Showing 3001 words to 6000 words out of 24149 words
zuwa makaranta koyarwa ta islamiyya.
Buɗe ƙofar da tayine yayi daidai da shigowar Farhana tana dariya,wacce Farhan yake binta a baya zai kamata da robot na wasan yara a hannunsa bashida kai.
Duka duka yaran basu wuce shekara uku da rabi ba,amma kasancewar kuɗi ya zauna da kuma kula,zaka iya cewa sunyi shekara biyar. Duk da cewa twin ne amma basa kama sosai saidai na jini,domin Farhan yafi kama da Ahmad,yayinda ita kuma Farhana take kama da mahaifiyar tasu Surayyah.
Saurin riƙeta tayi ta hanata shigewa ta gefenta zuwa cikin ɗakin,dariyar da takeyi ta haɗiye tana kallon mahaifiyar tasu wanda itama ita take kallo.
"Zo nan menene ya haɗaku mai kika masa?"
Tsuke baki tayi tareda yin inda inda kaman mai in'ina,hakanne yabawa Farhan damar faɗin abinda tayi masa.
"Ba itane ba ta cire min kan spider man ɗina,kuma ni ban cire mata kan barbie ɗinta ba,wlh sai na rama nima bazan yadda ba"
Ƙarisa maganar yayi yana kaiwa Farhana duka,wanda Surayyah tayi saurin hanashi.
"Ohhh waiku kullum kuna cikin faɗane kam,babu dama idan mutum yana tareda ku ya huta? Ina Nini ɗin taku tayi,data barku kuke ta yawo a gida kuna damun mutane?"
"Uhm ta tafi part ɗin su Maman sultan(Hajiya Hunaiza) kaiwa kayan Sultan na makaranta"
"Okay naji maza ku kama hanya ku bar wajennan,kuje wajen daddynku yana sashensa ku tayashi fira. Idan kuka sake dawomin nan kuna faɗa sai nayi punishing ɗinku,kunjini?"
Yanda ta ɗaga murya tana magana ne yasa Farhana tabe ɗan bakinta zatayi kuka,dan dama ita sakaliya ce duk da tanada tsokana.
Furzar da iska tayi daga bakinta alamar tana cikin damuwa tareda rusunawa ta kama kafaɗunta.
"Ohhh common my lily miye kuma na kukan ehh,kawai nace kuje wajen daddy yana ƙiranku kafin ninin ku ta dawo kinji,jiya ya siyo muku chacolate,ko bazaki sha ba?"
sakin fuskar tayi da sauri tareda ɗaga kai alamar zata sha.
"Yawwa kuje maza ku karba"
Hakan da tayi yayi tasiri don da sauri suka juya zuwa sashen mahaifinnasu wanda yake kallon nata babban falone ya raba.
Bayan sun bar wajen juya ido tayi tareda yin magana wanda ita kaɗai tasan mai ta faɗa sai kuma mahaliccinta.
Duk abinda suke Ahmad yana kallonsu daga back yard ɗinsa,da cup na tea a hannunsa wanda yake kurba a hankali. Ganin tahowar yaran zuwa sashensa yasa ya girgiza kai tareda yin murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo.
"Hmmm i don't know what the hell is happen,amma tabbas da abinda yake faruwa"
Wayarsa ce tayi ƙara wanda hakan yasashi saurin ɗagawa,da alama dama ƙiran yake jira.
"Hello Saleem ina jinka mai kake cewa ne"
Ɗaga ɗaya bangaren mai wayar yasake maimaitawa.
"Ahmad Ni inaga ka daina wannan zargin akan matarka bashida kyau ko kaɗan,duk wani bincike danayi da kuma gwaje gwajen dakasaka ayi dukka abu ɗaya yake nunawa.
Kwananann ni bansan mai yake damunka ba,idan ancemin wani zargi matarsa irin wanda kakeyi a yanzu to bazan taba kawowa kaine ba Ahmad,duk wanda ya sanka koda na mintuna ne to yasan yanda kakeson matarka kake mutunta ta kuma kake yabonta,amma for god sake wai kaine kake zarginta a yanzu?,kan abinda bakada masaniya akai,kawai wai haka zuciyarka ta baka. Yaushe zuciyarka tayi tasiri akan ka da har take son rabaka da wacce a baya ita ta nuna tana so. Yakamata kabar wannan abun tun ni dakai kaɗai muka sani,kada ka manta ko badan komai ba saboda ƴaƴanku da yanzu suke tasowa,sannan kafi kowa sanin gidansu ita da kuma inda ta fito,iyayenta ba ƙananan mutane ne ba,kaman yanda kakeda ƙarfin iko kasam itama tanada shi,bazasu yarda da wannan abin daka tsiro kake shirin ɗorawa ƴar su ba. Sannan kuma........"
"Enough Saleem enough enough please,don Allah ka dakata haka ya isheka haka"
Saurin kashe wayar yayi tareda zama akan kujerar da take gefensa,domin ji yayi gabaɗaya ƙafafunsa sun gagara ɗaukarsa. Zare glass ɗin idonsa yayi ya ajiyeshi akan tebur ɗin kana ya ɗora hannunsa akan goshinsa.
"Wayyo Allah na mai yake damuna ne haka,na kasa ƙaryata zuciyata saboda nasan tanada gaskiya,yayinda kuma na kasa yarda da ita saboda duk duniya idan da mai shaidar Surayyah kan bahaka bane to nine. Meyasa haka meyasa,miyasa meyasa sai ni"
Sambatu ya cigaba dayi tun yana yi a hankali har ya zamto yanayi da ƙarfi kaman mai magana da wani,cin ƙarfinsa abin yayi wanda hakan har yasaka shi zufar da ƙwallah. Ƙarar bugun ƙofar wajen dayake ne ya dawo dashi cikim hayyacinsa,saurin goge fuskarsa yayi tareda nufar ƙofar,yasan su Farhana ne,sai a lokacin ma ya tuna ashe ya ga lokacinda Surayyah ta turosu izuwa sashennasa.
Farhana ce ta fara shigowa,idonta ya sauƙe akan nasa.
"Abba mai yasamu idonka naga yayi ja?"
Dariya yayi tareda girgiza kai,halinta iri ɗaya dana surayyansa a baya,babu inda ta barta wajen kula da abinda yake tareda ita komai ƙanƙantarsa,banda yanzu da gabaɗaya ta sauya masa. Shauƙin so da kuma ƙiyayyane suka bayyana cikin zuciyarsa a lokaci guda,saurin kawar dasu yayi dukka,dayaga suna barazanar zautar dashi,bai taba ganin wanda emotion biyu mabanbanta ke ziyartarsa kaman shi ɗin ba a halin yanzu.
"Ahah sweety ƙwaro ne ya faɗamin a ido yanxu,mai kika yiwa bro ɗinki naji yana kuka da safennan,uhm uwar surutu"
Ya faɗa yana lakace mata kumatu.
Kamar dama jira take tashiga tsaramasa abinda ya faru,shikuwa Farhan tunda yakama ƙofar shigowa wajen bayan an buɗe musu bai ƙariso ba bai kuma koma ba.
Hannu Ahmad ya miƙa masa akan yazo.
"Sorry my boy ka daina fushin mana haka,zan siyo maka wani spider man ɗin babba wanda yafi wannan kaji,zo ka gaisa da daddy koh"
Sai a lokacin ya ƙariso wajen mahaifinnasu tareda sakin fuskarsa.
Rungumesu yayi dukkansu a jikinsa yana jan ajiyar zuciya,kana kallonsu kamar wanda ƴaƴa suka rasa mamarsu shikuma ya rasa matarsa.
"Abba yau kama mammy taƙi bari mu zauna a wajenta ta koremu,jiyama har dukan Farhan tayi daya zubar mata da madara,gashi sai tayi ta zuwa anguwa,kullum in mun dawo a makaranta sai mu samu batanan,ta daina yi mana homework da labarai kaman da. Mukam ka kaimu Wajen ummee bazamu zauna anan ba. Nini ma ta tafi wajen Sultan Har yanzu bata dawo ba,gashi yunwa mukeji"
Runtse idonsa yayi yana sauraron ƙorafin ƴaƴannnasa,ashe bashi kaɗai bane har yara ma sun fahimci hakan,to amma meyasa kowa ya faɗawa sai yaƙi yarda dashi,ƙarshe ma saidai yaga laifinsa?
Jin ƙorafinnasu bazai ƙareba yasa katsesu tareda ɗauke musu hankali da wani abun,duk da yasan gaskiya suke faɗa amma bayason hakan ya zauna a ransu harma yayi tasiri,shi kansa babba abin yana damunsa inaga kuma su yara.
Kitchen yashiga bayan yabarsu a falo domin haɗa musu abinda zasu ci, shi dama ma'abocin sha'awar yin girkine idan yanada lokaci,musamman ma yanzu da bayacin abinci a gidan.
Jallof ɗin taliya yayi musu da sardine,bayan sunci yayi musu wanka suka bar gidan. Don yanzu ko ran weekend ne baya sha'awar zama a gidan, idan yasan itama tana nan.
Safa da marwa tafarayi a cikin ɗakin,ganin tana ta ƙiran wata lamba amma har yanxu ba'a ɗauka ba.
Tsuka taja kaman zata zuqe iskar datake wajen gabaɗaya kana tace.
"Iskancin banza nifah wannan abun ya isheni haka,ace koyaushe daga wannan matsalar sai wannan,shi kaɗai guda ɗaya amma nakasa gamawa da babinsa,ayi mutum da zuciya kamar ta Samudawa sam sam taƙiyin laushi. Ni wlh nagaji da wannan halayyar tasa,Nayi zaton tsantsar soyayyar sa akaina yakeyi ba hali ba,amma na kula bani yakeyiwa soyayyar ba halinne. Kenan koda jinya na kamu dashi haka zai tsallake yayi tasa rayuwar idan yaga ya daina ganin abinda yake so? Lallai maza halinsu da nuna kulawarsu ba abin yarda bane"
Duk maganar tanayinta ne tana kallon kanta a madubi,bata ma san ƙiran da take yashiga ba.
"Hello surry yane kike ta zubamin ƙira kaman na kashe miki miji,"
Mai magana a ɗaya bangaren tafaɗa da muryar duniyanci tana ƙarisawa da wata ƴar iskar dariya.
"Mtsw bazaki gane ba Zeezah maganarki fah gaskiya ce,wannan mutumin bani yakeso ba,wancan halin yakeso,sam ko inda yake yaƙi yarda naje bare wani abun yashiga tsakanina dashi"
"Haaaa ai dama na faɗamiki,maza ai sun gama da mata,yafiso kullum yasamu mace tamkar karya da asurka sai yanda yajata tukunna zatayi,to ke ki koma yanda yakeso ɗin mana"
"What no no i can't do this bullshit kuma,wai a ina kikene nakejin hayaniya,akwai maganar da zamuyi"
"Ohh ni wai ina wani sabon club ne wlh da aka buɗe,bakiga wajen ba ya tsaru ya haɗu matuƙa,gashi nayi gamo da wani zazzafan gaye ohhhhhh rayuwar shaƙatawa fah tayi. Ko zaki fitone kema ki rage ƴar iskar guguwar da guy ɗinnaki ya zuba miki"
"Ni ba wannan ba maganar kawai zamuyi kuma ina so muyi cikin gaggawa,turomin address nazo na sameki,kina nan dai da biye biyen mazan kinnan,kinsan bazan iya wannan zubda class ɗin ba."
"Uhm gashi kuma Amjad ya juya miki baya ba,ina zan iya nayi tabin mutum yana garani,ga wannan saidai suyi ta binka kana ɗaga kai."
"Dan yaga ina sonsa ne shiyasa yakemin yanda yaga dama,amma soon zan ɗinke zuciyata zai kuwa san dawa yake buga wasa, domin son danake masa baikai son danake yiwa dukiyarsa ba. Ina sone na bishi a hankali amma shi baya ganewa"
"Wai harna tausaya masa,Allah sarki Amjad young billioneer bai san da wacce irin macijiya yake tare ba. Na turo miki kizo ina jiranki,wata wine na samu mai cajin kai,nasan zatayi miki daɗi sai kinzo kawai"
Ta ƙarisa maganar tana janta irin na wanda yafara lulawa duniyar gajimare.
Hmmmm omo wlh karku bari nayi labarinnan babu ku,akwai tafasa da tafashe tafashe ina faɗa muku hmmm😀😀😀
Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 4_⚫
Bayan Surayyah ta kashe wayar wardrob ta buɗe tana ƙarewa kayan cikin kallo,daga abayas sai atampopi da manyan gyalulluka da kuma hijabai,wata tsuka tayi tareda ɗora hannu a haka,ko me ta tuna sake ɗaukar wayarta tayi tashi wani malls layin kaya.
Wani arnen riga da wando na kanti Army green da baƙi ta ɗauka,inda ta tura address akan tanason delivery da wuri.
Ajiye wayar tayi tashiga wanka. Abinka da kuɗi da kuma ita kanta duniyar da muke rayuwa a cikinta a yanzu,kafin wani lokaci mai tsawo har saƙonta ya iso.
Already dama ta gama shiryawa,tana karba tacire su a parkage ɗinsu tafara sakawa,dama daaidai size ɗinta ta bayar.
Tayi kyau matuƙa,kasancewar tanada farar fata kayan sun amsheta sosai.
Bayan ta gama kallon kanta yanda suka karbeta baƙar abaya ta ɗakko a cikin wardrop ɗin ta saka tareda yane kanta da mayafin,sai yatsina take kaman an sakata dole.
Fitowa tayi zuwa wajen motarta,tun kafin ta isa wani mutum ya taho da sauri inda take.
"Ranki ya daɗe ina zamuje?"
"Ina zamuje dawa?"
Shuru yayi yana kallonta sai kuma ya sunkuyar da kai,domin baisan wacce irin amsa zai bawa maganar tata ba.
"Wacce irin ƙwaƙwalwace dakaine,shin sau nawa zan cemaka bana buƙatarka idan zan fita wani waje a yanzu,amma kullum sai kazo kasha gabana. Kada ka sake yimin haka in baso kake na koreka ba."
Da mamaki sosai a kan fuskarsa ya ɗaga kai alamar yaji tareda matsawa gefe.
Har taja motar tabar gidan bai daina bin inda tayi da kallo ba,saida ta ƙule kafin ya jijjiga tareda cewa.
"Wai mai yake damun hajiya kwana biyunnan ne,ita da in bananan sai tasaka an nemoni saboda bata fita da kanta,amma wai itace ke cewa zata koreni yanxu? Ohh dama ance baka shedar mutum musamman mai kuɗi,sauyawarsu batada wuya. To Allah shi kyauta"
Tana zuwa bakin wajen parking tayi tareda fitowa daga motar tata kai tsaye cikin wajen tashiga babu alamar shakka a tattare da ita,kamar daman shiga irin wannan wajajen ba baƙo bane a gareta.
Rarraba ido take a cikin wajen wanda dim light mai walwali taketa haskawa,da kuma sautin ƙida da wajen har diri yake.
A can wani table ta hango zeezah itada gayen data fara yimata firarsa a waya.
Tana ƙarisawa tun kafin suyi mata magana tace.
"Kafin komai nunamin inane rest room,inaso na rabu da wannan bargon jikinnawa,"
Ta faɗa tana nuna abayar da take jikinta.
Dariya zeezah ta sheqe da ita ta nuna mata wata hanya da yatsanta tana cewa.
"Hhhhhh wai kinaso kicemin tsoro kikeji har yanxu surry,da har bazaki iya saka abinda ranki yakeso ba sai kinyi badda kama?"
"Ahh no ba wannan ne case ɗin ba,plan ɗina baije ko ina da farawa ba,taya zan rugujeshi tun yanzu,idan hannuna yakai ga kan papers ɗin to komai yazo ƙarshe,anannne saina fanshe duk tsiyar da akayimin"
Tana maganar ne tana bin hanyar data nuna mata,bata fi minti biyar da shiga ba tafito sanye da kayan da suke ƙasan abayar,tayi kyau amma saidai ba kayan daya dace da matar aure bane,kuma a irin Wannan wajen.
"Haba Nabeel ya kakeso nayi maka ne wai,tun jiya nake rarrashinka amma kaƙi ji kaman wani ƙaramin yaro. Kada ka manta fah kwanannan na roƙeshi kan yabaka waɗannan kuɗaɗen,amma wai yanzu kazo kacemin sun ƙare na sake tambaya maka wasu.
Haka fa ka nace kai a UK kakeson yin makaranta,nasakashi ya turaka,ƙarshe koroka sukayi baka gama ka kama sharholiya,kazo ka gama anan daƙyar. Har ila yau na sake sakashi baka matsayi a companynsa amma haka kaci amanarsa dole ya sauƙe ka. Meyasa kake sakani zubda mutunci nane a gunsu,nida babban shirina shine zama suruka a gunsa idan na aura masa Safeenah,amma duk kanason rugujemin komai"
Cikin ƙosawa da halin Nabeel ɗin Hajiya Hunaiza take faɗan,wanda yake zaune ya tsuke fuska.
"Nidama nasan da wata a ƙasa,wato saboda cika muradin Safeenah ne yasa kikemin wannan tonon sililin,banyi zaton ko wani yayimin zaki ƙyaleba ballantana ke kiyimin ummah"
Yana gama maganar a zuciye yabar falon. Tashi hajiya Hunaiza tayi zatabi bayansa amma har yabar sashennata.
"Innalillahi ke ƴar nan na tunzurashi fah,gashi da zuciya yanzu sai yaƙi cin abinci wlh"
"Mtsww aikin banza,wlh umma ke kike ɗaure masa gindi ma shiyasa yakeyi,babba dashi yafah girmi Yah Ahmad ɗin ma,amma kiga abinda yakeyi,kwata kwata yasaka ƙarya da bin mata a ransa. Karki tambayi kuɗin nasan zuwa zayyi ya kashewa wannan budurwar tasa mai Hasken mayu na kanti"
A yatsine cikeda tsiwa Safeenah ta gama maganar,tana tauna cingam hannunta kuma da waya tana game.
"Ke Safeenah banason shashanci,ba yanyanki bane kike binsa da irin waɗannan kalaman, Inaso ki saita kanki ingayamiki da wannan surutun,saboda kar a samu matsala wajen waccar uwartasa,dan na kula gabaɗaya tafison Waccar mai zubin mayun(Surayyah)"
"Hhhhhh wannan da kenan umma,don bakya garinne wannan watan shiyasa bakisan mai yake wakana a estate ɗinnan ba. Kusan kullum yanzu sai yah ahmad yasamu rashin jituwa da Surayyah,dan naji ance har kwana yake a office,itama wai ta sauya sosai"
"Ke dan Allah meya faru haka ? Kodai aikin danayi yayi tasirine Wannan karon"
"Dan Allah umma kin iyo mana aiki? Shine ma yayi tasiri ba komai ba,dan kina tafiya abun ya fara,kai amma wanne malami kika samu mai iya aiki haka wayyo daɗi shine ma. Wannan karon munyi nasara,sai aiki na gaba umma ki karkato dashi kaina,wlh duk wata soyayya danake nuna masa ko kallona bayayi balle yasan mai nakeyi. Umma wlh ina sonsa zuciyata har zafi take innaga yanda yakeson waccar Surayyah wlh"
Ta ƙarisa maganar muryar kuka irinta shagwababbu tana buga ƙafa.
"Kiyi shuru haka dallah,ai tunda kikace aiki yafara ci to matakin nasarar mu kenan,yanzu tauraronmu zai fara haskawa,shegiyar yarinya da duk lokacin danayi mata aiki sai a ce ibadarta ce take tarewa,har na sare da samun nasara,ashe nasara kam tana tafe ohhh ni hunaizatu"
Ta ƙarisa maganar cikin Farinciki.
Suna cikin maganar Sultan yashigo da kayan makarantar sa a jikinsa, na islamiyya an taso su. Ɗan gidan Asiya ne Yayar Safeenah wacce take Aure anan garin Abuja amma wata anguwa daban. medical doctor ce tana aiki a Teaching hospital,Ita kaɗaice a ƴaƴan Hajiya Hunaiza duniya bata dameta ba. Tunda aka yayeshi yake wajen Hajiya Hunaiza kasancewar aiki yayi mata yawa.
Kai tsaye wajen hajiya Hunaiza ya nufah yana tabe baki.
"Ummah nima a wajen Hajiya ummee zan kwana yau"
"Hajiya ummee kuma meyasa?"
"Su farhana ma can zasu kwana,da muka je gidansu Abbansu yace akaisu wajen hajiya ummee su kwana,wai Mommynsu bata nan"
"Mommynsu bata nan ina taje?"
"Uhm ....uhm nima bansani ba haka Abbansu yace"
"To naji kaga jeka maza wajen nini tacire maka kayanka kaci abinci"
"To zanyi ball ma?"
"Ehh jeka in kaci abinci sai kayi kafin magriba tayi"
Da murna ya amsa tareda shigewa wata ƙofa da gudu.
Bayan tafiyarsa Hajiya Hunaiza kallon Safeenah tayi,suka saka dariya a tare.
"Ahhh lallai haƙiƙa nafara yarda da maganarki,yaune karon farko danaji Ahmad yakai su farhana wani waje su kwana a cikin gidannan,duk yadda hajiya ummee tayi daya bata farhana ƙi yayi ..,......ehh lallai tabb"
Amin magana ta wannan layin
09035784150
Sadi-sakhna ce.
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 5_⚫
Yafi awa a tsaye da alama wani abu yake jira,domin lokaci zuwa lokaci yake duba agogon dayake babban falon.
Jin ƙarar tsayawar motane yasashi saurin leƙa windown.
Fitowa tayi daga cikin motar da abayar data fita da ita a jikinta,cikin taku na nutsuwa ta tura handle ɗin falon tashigo. Turuss tayi ganin da wanda ta haɗa ido daga shigowarta. Saurin basarwa tayi tareda sakin ƙaramin murmushi.
"Ohh honey ka dawo kenan"
Tana faɗin hakan bata jira mai zaice ba ta wuce shi zuwa ɗakinta,muryarsa ta tsinkayo ya ƙira sunanta,hakan yasaka ta tsayawa cak tareda juyowa.
"Amm magana kakeyi"
"Ahah ba magana nakeyi ba ihu nake,shin daga ina kike,?yaushe kika fita? sannan da iznin wa har kika kai wannan lokacin a waje?"
"Wannan tambayoyin fah Dear,yaushe ka farayimin kulle da har kakemin waɗannan tambayoyin"
"Ohh ina tambayarki kike tambayata,yaushe kika fara ɗaukar aure a abin wasanki,sannan yaushe rayuwar damuke ciki tafara buɗemiki ido kiyi abinda kikaga dama. A matsayina na mijinki ko bazan hanaki ba i think inada haƙƙin nasan ina kikaje kana kuma yaushe zaki dawo. Na dawo gidannan Tun ƙarfe 4:00 na yamma,mai zan ci? Yara sun dawo daga makaranta mai zasuci mai akayi musu a makaranta mai zasuci mai suke buƙata ? Shin ƙalau suke? Duk waɗannan basu dameki ba daga shigowarki kawai ɗakinki zaki wuce"
"Yara yara yara.......!! Kullum maganarka yara,ni banida nawa ƴan cinne dazansha iska? Sannan da kake maganar haƙƙi yaushe rabonka kai da ka sauƙe naka haƙƙin,ko nikaɗaice mai haƙƙi akai kai? Batun abinci sau nawa kakeson na ajiye maka abincin na kuma roƙeka domin kaci?"
Kallon ta yakeda mamaki ganin yanda take maida masa martanin maganarsa,shin ina bada haƙurin dayazama halinta ko itace da gaskiya ko ba ita ba.
Lumshe idonsa yayi tareda furzar da wata iska ya wuce ɗakinsa kana ya turo ƙofar da sauri.
Saroro Surayyah tayi tana kallon inda yabi da kallo,saikuma ta tsinci dukkan jikinta dayin sanyi,ganin fushin dayayi bata taba ganin yayi kamarsa ba.
"Ke nura wai ina nuran tayi ne"
Hajiya Deedee ta faɗa tana lelleƙawa daga inda take zaune akan kujerar falonnata.
Nimrah ce tafito daga wani corridor tana