Showing 48001 words to 51000 words out of 108226 words
Chapter 17 - ZANYI BIYAYYA Complete Book Hausa Novels FENERH.pdf
haifeni jijiyoyin mazakuta na a weak waanda ko fitsari
some time sai nayi kuka yake fita,
Anfita dani kasashe da dama suna gwada ni tareda dorani kan magun guna Amma ba a dace
ba,
Lokacin da na fara balaga abin yayi worst saboda lokacin ya hadu da nafara Tara sparm kuma
bazai fitaba wanda duk lokacin da Abin ya motsa sai na suma,
Kinga ma yanda nakeyi ai first time da nayi attempting kusantar ki,
All this years ba likitan da ya taba fada ma iyaye zan samu lafiya sai wata rana da ciwon mara
na yatashi aka kaini Asibiti wannan doctor din ya ganni shine ya fada musu su kaini India akwai
wani kwararren likita, wanda a take ya hadamu dashi,
A lokacin sam bana wani farin ciki saboda ban wani sawa rayuwa ta neman Auren ba bama na
ra ayin Auren, wama zanje incewa inason ta after I no banida lafiyar da kowane namiji ke
takama da ita,
Shiyasa nake kin kula kowace mace ina harkar rayuwa ta,
A lokacin da mukaje India doctor yafada. Musu zan iya samun kafiya, and zai dorani akan
medication tareda surgery , idan nasha na one month sai ingwada ingani ko manhood dina
zaiyi aiki,
Hmm Dady yafada mai ya zanyi ingwada,? Yace ta hanyar saduwa da mace ne Kawai za a
gane na samu lafiya,
Don haka muna dawo wa Nigeria bayan yin aikin, suka bijiromin da zancen Aure wanda sam
banso ba a lokacin sabida ni banajin wani canji and kuma banason in takura kaina tareda wani
kokarin gwada lafiya ta akan wata, what if naje gwaji takiyi kamar ranar da nafara gwadawa a
kanki, nasan zata raina ni ko wacece amma, daga lokacin da aka kawoki gidan nan, nafara jin
wani irin sauyi da kuma son kusanci dake duk lokacin da NA kalleki nakan ji sauyin da bantaba
experiencing ba a rayuwa ta,
I contact my doctor, yafadamin cewar that means aikin da akayi min a jijiyoyin yayi kenan sai
ingwada ingani,
You no exactly what happened lokacin da NA gwada,
Lokacin bayan nan ma na kirashi na mai bayani yafada min indawo akuma gwada ni tareda
canja min medication din,
A ranar kuma momy ta dauke ki, bayan na gama deciding zamu tafi tare Indian muje can
ingwada inga ni in na warke Musha amarcin mu mudawo,
Ajiyar zuciya ya sauke tareda matsawa jikinta ya dora kanshi saman kafadar ta yana lumshe
idanun shi,
"I love you RAHAMA thank you my wife, thank you for all your support and care,
Nagode da bani dama na zama kamar kowane namiji, nasan badan ke bace matar da na Aura
zan iya fuskantar raini a wurin wata macen Amma ke din ta daban ce, na yarda you are
obedient, Allah ya miki Albarka,
Thank you for the precious thing ever, yeah that's your virginity, ni mai sa a ne wanda I no my
wife a leda take tuntuni nine zanbude kayana, inama duk yan mata yanzu su rike darajar su
tareda rike budurcin su, kamar tawa matar ? Da zasu samu mutunci da kima a idanun mazajen
su,
Rungume ta yayi gam jin har yanzu batace komai ba, " say something my wife, please, yafada
muryar shi na cracking " kinaso in yi miki kuka ne wai? Ajiyar zuciya tayi tareda girgiza kai tace
" zazzabi nakeji cikin wata irin muryar tausayi, domin ko ina na jikin ta ciwo yakeyi, ga kasan ta
da takeji kamar wuta saboda zafi, " subuhanallah baby muje Inbaki pain reliever, kinji, ya
dagata tareda rungume ta a gefen shi saboda shima kanshi baida karfi,
Dakin suka koma ya zaunar da ita tareda bude closet ya fito da wasu magun guna ya balloon
biyu ya bata tareda ruwa, kafin ya janyo wayar shi ya kira daya daga cikin yaran shi yace ya yo
musu take away,
Da kyar yasamu yayj wanka tareda Alwala yayi sallar la asar, kafin ya dawo gadon yaga tana
bacci gaba daya tayi wani irin cool dama ita batada wani hayaniya fuskar ta ya zubawa ido
tareda yin murmushi shikadai yasan irin kaunar da yakewa RAHAMA bare yanzu daya jita a
matsayin mace, abin ba acewa komai domin mata akwai baiwa a cikin su Wanda sai Wanda ya
leka zai san da hakan,
Zuba mata ido yayi na dogon lokaci har yaron shi ya dawo yafada mai ya siyo ya sauka tareda
karbo ledodin ya koma sama, Ajiyewa yayi ya shiga kitchen din ya hado musu coffee tareda
dauko plate da cups ya fito,
Ajiyewa yayi tareda nufar ta ya d'an buga kirjin ta kadan " baby get up kinji. Bakyau baccin
yamma, d'an bakinta ta turo tareda tashi ta bude idanun ta tana d'an ya mutse fuska saboda
har yanzu tanajin ciwon kan nata kadan kadan, ga kafafun ta tanajin sun kara tsami , ta ce "
karfe nawa ne? Yace to 5, tayi saurin dirowa tare da nufar hanyar bathroom tana dan din gishi
alamar tanajin zafi a kasan ta har yanzu, tafiyar ta yabi da kallo kafin yayi dariya ya sosa keya
yana cewa "yeah the machine gun is working, cikin dauriya tadan sa ruwan zafi ta yi tsalki
saboda tanajin zafi sosai da mugun zogi,
Tsalkin da. Tayi da ruwan zafi yasa taji wani irin sauki da kuma dadin wurin don haka ta dade
tana watsa wa kanta hurt water a wurin kafin ta dauro alwala ta fito,
Har ya shinfida mata dadduma tareda mika mata hijabi ta saka tareda tada salla, yana zaune
ya zuba tagumi yana kallon yanda takeyi cikin natsuwa da bin kaidojin sallah ba garaje,
Saida ta idar tayi azkar ya ce "madam a juyo a bani abinci am hungry,
Juyowa tayi tareda Dukar da kanta kasa ta gaida shi ya ce " ya jikin ki? Lafiya Kawai ta iya
cewa kafin, yayi murmushi ya matso sosai ya cire mata hijabin tareda janyota tsakiyar kafafun
shi,
Naman da aka gasa shi da romo romo ya bude a poil peper ya mika mata cup din coffee tareda
janyo take away dake dauke da lafiyayyar pride rice, taji hadi, ya ce " bismilah nasan kinajin
yunwa kema don duk na kwashe miki komai kamar yanda kika kwashe min nawa, ta d'an ci
sosai kafin tace ta Koshi, Shima yafara ci yanayi yana kallon ta, kamar ya hadiyeta yakeji a yau saboda so da tattali,
Saida ya gama ta mike cikin karfin hali ta kwashe komai ya bi bayan ta kamar wani bindi har
zuwa kitchen din data tsaya wanke cups din da suka bata,
RAHAMA rayuwar ta tayi saboda yanda sam batada raki, don da watace langabewa zatayi
saboda lalaci da iya shege, rungume ta yayi tsam tareda juyo da ita yayi capturing lips dinta
cikin doki da zakuwa baiki ya kuma wata sumar a jikinta ba yanzu da zata bashi dama zai kuma
lekawa garin maji dadi saidai, yana mugun jin tausayin ta da kuma wata irin zazzafar soyayyar
ta dake ratsa ko ina NA lungu da sakon zuciyar shi,
Dagata yayi cak tareda rungume ta tsam a jikin shi yafara bata wani irin tsotsa da ke rikita
kwakwal wa, baiki su kasance a haka Ba har karshen rayuwar su,
Saida yamata biji biji a kitchen din ya kyale ta saboda kiran sallar da akeyi ta magrib,
Fitowa yayi da ita suka wuce bathroom, tare, ya Tara musu ruwan wanka, tareda tube kayan
jikinshi ya shiga ya ce " kema ki shigo muyi wanka, kasa dago kanta tayi domin bazata iya
kallon shi a tsaye ba komai ba, don haka baya ta juya mai, saida ya fito tareda yin dariya yafara
kwabe mata kayan jikin ta,
"Baby this shame has to stop tunda mun riga munzama daya, kinzama ni Nazama ke ba wata
sauran kunya a tsakanin mu, haka tana noke noke yasata sukayi wanka tareda, yin salla tare,
a ranar yayi bacci cikin farin ciki da natsuwa,
Irin baccin da bai tabayi ba tsawon rayuwar shi, kwanciya gado daya da mace after your first
night, is the best in every couples history, and yayi matukar kokari ganin bai kuma neman ta ba
a daren domin yanaso ta saki jikinta dashi kafin a kuma yi,
Da safe ta tashi garau domin ba wani ciwo da tashi tareda gyara gidan ta like before ta shirya
musu breakfast, ta tsantsara Adon ta tareda baza kamshi, ta sakko kasa domin tanaso ta ga
inda tafara rayuwar Auren ta mai cikeda farin ciki da kuma cigaba da Alkhairi da dama datake
Gani a kullum cikin farin ciki take,
Sallamar da taji ne ya mugun bata mamaki, domin tasan safiya ce Al Ameen ma ko tashi baiyi
ba, and ba wanda zai zo musu gida by this time, saidai kafin ma ta gama tunani suka sawo kai
tareda gyara tafiyar su cikin yanga da nuna sufa sunci dubu sai ceto,,
Sunci uwar dauri kamar tsofaffin karuwai,
Ta gyara tsayuwar ta tareda zuba musu ido ta d'an daure fuska kadan tareda cewa "yaya
HAJARA kune haka gidan mutane da sassafe daga ina haka?
"Um kaji masu gida Allah mai gida, ina gidan yake? Wannan ne gidan Hmm yarinya watan
kunyar ki ya kusa tsayawa insha Allahu zakiga HAJARA a gidan da ya dama wannan ya kuma
shanye shi a haduwa,............ í ½í¶Š
*ku tayata wannan yakin domin yakamata yau dai ta tabuka ma kanta wani Abun, and HAJARA
yara irin su duniya Kawai ke koya musu hankali su shiga taitayin su saboda fushin iyaye babban
bala'i ne da kuma masifa a rayuwar ya'ya, wanda wanna labari yana nufin ribar biyayya ne a
wurin iyaye da kuma illar bijirewa zabin iyaye*
*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: Pls í ¼í¼»í ¼í¼»
*ZANYI BIYAYYA*
í ¼í¼»í ¼í¼»
*By FENERH*
*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel
200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun
banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip
kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire
charges dinsu a ciki, Y'an Niger í ¼í·³í ¼í·ª masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39
03*
3⃣7⃣&3⃣8⃣
Wani irin tukukin bakin ciki ne ya rufeta, musamman da ya juya ba wata kalma Mai dadi ya
tafiyar shi, wazobiyar hannun ta ta kara kallo tsohuwa da ita, ta ja kafafun ta tayi cikin gidan,
ko iya tsayawa batayi ba tafada Dakin su, ta saki kuka mai d'an kara, inna najin ta tace " ai
dama wanda baiji maganar iyayen shiba yana tareda kuka don haka HAJARA tukuna ma Y'ar
nan, tafada tana cigaba da sabgogin ta,
Bayan kwana biyu, suka kawo ganah must go din su guda uku kamar akwati da Babba da
masu binta babbar ma ba katuwa can can ba, medium sai binta da Y'ar karamar cikin su,
Inna ta kira makota aka Amsa tareda godiya dasa Albarka, makota aka tafi ana tsegumi,
Bayan sun watse inna tayi guda ta ce " ina HAJARA fito ga kayan Auren ki, Abin ba acewa
komai, dole ta fito, tundaga nesa tasa kuka ganin ganah must go din a tsakar gidan, " yanzu ita
HAJARA ce aka kawowa wainnan kayan Auren?
Dole tayi kokarin hadiye kukan nan, inna tace zauna mugani dakyau nida ke,
Inna ta fito da zannuwa roba guda kusan goma sai kuma kamfala ta roba itama guda hudu ga
takalma Y'an malabin guda biyu da wasu quality shoe irin na Y'an kauye, ta kalli kayan da ko
da take gidan ubanta da ba wani Arziki sukeda shiba tanada sutura ta kece raini domin mahaifin
su ba baya bane wajen share musu hawaye,
Kayan kwalliyar kuwa ko nata sunfi wainnan daraja goma sha Biyar, don yanzu haka kayan ta
da takeda su duk bana banza, inna tace " kai HAJARA kinga kaya ko, to Allah kade fitina ai
yayi kokari a irin sana'ar shi ya yi wannan uban kaya Allah dai ya mai Albarka, kallon inna
Kawai tayi ta mike tayi daki, batajin zata kuma yin musu da kowa, bare iyayen ta, koda wannan
Auren shine Ajalin ta dole ta karbeshi tayi BIYAYYA, duk da zabin tane ita takawo cikin rashin
sani,
Inna tace " bari in kai daki kafin bakanku ya shigo yaga harkar Arziki, daki takoma tana kukan
nadama tareda jin tausayin kanta tana hango daular da tayi wa kanta bakin ciki tunfarko gashi
Y'ar uwar ta NA ciki yanzu tana fanta mawa,
Ranar tayi kuka hartaba uku lada,
Washe gari baba ya kirata da sassafe kafin ya fita, yace ta zauna,
"Ummi gaki gani ga mahaifiyar ki nan, larai ki zama sheda, in har ummi kika tare kika dakko
kafar ki daidai da kwana daya kika dawo gidan nan da sunan yaji ko wani tashin hankali,
banyafe miki ba duniya da lahira kuma kinfita a cikin ya'ya na, domin tun farko da kike iya
shegen ki nasa miki ido banbari wani ya kyareki ba a gidan nan ga maifiyar ki nan nasha yima
ta kashedi akan karta ce miki komai zaki dawo hanya,
Alhmdulillah ki godewa Allah bello yaron kirki ne duk da baiyi karatu ba Amma yasamu shedar
Arziki a wurin kowa tundaga bakin aikin shi har gidan su, don haka innaji wani Abu to daga
wurin ki ne,.
Kuka tasaki mai cin rai tana girgiza kai " karku yimin baki don girman Allah baba ku yafe min
nagane nayiwa kaina a rayuwa ina neman yafiyar bijire muku da nayi a farko ku yafemin iyaye
ne wallahi koda zanje inci tuwon kasa a gidan bello baba ZANYI BIYAYYA bazan kuma yin
Abinda zai bata muku raiba insha Allahu, tafada cikin tsananin tausayi na iyaye suka ce
shikenan sun yafe mata Amma duk Furucin su akan gidan Auren ta basu janye shiba,
Daki ta koma ta zabga tagumi, waye zatayi tadi dashi ko ta rage bakin ciki, RAHAMA, wata
irin kunyar ta takeji me zata fada mata, wane zance zatayi da ita, ta mugun sakin damar ta
tunfarko, yanzu batada wanda zata fadawa taji sanyi,
A haka aka fara shirin Auren su Aliyu da Husna wanda su baba suka roki Alfarmar Bello ya bari
a yi tarewar baki daya, baiyi musu ba ya Amince don haka dole a haka inna ta fara shirya ta irin
na Amare, wanda a gefen su RAHAMA dai tana gidan momy Hankalin ta kwance koda yau
she Al Ameen na zarya Abin shi wata rana sai momy ta kada shi ya matsu ba a gama Auren ba
su gudu India wanda yana kan shirya mata visa,
Tanason zuwa gidan su domin Abu ya kasu mata kashi biyu itace gefen Ango kuma da gefen
Amarya domin yanzu husna kamar RAHAMA ce ta zamo babbar kawa a wurin ta ba matar yaya
ba,
Komai RAHAMA ke tsarawa, duk da tsakan kanin satikan tanajin wani irin canji a tareda ita, ga
zazzabi dake tashin mata duk dare zuwa safiya kuma tajita garau,
Ba wanda ya ankare da yanayin ta har ya rage saura sati guda Auren su Husna, ta shirya
domin zuwa gidan su taga nasu shirin saidai kullum tayi waya da inna, yau so take taje taga
kayan kafin akawo,
Al Ameen tafada ma zata fita, yace ta jirashi yazo suje, ta ce aa yadai barta ta tafi domin
batason ya ce zai kaita anguwa zai iya kwana domin kwanan nan rigima suke tayi akan yana
bukatar ta, taki yarda su hadu ko yazo gidan,
Don haka dole ya hakura ta tafi ita kadai a cikin dalleliyar motar ta ta tafi wannan karon Husna
ba zuwa gidan surukai,
Tun dosowar motar ta baba ya gane ita ce ya saki fuska cikeda farin ciki yana cikin mutane, ta
faka cikin Sauri ta fito cikin shigar ta ta mutunci hijabi har kasa ta dakko jakar ta, ta nufo su
cikin girma mawa ta gaida su baba, ya amsa cikeda farin ciki yace ta shiga ciki yana zuwa, ta
wuce cikeda dokin ganin inna itama, saidai tundaga shigar ta jikin ta yayi sanyi ganin Y'ar uwar
ta tana wanke wanke duk ta kode duk da bata cikin damuwa yanzu Amma ta canja kamar ba
HAJARA sarkin gayu ba, ita tafara yima RAHAMA sannu da