi abani ita in more, kai
dude mace cefa har da Rabi infada maka,
"You are mad wallahi bari ajika zakayi bayani, " Allah mugun burgeni takeyi she get everything
malam everything yafada yana tuna how her body and shape are,
Karar wayar shi ne yasa ya yi saurin dagawa, ganin sunan ta, " hello meenal, " come on mara
kunya nidai kazo ka mayarda ni gida a napep nazo " ok yafada yana dirowa, shirya muje gidan
ku tana can, "nifa ba zuwa gidan nan ba yau weekend gayen nan may be yana gida,
"Toh meye muje don Allah, yafada yana daukar key, tasowa yayi suka fito,
Daidai Maman nashi na fitowa daga kitchen, masha Allah nafada domin mata sunzama iyaye
Husna ancika ko ina anzama mama da yara uku ga nasir sai kannin shi biyu mata,
"Ina zakuje ayawo? " gida zamuje mom Auwal yafada, " ok ku gaida Aunty RAHAMA to,
momy dady ya tashi? Aa tafada tana karawa gaba,
They really like this family kowa d'an Uwan kowane,
Ga hadin kai da karfin zumunci,
Allah Allah takeyi su iso tabar gidan itama domin sam batason ma taganshi ya fama mata mikin
da take kokarin rufewa, don haka ta fito tareda Sallamar momy, tace zata tafi, leda ta mika
mata tace ta kaiwa yaya HAJARA, sannan ta fita,
Daidai suna shigo da motar su cikin gidan itama tana fitowa,
Budewa kawai tayi tashiga, suka fara gaisheta, " kuna kusa ne koda nakiraka? "Aa kawai
munyi gudu ne Karki gaji kihau napep, and I dont like it ace classic beb kamar ki a napep, "
hmm har mashin ma zan iya hawa inta kama, bawai napep ba kawai don yama fi sauri,
"Malama ki koyi mota kawai a baki ta hawa tunda kinada ni, nasan kota mama Hajara kya hau,
"lallai mama ce Zata bada motar ta bakaji da kyau ba mama ce zata wani bari a hau mata mota
yanda take mugun jida ita dinnan ,
Dariya sukayi har suka sauketa, saida suka shiga suka gaida maman suka tafi,
Ta mika mata sakon tareda zama tana bata hakuri, " mama kiyi hakuri bazan kuma musu
dakuba ko yanzu kuyi mini Auren na shirya,
"Alhmdulillah naji dadi Sosai da bakiyi shirme irin nawa ba kuma ki kwantar da hankalin ki
zakiso mijin da za a baki insha Allahu , yau bagani ba a gidan baban ku kuma ina farin ciki, me
ya same ni? Don haka kibi iyaye ya'yan ki su biki kema wata rana............ í ½í¶Š
*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: í ¼í¼»í ¼í¼»
*ZANYI BIYAYYA*
í ¼í¼»í ¼í¼»
*By FENERH*
6⃣5⃣&6⃣6⃣
Bacci Yayi sosai a part dinshi, sai kusan Karfe goma sha biyu ya tashi ya yi wanka tareda
barin gidan batareda ya waiwayi kowa ba, grandma Kawai yakeson gani,
Tunda ya shiga gidan ma falo kawai ya zube ba kowa ya runtse idanun shi so yake ya tuna if
ma tanada Abinda ke burgeshi a jikin mace, don baya wani tsayawa kallon ta shi baifa masan
kalar ta da kyau ba, duk da yana son Aure and bai kumada zabi, still baya sonta she is too old
for him. Fitowar grandma ta ganshi zaune ya runtse idanun shi, tace "ikon Allah kai kuwa ka shigo
gidan bako sanarwa saidai infito inganka lafiya kuwa?
Bude idanun shi yayi ya kalle ta " Inafa lafiya don Allah kinja sun likamin wata meenal gaskiya
nidai an cuce ni da kuruciya ta a manna min tsohuwa,
"Iya shege sa ar Husna ce ita ko sa'ar RAHAMA?
Saurin kallon grandma yayi "haba kuma yazaki ha data da su momy na, "eh naga kace tayi
tsufa shiyasa na kwatanta da iyayen ka, " gaskiya ayi maganar gaskiya bana sonta ni impact
ma I don't like this hadin zumunci or what ever you call it bazaku nema min a waje ba ni Allah
bana son raini and