Showing 12001 words to 15000 words out of 24149 words
a hankali kafin tayi masa murmushi.
Kallon ƙyama haɗe da tsana yabita dashi kafin ya tabe baki,wato flavourn sheeshar ta haɗashi maye kenan,mai yake damun wannan matar ne,shin ko cikin jikinta bata gani,bata tunanin irin illar da zayyi mata itada abinda yake cikinta. Kodayake in suka margaya ma su suka sani.
Saurin Istigfari yayi a zuciyarsa,ganin yana zatawa jariran da basuji ba basu gani ba mutuwa a sanadiyyar uwarsu.
"Tsakanin jiya da yau ina kika je?"
Kallonsa take kaman mai son gane abinda ya faɗa,saida ya maimaita cikin ƙufula kafin ta nuna ƙirjinta tana rinshe ido.
"Ni......uhmm.......ina kuwa naje banda waje.......sai kuma jeji cikin can duhuwa ..........duhuwa fah hhhhhhhj.....zakaje da dodo a wajen zai cinyeka"
Maida hankali yayi a tambayar tata,musamman ma dayaji tace cikin jeji.
"Me kika je yi a jejin,meyasa kika kasheshi"
"Ohhh that guy yes i stab him And so if i killed him, it just a stab did he die?"
"Menene wanne mutum kika soka kika kashe,kinsan sunansa faɗamin"
"Yeah i stab him but........"
Faɗawa tayi da bayanta kan gadon bacci ya ɗauketa.
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun,kenan da gaskene duk shedu sun nuna itace ta farmakeshi data gane yana bibiyarta,koda shaidun sun nuna haka nasan ko a gidanmu babu wanda zai yarda Surayyah zata iya farmakar Ƙwaro ma ballantana mutum,musamman ma hajiya mama. To inaga kuma gidansu ita.
Taya zan tunkari iyayenta nace musu gashi gashi yanda Surayyah takoma,taya ma zasu yarda dani. Haka kenan zanci gaba da zama da ita ina fama da baƙinciki. Taya zan hukuntata da abinda tayi,dolene nayi wani abu akai"
Maganganu yake tayi na sambatu,wasu ma baisan mai yake cewa ba,a ranar bacci ko kaɗan baiga ahmad ba,da alama shirin kwana zayyi yana neman mafita a wajen mai duka da kuma ƙwaƙwalwarsa.
*** ***
Talatainin darene,mutum baya iya ganin komai sai iya tsananin duhuwa da kowanne saƙo,sai kuma ƙarar ƙwari da motsin karashiyoyi. Wannan shine zai tabbatarwa mutum a cikin jeji yake ko kuma cikin dokar daji.
A wannan halin ta farka daga baccin daya ɗauketa mai kama da suma,wanda tayishi tun a yammacin jiya sakamakon gudun famfalakin data sha.
Ajiyar zuciya tasake ta waiga damanta da hagunta,sannan da kuma waigawa gaba da bayanta,wai ko zataga wani abu mai kamada haske na alamar mutum,amma shuru babu komai.
Yunƙurawa tayi ta tashi tareda saka hannunta tana kaɗe lakar da take manne a jikin rigarta ta wajen mazaunai. Da alama inda ta faɗin jiya cikin laka ne na ƙasa. Batadamu da halinda suturar dake jikinta take cikiba ko ita kanta tafara saka ƙafafunta tana tafiya.
Jefasu take ƙafa bayan ƙafa batareda tasan inda suke sauƙa ba,kawai tabawa Allah a lokacin zabi akan yakaita duk inda zanen ƙaddararta ya sauƙa.
Tayi tafiyar wasu sa'o'ida daƙiƙu kafin tasamu gindin wata bishiya ta zauna.
Wani waje take kallo daga cikin sararin samaniya wanda yayi haske fiyeda sauran wajajen dasuke saman. Da alama alfijir ne yake shirin ketowa.
A daidai lokacin kuma taji muryar wani bil'adama daga can nesa na yanki a duhuwar yana ƙiran sallah,duk da cewar kaɗan kaɗan sautin muryar yake tashi,amma kasancewar darene bai hanata jiyo muryar tasaba.
Ajiyar zuciya tasake tareda godiya ga ubangijinta,koba komai wani yanki na zuciyarta yasaka yaƙinin samun wata dama a gaba na rayuwarta.
Yunƙurawa tasake yi a karo nabiyu tafara nufar wajen da sautin yake fitowa farinciki fal zuciyarta.
Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 11_⚫
Yana gama ƙiran sallar ya sako ƙafa daga cikin masallacin wanda akayishi da ginin ƙasa da kuma rufin zana. Saurin komawa yayi da baya tareda yin zaman ƴan bori,Addu'o'i yafara zayyanowa duk wanda yazo bakinsa,jikinsa kuwa ya dauki rawa kar kar.
"Innahu sulaimanu wa inna huhuhuhu......"
Sororo ta tsaya tana kallonsa,sai kuma ta kalli jikinta wanda hasken fitilar hannunsa wacce tafaɗi ta haskata,shi ya bata damar ganin jikinnata,sai a sannan ta kula yayi zaton ita fatalwace shiyasa yayi wannan razanar.
Bataga laifinsa ba,don Itama kanta da ita tayi gamo da irinnata kuma a irin wannan lokacin sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen gudu. Ƙarisawa tayi inda yake a hankali gudun kada ta razanashi irinna na ɗazun. Sallama tayi masa cikin ƙaramar muryarta kana ta ɗora dayin magana ganin bai amsa mata ba,amma kuma ya ɗan nutsu daya gane ita ɗin bil'adama ce.
"Baba kayi haƙuri dama wani taimako zakayi min,sannan kuma zanyi maka wata ƴar tambaya."
"To to ina jinki,amma kafin nan mai kike yi a wannan lokacin a wajennan kuma cikin yanayi haka marar kyan gani"
"Abubuwa dayawane suka faru wanda wasu ban tuna ba ballantana na iya faɗin mai yafaru,tambayar da zan maka shine nan ina ne? Sannan ko zaka taimakamin da masauƙi da kuma abinda zanci ? Yunwa nakeji sosai"
"Nan Garin Samurai ne,sannan abinci kam kinsan yanayi na mutum ƙauye,akwai dai tuwo wanda akayi jiya,na safe kuma saida hantsi tukunna za'a ɗumama shi. Idan zaki iya cinsa da sanyi sai muje na baki,ko kuma nasaka hansai ta ɗumama miki idan ta hura wutar kokon safenta.
"Amma yarinya daga ina kike kuma ya sunanki?"
Shuru tayi kaman mai cutar tabin hankali daga can kuma saita girgiza masa kai tana share hawaye.
"Ban tunaba malam,kawai abinda na tuna shine wani mutum ya since sarƙa a hannuna sai yace na fita nayi ta gudu shima yana zuwa,nayi abinda yace nayi ta gudu,daga nan bansake ganin komai ba sai tashi nayi naganni a cikin Jeji ko ina duhu,muryar ƙiran sallar ka naji saina biyo na taho. Bansan mai yafaru dani ba,amma a jikina nakejin kaman an cutar dani,an zalunceni an ɗaureni a wani waje sai kuma wani mutum ya ceceni"
Jijjiga kai mutumin yayi cikeda jimamin maganar ta,tabbas kaman yanda ta faɗa duk wanda suka kamata sun cutar da ita,domin ga alama nan jikinta da yanayinta ya nuna.
"Ikon Allah to Allah ya shiga tsakaninmu na macuta,zo muje gidan"
Amsawa Tayi da to tareda bin bayansa,tafiya suka ɗan taka babu mai cewa komai har suka zo gidan. Tura kyauren gidan yayi suka shiga,yana haskawa da wata ƴar fitilarsa wacce tafi babu,alamun batiran cikinta sunyi laushi.
Awaki ne a kwance manya manya a zauren gidan,saika tsallakasu kafin ka wuce,gashi anyi ruwa zauren banda zarnin fitsarinsu babu abinda yakeyi.
"Tofah tofah hmmmm mata dai mata dai,zafin neman su ba kasafai yake kawo samu ba,komai sunayi inka tabasu suce basuda kuɗi. Yanzu duk wannan kiwon ina zata kaisu,tarage taƙi inka matsa tace saida su zatayi tai kayan ɗaki na auren ƴaya. Banda jawomin magana a mutane da kai ƙara gun maigari in sun shiga gonakin mutane babu abinda sukeyi"
Ita dai tana jinsa yanata sababi a haka suka tsallakasu suka shiga cikin gidan.
Babu kowa a tsakar gidan sai wata mata tana tace ruwa a cikin wata balangada sallamar da yayi ne yasakata ɗagowa ta haskashi.
"Ahh malam yana ganka kuma tun yanxu anyi sallar kenan? Hala.......?"
Maƙale sauran maganar tayi da hasken fitilarta ya sauƙa kan fuskar wacce take tareda shi"
"Malam......wannan kuma wacece?"
"Ahh daɗina dake hansai gajen rashin haƙuri,ki bari mana nagama yimiki bayani tukunna....yanzunnan bayan na gama ƙiran sallah nayi gamo da ita,da harna tsorita,saida tacemin ita mutumce kafin na tsaya na saurareta,neman taimako takeyi wai yunwa takeji shine......."
"Hehehe hhhhhh heeee malam kenan,yaukuma ta wannan labarin ƙanzon kuregen kabiyo,ana cemin an ganka kana zuwa hira gidan malam audu,dan kaji nayi kunnen uwar shegu da maganar bai isheka ba sai ka ɗauko wannan mata jawur da ita ga ciki ɗaram ka kawomin koh"
Taƙarisa maganar tana haske cikin matar.
Bayan ta faɗi hakan daga malam ɗin har matar kallon cikin sukayi wanda yafito har ya ɗaga riga. Kowanne fuskarsa ya nuna alamun sannan ma yasan da zaman cikin.
Jijjiga kai tafara tana kallon malam ɗin,alamun ta tareshi akan koda zai tambayeta zancen cikin batasan dashi ba.
"Girgiza kan me kikeyi na munafurci,ko shine yayi miki kai,wanda yafara shirin auren ƴar yarinya ta cikinsa kam menene kuma bazayyi ba"
Zaro ido sukayi a tare suna kallonta don sunyi mamakin furucinnata sosai.
"Ahah bashine yayimin ba,hasalima bansan yana jikina ba saida kika faɗa,dan Allah yunwa nakeji ku taimaka min da abinci,niba budurwar mijinki bace kawai....."
"Ke dallah rufemin baki karuwar banza karuwar wofi,wlh ko kifice kibarmin gida ko kuma na tumurmusaki yanzunnan"
"Hansai hansai ke kuwa wacce iriyar matace wacce batasan daidai ba,yanzu daga kawo yarinya domin ki taimaka mata da abinda yafi ƙarfinki saiki nemi yimana ƙazafi nida ita,kuma ma abinnaki yawuce kan kowa saini hansai"
"Kaiɗin waye to,bazaka iya bane,ai tunda ka fara neman auren yarinya kam mutuncinka ya zube murus a ido na malam"
"Hmmm to shikenan kuma duk wannan borin dakike aure kuma ba fashi yanzu ma nafara shiri"
"Oho kuma can maka,tujara ce nima yanzu na shimfiɗa tabarmar zama na fara ta,shege ka fasa nida kai"
Juyawa yayi da sauri yabi bayan matar wacce har ta fara tafiya domin barin gidan,hannunta dukka yana kan cikinnata,hankalin ta kuma ya tafi wata duniyar ta tunani.
"Sannu yarinya yanzu kuma ina zaki tafi,bai kamata a barki ke kaɗai a wannan halin ba"
"Ahah kabarshi malam yunƙurin taimakon dakayimin ma nagode,zan jira idan mutane suka fito gari ya waye zanyi bara"
Shuru yayi yana nazarin maganar ta can kuma sai yace.
"Ahah kinga zo muje gidan yayata Addah anan baya take,gidan yanada ɗakuna da yawa duk ta bada haya,Ranar danaje takecemin shikaɗai ya rage bakowa a cikinsa idan zan saka amfanin gona. Muje idan na mata bayani saiki zauna wajen kafin ki gane asalinki,kinga ko wani abunma saiki ɗan dungayi ki riƙe kanki. Yafi dai zama a titin kina bara"
Bayaninnnasa ya gamsar da ita,dan haka babu musu cikin jin daɗi tabi bayansa zuwa gidan addar tasa.
Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 12_⚫
Kaman yanda ya faɗa basu daɗe suna takawa ba sai gasu a gidan,sallama yayi tareda shiga gidan itama tabi bayansa. Bashida girma sosai amma baza'a ƙirashi da karami ba.
Ana shigowa tsakar gidane sai kuma ɗakuna sun zakagayeshi kowanne da shirgi a ƙofar ɗakin alamar da mutanen da suke amfani dashi.
Gidan shuru kamar babu kowa,sai kukan wani yaro dayake fitowa a ɗaya daga cikin ɗakunan gida,da kuma wata tukunya babba akan murhu tana turiri,alamar mai jaurar safece ta ɗora.
A karshen tsaƙar gidan wani ɗan lungune na hanyar wucewa,nan suka shiga inda wani ɗaki yake da dan farfajiyarsa da kuma banɗaki a gefe. Dukka gidajen gidan na ƙasane anyi masa shafen suminti,amma wani wajen flastar ta fara fita,alamun ginin yaji ruwan damina.
Ɗaga murya yayi yaƙara sallama,daga ciki wata ta amsa musu tareda faɗin tana zuwa.
Dattijuwa ce amma ba wai tayi tsufa tukuf ba,domin kana ganinta kasan da alamun ƙarfi tattare da ita.
"Lale maraba sannu,ahhh Baban Isa kaine tare kuma da baƙuwa,sannun ku da zuwa barina ɗauko tabarma"
Komawa ciki tayi ta dawo da tabarmar karauno ta shimfiɗa ɗaya ta gefen sa,ɗayar kuma ta shimfiɗa ta gefe tareda nuna mata itama ta zauna.
Bayan sun zauna gaisheda ita yayi cikin ladabi kafin ya ɗora dayin magana.
"Wato Abinda yakawo da sassafennan wata magana ce"
"To inajinka maike tafeda kai?"
Kwashe yanda sukayi da baiwar Allahn ɗazu Asuba yayi ya faɗa mata,bata katseshi ba har saida ya kai aya tukunna.
"To naji zancenka ɗaki dai gashi can amma jiya wasu ƴan ci rani shida matarsa sunzo sun dubashi,basu bada kuɗi badai bamu ƙarƙare magana ba.Domin tun ranar danaga baka maida hankali ba dana baka kasaka amfani gona na sakashi kasuwa. Amma tunda dai harkar taimako ne kayi niyya nima bazan ƙi tayaka ba mu samu ladan tare,shi mutum duk inda yake maganine. Dabba ma kana iya taimakonta tayi maka rana balle kuma Mutum.
Ga nan ɗaki sai taje ta share ta zauna,akwai sana'o'i da dama a garinnan shiyasa mukeda baƙi sosai,ta zabi daidai ƙarfinta ta dungayi tana yiwa kanta ƴan laluran da baza'a rasaba. Na yafe mata kuɗin hayar shekarar nan,amma wata shekarar idan tasamu abinda zata dogara da kanta to saita biya kuɗin hayar ta in Allah ya kaimu da rai in kuma ta tuna ita wacece ta tafi gurin danginta da mijinta to haka ake fata. In ma batada miji to wannan ita ya shafa taje ta ƙarita,amma dai kyakykyawan zato ake fata"
"Nagode addah,dama nasan idan har na zi wajenki ke bazaki koreta ba kamar Hansatu,ke kuma saikiyi mata godiya da taimakon da tayi miki,sannan ki zauna lafiya da mutan gidan ki kama kanki,karki bari wata matsala ta kunno ta sanadiyyarki"
"Nagode nagode inna Allah yasaka miki da alkhairi,kaman yanda kika taimakeni Allah ya hanani baki kunya,namiki alƙwarin inshaallah babu wata matsala dazata faru,zan iya ƙoƙarina naga in wata shekarar Allah ya kaimu da rai na biya kuɗin. Saidai kafin sannan ina roƙonki da ki nunamin yanayin zaman garin da kuma menene yafi dacewa wanda zan fara dashi?"
"Wannan ba wata matsala bace inshaallah,munada babban rafi daya kewayemu ta yamma maso kudu,anan ana noman Samurai sosai,shiyasa mutane daga cikin garuruwansu suke zuwa suyi noma. Yanzu lokacin damina ce nan gaba kaɗan za'a fara rainon iri,yanzu kuma lokacin yin kwanduna ne,bari inkikayi wanka kikaci abinci kika huta zan kaiki wajen wata aminiyata tana koyar da yin kwandon saiki koya ki dingayi ki tara. In lokacin nemansa yayi saiki siyar kiyi wasu buƙatun,sannan in kina zaune keda kanki zaki gane wasu dabarun sana'ar kifara inshaallah,garinnnan ƙaramine amma yanada albarkar samun kuɗi sosai idan mutum ya tashi ya nema."
"To addah ni zan wuce zan barki da ita,idan da wani abun daya kamata na sani saiki sanar min"
"To shikenan ka gaida su isa da wannan birkitacciyar matartaka,da bata iya komai ba sai kishin tsiya"
Ta ƙarisa maganar tana tabe baki ta buge gefen zaninta data tashi tana gyarawa.
"Ɗan murmushi yayi ya jijjiga kai tareda yimata sallama"
Da alamun Addan tanada kirki amma kuma sam babu shuru shuru da kuma haƙuri a lamarin ta,wayayyiyar matace maiyin komai kai tsaye.
"Salamu alaikum Addah barka da safiya naji motsinki ai nace to kin tashi"
"Ehyi na tashi ya akayi?"
"Ahhh baƙuwa kikayi ne da safennan itakuma daga ina take hala ba ƴar garinnan bace,naga ban saida Fuskarta ba"
"Ahh Zulai uwar surutu da gulma dama kowa kika sani a garinnnan da saikin santa?"
"Hhhhh ahah ba haka bane Addah amma kinsan yanda nasan garin Samurai ciki da bai kaman ɗakin uwata zayyi wuya bansan mutanen cikinta ba. Duk da ni baƴar garin bace amma daɗewar danayi da kuma sanin danayiwa garin ba ɗan kaɗan bane"
"To naji, ina ƙoƙon zuba koko kikazo karba da kuma kuɗin jiya? To gashi. Wannan kuma baƙuwace itama zuwanta garin kenan a ɗakin gefen Ramma zata zauna. In kin gama kokon ma kisaka Su umaru don Allah su share minshi"
"To shikenan ayyah ashe baƙuwa mukayi kuma abokiyar zama,sannunki da zuwa,ya sunan ki kuma,mijinnki yana wajene naga hadda yaron ciki gashinan yafara girma. Hala zamusha suna nan kusa kenan"
Duk wannan tambayoyin baiwar allahn take jerawa wacce ta tsaya kurum tana kallonta batareda ta motsa bakinta ba ballantana ta bata amsar ko guda ɗaya ne.
"Kuma gata kyakkyawa kaman jinin buzaye ga........."
"Haba haba Zulai wannan wanne irin tambayane na ya uwaka ta haifeka,don Allah kije ga ruwan kokonki kada ya tafaso ya zube,mutum yana girma amma yana cigaba dacin ƙasa haba"
Ganin Addah ta hauta da faɗane yasa ta amshi kwanon shan kokon ta tafi,amma a idonta cike take da zumuɗin son jin amsar tambayoyinnata.
"Wai hmmm ai kinga takanki aikine yakeso ya ganki,wanann gidan da kike gani da matan cikinsa saikinyi a hankali."
Ɗaga kai kawai tayi batareda tace komai ba.
"Sannan wannan tambayoyin datayimiki dole ki tanadi amsa daidai dasu. Kince bakisan sunanki ba,idan sun tambayeki kice sunanki Salaha sunan ƴata ne data rasu,inason sunan sosai dafatan zaki karbeshi kafin ki tuna naki. Sannan in sunce ina mijinki kice ya tafi rani sai ya barki anan."
"To inshaallah zan kiyaye,sunan yayi sosai nagode, Allah yasaka da alkhairi"
"Ameen barina yi ɗumame kafin ta kawo kokon idan ta zuba saiki sha"
Daga haka Addah da salaha suka ɗan fara taba hira sama sama,don ma addan tana yi a takaice don taga ita batada yawan surutu.
Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 13_⚫
Buɗe idonta tayi kana ta sake lumshesu,wani irin nauyi da sukayi mata,a haka tayi ta ƙoƙari jikinta babu ƙarfi har ta samu damar tashi zaune a tsakiyar gadon.
Hango kanta tayi a madubin jikin wardrop yayi bitsi bitsi dashi kaman mahaukaciya sabon kamu. Idon kuma ya ɗan kumbura na alamun nauyayyen baccin daya dauketa.
Hannunta tasaka tareda bugun goshinta sannan taja dogon numfashi.
"Ohhh shitt nasan wannan aikin zeezah ne,na hanata sakamin Alcohol vipe amma bataji,i don't like this drowness"
Wayarta ce tayi ƙara tana cikin juye juyen
Dubata takeyi harta samota a ƙarshin gado,tana buɗewa zaro ido tayi ganin missed call sunfi goma na wata nurse ɗaya daga cikin mutanenta.
Message ɗin data turomata ganin bata ɗaga wayar ba tashiga karantawa.
"Hi madam na ƙiraki baki ɗaga ba,ɗazu Amjad yazo da wata leda ɗaukeda safar hannu a ciki da kuma wata riga dukka da jini a jikinsu,yabada anyi gwajin DNA dana wani majinyaci da suka kawo Rai a hannun Allah,kuma yayi matching jininsa ne. Likitan yace in yasan wanda ya aikata hakan yakamata a sanar da ƴan sanda,amma sai yace wai bayason kowa yasan zancen. Daya fito daga asibitin ya tada mota,nabi bayansa domin naga ina zayyi,saikuma naga ya nufo nan gidan inda kike. I think he figure something madam"
Wani abu ƙwaƙwalwarta tariyo mata,ta sauri ta sauƙo daga kan gadon tana jujjuya ido alamar mai tunani.
"Ahmad yashigo ɗakinnan jiya da daddare,kuma tabbas nayi magana dashi. Ohh god nasan daƙyar in ban faɗamasa abinda yafaru ba jiya,babbar tantama ta mutuminnan nasane,sannan munyi tracking ɗinsa bamu ganshi ba,da alamun sun samoshi kenan. Shikenan idan na faɗamasa to asirina in bai tonu bama yana dabb da shirin tonuwa........kai yama tonu zama bai kamani ba dole naje wajen zeezah,aiki baƙi ba ja ba ya ballo mana"
Tunda ya shigo ɗakin take binsa da kallo ko gaisuwar da yayi mata bata amsa ba,kwata kwata hankalinta ya shagala da kallon yanayinsa da kuma son gano mai yake damunsa.
Shima tsarguwa yayi da yanda ta kafeshi da ido,dan haka ya ɗago kansa dayake sunkuye suka haɗa ido. Kawar da nasa yayi tareda ƙwaƙwulo wani murmushin dole yayi.
"Ummee menene kiketa kallona haka,ƙalau fah nake babu abinda yake damuna"
"Babu abinda yake damunnaka ka kwana bakayi bacci ba,kowa ya kalli idonka ai yasan baka samu hutun da kowanne ɗan adam akeso ya samuba idan dare yayi"
"Ehh bansamu nayi bacci ba na tsaya duba wani aikine"
"Hmmmm shikenan Allah ya kyauta,koma menene ba laifinka bane laifinmu ne ya kamata a duba lamarin. Yanzu dai ba wannan ba,tunda ka gama karyawar maganace Babanku yabani na baka. Jiya Uwar taku Hunaiza taje ta Sameshi a falo sun tattauna,tace tana