Showing 30001 words to 33000 words out of 108226 words

Chapter 11 - ZANYI BIYAYYA Complete Book Hausa Novels FENERH.pdf

FENERH   

03 Oct 2025

12544

her more than words can express, ya naji a
jikin shi without her by his side bayajin zai iya walwala da farin ciki bazai iya kallon fuskar ta
tana barin gidan shiba, mikewa yayi ya nufi dakin shi batareda ya iya kallon ko Aliyu ba,
Yana shigewa jikin HAJARA yafara shaking, domin duk duniya ba wanda take tsoro sama ga
yaya Aliyu, don haka ya bata wani irin kallo, yace good very good and well done kinji, wuce
muje gida, yafada batareda nuna mata hanya,
Ko mayafi babu a jikinta tafita daga ita sai wayar ta, ya tsayarda napep suka shiga duk sai
yanzu tafara raina kanta,

Ana ajiyesu kofar gidan ya biya tafito, ya nuna mata hanya tayi gaba, ta wuce da d'an gudunta
ta shige, datse kofar gidan yayi bam da kwado, yana shiga tayi tsaye takasa cewa komai inna
data fito da ga kitchen rikeda flask tagan ta,
"Aa yau kuma? To sannu ko, shigowar Aliyu yasa inna tace "ina kasamota?
Hmm yace tareda nufarta a zafafen da batayi tsammani ba tajita tum akasa ta buga uban ihu
tareda dafe gadon bayanta, saboda ta bugu bana wasa ba,

"Wato ke tacewar ki takai ki dauki kafarki saboda kunyi hannun riga da kunya kitafi gidan
kanwarki ki zabga mata karya wai ankoreki a gida, saboda kinsan ta da tausayi da hakuri sai
zuba mata iskanci kikeyi a gidan ta na Aure kina matsayin yayar ta,
Wallahi da ki zubar mana da mutunci gwara inkasheki kowa ya huta da mugun iri, "salati inna
tasa da salallami tace "oh ni larai yanzu HAJARA Abin kunya da zagin da zakiyi ja mana
kenan? Yanzu a, Al adar bahaushe har ma dai mu sakkwatawa da mukasan yak'ana da kunya
da Kara, ki dauki kafafunki kije har gidan kanwar ki ki share gindi ki zauna, innalillahi wa inna
ilaihirraji un, Amma Y'ar nan kin cuce mu kin cuci Y'ar kanwarki da batasan komai ba,

"Inna da kinji dibar Albarkar da take mata ma da ranki sai yafi haka baci , Yafada ma inna komai
sannan yace yanzu haka, Nasamu momyn su ta tafi da RAHAMA bansan wane tuggu ta hada
musu ba har momyn shi ke kokarin kashe Auren,
Kuka tasa Amma bana nadama ba, "wallahi yaya ni bani nasa aka dauke taba dama ba kaunar
ta yakeba cusa mai kukayi yanzu dole a...... Wani irin hambari ya kaimata, tareda Zaro belt,

Inna tace tsaya Aliyu kafin ka kasheta infada mata Kalmar da bansamu fada mata ba tun a
farko kar in tabka asara,

"HAJARA bamu kika cutaba kanki kika cuta a rayuwa, munfita hakkin ki koda kika gudu kika
dawo gidan nan ubanki hana yayi a duke ki, Amma saboda sharri kika kwashi kafa kika tafi
gidan Y'ar uwarki kika shara mata karya mu mun koreki, kalma daya kawai zanfada miki yanzu
"wallahi duk Abinda ya samu RAHAMA ko rayuwar Auren ta bamu yafe miki ba HAJARA duniya
da lahira banyafe miki ba kuma duniya ce gata nan ta isheki riga da wando, wanda ma bai
shigota ba jiran shi takeyi,



"Kai kuma inka kasa kasheta inada fiya fiya zan kanbada ma tanbadaddiya murage ire iren ta a
duniya, ta shigewar ta dakin ta ta datse tareda kunna katon redion ta,
Ai kuwa dukan kawo wuka ya mata har saida ya ji bata motsi yajata dakin su ya wurga ta ya
kulle ya fice, duk da haka baiji sanyin Abin da ya mata ba bai gama gamsuwa ba, saida ta dauki
dogon lokaci ta farfado bakinta idonta fuskar ta ko ina ta kunbura saboda dakuwar da tayi, Aliyu
mala'ikan daukar raine na duniya baida imani kona anini don ina kallon fuskar HAJARA nace
Kuth dama Soja yayi kawai don suke canja kamannin mutum cikin minti biyu, don inka ga fuskar
ta bazakace wannan hajon bace bai ji da kyau da kuma kwalliya,

Dakyar ta iya motsa kugunta tana Allah ya isa a cikin zuciyar ta domin bazama ta iya magana
ba saboda kunburin bakinta,
Amma ta kudurta koda zai kasheta bazata taba goge kudurin zuciyar ta ba,


*****************
Yau RAHAMA ta kuma yarda da al marin Al Ameen dole yayi girman kai ganin irin gidan iyayen
shi duk da ba irin nashi bane ta san cewa shi din d'an gatane da dole yayi girman kai, momy ta
zaunar da ita tabata hakuri domin tasan ta tsorata ta da fada a, farko, "RAHAMA kiyi hakuri, ni
na haifi Al Ameen nasan rayuwar shi, don haka kiyimin biyayya kamar yanda kikayi wa iyayenki
zakici ribar Abin kinji,
Toh tace batareda ta nuna komai ba momy ta shinfida mata hujjojin ta tace nasan ke ya'ce mai
biyayya da hakuri don haka bazaki tabema dole kiyi dariya kiyi farin ciki a rayuwar ki RAHAMA
kema sai kin shigo gari yanda ba macenda zata nuna miki isa,

Dole sai kin daura damarar yaki da gidan Auren ki akwai kalubale a cikin rayuwar kowane
zaman Aure don haka ki zage damtse ki koyi zaman gidan miji wanda koda Aure Al Ameen
yakara kizama gwarzuwar shi a zuciya,
Haka momy keta tattalin ta, daga baya suka shige dakin Husna dake zaune tayi shiru, tana
ganin RAHAMA ta zabura, tace yauwa sister in low ke nake jira, ta riko hannun ta suka zauna
gefen gadon, tace "tell me About your brother, "me kike sonji akan shi? Labarin budurwar shi,
Murmushi tayi tace "ai yaya baida budurwa Amma Y'an mata nabin shi sosai, yace bazaiyi

Aureba sai yaga ya wadata iyayen mu,

"Allah sarki shima yanada zuciya mai kyau, Amma haka yake baya magana da mutane? "Eh
haka yake, kice halinku daya da yayanki sister inlow, tafada tana dariya,
RAHAMA tana cikin damuwar halin da Al Ameen ke ciki gashi har yanzu bai zoba she thought
zai biyo bayansu, she is very worried, haka ta wuni sukuku a gidan duk da momy da Husna na
iya bakin kokarin su,

Al Ameen kuwa yayi matukar daukar zafi don gani yake da RAHAMA ta nuna bazata bisu ba
bazasuce zasu tafi da itaba, don haka ya nuna zuciya yaki ko zuwa gidan, Baban shi ya kira da
shigowar shi kenan gari yace "Dady zan tafi gobe inga doctor, "to Allah ya kiyaye zaka iya
tafiya Abuja yau gobe katashi you have everything, "yes dady Amma momy ta dauki RAHAMA
yafada cikeda fatan Allah yasa dadi yace yazo ya tafi da ita
"Haka nada kyau ba damuwa nima yanzu na shigo zan fara duba office kafin intafi gidan if you
like zaka iya zuwa mu hadu a office din sai ka wuce, in kuma kana sauri sai ka dawo ko ince
sai munyi waya, ya datse call din, batareda ya jira cewar Al Ameen din ba,

Don haka yasan cewa koma meye yasan da yardar shi momy keyi don haka yasan ba wani
Amfani da zuwan zaiyi mai gidan,
Kayan shi ya hada ya tattara ya fito tareda kudurin bazai dawo ba sai sun gaji sun nemo shi,
Yaron shi Amintacce ya kira tareda damka mai komai ya mika mai wani envelope yace ya kaiwa
RAHAMA ya fada mota ya dauki hanyar Abuja zuciyar shi kamar transformer saboda zafi..........
🖊




*Matar Soja*
2/28/21, 6:17 PM - Q: 🌻🌻
*ZANYI BIYAYYA*
🌻🌻



*By FENERH*



*ga masu bukatar biya ku hanzarta kar Abaku labari ku biya ku karanta cikin Aminci,katin Airtel
200 zaku turo normal vip 500 kuturo katin ku ta wannan numbar 09011251444 ko ta Asusun
banki na 7304736012 nafisa sani Fcmb don Allah vip Kudaina turomin kati idan kana son vip
kutura min ta banki katin nayimin yawa sosai in bakuda Account kibayar a pos don Allah sucire
charges dinsu a ciki, Y'an Niger 🇳🇪 masu bukatar biya ku nemi wanna number +225 48 15 39

03*


2⃣1⃣&2⃣2⃣

A kwance take a dakin Husna, takasa bacci ba abinda take tunani sai Al Ameen da daren su na
jiya, wani irin kewar shi takeji, gashi yaki zuwa ta ganshi, wani irin sanyi ke bin ko ina na jikin ta
idan ta tuna da duk Abinda ya shiga tsananin su, a gaskiya rayuwar Aure na tattare da ni'imomi
daban daban, domin tasan yau ma da suna tare haka zai shayar da ita madara mai wuyar
mantawa, moment dinta da Al Ameen jiya was unforgettable, ya shiga cikin tarihin rayuwar su,
Tunawa tayi da ciwon shi, tuni taji wani irin tausayin shi, yanzu All this years Abinda yake fama
dashi kenan,?
Tunawa tayi da lokacin da ake fama da HAJARA ta yarda da Auren shi taki, tana cewa ai
nakasashshe ne, yanzu wannan ciwon ne HAJARA ke kira nakasa? Ai wanna Abun a tausaya
mai ne domin kowa kallon mai lafiya yake mai ita dai bataga ciwon da zaisa ta kasa zama dashi
ba koda kuwa gurgu ne, mutum ne mai halin kwarai idan ka fahimce shi,
Tunda taje gidan shi bai taba yi mata iyaka da wani Abinci ba sai dakin da ya turata wanda ita a
wurin ta yafi mata saukin zama matsayin ta na Y'ar talaka,
Murmushi tayi tunawa da lokacin da yace zai horata, da aiki sai taga ma shi baiko iya shirya
mugunta ba tunda bai iya daukar hannu yace zai daki mace,
Kwana tayi juyi tareda kewar Al Ameen sosai wanda batasan ta Ina takejin wani bakon Al Amari
ba,




HAJARA dai wasa wasa kafarta ta kunbura saboda targadata da Aliyu yayi da duka dakyar take
taka kafar ta, koda baba ma yazo yaji labari dakin ya, leka yace "ummi Allah ya shiryeki domin
bamu yi miki bakiba ma kina ganin rayuwa bare kuma mun biki da mum munan lafazi, Amma
kisani baki kyauta mana ba baki kyauta wa Y'ar uwar ki ba, kema baki kyautawa rayuwar kiba,
kibi a hankali ummi ke ya' mace ce duk kuskuren da zakiyi zai zama cikin tarihin rayuwar ya'yan
ki ne mai kyau ko mara kyau, yau bakya Alfahari da yanayin rayuwar yar uwar ki, RAHAMA ta
gama dacewa, kina nan kina kokarin ruguza mata rayuwa Allah nakara daukaka ta,

Karatun nata da aka kutsire mata tana can zataci gaba saboda biyayyr iyaye, karkiga mun
zuba miki ido HAJARA, wallahi ko infada ko kar infada sai duniya ta koya miki darasi ko yau ko
gobe don haka Allah ya kare ki daga fadawa halaka,
Ya juya ya fita,

Wanda da kanshi ganin yanda take fama da kafar ya gyara mata cike da tausayi na mahaifi da
kuma tsantsar soyayyar HAJARA da har yanzu tana nan domin soyayyar iyaye ta daban ce duk
wanda ya rasa su yayi kuka wallahi duniya su din gatan mu ne jigon mune garkuwar mu ne su,

duk da inna tayi fushi da ita Amma ta tausaya mata ganin yanda duk ta koma abin tausayi,

Amma Abinda basu sani ba sam rayuwar HAJARA babu nadama kudurin ta na nan na inhar
bazata samu Al Ameen ba RAHAMA ma bazatayi farin ciki ba,
Daga zaune ta kira kawar ta mai zugata Ladidi wata irin yarinya ce masu irin yawon nan da son
Abin duniya itama ba wai Y'ar masu kudi bace Amma tsabar son Abin duniya yasa ta zage
damtse take yawon ta zubar domin ta rika karya,

Kawancen su da HAJARA ya samo Asali ne a school tunfarkon shigar su, d'an fodio, kusan
halin karyar su yazo daya da HAJARA shiyasa suka dunke ko yanzu ita ta ke zuga HAJARA
akan duk Abinda takeyi,

Cikin shasheka take mata magana, " ki kirani takare min,
Cikin karad'i tace "kawata ya akayi ne? " Kedai kikirani, ta katse,
Ladidi ta kirata tana dauka tace "yadai? Anan ta kwashe komai ta fada mata, ta labto Ashar
"wallahi akwai kan uba kenan sha kurumin ki yanzu ki nuna komai ya wuce mu munsan ta inda
zamu bullowa lamarin, tunda kikaga ta koma gidan su ba dadewa zatayi ba zata dawo by then
munfito da wani salon kawata kiyi kwanton bauna kawai, inta kama ko kan dutse ne sai mun
leka don da muji kunya gwara Aljihun mu ya, bushe tawan, bari inturo miki kati, tafada tana
kashe kiran tareda antayo mata dubu guda kai tsaye,

HAJARA tayi farin ciki, sosai a nan ta samu na data,
Ganin sababbin hot pictures din Al Ameen a Mumbai yasa tasan baya kasar so take tasani da
RAHAMA yatafi ko shi kadai,?
Wani irin murmushi tayi tunawa da yanda momyn shi ta wuce da RAHAMA tasan for sure
RAHAMA na garin sokoto,
"Don't worry my little sister wasan bai kareba, ban shiga daulaba kema bazaki shiga ba ban
Auri Al Ameen ba kema bazaki taba Auren shi ba, kiji dadi ba, mu zuba nidake,


**************************
Wasa wasa An kwashe wata guda ba labarin Al Ameen bai kira kowa ba saboda fushi, yaron
shi ya kawowa RAHAMA Envelop da kudi cike da kuma takarda mai dauke da kalamai masu
cike da soyayyar ta da kuma matsayin ta a zuciyar shi wanda saida ta koka a ranar ita kadai
tareda jin kamar tayi tsuntsuwa ta bishi wanda ya fada mata zai dawo idan su momy sun dawo
mai da ita gidan shi,

I can't stay in my house without you nasaba da ke nasaba da rayuwa a inuwa daya dake duk da
we are not too close amma ji nake munyi shakuwa mai girma Rahama take care of my marriage
and take care of your self zandawo gareki da yardar Allah I no banda matsala dake kedin mace
ce ta gari ina farin ciki ina Alfahari, za akawo miki waya ki fadawa Husna ta bude miki watsp
zamu rika chart kinji,

Zuciyar ta tayi matukar tsinkiyewa da karyewa saboda yanzu ne takejin dadin zama dashi yanzu
ne takeji zasuyi zama mai dadi, memory dinta na dada tariyo mata rayuwar su ta daren da zasu
rabu wannan daren bazai taba gogewa a zuciyar taba,

Dady ya kammala mata duk wani shirye shirye domin ta zana jarabawar ta a cikin watannin,
bakaramin farin ciki tayi ba lokacin da dady ya kawo mata zancen karatun ta, koda aka kawo
mata wayar momy karba tayi tace bani kar ya sauya miki ra'ayi nasan halin shi ki kyale shi inya
matsu zai biyo jirgi ya dawo, wanda hakan sam baiwa RAHAMA dadi ba taso ta ji murya shi ko
da sau daya ne,
Gashi tana jin kunyar Husna bazata iya tanbayar ta ba, dole ta share ta fuskanci Al amarin
karatun ta, domin Allah yagani tanada burin ganin ta zama likita a rayuwar ta,

Momy kula take bata sosai har ta saki jiki da su yanzu ta rage kunshe kanta domin bakaramin
fada momy ke mata ba akan rashin kama jiki, wanda dole ta saki komai na gidan yanzu sukeyi
ita da Husna kullum suna kitchen tare, wanda hakan ma farin ciki yake karawa momy Domin
Husna dole tayi girki da aikin gidan, Tun tana korafin "sister inlow gaskiya ki koma gidan mijin ki nidai kinjamin aiki har ta hakura
Abin yafara bin jikinta,

Idan ma fita ya kama tare sukeyi da Husna, tana kiyaye ka'idojin fitar ta wajen suturce kanta
tareda kiyayewa,
Gyaran jiki duk sati sai sunje anyi musu itada Husna, tana waya da su baba da inna yaya Aliyu
ma har zuwa yakeyi wanda yanzu yake aiki da first bank saboda yace bai ra ayin aiki karkashin
Alhaji shuaibu kuma ko baba yanzu katon Kanti ya bude da kudin Sallamar da yasamu a wurin
Alhaji, saboda shekaru sunja gashi suruki dole ya Ajiye driving,

Ganin HAJARA ta sakko tareda gyaruwa yasa baba ya barta tacigaba da karatun ta kafin Allah
ya kawo mata miji su mata Aure a cewar su,
Wanda ita sam wata dama kawai take nema, ta kuma shuka tsiya wanda iyayen ta na binta da
Alkhairi tana musu kudurin tsiya mujedai zuwa Zamugani,


******************
Tundaga nesa nake kallon su cikin dogayen riguna pitch colour, sun yafa mayafi mai wadata
tareda maka tafka tafkan eye glass, a idanun su , dole ka kallesu ka kuma marmarin kallon su
saboda kyau da murjewa wanda dayar tafi daukar ido. Tayi wani irin ja mai kyau da daukar ido
ta canja canji na mamaki saida na matsa da kyau nagane wacece "RAHAMA 😲 ina hijabi da
kunbiya kunbiya,? Kana ganin ta kasan wayewa ta zauna tazama big girl ba duhun kai,

Mika ma Husna key tayi tareda cewa " look I can't drive today, you drive, "aa gaskiya wannan
wayau ne kawai to meye Amfanin iya motar taki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login