Showing 18001 words to 21000 words out of 24149 words

Chapter 7 - MUMINA KO AZZALUMA 1 By Sadi-sakhna.txt

18 Oct 2025

456

zan aika a kaimiki har gida"

Duk da cewar Allah Allah Surayyah take tabar wajen amma haka kawai taji wani iri datace mata wataƙila haɗuwar ƙarshe sukayi.

Har bakin wajen motar ta ta rakota,daganan sukayi sallama saida taga tafiyar Surayyah kafin tayi murmushi ta bace batttt😜 (nima na bace na daina rubutun?)
Ga wanda basu fahimta ba..... Inaya Aljana ce kuma ƙawa ga Surayyah dasukayi makarantar secondry ta kwana tare. Har suka gama gwagwarmayar su suka kwana tare suka tashi tare Surayyah batasan Inaya Aljana ce ba saida suka zo rabuwa a ranar yin candy take faɗamata ainihin ita wacece,sannan tayi mata kwatancen yanda zata sameta idan tanaso tayi mata wani abu. Duk da a tsorace Surayyah ta rabu da ƙawarta ta da taji cewar ita wacece? Hakan bai hana ta tuna kwatancen datayi mata,bata kuma taba nemanta ba ko tunawa da ita sai yau da buƙatar hakan ta taso mata.

Wayar tace tayi ringing tana cikin tafiya a motar bayan tashigo cikin gari. Tana ɗauka sunan bro ne ya fito akan wayar. Da kaman bazata ɗaga ba saikuma ta ɗauka batareda tace komai ba
.
"Hello aunty Surayyah wai kina garinnan kuwa,Mama tace rabonki da kizo gida anfi wata huɗu,yanxu ma batada lafiya dawowarmu kenan daga asibiti hawan jininta ya tashi,kowa yaje amma babu wanda yaganki sai tambayarki ake,kowa yana cewa yanxu bakya ƙiransa a ƴan uwa gabaɗaya kin sauya"

"Kaga naji wannan ƙorafin,yanzu dai ina maman take ya jikinnata?"

"Da sauƙi sosai ta ɗan warware ma"

"Ohk bari na dawo daga wani wajene bari naje gida na shirya gani nan zuwa"

Bayan ta kashe wayar tabe baki tayi tareda juya ido.
"Ohh again mutum bashida hutu daga wannan sai wannan wai,ni marana ma ji nayi kaman ciwo take this irritating pregnancy wlh da baikai wannan girman ba zubar shi zanyi don ya isheni,to ma meyasa ma na yarda na barshine,a garin kwaɗayina na haɗa kaina da wuya,gashi yanxu it became useless mtsww"

Ita kaɗai take tafiya tana masifa harta isa gida.
Babu kowa a gidan data shigo alamar gogan bai dawo ba kenan. Watsa ruwa tayi ta sanja kaya,cikinta a cike yake da kayan marmarin datasha a gidan inaya dan haka hanyar ƙofa tayi zata fita.

Ta buɗe kenan sukaci karo da Nimrah zata shigo.
"Ahh aunty Surayyah fita zaki sake yi kenan?"

"Eh ko kin bani aikin wani abune banyi ba kike tuhumata"

"Ahah ba haka bane dama Hajiya Ummee ce take ƙiranki akan zakuyi magana,sannan sunga kin daɗe baki shigo ba sukace nazo na duba in jikinne suzo dubaki"

Ɗan juya ido tayi,ashe fah ita rabonta da shiga sashen mutanen gidan shima anyi wata huɗun,gabaɗaya ta manta da wasu sashenma a gidan bayan nasu.

"Kice musu ƙalau nake ni babu abinda yake damuna. Batun wama kikace sunan ta,hajiya waye? ......tajirani akwai inda zanje idan nadawo naga inada time ban gaji ba zanzo"

"Hajiya Ummeen ce zata jiraki?!!!......"

Nimrah ta faɗa tana zaro ido.
"To so what bazata jirani ba,nima wajen tawa uwar zanje batada lafiya,ko ganin tawa uwar zan ajiye naje ganin ta wani. Dan haka kaman yanda ta aikoki in kinaga zaki sake maida aiken kice da inda zani tajirani saina dawo"

Tana gama faɗin hakan tashiga mota tasake fita a gidan.

Sororo Nimrah tabita da kallo tana jijjiga kai kaman ƙadangare.

"Hmmm ba ina faɗamusu wannan matar ta kwance ba batada mutunci amma saisu hauni da masifa su hanani faɗa waisu ga dattijai iyayen dattaku,inama a gabansu tayi wannan tujarar naga ya zasuyi tabbb. Aike na kawo miki kam kema kika bani zan kuwa je na faɗamusu yanda kikace. Inkuma suka ƙi yarda zan zuba musu ido. Idan kere na yawo zabo ma na yawo ai dole zasu haɗu. Tunda kinayi ba ƙarya nake ba wataran dole zakiyi a gabansu su gani ai"
🥱🥱🥱 To nima sadi-sakhna nace zatayi kam.....ku jama'a aradu bacci nakeji,kafin sumayya ta tashi nima barina ɗan runtsa koh?"




Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 17_⚫


"Yeee ga aunty Surayyah tazo,Granny kinga aunty Surayyah tazo"

Ƴar yarinyace take maganar wacce bazata wuce shekara shida ba,kyakkyawa ce anyi mata kitso a dogon gashinta ta sha riga ƴar kanti pink mai kyau.
Da gudu ta tafi ta rungume Surayyah data fito a cikin mota.

"Aunty Surayyah inasu Farhana baki taho dasu ba,kullum fah dasu kike zuwa amma yau bakizo dasu ba. Aunty ina chacolate ɗina,ina yau kam zaki ɗanani a mota kaman yanda kikace jiyaaa?"

Duk wannan surutun tana riƙeda ƙafar Surayyah takeyinsa,ko ɗaya bata bata amsa ba amma hakan bashi ya hanata yin shuru ta daina tambayar ba
.
Wani tabe baki Surayyah tayi ta juya ido kafin ta matsar da yarinyar gefe a hankali cikin dabara.
Ɗan murmushi tayi mata tareda cewa.
"Intisar ina mamanki?"

"Uhmmm tana part ɗinmu"

"Yawwa to maza jeki kice mata nazo ko?"

Ɗan bata rai tayi alamar batason tafiyar tareda noƙe kafaɗa,jakar hannun Surayyah take kalla,da alama wani abun take tunanin samu a ciki. A bangaren Surayyah kuma gabaɗaya yarinyar ta dameta.

Muryar Mama sukaji tanayiwa Intisar magana.
"Inti jeki maza wajen mommy ko,kinga yau auntynnaki batajin daɗin biyeki kuyi tayi kamar kullum kinji"

Badan taso ba ta nufi hanyar sashennasu,Mama tabita da ido tana murmushi. Ƴar yayansu Surayyah ne na fari,anan cikin gidan yayi aure a nasa part ɗin. Intisar itace babbar ƴarsa saikuma Saddiq shikuma ƙaramine bai wuce shekara uku ba.

Juyawa Mama tayi zuwa sashennata yayinta itama Surayyah tabita.

A falo suka zauna dukkansu,saidai suna shigowa Mama tasaka ƴar aikinta ta kawowa Surayyah ruwa.
"Mama na sameku lafiya ya jikin,haka Faisal yace bakiji daɗi ba harda asibiti"

"Eh wlh amma dai ba mai tsanani bane sosai kwana na ɗaya,har yayanku yafara faɗa akan ya bakizo ba nace su barki kema ba daɗi kikejiba,wanda bashi kaɗai ba baya rabuwa da laulayi dole a dunga yi masa uzuri. Ya can wajennaku dai ƙalau ko,su hajiya mama da Ummee,ina cewa dai zansaka Faisal ya kaini mu gaisa to kinga lafiyarce gabaɗaya taƙi daɗi sam.

"Hmm hakane kam,to Allah yaƙara sauƙi"

"Ameen ya Allah,ni ya zancen fara kasuwancinnaki kinfara ne ko har yanzu kina nan dai zaune a gidan. Ba'a haka Surayyah,gwara kiɗan samu wani abun ki dungayi,duk da cewa miji yanada rufin asiri amma iya juya taro zuwa sisin shima wani abune,zaki dungayiwa kanki wani abun batareda miji yasani ba"
Shuru Surayyah tayi tana sunkuyar dakai daga baya kuma tace.

"Ehh yanzun kam banayi amma zaije ƙasar waje bari inya dawo zanyi masa maganar naga mai zan fara"
"Kin fasa yin harka Kayan sakawar kenan. Shikenan duk yanda kukayi dai Allah yasaka albarka ya inganta,baki tambayi mutuniyar taki ba,dazu kuwa tagama ƙorafin kin daɗe bakizo ba,itama bata daɗe da fita ba"

"Ohhh Ameera? Ni sungama makarantar ne"

"Ahah da dan saura dai,set ɗinsu ɗaya dasu zainab ai ƙanwar taki. Ana ta fama dai aski yazo gaban goshi. Kije ku gaisa da Babannku yana ɗakinsa,da kuma hajiyan Su Faisal kafin nan bari nima nayi sallar la'asar"

"To shikenan bari na shiga sashen su intisar mu gaisa nima"

Daga haka Surayyah ta tashi ta nufi wani bangare na gidan.

Bayan ta fita Tashi mommy tayi tai sallah,daga nan da kanta tashiga kitchen yimata abin ƙwalama na masu ciki.

Ɗan na sululu tayi mata yasha kayan vegitable da kuma manja da yaji. Mai aikinsu tana cikin jerawa Surayyah tashigo falon,abinka da dama masu ciki lokaci guda yawunta ya tsinke tana lelleƙawa taga ta inda ƙamshin yake tashi.

Bismillah mommy tayi mata ta juice na ginger shima an ɗan matsa masa lemon tsami.

Tana ci tana lumshe ido tana kora lemon saida ta kusa ganin bayan kwanon kafin ta sarara. Duk da AC dake falon amma ta haɗa gumi sai shishutu take saboda yanda take barbaɗa yaji.

"Kai Mommy amma abinnan akwai daɗi,anya kuwa na taba ci?,gaskiya inaga rabon danayi ƙoshi irin wannan harna manta,nake cewa ni bana laulayi na zaben abinci ashe bansamu bane. Dan Allah mommy a ina zan dunga samun irin waɗannan abubuwan?"

Dariya mommy tayi tareda jijjiga kai,jin yanda Surayyah ta baje a kan carpet ɗin falon tana zuba santin abincin.

"Kai Surayyah kema dai da shiririta kike,wanne irin baki taba ci ba,daman wannan ai abinda kike so ne tun kina gidama,saidai kice kin manta dai saboda santi, mesunan babannawa ne zaizo ya daukeki ne,naga kinyi dare?"

"Wanne mesunan baban kuma waye haka?"

Harara wasa mommyn tabi Surayyah da ita,kafin tace.

"Ke lafiyarki kuwa ko cikinne yamaidaki haka,mijinnaki kika manta wayeshi.....wai naga in kikayi dare shike zuwa ɗaukanki,ko yayi ta ƙira in bayanan akan ki koma gida da wuri,naga harkin fara tuƙi da kanki ina umarin?......uhmm girma mai saka mutum ya sauya,gabaɗaya ɗabi'unki sun sauya yanxu babu wannan lankwasar dakan da kalar abin tausayin kinfara zama mace mai kwarjini"

"Ehh wlh kuwa Mommy,gabaɗaya aunty Surayyah ta sauya,kinaga wai yau itace tazo da gida da gyale kuma tana tuƙa mota ba driver,kiga wayar hannunta ma fah.....kai Mommy gaskiya dole na zama business man sosai,kuɗi fa ba wasa ba yana sauya mutum sosai"

"Kaga sarkin surutu to ya isa karka dameta,ɗan shige muje in kaji ana faɗa ka shige gaba"

Ɗan jimm Surayyah tayi kafin tayi dariya,can kuma sai tace.

"Mtss gaskiya inaga dai yanayin cikinee danni kaina naga na sauya dayawa,Abban su Farhana Bazaizo ɗaukana ba yana wasu ayyuka. Abba bai dawoba ko bamu gaisaba"

"Ahah bai dawoba sun tafi wani Ƙauye shida Malam Hashim akan wani ambaliyar ruwa da akayi,zasuyi jaje ba lalle ya dawo da wuri ba.kije dai cikin gidan kuyi sallama to kizo ki tafi"

Amsawa tayi da to kafin ta miƙe tafita,itakuma Mommy ta hau tattaramata ɗan abinda zata tafi dasu wanda baza'a rasaba.

Sai wajen misalin ƙarfe tara Surayyah ta danno hancin motarta cikin etate ɗin,waƙar Viviano takeji tana rausayar da kai,gabaɗaya tama manta da zancen wai zasuyi magana dasu Hajiya mama dan haka kai tsaye sashensu ta nufa tana yatsine fuska alamar ta gaji.

Ahmad tagani a bakin ƙofar shiga cikin falonsu ya kama kunkumi yana kallonta,ɗan tabe baki tayi kafin ta fito daga motar ta nufeshi tana tura ciki wanda yafara fitowa.

"Daga ina kike?"

"Miye damuwarka da inda nake,ka damu ka dunga sanin wannan ne,ko kuma yau wani abun kakeji dashi,to daga gidanmu nake"

"Nimra tacemin ta faɗamiki zakuyi magana dasu Ummee kikace mata wai su jiraki,su jiraki fah kikace? Surayyah kin sauyamin tun ina tantanmar cewar anya kuwa kece yanzu kam na fara gaskatawa,ki faɗamin gaskiya anya kuwa kece wacce nayi soyayya da ita harna aureta,kokuma dama waɗannan sune halayyarki kika boyemin,to in haka kike ko kuma koya kikayi yanzu menene dalilinki na boyewa sai yanxu ki nuna,wani abu nayi miki kike ƙoƙarin ɗaukar fansa akaina?.....

"Hhhhhhh haba ahmad gaskiya na raina wayonka,menene ya ɗaukeka tsawon lokaci kafin ka gano hakan...........




Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 18_⚫



.....A farko inasonka soyayyarka ce tasa nayi abinda zanyi harna zauna dakai,amma yanxu am no longer anymore,kanaso komai yadawo yanda yake? Idan har kanaso to kajira zan kawo maka wata takarda kayimin signing na abinda nakeso,bazai wani wuce billion 10 ba,in har zaka bani to komai zai koma normal,amma idan ba haka ba you will continue think shin a duniyar mafarki kake ko kuma duniyar mutane. Saboda wani abun idan kajishi sai kwakwalwar ka tayi shuru na wasu mintuna kafin ta dawo daidai. Believe me bazaka so jin menene yake binne ba,idan kuma ka damu harka jiyo to fah damuwarka ce ba tawa ba"

Da ɗan murmushin shu'umanci ta ƙarisa maganar kafin ta zagayeshi ta bar wajen,inda ta barshi sororo yana tunanin shin lafiyarta kuwa?.

Bayan ta shiga ɗaki wurga jakarta tayi akan gado tareda ɗosana jikinta akan gadon. Ɗan runtse ido tayi tareda matsa ƙasan mararta kaɗan,da alama ciwo yake mata.

Banɗaki tashiga bata daɗeba ta fito,da alama fitsari tayi. Ledar da ummansu ta bata ta buɗe data tuno da ita,sauran abincin datacine ta sakamata a flask sai kuma wasu tarkace na abincin gargajiya irin su kuka daddawa citta da sauransu,sukam ajiyesu tayi gefe don ba abincin takeyi ba ballantana tayi amfani dasu.
Ta gama cin abincin babu zancen yin sallar isha anan ta zube bacci,saboda gajiyar da ta tarawa jikinta a ranar.

Da safe data tashi kai tsaye farar takardar dake kan wardrop ɗinta ta ɗauka,da alama dama tasan tana wajen ko kuma wanda ya ajiye ya sanar da ita a bacci. Buɗewa tayi ta karanta abinda yake cikin takardar,ɗan jimm tayi ta jijjiga kai,da alama abinda ke rubuce ya taba zuciyarta,don ga alamun nadama nan sun kwanta akan fuskarta.

Naɗewa tayi ta buɗe gefen drawerta ta saka.
Tashi tayi tashiga bayi,daganan ta fito ta warwatsa wata sallah sama sama a makare,don rana harta fara fitowa.

Tana fita kitchen ta nufa kaman zata tashi sama,da alama yunwa ce ke cinta sosai.

Mai akinsu hannatu tagani ta gama abinci tana wanke kwanukan da tayi amfani dasu,gaishe da ita take da taga shigowarta,amma hankalin ta yana kan kulolin abinci take amsawa,don dama tace mata ta dunga dafa mata abinci da wuri tun kafin ta tashi.
Soyayyar doyace ta miyar ƙwai,plate ta ɗauka ta zuba yanda zai isheta kafin ta fito falon.

Daidai lokacin ahmad ya fito daga cikin ɗakinsa da trolly a hannunsa yana ja,mai matsaikacin girma ne,hakanne ya tabbatar da alamar zai daɗe a tafiyar kenan.

Agogon hannunsa yake gyarawa ya ɗago idonsa suka haɗa ido,kayan jikinta ya ƙarewa kallo half vase ce sai gajeren wando,ga ciki yafito babu dai tsari ta zauna a falo da kayan,saidai wannan abune daya zama abun kullum kaman cin abinci,dan haka yaja bakinsa ya tsuke bai ce komai ba.

Har yazo fita daga cikin falon sai kuma ya ɗan tsaya tareda juyowa ya kalleta a karo na biyu.
"Am zanyi tafiya,i think kuma zan kai two month kafin na dawo,akwai new side ɗina a dakeyi a cikin estate ɗinnan,an kusa kamallawa in angama zaki iya komawa naki sashen kafin a saka amarya, akwai abinda kike buƙata?"

"Uhmm funitures kuma fah da sauran home decors banji anyimin magana akai ba"

"No nariga na gama da wannan shima,sashe uku a ciki idan kin zabi ɗaya daga cikin biyun kuyi magana da managern zasu baki samples na interio design nasu ki zaba,ni zan wuce saina dawo,idan kina buƙatar wani abun just contact saleem"

"No bazan buƙaci komai bama,infact inna buƙata zan nemo da kaina,am no loger a cling woman"
Yanayin yanda tayi maganar baiji daɗinsa ba,amma ya basar ya fita.

Itama ko a jikinta ta juya tacigaba da cikin abincinta.
Saleem ne yatafi kaishi airport bayan yayi sallama da mutanen gidan,hajiya ummee nata jefa masa maganar aurensa da Safeenah,amma sai ya basar bai kula maganar ba. A hanya ma na zuwa filin jirgin kowa shuru yayi a motar babu mai cewa komai,danshi uban gayyar waya yake dannawa kuma duk hankalinsa kacokam ya tattara kan wayar,saidai akace sanin hali yafi sanin kama,shikansa Saleem yasan hankalinsa ba akan wayar yake ba don kada ya jashi da magana ne yayi hakan,shiyasa bai kulashi ba har suka isa.

Suna zuwa direct wajenda zai comfirming katinsa ya nufah na VIP,yanayi kuwa yaja jakarsa zai wuce,Saleem ne ya riƙe jakar tareda cewa.

"Haba my man ba magana ne ballantana bankwana?"
"Sorry saleem i have alot in my head,yanzu dai saikun ganni kawai"

"Ohh babu ma rana lallai mutuminnan,kace ƙaurace mana kawai kayi bawai maganar business kaɗai ba koh.

Okay shikenan saika dawo Allah ya tsare,inda rabon za'a ɗakko mana ƴar can to"

Ahmad yana shirin shigewa yayi masa maganar yasan yajishi amma bai tanka ba har ya wuce.
Bai jima da shigaba jirginsu ya ɗaga Ahmad yace ga garinku,na bulaguro bana mutuwa ba.

Saida saleem ya gama kallon ƙulewar jirgin cikin gajimare kafin ya numfasa tareda sauƙe ajiyar zuciya.
"To ko dai Amjad dagaske yake ne kai akwai wani babban al'amari dangane da gidansa,wanda Allah ya bayyanawa gashi ka ɗai. Domin ba ƙaramin abu bane zai saka ya sauya lokaci guda cikin abinda bai gaza watanni shida ba,kuma har abin ya gagareshi har yayi silar barinsa mahaifarsa,shida bayason zaman wasu kasashen bayan ƙasarsa yau shine mai faɗin dawowarsa a wata biyun ma ƙila wa ƙala ne?"

Dafa goshinsa yayi kaman wanda ya tuno wani abu daya sakashi nadama.

'"Ohh god gaskiya banzama aboki na musamman ba,a ɗan wannan lokacin komai ya faɗamin musa shi nake ko kuma na ƙarya tashi,har saida abin yakai ga haka,in ba bashida lafiyane yasa yake kamata yayi na dage wajen taimakawa a nema masaagani,bawai na barshi har abin yafi ƙarfinsa yasakashi guduwa ba"

Shikaɗai yake sambatun a cikin motarsa bayan ya shiga ya niyyar komawa gida amma kuma ya gagara tada motar ballantana ya tafi. Jikinsa ya sanyaye kana daga baya yabar wajen.

Bayan ta gama cin abincin tv ta kunna,ta daɗe tana zagayawa cikin tashoshin dake cikin television ɗin,da alama bata,samu abin gani wanda ranta ke so ba,dan haka ta kashe tvn tareda nufar ɗakinta.Bata daɗe ba ta fito da alama kayan jikinta da sauya.

Riga da wandone a jikinta kaman ɗinkin pakistan marar nauyi,sai ƙaramin gyale shima kalar Navy blue irin kayan,key ɗin motarta ne a hannunta,shigar bayyi kama da tafiyar nisa zatayi ba,wataƙila cikin estate ɗin zata zaga.

Hakanne kuwa ya faru domin hanyar sabon sashen da ake gina musu ta nufa tana tuƙi cikin nutsuwa sannu a hankali,a ɗaya bangaren kuma hankalinta yana kan abubuwan dake gefen titin na furanni da bishiyoyi.

A bakin gidan ta faka motarta tareda fitowa ta nufi gidan.

Kaman yanda Ahmad ya faɗa haka tagani,part uku ne a jere,wanda yake tsakiya amma baikai sauran girma ba,sannan kuma ya haɗu da kowanne a ciki ta corridor,kana gani kasan anyishi ne domin mutum mai mata biyu.

Ƙaremusu kallo tayi kafin saukar da idonta kan wani engineer ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen.
"Ina babban ku yake?"

"Ehh ranki ya daɗe suna sama wajen ɗaura roofing"
"Okay je kace inason magana dashi"

Amsawa yayi da to tareda barin wajen ya nufi inda ma'aikata ke aiki a sama.

Bai jima sai ga wasu maza sun taho su biyu. Managernne da kuma Saleem suke tahowa suna magana,da alama maganar bazata wuce akan ginin ba.

Domin gurin ba ƙaramin filine dashi ba,bayan waɗancan part ukun tsaf za'a iya saka wasu ukun a harabar wajen.

"Lahh ashe madam ce ke ƙiran barkanki da warhaka."

Managern ya faɗa cikin girmamawa,amsawa tayi sannan suka gaisa da Ahmad shima.

"Amjad yayi min magana kancewar nazo na zabi wanne part nakeso saboda asan wannan irin decor za'ayi,to a yanayin dana duba wancan na ƙarshen nakeso saboda banason hayaniya"

"Ehh to amma madam amarya sunzo da ƙawayenta jiya itama shine wanda ta nuna tanaso,don har anfara saka wasu abubuwa ma data zaba tanaso"

"To a cire su"

Dukka kallonta suke da mamakin furucinta,ko kaɗan hakan bai dameta ba ta ɗora da cewar.
"Waye ya faɗamata cewar sai ta ɗauki part ɗin da takeso kafin ni na ɗauka,itace gaba dani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login