Showing 9001 words to 12000 words out of 24149 words

Chapter 4 - MUMINA KO AZZALUMA 1 By Sadi-sakhna.txt

18 Oct 2025

466

fuskarka babu alamun kaji daɗin zancena. So tunda wannan hanyar ka zaba shikenan sai mu bita. Yanzu na riga nasan you no longer love me,since you can't accept my blood anymore".

Maganganunnata gabaɗaya sun isheshi,kawai so yake tafaɗi mai take so.

"Kowanne jinjiri ɗaya daidai yake da company ɗaya da suke ƙarƙashin wannan ginin. Idan har zaka bani companynka guda biyu da suke kaduna AMJAD GOLDEN TOWER da kuma AMJAD VIP PALOUR. To a shirye nake dana zubar dasu,idan kuma ba haka ba to bazan zubar ba,kuma halayya yanzu ma tafara sauyawa daga gareni"

Bayan yagama jin bayanan nata murmushi yayi tareda murza biron dayake hannunsa.

"Go and keep your belly safe,zanyi tanadin tarbarsu a matsayina na ubansu,ƴaƴan ki ba farko ma i think kin gani basu gagareni riƙewa ba,amma soyayyata kaman yanda taki tazare a zuciyata haka suma tasu tazare daga zuciyata. Sannan suma in kin haifesu zan nisanta ki dasu kaman yanda na nisantaki dasu Farhan. Abinda kika buƙata bazai samuba"

Kallonsa take da mamaki ganin ko ja in ja basuyi ba har yafasa yin deal ɗin. Bayan waɗannan companyn bakomai ne a wajensa ba don ya rabu dasu. Karon farko da fito da ƙudurinta fili amma batayi nasara ba,to daga ina mistake ɗin yake?.




Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 8_⚫




"Ke wacce irin marar tunani ce,tsawon lokaci ina aikina zaki wargazamin shi a wautarki nan. Tun wuri ma kije ki gyara abinda kikayi,idan har kika saka yafara binciken wani abu anan kaduna saboda ambatar sunan dakikayi to sai ranki ya baci. Babu ruwana daya yake a wajenki kinsan halina sarai"

Shuru tayi tanajin mai faɗan daga ɗaya bangaren,saida ta gama batareda tace komai ba ta zauna a kan kujerar.

Haɗa ido sukayi da zeezah dukkan su fuskokinsu ɗauke da tashin hankali. Da alama ba ƙaramin tsoron matar suke ba.

"To amma ke surry meyasa kika ambaci sunan kaduna,sanin kanki ne idan aka samu matsala ba iya ke kaɗai ba hatta ni kashinmu ya bushe a wajen Anty Mommy"

"Ya takeso nayi ne to zeezah,shikenan ni banida wani zabi na kaina,saidai abinda tace kuma takeso,a dalilinta na zama haka,a dalilinta nakeyin komai,amma duk a hakan ma bai mata ba?"

Cikeda baƙinciki da shiga damuwa Surayyah take maganar,da alama abune daya daɗe kuma yake damunta a cikin zuciyarta.

"Hakane kam amma kinsan babu yanda zakiyi,dole kiyi abinda tace idan ba so kike tazo garinnan ba,idan tazo kinsan kan me uwa da wabi kowama cutar dashi zatayi,kuma a yanda nake ganin tsagwaron son Ahmad a idonki bazaki so hakan ba"

"Tagumi Surayyah tayi inda ta tsurawa bangon ɗakin zeezar kallo"

"To yanzu dai kinyi wannan kuskuren,ya kike tunanin idan tagano kuma cikine dake a yanzu?"

"No bazama tasani ba,nasan idan tasani ma ba lallai yashiga mata kai ba,tunda bashine target ɗin ta ba tun farko,amma bakasanin mai zata aiwatar tsabb sai tayi amfani dashi ta wata hanyar,kaman yanda tasoyi akan su farhana"

"Hmmm ni wlh duk tsiyata ina tsoron shiga gonar matar nan,gani nake kaman tafi shaiɗan ma iya tsiya"

Zeezah tafaɗa tana cigaba da zuqar sheesharta.

"Shin mai yasa ma na haɗu da ita,duk duniya meyasa saini,meyasa zan dunga karbar hukuncin dabani nayi laifin ba tun a farko,meyasa bazan tafiyar da rayuwata yanda nakeso ba. Meyasa kullum ina tsoron barazanar ta meyasa meyasa zeezah. Duk nima da nawa laifin amma ko kusa bai wuce ta sanadiyyarta ba"

Kuka ne ya kubcewa Surayyah saida tayi ta ƙoshi kafin tayi shuru,can kuma kaman wacce aka tsikara ta tashi tareda ɗora wani murmushi akan fuskarta.

"Zama waje ɗaya bana mai nema ba ne,rayuwata ce tariga tagama ruguzawa,kowa a yanzu ba iya ahmad ba da baƙin fenti yake kallona kuma zai cigaba da kalla. Abu ɗaya na sani sai kazama ɗan duniya kafin ka samu duniya. Zan sakarwa ƙaddarata ragama tajani yanda takeso. Tunda naga innayi ƙoƙarin kama igiyar ma tsinkewa take. Dole nazama ƙarfe kafin na doki ƙarfe. Idan nace zanshiga rami bina zatayi tayi har mukai ƙarshensa ta iskeni,gwara na fito nima nawa kan ya waye inyaso mu gwabza. Zeezah na tafi saikinji wayata"

Tana gama faɗin hakan ta soka baƙin glass ɗin dayake cikin jakarta a fuskarta,fuskar bosawa tayi ta tsime kafin tabar cikin ɗakin.

Ta kallon tsausayi da kuma mamaki zeezah tabita,tana tausaya mata ta wani fuskar kuma tana burgeta yanda duk farmakin da Aunty Mommy ta aiko mata tana tareshi tashanyeshi kuma ta tashi. Duk da cewa kullum rayuwarta a cikin taka tsantsan take na mutanen da suke kewaye da ita.

A bangaren Ahmad kuwa tunda Surayyah ta tafi yaketa nazarin maganar ta. Abinda yafi tsaya masa a rai shine meyasa duk faɗin Nigeria bata nemi dukiyarsa a ko inaba sai Kaduna meyasa?

Wannan abun ya tsaya masa a rai har ya gaza yin komai.

"Menene alaƙarta da kaduna,a iya sanina batada ƴan uwa a kaduna,dama adamawa tacene zance saboda garin kakannunta ne,amma kaduna why?"

Abun yaƙi barin zuciyarsa dan haka ya ƙira wayar da take gefensa,daga can ɗaya bangaren aka ɗauka.

"Am Sagir dafatan bazan katse maka aikinka ba,zan turo maka wani hoto,inaso dakai da sauran mutane kuyimin ƙwaƙwƙwaran bincike gameda shi,duk wanda kuka samu shima yanada alaƙa da hoton to kuyimin bincike akan sa"

"Okay to shikenan Sir zamuyi iya ƙoƙarinmu,iya ga cikin companonin ko harda cikin gari?"

"Ko ina da ko ina a garin kaduna nakeson binciken yashafa"

Suna gama wayar ya tura masa hoton Surayyah.
"No wonder nayi mamakin sauyawarki,dole da akwai abinda yake faruwa,koma menene da sannu zai fito fili"

Lokaci yaɗan ja har Surayyah tafarawa sauyawa,alamun ciki sun fara bayyana a jikinta,kuma tundaga wannan maganar da sukayi a office wata magana batasake shiga tsakaninsu ba. Illa iyaka zai dawo gida ya kwanta ko ya sauya kaya,wani lokacin zai ganta a falo ta baje abinci,wani lokacin kuma tana kallo ko kuma bata gidan. Tun abin yana damunsa yanzu har ya cireshi har itan a ransa.

Su farhana kuwa ya maida su da kayansu sashen hajiya ummee duk yanda akayi dashi yabarsu wajen mamarsu yaƙi,tun hajiya ummee tanayi masa magana itama harta ƙyaleshi ta zuba masa ido.

Kuɗi sosai take chazarsa da niyyar duk a cikin yake tafiya,shidai kawai ya tura mata aniyarta yana bata ne. Ga walaƙanci da halayya kala kala tana fito fili,tayi fari ta ƙara kyau tana abinda taga dama,wani lokacin sai tayi kwana uku batanan,a jikinsa yabashi akwai abinda take ƙitsawa,amma kawai sai ya saka mata ido tareda bawa wani aiki ta dunga bibiyarta a sirrance.

A zaune yake ta bayan corridor ɗinsa ta palm top a hannunsa kunnensa kuma da airpod,gabaɗaya ya tattara nutsuwarsa da alama wani kasuwanci suke tattaunawa da wasu fararen fata.

Ƙirane yashigo wayarsa,yana ji amma ya share,domin baya buƙatar abinda zai taba masa hirar dayakeyi a lokacin. Sai bayan kaman minti talatin sun gama kafin ya duba wayar. Ƙiran imraan yagani yafi 10 missed call,haka kawai jikinsa yabashi ba lafiya ba.

Da sauri ya maida ƙiran,kaman zata katse ba'a ɗaga ba saikuma ya ɗauka. Nishi yakeyi haɗe da haki,duk wanda yaji sautin yasan yana cikin tashin hankali.
"Yalla.........bai kazo kazo ......akwai matsala .........matarka matarka.........babbbbb ba. Ta ta ta ........."

Daga haka yaji kaman yana wani irin tari da aman jini,saikuma ƙiran ya katse.

Saurin miƙewa yayi yana hello hello amma shuru babu amsa.
Wani layin yasake ƙira,security division na companynsa.

"Hello bawani dogon bayani zan turomaka wata number inaso bi diddiginta a ganomin inda take,sannan maza akai ɗoki wajen,ka faɗawa commisioner na ƴan sanda shima ya tura jami'ansa wajen.

Yana gama isarda saƙon kashe wayar yayi tareda shiga cikin gidan.

Kai tsaye ɗakin Surayyah ya nufa tasaka key alamun bata nan,kuma in bai manta ba rabonsa daya ganta kwana uku kenan,to wai ina take zuwa ne. Anya kuwa bayyi sake dayawa ba kuwa.

Komawa ɗakinsa yayi ya ɗauko spear key na ɗakinta.
Yana sakawa daya murɗa ya buɗe,rabonsa da shigowa ɗakin wata huɗu kenan,ba ƙaramin sauyawa yaga yayi masa ba sosai .

A hankali yake ƙarewa ɗakin kallo har idanunsa ya sauƙa kan abinda hake bedside drawer,zaro ido sai kuma ya runtsesu yana maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji'un........




Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 9_⚫




Hannunsa yana rawa yasaka ya ɗauki kwalbar shishar,yakai rabi a ciki,alama tana sha kenan.

Runtse idonsa yayi tareda maida ita a jiye a inda ya ganta ,idonsa sake kaiwa yayi inda wasu takardu suke. Bayanai ne na companynsa dayake Kaduna.
"Again yafaɗa cikeda mamaki"

"Shin menene alaƙar ta da companyna na kaduna?"
Wayarsa ya ɗauka ya ƙira Mutanensa nacan kadunan.
Yana ɗagawa bayan sun gaisa yafara yimasa bayanin abinda ya samu sakamakon binciken dayayi..

"Sir wato gaskiya abin ya ɗaure mana kai,da alamar tana garinnan,ko satin sama ma wata cctv ta nuna mana shigowarta cikin companyn ka na Golden tower,amma kuma da muka duba bayanai bai nuna mata itaba ko wani abu dangane da ita. Gaskiya abin ya bamu mamaki,sannan ko kidan tv muka kai akan su ɗora mana koda wanda yasanta,har sun karba washagari saiga directorn har durƙusawa yayi akan gwiwoyinsa akan nayi haƙuri bazasu iya ɗorawa ba,kuma ma wai duk wanda zan tambaya bazai iya bani bayani akan hoton ba.

Ni ina ganin akwai abinda ta taka ko kuma akwai wanda yake take mata baya. Indai har abin is serious i think yakamata kazo da kanka zaifi"

Har ya gama bayanan Ahmad bai tanka masa ba,saida yakashe wayar kafin yasaki ajiyar zuciya. Hannu yasaka ya murza a cikin sumarsa wacce take mimmiƙe tasha gyara amma halin rayuwa yasa duk ya birkitata.

A wajen arear jejin Abuja cikin duhuwa aka samo Imraan a yashe tamkar matacce,bayan lokacin da aka ɗauka ana tracking wayar sa. Da motar ambulance dama aka je,suna zuwa maza aka fara bashi agajin gaggawa. Amma shuru baya motsi,ganin haka yasa maza sukayi dashi asibiti emergency.

Shigowar Ahmad da sauri shida Saleem kai tsaye office ɗin likitan dayake kulada shi sukayi,a gigice ya tsaye akan jikinsa har rawa yake.

"Meya faru dashi,har yanzu bai farka ba?"

A gaggauce yayi maganar alamun yana buƙatar ƙarin bayani cikin gaggawa..

Shima likitan a nasa bangaren har hankalin sa ya tashi ganin yanda suka shigo kannasa,amma yasan wanene bashida ikon yin magana.

"Kayi magana mana ya zaka tsaya kana kallonmu mai makon kayi mana bayani mai yake faruwa ya mutu ne kome?"

Duk da Ahmad ya sake tambayarsa a karo na biyu bai musu magana ba,illah tashi da yayi yakuma yimusu alamar su biyo bayansa.

Wani ɗaki ya nufa dasu da alamar na musamman ne,domin babu sawun mutane a wajen.
Suna shiga akan mutumin dayake jikin injin suka haɗa ido .

Tako ina wayoyine a jikinsa,da alama sune masu agaza masa a rayuwarsa.

"Wannan shine halinda marar lafiyanku yake ciki,munyi iya ƙoƙarinmu alhamdulillah Allah yabamu sa'a mun ceto rayuwarsa"

"Mashaallah hakan yayi,amma zuwa yaushene zamu samu magana dashi"

Jimm yayi kafin ya ƙara da cewa.

"Ehh to wannan da kamar wuya nan kusa,domin a halin yanzu ya faɗa doguwar suma da babu wanda yasan ranar da zai farfaɗo,wannan injina da kake gani suns zasuyi ta aiki a matsayin gangar jikinsa har zuwa lokacin da ta Allah zata kasance,am sorry sir wannan shine halinda muke ciki"

"Inna lillahi inaso ka haɗamin file ɗinsa zan fita dashi india ko egypt,wajen ƙwararrun likitoci muga ko za'a dace"

"Gaskiya hakan bazai yiwu ba,ko ɗakinnnan babban hatsarine yabari ballantana kuma wannan ƙasar,yasamu babban rauni makamai a jikinsa masu matuƙar haɗari,jikinsa baya buƙatar a dameshi wajen warkewar raunikan..

Jin bayani na biyun samun waje Ahmad yayi ya zauna, kenan babu abinda zai iya a lamarin saidai kawai ya zubawa sarautar Allah ido kenan.

ya ɗauko mutum daga cikin iyalansa ya bashi aiki,bai taba tunanin abin yanada haɗari haka ba,da bazai ɗaukeshi unserious haka ba. Yanzu wani sabon abin ma bai san taka maimai waye yayi masa wannan ɗanyen aikinba,duk da kashi casa'in da tara na zuciyarsa yana raya masa Surayyah ce tayi masa,to amma bashida hujjar kamata,tunda shi wanda akayiwa yana kwance bashida ikon tashi balle ya faɗi abinda yake faruwa. Shifa yanzu ankai wani mataki da yafara tsoron lamarin wannan matar tasa kwata kwata.

"Hmmm saleem tashi mu tafi mujira kaman yanda sukace ɗin"

Babu musu daya tashi daga kujerar ya nufi ƙofa shima yabi bayansa.

A motane ganin sunyi shuru babu mai cewa komai Saleem ya katse shirun ta hanyar jefawa Ahmad tambaya.

"Wai Amjad wanne aiki ka saka Imraan ne haka da har wannan abun ya faru"

Shuru Ahmad yayi kamar bai jishi ba,sai can kuma ya buɗi baki yayi masa magana.

"Nasaka shine ya dunga bimin sawun Surayyah akan mai takeyi,ina taje dawa take tare,ta kamashi yana bibiyarta i think shine tayi masa wannan aikin. Na faɗamuku wannan matar is become a dangerous person amma kun ɗauka wasane ko?"

Sakin baki Saleem yayi yana kallon Ahmad wanda yake masa bayanin.

"Ahmad kasan mai kake faɗa kuwa,taya Surayyah zatayiwa imraan wannan aikin,to ko ƴar fashi da makami ce tana mace taya zata iya yiwa imraan ƙwararren security wannan raunin. Gaskiya idan mafarki kake dai ka farka,sannan shawara zan baka karka sake faɗin maganar nan wani yaji,hakan zai iya jawo babbar magana."

"You see dama nasan haka zakace saleem amma shikenan with time komai zai bayyana,nasan duk abinda zan faɗa babu wanda zai yarda dani a yanzu,amma tunda ɗan macijine dole zai nuna asalinsa"

"Mai kake nufi,Surayyah ce ƴar maciji,amma dai baka daga cikin wanda zan faɗawa nagartar iyayen ta da kuma martabar asalinta koh?"

Ganin maganar tasu zata kaisu inda basa ƙauna yasa sukayi shuru,domin da alama yafiye musu akan hirar da sukeyi.

Sashen Hajiya mamee ya wuce bayan ya dawo gidan,duk maganar da tayi masa akan yafaɗa mata mai yake faruwa shuru yayi. Iya abinci yasamu turawa a cikinsa kaɗan,daga nan ya miƙe akan 3 seater ta. Su farhana sai damunsa suke da kawo ƙara amma sam ko buɗe ido ya kallesu bayyi ba,abinda bai tabayi ba,kuma ba halayyarsa ba duk su yake aikatawa.

Saida aka ƙira sallahr magriba kafin ya ɗau falmaran ɗinsa ta kayan jikinsa ya nufi masallaci,a nan ma zama yayi ya taba karatun qur'ani ko zaiji sauƙin abinda yake damunsa,har akayi isha kafin ya nufi gida.

Daidai yakama handle ɗin zai buɗe yaji muryar mai kulada fulawoyi yanayi masa magana,mai yake anan har zuwa dare,yayi kansa tambayar a cikin ransa.

"Ranka ya daɗe ranka ya daɗe barka da dare"

"Yawwa barka,mai kakeyi kai kuma anan har zuwa dare"

Jikinsa yana rawa ya ajiye baƙar ledar a gaban Ahmad.

"Ranka ya daɗe niba securety bane amma tunda naga wannan abin hankali na ya tashi. Safar hannu ce da kuma wani mayafi dukkansu sun wanke da jini sharkaf"

Jin wanann bayani da sauri Ahmad ya haska fitilar wayarsa tareda tsugunnawa ya buɗe ledar,safar hannun bai santa ba,amma wannan mayafin babu tantama na Surayyah ne.

Ɗaga kai yayi cikin ƙidima ya tambayi gardner ɗin.
"A ina kasamu wannan abun"

"Wlh yallabai kullum inayin ban ruwa da safe,to sai mai ɗakina ta haihu bansamu zuwa da wuri ba,danaga lafiya lafiya saina ce bari nazo nayi da yamma. To a waccar bishiyar da take cikin duhunnan anan nagansu a ajiye,na tsorita saina kasa zubarwa nace bari na jira in ka iso na sanar dakai kuma na nuna maka"

"Okay amma sanda ka ɗau kayan ina matar gidan tana nan?"

"Ahah lokacin dana shigo banganta ba,har zuwa yanzu ma banganta ba,amma da alamun tana cikin gida tunda ga motarta can"

Jan ajiyar zuciya Ahmad yayi tareda sallamar mai gadin.ko gidan bai shigaba ya fito da key ɗin motarsa ya nufi wani waje da ledar.


Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.


⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫

Available on:wattpad&arewabook



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 10_⚫



Asibitin da aka kwantar da imraan Ahmad ya nufa kai tsaye,wata nurse daya ci karo da ita ya tambaya akan likitan dake kulada case ɗin imraan ɗin.

Abinka da mai hannu da shuni,cikin ƙanƙanin lokaci aka bashi contact ɗin Likitan..

Bayan yayi ƙira biyu ana ukunne yaji muryar mace ta ɗauka.

"Assalaam wayake magana"

"Ki sanar dashi amjad ne idan babu damuwa ina nemansa da gaggawa a asibiti yanzunnan"

"To yashiga wanka bari inya fito zan faɗamasa"

Bayan kashe wayarta da wasu mintuna likitan yasake ƙiransa akan yana hanya.

Safa da marwa Ahmad yake da ledar a hannunsa a bakin office ɗin har likitan ya iso. Tun kafin yayi masa bayani ya miƙa masa ledar tareda ɗorawa da cewa.

"Da sauri inason ka gwada jinin jikin kayannan ko yayi daidai dana imraan"

Karba yayi yana jujjuyawa kafin yace.

"Okay to amma wanann ba nawa aikin bane na lab ne,saidai bari nasaka sister nafeesa tana dutyn dare zatakai su ɗauki sample ɗin"

"Eh nasan bakai ne zakayi ba amma ai imraan patient ɗinka ne,bamai tabashi batareda izninka ba ko wannan babban dalili ya auku,shiyasa na ƙira,am sorry dafatan ban shiga haƙƙinka sosai ba"

"Ahh bakomai bari yanzu zamuyi comparing na samples ɗin inshaallah"

Wajen zama ya bawa Ahmad shikuma yabi bayan Nurse din daya aika,domin yaga ahmad da alama yana sauri da abin kuma babbane,don inda yabashi ya zauna ma ya gagara.

Basu wani daɗe ba sai gasu sun dawo da takarda a hannunsa.

"Ranka ya daɗe hala kun samo wanda ya aikata laifin? A dokance dan dai kaine amma da bai kamata na miƙa maka wannan takardar ba saina ƙira ƴan sanda,saidai saboda nasan kanada enought security ne dasuke aiki wanda yafima na ƴan sandan namu a yanzu,sannan kuma shi kansa wanda yake kwance ɗayane daga cikin mutananka"

"Kaga dr. Enough for this talking,kawai ka fadamin abinda nazo neman sani"

"Uhmmm result ɗin yayi matching 99.9%percent,a taƙaice dai jinin dayake jikin wannan kaya jinin imraan ne"

Wata irin sauyawa fuskar Ahmad tayi nan take,da alama baiso yaji irin wannan sakamakon ba.

"Shin a ƙira ƴan sanda ne tunda an samu culprit ɗin,da alama ma kaman macece tayi kisan,za'a iya samunta ta hanya duba thumb print ɗinta a jikin kayan"

"Bana buƙata dr. A taƙaice ma maganar ta tsaya iya nan banaso najita a bakin kowa,dagani saikai"

Yana gama faɗin hakan ya karbi takardar sakamakon ya nufi gida.

Ikon Allah ne kaɗai yakai Ahmad gida lafiya,a hanya babu abinda bai saƙa a ransa ba har Allah yasa ya isa gida lafiya.

Kai tsaye ɗakin Surayyah ya nufa,bai tsaya kojin mai zataje ba ko tana nan kokuma batanan kawai ya banka cikin ɗakin.

A zaune take akan gado daga ita sai towel,da alama tunda ta fito daga wanka ko kaya bata sakaba tayi zaman ta haka. Cikin jikinta bai wuce wata uku da satikai ba amma har ya fara fitowa,kaman dai yanda yayi mata ana su farhana,dayake shima na ƴan biyunne.

Sheesha ce a hannunta sai zuƙa take kaman mai shirin yin maganin yunwa da ita.

Saurin ƙwace handle ɗin yayi ya jefar dashi gefe.

Wata ɗagowa tayi tana risa ido alamar maye yafara kamata,saida ta rufe idon ta buɗe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login