Showing 1 words to 3000 words out of 24149 words

Chapter 1 - MUMINA KO AZZALUMA 1 By Sadi-sakhna.txt

18 Oct 2025

464

⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

Available on:wattpad&arewabook


⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫





BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
Da sunan ALLAH muke farawa mai rahama a duniya mai jin ƙai a lahira.

Ayimin afuwa kasancewar na ɗauki wani Loto(lokaci) ba'aji ɗuriyata ba,saikuma na bayyana da wani sabon littafin mai sabon salo da kuma sabon labari. Ah kunsan in mutum ya ɗauki wani lokaci yakanji abu ya fita masa rai,amma maƙasudin ajiye labarinnawa na JODAH shine na samu haɗarin rasa takardun baya,to waiwaya wa nasake rubutawa daga farko sai ya faskara,musamman dana ci karo da wannan labarin a cikin kwanyar kaina,sai kuma naga kaman zaifi armashi da bada citta haɗi da tafiya da ra'ayin ku masu karatu. Wannan ƙunsasshun dalilai suna sukayi tasirin sauya akalar alƙiblar alƙalaminnawa zuwa kan wannan labarin mai suna MUMINA KO AZZALUMA dafatan zaku gama aikinku ku zauna bisa kujera ko gado mai laushi ku bani haɗin kai mu antaya cikin Wannan labari mu ragargazoshi muga mai ya ƙunsa a ciki.......nice dai takun SADI-SAKHNA mutuniyar makaranta kamar kullum. zamu fara da littafi na farko kamar koyaushe a kyauta ne,domin na bawa mai karatu babbar damar tantance tantamar sa na shin zai bimu ne ko kuma zai yada zango anan.Sannan daga baya mu ɗunguma littafi na biyu wanda shikuma tafiyar sa saida masu sulalla za'a yishi,naira na gugan naira har naira 400 kacal to in kun shirya zamu fara shiga cikin labari. Allah yabamu sa'a yayi mana gamdakatar,ya fiddamu cikin wannan damuna lafiya sannan yabamu iri mai amfani ameeeen.......




⚫ _PART 1_⚫





Katafaren ginine daya ƙawatu da fasaha irin ta zamani,iya filin da ginin ya mamaye yayi bake bake a wajen ma a tsakiyar garin abuja ya isa ya faɗamaka cewar mamallakin ginin kuɗi dai ba wani abun ba sun zauna a cikin aljihunsa.

Babban kampani ne daya ƙunshi abubuwa da dama a waje guda,akwai fannin wajen ƙera kujeru da kayan ɗaki na alfarma irinna ƙasashen ƙetare,fannin motoci fannin gwalagwalai da sauransu.

A gaban fuskar babban ginin an rubuta AMJAD EMPIRE da wani rubutu mai kamada launin lu'u lu'u. Amjad empire shine headquater na dukka kampanonin da suke ƙarƙashin mai wannan suna. Bayan wannan akwai wasu ƙananun kampanin a sauran jahohin da suke ƙasar ta Nigeria. Sunan na Amjad ya samo asaline daga mamallakin wajen wato AHMAD JALALUDDEEN (AMJAD) ƙaramin matashi mai ji da tashen ƙudi da damawa a duniyar ta masu hannu da shuni, duk da cewar familynsu ma ba ƙananan mutane bane,amma kuɗin da Allah yabashi da baiwar juya taro zuwa sisi cikin fasahar zamani shiya taka rawar gani wajen bashi nasarar tara maƙudan kuɗaɗe da kuma taka babban matsayi a shekarun da basu wuce talatin da biyar ba. Ahmad Jalaluddeen shine sunansa na ainihi,amma mutane sun fi ƙiransa da Amjad,wannan dalilinne yasa duk wani abu nasa yake amsa ƙiran sunan. Mahifinsa Jalaluddeen Mahraz ɗan asalin ƙasar Chad kasuwancin fulawa ne yakawo mahifinsa Mahrazu ya taho dashi shida ƙanwarsa Hunaiza, ganin mahaifiyarsu ta rasu kuma ya kafu a Nigeria cikin birnin Kano yasa yaƙi ƙomawa ƙasar tasu ta chad,yacigaba da kasuwancinsa har ya buɗe gidajen buredi da gurare da dama,ya tara dukiyarsa daidai gwargwado inda ya ɗora ɗannasa Jalaluddeen akan Harkar,saidai shi ba irinna mahaifinnsa yayi ba,mai makon haka sai ya juya akalar kasuwancinnasa zuwa siyan alkama a wurare daban daban ya dungayin fulawar. A haka har ya dawo Abuja da zama bayan Rasuwar mahaifinnasa,ita kuma Hunaiza a can garin kano tayi aure ta tara nata iyalan.

Shima Alhaji Jalaluddeen tun a garin kanon yayi aure mahaifinsu yana raye da wata ƴar aminin mahaifinnasa wacce ya sauƙa wajensa zuwansa garin Saidai Aisha wacce yaransa ke ƙiranta da hajiya Ummee bata taba haihuwa ba,bayan itane ya ƙara auren Amina ,sukuma ba ƴan nan bane kasuwancin ne yakawosu daga garin gombe.

Haɗuwar fulanin gombe da kuma na Chad shine ya taka rawar gani wajen zunzurutun kyau da ƴaƴan Alhaji Jalaluddeen ɗin sukayi. Hajiya mama (Amina matar Alhaji Jalaluddeen itama tanada haƙuri irinna Hajiya ummee amma tanada faɗa in akayi abinda bai dace ba. Yayinda itakuma Hajiya ummee in kaji maganarta to an taba mata Ɗan ɗakinnata wato Ahmad. Ahmad shine na farko, tun yayensa Hajiya Mama ta badashi ga hajiya ummee, sai kuma ABDULHAKIM da ABDULKADIR wanda su ƴan biyune sai kuma NADIYA Da NIMRAH sukuma wa da ƙanwane,Nimrah itace autarsu itama ganin Hajiya Mama tana mata faɗa sabanin hajiya ummee yasa ta tattara kayanta ta nufi can. Dukkansu a cikin Estate guda suke rayuwa wacce Ahmad ya gina ya dawo da dukka familynsa ciki harda ma Babar su Hunaiza da iyalanta. Da kuma Mamar mahaifiyarsu wacce itama tana raye,saboda ya farantawa mahaifiyar tasa rai.

Hajiya Hunaiza tanada zafi da kuma son kanta da yaranta,sannan ga nuna isa da gadara akan dukiyar yayannata da ƴaƴansa,yayinda itama Deedee mamar Su Hajiya Mama mahaifiyar su Ahmad ita kuma takeda surutu da ƙin ganin taga gaskiya ta ƙyale.

Shi uban gayyar wato Ahmad nasa bangaren daban inda suke zaune da matarsa Surayyah da ƴaƴansu ƴan biyu Jalaluddeen da kuma Mai sunan Mamarta Maryam inda ake ƙiransu FARHAN da FARHANA shekararsu huɗu da aure ƴaƴansu kuma shekara uku.

A ƙarshen Hawa na goma na ginin anan Aka shimfiɗawa CEO na kampanin wato Ahmad Amjad wani katafaren office mai kama da Gidan alatu, Ba kowane zai gani yaƙira wajen da office kawai ba saboda girma da kuma tsarin da wajen yayi. Akan kujerar dake gaban babban table ɗin yake zaune hannunsa riƙe da ink biro yana ɗan kaɗashi akan Table ɗin. Takardune a gabansa da alama sign wasu Papers yakeyi ya tsaya,duk wanda yakalleshi duk kayan alatun daya tara,dan suit ɗin dake jikinsa ma abun kallone,amma kai tsaye zai gano tsagwaron damuwa da rashin kwanciyar hankali a cikin ƙwayar idanunsa.
Turo ƙofar glass ɗin akayi wani mutum ya shigo wanda shima bazai wuce Sa'anni da Ahmad ɗin ba. Saleem kenan PA ɗinsa hakazalika kuma Abokinsa ƙwara ɗaya tal kaman rai. Wasu takardun ya shigo dasu a hannunsa,yana isowa kan table ɗin ya ajiyesu kana ya zubawa Ahmad ido.

Shima ɗago da idanunwasa yayi wanda suka ɗan saka launin ja a cikinsu na alamar mutum baya samun nutsuwa da bacci.

"Shin sau nawa zance maka idan bangama wani aikin ba kada ka kawomin wani Saleem,wai yaushe na zama injine ni banasani ba."

Cikin sanyi da nutsuwa yake maganar amma shi a hakan wai faɗa yakeyi.

Saida yagama maganar ko nace faɗan kafin Saleem ya murmusa tareda jan kujerar gefensa ya zauna.

"Mutumin dayake cewa shige da ficen aiki yana kaɗan wai yau shine yake cewa aiki yayi masa yawa,Amjad wannan takardun fah dana kawo maka yau kwanansu uku ana jiran sign ɗinsu bakayi ba,tun ranar monday yakamata ace anyi,domin na contract ɗinmune da companyn Ƙarfe dake china. A da nasan ko awa bazasuyi ba da kawowa zaka gama dasu,amma yanzu kalli aikin dake gabanka tun wancan satin baka gama ba. Ba wannan bama Sectariyarka tace yau kwananka uku bakaje gida ba anan kake kwana. Amjad wai lafiyanka kuwa menene yake faruwa,kaida tun lokacin da kayi aure komin aiki zai kaimu 2 na dare kai 3 na dare ma sai ka tafi,bakinka ya dunga ambatar ka bar Surayyah ita kaɗai, kasha barin tafiya ƙasar waje ka haƙura da shi akan kayi nesa da ita lokacin da take da ciki,amma wai kaine ka kwana uku a office baka tafi gida ba,shin wanne irin faɗane ya haɗaku haka, gashi Surayyah batayi maka kama da wacce zata bata maka rai irin haka ba. Dan yanzunnan na haɗu da ita a bakin ƙofarka wai kace kada a barta ta shigo,har kuka tayi sannan ta juya ta tafi.

"Ba wai inason shiga lamarin gidanka bane amma Amjad wannan fa babban lamarine da zai tabaka ya taba iyalanka harma ya taba Kasuwancinka"

Har yagama bayaninsa Ahmad bai tanka masa,saida ya tabbatar yagama kafin ya ɗauki envolope ya miƙa masa kana yace.
"Gashi akwai dukkan bayanan da ake buƙata da abubuwan daza'ayi amfani dasu,inaso kaje kayimin bincike akai"

Karba Saleem Yayi ya buɗe ya fito da takardun da kuma wani abu anyi sealing a leda. Bayan ya karanta zaro ido yayi tareda kallon Ahmad ɗin,wanda shi ko a jikinsa kamar bai san mai yagani ba.

"Are you serious Ahmad (tunda ya ƙirashi da ainihin sunansa to abin babbane) kana nufin abin har yakai kayi irin wannan binciken akanta,ban taba tunanin abinda kake faɗa gaskiya ne ba sai yanzu. To........."

"Look Saleem surutunka yashiga kwanyata har ya cikata,idan har bazaka iya yimin ba ka kawo zan bawa wani yayi min,Ina sonta amma a yanxu ko kusa zuciyata ta gaza aminta da ita,i love her but i can't trust her,so i don't have a choice daya wuce nayi bincike akanta........"

Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

Available on:wattpad&arewabook


⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 2_⚫





Koda ya isa Babban katafaren Estate ɗin ba nasa part ɗin ya wuce ba,sai ya nufi sashen Hajiya Ummee,babu kowa a falon daya sha kayan Set maroon colour,ga ƙamshin turare da kuma sanyi AC dayake ratsa falon. Kai tsaye ɗakin dayake damansa ya wuce,a zaune take tasaka gabanta gabas da farin hijabi a jikinta.

Kwanciya yayi a gefen daddumar tata yana kallon POPn dayake saman ɗakin,wanda yasha design daga wajen ƙwararru.

Bayan tayi sallama daga sallahr ta shafa, ƙare masa kallo tayi cikeda kulawa,duk da idunsa a yanxu a lumshe suke amma daga yanayin fuskarta zai nuna maka ta gane wanne irin yanayi ɗannata yake ciki.

"Akwai abinci akan dinning na ajiye maka,tuwon shinkafa ne miyar kubiya"

Ɗan murmushi tayi ganin duk da ta ambaci sunan kalar abincin amma ko buɗe idonsa bayyi ba ballantana ya motsa ko kuma ƙoƙarin tashi.

"Ahmad!!"

Buɗe idonsa yayi ya zuba mata su yana jiran yaji mai zatace,bata fiye ƙiran sunansa ba,shiyasa a duk lokacin data ƙirashi dashi yake tattara nutsuwarsa gareta,domin yasan magana mai muhimmanci ce zata biyo baya.

"Shi ɗan adam baya kasancewa a kullum cikin farinciki batareda Allah ya jarabceshi da shiga damuwa ba,kaima bazan tsameka daga jerin jaddawalin ba,nayi ƙoƙarin na ƙin shiga lamarin abinda yakasance kai kaɗai ya shafa,amma dana auna yanayin damuwar ka sai naga ta wuce bisa ƙa'idar da za'ayi shuru batareda anyi maka katsalandan ba. Ahmad wai shin mai yake damunka,menene tsakanin ka da matarka?"

Tambayar batazo masa a bazata ba,domin dama yasan dole za'akai ga hakan,amma sam bai shirya jinta a yanzun ba,musamman da shima neman makama yake bashida cikyakykyiyar hujja.

"Ummee mai kika gani babu abinda yake tsakanin mu,kawai dai......."

Murmushin da tayi ne yasashi tsuke bakinsa yayi shuru bai cigaba da bayanin ba,domin yariga yasan bashida amfani tunda ba tasiri zayyi ba ga kunnen dayake saurare ba.

"Koda ace ka girma Amma ɗan ummee baka kai kayimin wannan wayon ba. Bani kaɗaice shaida ba hatta ga mutanen da suka sanka su shaida ne da irin son da kakeyiwa matarka Surayyah,har buya kake a gida kabada uzurin baka nan,saboda kar kayi nesa da ita,idan kuwa ka zauna a waje bazaka tashi ba batareda ka yabeta yafi sau a ƙirga ba. Laƙaninta a bakinka kuwa shine ƴar aljanna,domin kaida bakinka kace indai ƙafarka ce to ka ɗaga mata tashige. Kuma zancen ba iya ga fatar bakinka bane kaɗai saboda soyayya ya tsaya ba,domin mu kanmu shaidane da kayi dace da samun mace tagari,domin hankali kwance na miƙa mata ragamar kulada kai dayake hannuna,saboda ganin sauyawarka da kuma nutsuwar da kake samu a tattare da ita. Amma.....yanzu ko wata ɗaya ba ayi ba kaga yanda ka koma ahmad!!! Kayi baƙi ka rame baka zama a gidanka,ina kulada kai idan dare yayi ka dunga zagawa kana jera ƙananan tsuka saboda bakason zuwa sashenka. Wai a hakan ma kana boyewa ne domin kar mu gane,amma nasan da kai tsaye zaka ƙauracewa part ɗinnnaka. Ina so ka sanar dani mai yake faruwa,shi zaman aure idan aka samu akasi aka kai wani mataki matsala bata warware ba,to dole manya su shiga lamarin. Na zuba maka ido amma naga har yanzu baku saita kanku ba"

Tunda take maganar Ahmad ya zuba mata idanu yana kallonta,duk abinda take faɗa samsam bazayyi musu ba,domin gaskiya ne zancenta,shi kansa yana mamakin yanda lokaci guda zuciyarsa ta sauya akan matar tasa. Tambayar da tayi masa a ƙarshen sam bashida amsarta domin ko za'a kasheshi bazai ce ga abinda ya haɗasu ba a zahiri,amma ga baɗini ji yake kaman an haɗashi zama da wani mutum daban da bai sanshi ba.

Jijjiga ma hajiya ummee kai yayi tareda yin magana cikin nauyayyiyar murya.

"Bansan amsar tambayar da kikeyimin ba nima a yanzu ummee,abinda nakeji a zuciyata kuma kona fesar babu wanda zai yarda dashi,domin ni kaina har yanzu ƙwaƙwalwata bata yarda dashi ba tukunna. Barina je na ɗan huta ummee kaina ciwo yake"

Bai sake bari ta jefeshi da wata tambayar ba ya ɗau ƴar saman rigarsa ya gudu.

Tun daga bakin ƙofar shiga sashennasu yake ta ɗaga hanci,burinsa ya jiyo ƙamshin turaren da kullum yake yi masa barka da zuwa,amma shuru yau tsawon wata guda kenan da daina jin irin waɗannan abubuwan. Wata ƙaramar tsuka yayi kana ya kama handle ɗin ya shiga falon.

Sai a yanzu yake dana sanin akan meyasa bayyi part ɗinsa daban ba wanda yake can gefe,giyar soyayya da muradin zama kusada matar tasa yasa ya haɗa komai a ciki,kama daga Sashen yara kitchen ita nata sashen da kuma nasa duk suna waje ɗaya. Hatta extra ɗakin dake cikin sashen shima duk a tare suke waje ɗaya.

Babu motsin kowa a falon sai kallo wanda wasu ƴan nigerian film suke ta cashewa dagasu sai wandunan da su gwara babu su. Innalillahi wa inna ilahi raji'un ya ambata kafin ya kashe tvn da sauri,Allah yasa ma su farhana basu gani ba,ya faɗa a ransa.

Bai bi takan ɗakinta ba nasa ya wuce,yanda ya barshi a haka yazo ya tarad dashi,babu abinda aka ɗaga ballantana a goge. Jijjiga kai yayi ya wuce banɗaki ya watsa,kafin ya iyo alwalar sallar la'asar,dan yaji wasu masallacin sun fara ƙira.

Jallabiya yasaka milk sai tashin ƙamshi take,sannan ya ɗan ƙare turare ya taje kansa ya fito. Ido suka haɗa da Surayyah wacce take sanye da mini skirt da kuna best a jikinta. Tana ganin fitowarsa ta taho da sauri zata rungumeshi. Saurin ja da baya yayi yana ƙare mata kallo kamar yaga mushe.

Rigar jikinnata gabanta tamkar net yake kana ganin komai a fili,haka shima skirt ɗin na jeans ne amma duk an bubbulashi wai saboda gayu.

"Shin su farhana suna nan?"

Yayi mata tambayar yana kallonta sama da ƙasa.

Turo baki tayi wanda yayi mata kyau,kuma danyayi kyau ɗin dama tayi.

"Eh suna nan mana yanzu suka shiga ɗakin wasansu,kana son ganinsu ne?"

"Ahah....amma kikayi wannan shigar a gabansu?"

"To menene a ciki ba yarana bane,kuma naga basuda wayo sosai"

Duk da matsawar dayayi taji babu daɗi,amma haka ta basar tasake ƙoƙarin shigewa jikinsa,wannan karon hannun ta data saka a kunkuminsa ya cire tareda matsar dashi daga jikinsa.

"Menene haka Surayyah,wai bakya ganin masallaci zanje ne"

Marairai cewa tayi kaman zatayi kuka kafin tace.

"Wai meyasa Honey kakeyimin haka ne,duk lokacin dana matso jikinka saika dunga guduna,ga abinci can nasaka Hannatu ta dafa maka amma nasan ko nace kazo kaci bazaka ci ba"

"Nace miki masallaci zanje,ko so kike na makara a sallah,sannan ai kinfi kowa sanin banacin abincin masu aiki,yaushe kika daina saka hannunki kiyimin abinci saidai kibawa masu aiki suyimin. Wai mai yake damunki ne Surayyah,mai yasa dukka kika sauya daga fari zuwa baƙi,shin nayi miki wani abune da bakyaso,ko kuma wani abun yana damunki ki sanar dani mana"

"Daga baƙi zuwa fari? Wato duk kyautata makan danakeyi a baƙa nake ma a wajenka"
Bai bata amsar tambayar taba illa wucewa da yayi yabarta a wajen. A bangarenta tana ganin duk abinda tayi har yanzu batayi masa gwaninta ba,yayinda shikuma yake ganin anya lafiyarta ƙalau.

Saurin buge hannunta yayi wanda yake shirin isa ga fuskarsa. Cikin tsuke fuska ya ɗauke idonsa daga kan i pad ɗin dake kan cinyarsa ya zuba su akan Surayya wacce itama take kallonsa cikin mamaki da alamar tambaya.
Kayan baccin da suke jikinta ya ƙarewa kallo,riga da wandone masu sharara baƙaƙe wanda suka fito da ainihin zatin kyakykyawar farar fatarta da kuma kyan surarta a ciki.
Baza ƙamshin shu'umar humrah take mai sanyin daɗi wacce ta dace da yanayin garin,a taƙaice dai babu mai lafiyar dazayyi ido huɗu da ita a lokacin baiji tsimin sa ya motsa ba,musamman ma samunta kusada shi tana miƙa masa tayinta cikin sauƙi.

Saidai ga Ahmad ba haka lamarin yake ba,domin kallonta yake da shauƙin data gaza fahimtar wanne irine,shin na tsana ne ko kuma na rashin buƙata ne,amma dai bana buƙata bane,domin kwata kwata kallon dayake mata bayyi kama dana so ba. To mai yake damun mijinnata? Tayi wannan maganar cikin ranta.

Ajiyar zuciya ta damuwa ta sake kafin ta karyar da wuya gefe kaɗan.

"Abban Farhan mai yake damunka ne haka,gaba ɗaya ka sauyamin a kwanannan,bakacin abinci idan nayi,baka kwana a ɗakina,baka doguwar hira dani,a matsayina na mace na jure ƙauracewarka na wasu lokuta,amma ganin bakada niyyar waiwayata yasa na cire kunya ni nazo inda kake,amma abin har yakai ka haramtamin taba jikinka Abban Farhan ? Mai nayi maka haka dana cancanci irin wannan hukuncin?"
Cikin sanyi da kuma karaya ta ƙarisa maganar kaman zatayi kuka.

Ko kaɗan maganganun Surayyah basu saka Ahmad daidaita kaifin kallon dayake mata ba. Lumshe idon yayi kafin ya ɗauke kallonsa daga kanta ya maida zuwa ga i pad ɗinsa. Cikin miskilanci kamar wanda aka yiwa dole ya motsa bakinsa.

"Bakya buƙatar son jin dalilin hakan daga gareni,domin kin riga da kinsan amsarsu,idan har da dama zan so ki fita ki bar ɗakinnan yanzunnan,domin a halinda nake ciki banason ko haɗa numfashi dake"

Wani zaro ido tayi jin furucin da yayi mata,wanda takejin kaman an caka mata ƙusoshi ɗari a kan zuciyarta. Haka babu yanda ta iya ta zare jikinta daga kan two seater da suke a zaune tayi hanyar ƙofa domin barin ɗakin kamar yanda ya buƙata. Saida ta sake juyowa ta kalleshi kafin ta ɗauke ƙwallar datake shirin zubo mata tabar ɗakin haɗe da jawo masa ƙofar.

Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

Available on:wattpad&arewabook


⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 3_⚫




Kukan Farhan ne ya tasheta daga bacci,wanda yake ta ihu kaman ana zare masa rai. Mitstsike idonta tayi kaman bata so ta zaro ƙafarta daga kan gadon.

Bacci ne a idonta sosai saboda abinda Ahmad yayi mata jiya,amma tasan bata isa tayi ba tunda yau ɗin weekend ne,gashi Hajiya mama bata nan mahaifiyar Ahmad kakarsu ballantana ta turasu wajenta.Ita kuma Hajiya ummee tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login