Showing 21001 words to 24000 words out of 24149 words
ko kuma nice gaba da ita,ko kuma shi mai ginin ne yace mata ta fara ɗauka. Idan babu ɗaya daga ciki to a tattara mata abubuwan da tace tanaso a kaimata wancan. (Tana nuna part ɗin dayake farko) Zan turo maka abubuwan,danakeso a saka sai a fara aikin"
Sororo suke kallonta tana maganar harta gama tabar wajen.
Juyowa managern yayi ya kalli saleem.
"To yallabai kaji abinda madam tace,ya zamuyi kenan?"
"Kuyi yanda tace ɗin,domin daga ganin yanayinta babu alamar tanƙwasawa, sannan kaman yanda ta faɗa itace babba ita yakamata tafara zaba daman"
"Toshikenan yallabai za'ayi hakam,saidai itama amaryar fah da alama ba tayar baya bace"
"Hmmm aini sai yanzu na fara
hango ƙurar da Ahmad ya gudu ya bari ba ƙarama bace,kawai dai Allah ya kyauta."
Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 19_⚫
Bayan ta fita har zata wuce sashensu sai kuma zancen neman dasu hajiya ummee sukeyi mata ya dawo kanta. Ƴar ƙaramar tsuka taja ganin ƙwaƙwalwarta tayi tasirin tursasa zuciyarta ta amince da zuwan,amma kuma tsukar da wani gutun murmushi ya ƙare,da alamar akwai abunda zuciyarta ta kissima mata zata shuka. A bakin harabar gidan ta faka motarta kana ta fito ta nufi ƙofar da zata sada ta da shiga sashen hajiya ummee.
Bakinta ɗauke da sallama ta shiga cikin falon,hajiya ummee na zaune da wata mata sai kuma hajiya mama, sunyi nisa cikin hirar tasu,muryar Surayyah ne ya dakatar su dukka suka ɗaga ido suna kallonta.
Kanta a sunkuye kamar matar arziki tasamu waje ta zauna,gaishesu tayi a takaice kafin ta ɗora da cewar.
"Kuyi haƙuri hajiya nimrah tace kuna nemana to a lokacin kuma anƙirani ummah na batada lafiya shiyasa natafi".
Hajiya mama ce ta fara magana.
"Allah sarki ai kinkuwa kyauta gwara da kikaje ganota,muma da mun sani ai da mun dubota da jikin."
"Ahhh da sauƙi sosai nima danaje ɗin har an sallamota kasancewar banajin daɗi bansamu zuwa da wuri"
"Ahhh bakomai dama akwatine na faɗar kishiya da ake cewa a al'ada za'a haɗa,nakeso kizo muji mai da me kikeso,kar ayimiki abinda bakyaso,sannan kuma koba komai yakamata kizo ayi komai dake,duk da babu daɗi amma shi girma haka yake idan yakamaka dole sai kayi haƙuri. Ya jikinnaki to da sauƙi ko?"
"Ehhh ummee da sauƙi sosai,yanzu ma daga sashen dazamu koma nake naje nagano,abbansu farha yace nagani na zabi wanda nakeso kafin itama ƙanwartawa ta zaba"
"Allah sarki kinkuwa kyauta,sannu fah kinji"
Hajiya mama tayi maganar cikin tausayawa.
Cigaba Surayyah tayi da faɗin.
"Batun kaya kuma hajiya karku damu wlh ku barsu,sutura kam ai saidai ka bawa wani ma,al'ada ne amma idan ba buƙatar hakan gwara ayiwa masu buƙata,kawai ɗinki na fitar bikin ma sun isa."
"Ahah kar ayi haka ƴar nan,haƙƙinki ne ki bari ayimiki yanda akewa kowa,abun ai sai yayi yawa idan ba'ayimiki ba,ballantana kuma da halin yin"
"Ahah hajiya aini nace a barshi saboda bana buƙata,babu komai wlh a barshi,ita kuma Allah ya kawota ya haɗa kanmu. Bari intafi kar rana tayi na barku lafiya"
Yunƙurawa tayi ta tashi fuskarta dauke da murmushi kaman yanda suka santa ta fita a falon.
Tana fita waje bayan ta shiga motarta wata arniyar dariya ta kwashe da ita tareda cewa.
"Kai lallai wannan dattijan hamagawa ne aradu,ki duba fuskarsu yanda suke wani narke duk sungama tsuduma a cikin wannan kafcennawa,ina ma a gefe akwai wani wanda yakemin video dana kalla daga baya. Ai daga ganin yanayinsu nasan komai nayiwa Amjad bazasu yarda idan yafaɗa,hmmm ta ƙaremaka ɗan hamshaƙin mijina,wato kai ka gudu ko,to wlh ta ƙare maka,har ni zaka kujewa saboda ka rainamin hankali hmmm."
"Hmmm kingani koh Ummeen yara,shiyasa fah nake kwabar Nimra inta zomin da wannan surutunnata,gadai yarinya babu wani abu daya sauya a tattare da ita saima ƙarin hankali da tayi. Ni wlh bakijiba duk tausayinta ya kamani,ka ciki daga gani shima ƴan biyunne in kika auna girmansa da watanninsa,sannan kuma gashi ya tsallake ya gudu ya barta,ƴaƴan dazata gani taji daɗi shima ya ɗebesu ya rabata dasu. Sannan uwa uba ga kishiya. Allah ne kaɗai yasan wanne hali take ciki yarinyar nan. Ƴaƴan ta za'a kwasa a maida mata gabanta ta dunga ganinsu,sannan shima yau zamuyi waya ya tattaro yadawo ya kulada matarsa"
"Hakane kaman maman zainab zancenki bazan ƙi ba tunda nima naga yanayinta da idona,kwata kwata batayi yanayi da yanda nimra ta fassara ba da kuma shi maigidannata. Saidai wataƙila yanda kika fada a bayanne cikinnne yasa ta sauya halayya shikuma ya kasa jura,inaga tunda bai daɗe da tafiya ba mu barshi yaɗanyi ko wata ɗaya ne kafin muyi masa maganar dawowar,tayiwu sanadiyyar hakan su dawo suna ɗokin juna. Su farhana kuma inaga cikin bamai son hayaniya bane shiyasa ganin tana nuna musu wata halayya daban yasa yakasa jura ya dawo dasu nan,in hakane inta haihu ai komai zai dawo yanda yake. Tunda kinga itama bata nemesu ba,haka suma tunda suka dawo basa nemanta"
Da haka hajiya ummee tashawo kan hajiya mama ta lafa da zancen ɗaukar mataki akan lamarin Ahmad da Surayyah.
***
A zaune take ta dage sai aikin zarga igiyoyi take na kaba,a dole ita hakan gwando takeyi wanda ake amfani dashi wajen saka kayan gwari.
"Kai gaskiya salaha kin bani mamaki,ɗazu da safe fa kika dasa amma har kin kusa rabi,a haka kaman bazaki iya ba amma gashi har kinyi biyu yaune ma kuma satinki da iyawa"
Wata budurwa ce tayi maganar itama tana aikin saƙa kwandon.
Dan murmushi salahan tayi kafin tace.
"Zakiyya kenan idan ban dage ba mai zanyi,kada ki manta wannan shine kaɗai hanyar dazanbi wajen samun abinda zanci,bazaiyiwu na zauna bana komai Adda tana cida ni ba,dole watarana zata gaji,tunda ko ɗan daka haifa a cikinka zakaso ace yana neman na kansa domin dogaro dakai"
"Ehh hakane kam kinada gaskiya,to Allah yasaka mana albarka a ciki ya bunƙasa mana"
"Ameen ya Allah,ni inaga ma lokacin tafiyata gida yayi,zanyiwa Babar Audu magana (wacce suke koyon sana'ar a wajenta) zan tafi dashi gida naje inayi kawai,idan nagama wannan zan siyar dashi nasiya kayan yi na gaba,ke gwara ke gidanku babu nisa nikuma sai nayi tafiya mai ƴar tazara kafin nake isowa,amma inna koma gida inayi hakan zaifimin sauƙi"
"Ehh hakane kam,kuma kina da saurin ɗauke abu tunda kin koya gwara kinayi a gida,amma wlh zanyi kewarki salaha,ke macece mai daɗin zama ga hankali da sanin mutuncin mutum,mijinki yaji daɗinsa"
Lokacin da zakiyya ta ambaci miji gaban salaha ne ya faɗi,tun ranar da tazo aka gama cale cale tasamu wajen da zata tsugunna sannan ga wannan zigilar koyon sana'ar gabaɗaya saita manta da zancen wani abu waishi aure,miji da kuma ciki. Lallai tsugunne bata ƙare mata ba,to ita da batasan ma ko wacece itaba taya zata san waye uban cikin jikinta,shegene ko ɗan sunna wannan amsar tambayar tata yafi komai ɗaga mata hankali,ita ƴar inace,suwaye iyayenta,shin suna can suna nemanta,waye maƙiyinta da yayi mata wannan aika aikar?
A fili ɗan taƙaitaccen murmushi tayiwa zakiyya kafin ta ɗauki hijabinta wanda shikaɗai ne gareta,shiɗinma Adda ce ta bata daga cikin nata da kuma sutura guda biyu,ta wanke ɗaya ta saka ɗaya. A hakamma kullum cikin godiya take ga Allah daya haɗa da mutane nagari masu kirki a lokacin da batada kowa koda kuwa kanta ne batadashi a lokacin tunda bata tuna komai sai abinda takalla a sannan.
Bayan sungama magana da mai saƙar gwandon dayake ƴar uwar adda ce saita amince mata akan taje gida ta dungayi kawai,musamman da ita kanta ta yaba da basirar salahan.
Ɗoroshi tayi aka sauran igiyoyin kuma ta riƙosu a hannu,a haka ta kamo hanyar ko kulada masu ƙaremata kallo batayi ba,hankalin ta gabaɗaya ya tafi duniyar tunani na rayuwar data tsinci kanta.
Kaman a sama taji wani yayi mata magana,
"Ƴan mata jimana bazaki kawo na tayaki ɗauka bane?"
Ɗaga kai tayi ta kalli mai mata maganar,bata san sunansa ba amma taganeshi jiya yaje wajen adda da yamma,wai ɗan ƙanwarta ne wanda ya dawo daga Suleja yawon ci rani.
Kakkauran baƙin saurayine yasha ɗamammiyar t-shirt wacce ta kama ƙirjinsa gamm,wandon jikinsa kuma irinna gayunnan jeans ne amma duk an yayyankashi kaman rake. Kansa kuma irin dadarnnance anyi cibil cibil dashi babu daɗin gani.
Saida ta ƙaremasa kallo daga sama har ƙasa kafin ta jijjiga masa kai a hankali,sannan cikin sanyi na muryarta tareda sunkuyar da kai tace.
"Ahah ka barshi nagode,ai na kusa isa gidama"
"Haba baby kyakykyawa ya ina neman taimaka miki kina maida hannun taimako baya"
Wannan karon bata tankamasa ba illa cigaba da tayi da tafiyarta,wani ne daga gefe yasaka baki a lamarinnnasu ganin bai daddara ba yasake shan gabanta.
"Haba Jazuli Kayi mata magana tace kayi haƙuri,ka sake yimata magana bata tanka mata ba ai sai ka ƙyaleta ko,sannan matar nan baka gani kaman juna biyu gareta,idan matar wani ne fah ka tsaya kana tareta a titi. To wlh kaji da wai mu a nan munada ƙa'ida sannan hisba tana aiki bazamu yarda da wannan tujarar ba ta garuruwan marasa sallah."
"Kai kaji wani zancen banza,to kai da kake wannan maganar kafini saninta ne,kuma wama yace maka matar aurece,cikinda yake jikinta babu maishi na titi ne,itakanta itama ta titince duniya ta shigo. Nikuma da kake zagi rufamata asiri zanyi na aureta,tunda tanada kyau nasan inta haifi ƴa irinta zatayi kyau tazamamin jari"
Maganganun da Jazuli yake gasawa tabbas garwashine dayayiwa zuciyarta zafi,wasu zafafan hawayene suka fara kwararowa daga cikin idanunta zuwa kan kumatunta. Bazata ce gaskiya yake faɗa ba haka kuma batada hujjar ƙaryatashi,babu abinda zatayi daya wuce in bacci ma tayi tashiga duniyar manta halin da take ciki ganin ta haɗu da mutanen kirki,to tayi saurin gaggauta farkawa ta tunkari kalubalen rayuwar dayake shirin tunkararta.
Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 20_⚫
Tazarar tafiyar babu nisa amma gani tayi kaman ta ɗau wasu awanni masu yawa kafin ta isa gidan. Yara tagani sun taru a tsakar gidan,kuma a yanda ta lura hayaniyar tafi yawa a sashen ɗakinta,muryar Zulai tajiyo yana fitowa daga cikin ɗakinnata da sauri ta isa wajen haɗe da leƙawa domin taga mai take yimata a ɗakin.
Tun kafin tayi magana Zulai data ɗaga kai ta kalleta tafara cewa. Murjani nane ya bata kuma ainihin mai tsadar ne wanda Kaka ta Hajiya delu tazo dashi daga makka ta bawa uwata itama tabani,na nemeshi na rasa kuma nasan barawon bazai wuce a gidannan yake ba,shiyasa nace saina caje kowanne ɗaki a gidannan na nemo abuna. Ai daman ganin nafi kowa babbar kadara ta abun wuya,ina ado ina kece raini a babban taro nasan zuciyar wani zata raka ya rabani dashi.
Ta sababin kuma bata daina bankaɗe kayan Salaha ba wanda basu taka kara sun karya ba. Daga wata ƴar tabarma sai wani buhu data saka ƴan kayanta,sai kuma ƴar buta a gefe.
Ƙarisawa tayi cikin kiɗima wajen da Zulai take sai soki burutsu take da kayanta.
"Haba Zulai niban ɗauka miki komai ba,kuma ma idan wani abu kike buƙata ai saiki tambayeni koh"
"In tambayeki? Kenan ma ban yaddda sata kikayi ba idan na tambayeki,to barikiji saina caje ko ina na nemo murjani na"
Kunnen uwar shegu tayi da magiyar da salaha keyi mata tacigaba da bincika gidan. Muryar Adda sukaji daga bakin ƙofar gidan.
"Lafiya mai yake faruwa a ɗakin,ke Zulai mai kuma ya kawoki ɗakinta da tsakar ranar nan kina birkita mata kaya?"
Fitowa Zulai tayi daga ɗakin salaha ta haɗa gumi shirkif tana kallon Addan wacce tasha lullubi na gyale da alama daga anguwa ta dawo.
Sosa goshi Zulai tayi tana ƙikkifta ido alamun bataso addan ta dawo a lokacin ba.
"Ehhh dama Addah murjani nane ya bata,kuma ranar dana saka sainaga tafiya kallonsa,shine danake nema na fara da bincika ɗakinta"
"To yanzu dan kina neman murjani shine saikin haɗa yara da yan anguwa kin birkice mata asirin ɗaki,kaman dama itace ta sacemiki? wato saboda kinga tanada haƙuri da rashin magana ko,su sauran matan gidan ai baki isa yimusu irin wannan tujarar ba"
"Amma dai addah murjani na mai tsada nace miki ya bata,inda adalci ai dole a barni na ɗau matakin nemoshi,kuma sauran ma ai zanyi musu cajen ba iya ita kaɗai ba ko?"
"Ƙarya kikeyi bazaki iya yimusu ba,itan dai zaki iya yiwa tunda ita kika raina. Tukunna ma murjanin da kike magana akai bazai wuce Iliya ne babban ɗanki ya ɗauka ba,domin na ganshi a hanyar shigowata da sabon ludo guda uku shida abokansa sunata wasa dashi,da wanne kuɗi zai siya in ba wani abu ya ɗauka yaje ya siyar ba. Hala kin manta da halin bera irinnasa,duk kun fitini mutane keda iyalanki,ƙanana kukan banza su tashi mutane tun asubar fari,manya kuma sai sace sace kaman gafiyoyi.
"Haba adda daga na nemi abuna na rasa ina nema saiki hau ƴaƴana da zagi kaman dama cike kike dasu. Da ɗinta ma in aikene su ake aika ai amma kuma abu kaɗan zasuyi a sakasu baki"
Ta ƙarisa maganar tana juya ido da mintsila baki kana kuma hannunta na hagun riƙeda kunkuminta tana jijjigashi.
Sakin baki adda tayi tana kallon Zulai wacce ke zubamata rashin kunya da ranar allah,kuma tayi ƴa da ita.
"Ehhh lallai nasan dalilin wannan rashin kunyar taki,saboda kinga mijinki ya biya muku kuɗin ɗakinku ne shine barikiyimin tujara ko,to wlh ki shiga hankalinki kuɗin yanda ya bani su suna nan ban taba ba,yanzu saina bashi kuɗinsa ku tattara kuyi gaba,koma taƙamarki bai wuce idan kun fita aida kuɗi hannunku zaku samu wani gidan ko. To nafiki iya shege,saina ɗau kuɗin na miƙawa sarkin noma nace sauran kuɗin jinginar gonarsa ne daya baku ku noma,ba dama ƙaryar bakuda kuɗi kuka masa ba ya barku sai kaka'a?"
Jin wannan batu da Zulai tayi daga bakin Addah gabaɗaya yasa kwanyarta ta dawo cikon saiti,ta sani sarai idan har mijinta Gadanga yasan cewar itace sanadiyyar rasa hayarsu da kuma kuɗinnan ba iya ƙwallo ba har maidata ƙwallo zayyi.
Zare ido tayi tana susar kai sai kuma ta sauƙar da idonta tareda jefar ƴar guntun tabarmar Salaha wacce ke hannunta.
"To naji shikenan zanje ɗakinnawa na duba,yarona ma nasan bashi ya ɗauka ba,saidai yana wani wajen"
Da kora kunya da hauka ta bar wajen kowa dake wajenma ya watse, Ƙarisawa inda salaha take hawaye suna silalo mata adda tayi,tafata tayi cikin tausaya kafin ta ɗora da cewa.
"Haba salaha shurunki da haƙurinki yayi yawa,a ɗan zamana dake na fahimci haka,bakya tabuka komai na kare kanki koda kuwa wani ya yunkuro zai cutar dake. Ai ba'a haka duniya tazama yanzu saida kare kai,inba haka ba rayuwar saita gagareka kaida jininka,saboda mutane sun zama zuma saida wuta. Meyasa bakyagani batayiwa kowa a gidan ba saike,saboda ta lura dake komai akayi miki bakya tankawa ballantana ɗaukar mataki,sannan duk yanda taso jan ki a jiki ta samu labaran da zata ɗorar bata samu ba,shiyasa ta biyo ta nan."
"Addah babu yanda zanyi,nace mata ban ɗauka ba taƙi yarda"
"To dama da zata yarda baki ɗaukaba zata fara yin hakane,kema dai wlh asara ce. Nasan baya wuce da wannan halayyar taki akaci galaba akanki har kika tsinki rayuwarki a haka. To kuwa idan har kinaso ki kare kanki ki kare abunda ke cikinki wanda shi kaɗai kikeda dole saikin jajirce kin ɗau damarar zama tareda bi da uba kowa. Muje na ajiye abinci kafin na tafi muci,idan rana tayi sanyi zan bawa yaro yasiyo miki kwaɗo ki kulle bakin ƙofar,dama ina zuci zucin hakan sai kuma wannan tujararriyar tayi wannan aikin. Zama da ɗaki babu kwaɗo kuma kana fita ka barshi ai bayyi ba sam.
Da dare yayi anci tuwo shiga ɗaki salaha tayi,domin tai sallahr isha kuma taɗan biya tilawa,adda ta bata aron qur'aninta ganin ta tsinci kanta da iya karantawa,harma dana turanci da hausa. Wannan abun ba ƙaramin daɗi yayi mata ba har hawayen farinciki saida tayi. Tana gama yin sallahr kuwa tajawo qur'anin tana karantawa,suratul mulk take karantawa cikin siririyar murya a hankali,wanda sai kayi dagaske kafin kaji harrufan suna fita akan labbanta.
Yarone ya banko ƙofar langa langar wanda saida yasa salaha razana ta ɗago da sauri,ɗan gidan Zulai ne wanda yakebin Iliya.
"Salaha wai kizo inji wani a waje"
"Wani a waje kuma ni,waye?"
To waye zai nemeni kuma ma da daddarennan,a ranta tayi wannan tambayar kafin yaron yabata amsar tambayar da tayi masa a zahiri.
"Bansanshi ba kawai dai yace dan Allah kizo"
Har ta buɗe qur'anin zata cigaba da karantawa saikuma maganar da sukayi da addah shekaranjiya ta faɗo mata,kan cewar tunda a cikin abinda ta manta na rayuwarta banda ilimin ta,shine ta bata shawara kan ta nemi koyarwa a islamiyya da boko idan har ta samu ko dubu biyar biyar suke bata zata rage wani abun,idan ta dawo kuma sai tana saqar kwandonta a gida ko ɗakinta. Bayan ta amincene Addah tayiwa wani malamin islamiyyar bayansu malam baqeer maganar salahan,kuma yace idan yadawo daga karatu zai biyo suyi magana tunda suna hutu ballantana ta sameshi a makaranta.
To duk a tunaninta wataƙila bazai wuce shi ba,to amma da daddarennan? Share tantamarta tayi ta saka hijabi kana ta nufi ƙofar addan.
A zaune tasameta itada wata baƙuwa ta zomata hira,suna kuwa tayin hirar cacai cacai kamar tsuntsaye.
"Assalamu Alaikum adda dama a wajene wai ana sallama dani inji yaro,shine zanje na dubo ko malam baqeer ne dayace zai zo"
"Ehhh bazai wuce shiɗinba inaga sun tashi a karatun darene ya biyo ganin yanada lokaci,to kije kuyi maganar Allah yabada sa'a"
Ameen ta amsa dashi a taƙaice kafin ta nufi ƙofar gidan cikin nutsuwa.
A cike ƙofar gidan yake da yara sunata wasa,maza suna guje guje mata kuma sai shewar gaɗa ce take tashi.
A can gefe ta hango mutum yana jingine da wani kututturen bishiya,ganin fitowarta ya tashi daga jinginen ya tsaya,hakan yabata alamar shine ke nemanta. Saidai daga inda take tsaye tana hango ƙananan kayane a jikinsa riga da wando. Wanda aka ce ustazine mai ya haɗashi kuma da saka ƙananun ƙaya. Daurewa dai tayi ta isa saboda baka shedar mutum tun bakayi ido huɗu dashi ba.
Da sallama a bakinta da ƙarisa wajen,saidai maimakon sallama ta dawo gareta da mutum mai addini sai kuma wata shakyakykyiyar murya data doki dodon kunnenta.
"Barka dai sarauniyar matan duk duniya,nayi zaton bazaki fitoba,sai kuma gashi ga mamakina kin amsa ƙirana kin zo gareni"
Razana salaha tayi tareda ɗora hannunwanta a ƙirji tana kallonsa da idonta kaman zasu fito waje.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"
Sune kalaman da bakinta yafara maimaita da sauri,ganin hakanne yasa Jazuli matsowa a hankali kusada ita domin ya kwantar mata da hankali. Maimakon hakan ya taimaka saima ƙara ta'azzara abin dayayi,domin ganin ya matso inda take da sauri salaha ta juya ta koma gidan a tsorace. Shima